Showing 36001 words to 39000 words out of 96510 words

Chapter 13 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

249

zo da Farhan,Shukura cikin Zumudin ganin Ahleef ta damu Umma sai sunyi girkin da yafi wanne dadi,Umma ma biye mata tayi Sabo da Ahleef abin a kyautata masa ne,Girki suka Shirya kala biyu da kayan sha,Shukura ta kara gyaran part din Yasha turaren wuta ko ina kamshi ke tashi na daban,tana yin sallar laasar ta shiga wanka ta tsiri shafe shafen da bata yi ma,cikin mayukanta Masu kamshi Wanda duk cikin kayan Ahleef ne da ya siya mata,tana gama shafawa ta bude kayan da gaba daya Ahleef ya siya mata su,ta zabi wata atamfa Green and black Riga da skert ta sa yar Bra dinta,dinkin das a jikinta ta cika skert din fam kamar a sace ta,Bata iya kwalliya ba sai ta shafa powder da jambaki Red kawai tasa kwallinta,tayi masifar kyau tana bulla kamshi abinta ta fito palo ta zauna tare da daukan littafi tana dubawa irin ba dan kowa tayi kwalliyarta ba wai dama haka take.

Umma ta kalleta kawai tayi murmushi tare da cewa Mashaallah duk Wannan kwalliyar ta Yayan ce ? Murmushi Shukura tayi tare da cewa Umma ai ni badan su nayi ba,Umma Bata ce komai ba tace to yan matanci ne ya motsa ashe ta furta tare da cewa bari na watsa ruwa ta shiga dakinta.
Umma na shiga Su Ahleef suka shugo bakinsu dauke da Sallama,Shukura ta amsa tare da cewa Oyoyo Yaya fuskarta dauke da fara'a,Farhan ma ya shigo yana karewa Shukura kallo ba kyafta ido yanda ta gaji da haduwa abin ba acewa komai,Ahleef kuwa yayi mamakin dama haka take da girma ko ina a cike amma sai yayi kamar bai ganta ba, ita kuma so take taga yana kallonta a nan Zata San lallai tayi kyau idan har Ahleef yana nacewa kallonta,amma ina Sam bai nuna ba ko kallonta baya yi,Farhan ne ya koma kamar yaga Tv, ta gaishesu tare da sanar musu Umma Zata fito yanzu ta shiga wanka,Kitchen ta mike ta shiga,Farhan yabi bayanta da kallo Ahleef yace mene haka kuma ? Sai kace maye a gaban yarinya dan Allah ni bana son haka so ya dinga masifa ba ji ba gani karshe yace a haka kake so na aura maka ita ni bana son ka jawo mana raini kaja mutuncinka aikin banza yau ka fara ganin mace? Farhan yace amma anyi dan iska wannan masifar fa ni da Babyna dan na kalleta sai nayi laifi ? Da ganin yanda kake masifa ma kishi kake ji,Ahleef yace sharrin da zaka min kenan ? Farhan yace nifa malam dalla rufe min baki wlh bazan taba son wannan na aureta ba kazo kana fakewa dani Kaje da abarka sai abu yayi nisa kazo kana Gaba dani kuje ku karata, Baka sonta fa kace,kamar Shukura zaka ce baka sonta a hasale ya furta,bafa nufina bana sonta ba No bada aure ba tafi karfina sai dai kai,Tsaki Ahleef yaja ni bana bukata wlh kaf mata babu wacce zan iya aura.

Murmushi Farhan yayi tare da cewa to Allah kyauta,idan so kake ka aurar da ita to ga Muhseen kasan bazai wuce tayinka ba,Har Ahleef zaiyi magana sai ga Umma ta fito suka gaisa tare da hira,Shima Farhan yasha mamaki Me kama da abokinsa,Baba ya dawo daga Masallaci ya zauna shima suka sha hira,Shukura kuma ta cika musu Gaba da kayan abinci,sannan ta koma gefen Farhan ta zauna kusa da shi,Babane ya mike ya shiga Bedroom Umma ta bi bayansa,Farhan kwakwalwarsa ta tsaya da aiki Sabo da kamar Baba da Ahleef haka Umma ma, Ahleef ne yace kawo min schl Bag dinki na gani,Wai dan karta zauna kusa da Farhan,taje ta kawo sai ya nuna mata gefensa tare da cewa Zauna mu duba books din,Farhan kuwa kallonsu yayi kawai yayi murmushi ya fara cin abinda aka kawo musu,Books dinta ya dinga tambayar abubuwa a ciki yaji duk ta iya, yaji dadi kuma ya jinjina mata, wani Assignment na English ta dakko masa tare da cewa Yah na kasa wannan wlh tun jiya,Sai da ya karba ya gani ba zato taji Saukar biro a kanta ya rankwala mata shi,wajen ta dafe tare da sakin yar kara Muryar Shagwaba tayi Yah da zafi fa,Koya mata yayi har ta iya sannan Shima yaci abinda zai iya sannan Umma ta fito suka mata sallama suka tafi tare da mikawa Shukura wata katuwar leda wai inji Farhan saurayinta kuma Ahleef ne ya siya komai,Farhan yace ka gama gulmarka.

yau Monday yaune kuma Zahra ta fara teaching dinta a makarantar su Shukura, Yau second period ta shiga ajin su Shukura,kamar abin kirki ta gama teaching dinta sai ta bada Test tare da cewa wace Shukura ? Shukura ta daga hannu,Zahra ta girgiza da ganin me kyau haka kamar ba mutum ba,tace a gidan su Ahleef kike ? Shukura tace ae,Murmushi Zahra tayi tare da cewa duk wanda ya gama ya bawa Shukura ta hada ta kawo mata ta fita abinta. Har Office Shukura ta samu Zahra da Test,Zahra ta kalleta da Fara'a tace Shukura kina da kyau,tnx Shukura tace itama tana murmushi,Idan Baza ki damu ba zanso mu zama frnds duk da na girmeki amma ni wlh kawai kina birgeni,Shukura ganin yar gayu irin Zahra kuma me kudi gashi tace tana sonta da kawa gaskiya mutuniyar kirki ce Zahra bata da wulakanci ai dole ma ta zama kawarta,a fili Shukura tace nima ina Sonki ba damuwa,Shukura ta dade suna Hira da Zahra har suka fara sabawa sannan ta koma class,Zahra kuma Shukura na fita ta tabe baki tare da cewa ina samun shiga wajen yayanki zan raba ku kema bazan so me kyau irinki ta rabeshi ba.

Allah sarki Shukura Bata da kawa murna takeyi Allah ya Bata kawa malama guda, Babba kuma yar gayu,Su Latifa Yanzu suna Jin tsoron Shukura tunda ta tsillewa Latifa kai suka rage yi mata abu, kullum yanzu idan anyi Break suna tare da Zahra suna hira Amma Bata yarda ta fada mata sirrinta, Zahra kuwa buri takeyi taga ranar da Ahleef zaizo wajen Shukura kuma taki nunawa tasan wani Ahleef ma,Hafcy kuwa kusan kullum tana gidan su Niima ko Zata ga Ahleef yazo amma Shuru ba labarinsa,Niima tace ta shirya suje har Office dinsa ranar Manday akwai wasu takardu da Momee tace a bawa Ahleef zai mata Posting dinsu zuwa Jordan,sun samu hanyar ganinsa ba tare da ajinsu ya zube ba,Hafcy Murna wajenta kamar zatayi Hauka ranar Monday wankan da bata taba yi ba shi tayi har gidan makeup taje kamar Amarya haka ta fito.

Shukura Sun samu Free period dab da za a tashe su,Zahra ta nemota Office suna hira har aka tashesu Zahra tace tazo ta kaita gida a motarta,Fitowarsu kenan sai ga Ahleef a wata mota sabuwa gal ta gaske fara kal kayansa ma shadda fara komai White ba karamin kyau yayi ba,Zahra ce ta fara Ankara dashi Ji take kamar ta dira tsalle sabo da murna,Shukura sai gani tayi kawai Zahra ta canja tafiya tana lankwashewa,Ahleef bai gane Zahra ba ko kadan Shukura ya dannawa Horn,laaaaa Yayana yazo yau shi zai daukeni Kawata kalleshi can,Wani kishi ne ya tokarewa Zahra a boye ta makawa Shukura Harara a fili kuma ta washe baki suka tafi har motar Ahleef,ta Window ta leka side dinsa tare da cewa ranka ya dade yaya fit ta zagaya da murna ta shige gaban mota sannan ta dagawa Zahra hannu bye Aunty kawas,Zahra tayi dariyar dole ta daga mata hannu tare da cewa Ina yini tana leka Motar kallon Up and down yayi mata da kyar ya iya cewa lfy, sai da tayi magana ma ya gane ta,Wani kallo da ya mata ya dauke kai sai da ta raina kanta jikinta yayi sanyi,yaja mota suka bar schl din direct Office dinsa ya nufa,Yaya Ina zamuje kuma ? Umma kar taga na dade wlh fada ne Da ita sosai idan anyi laifi Shukura ta furta kamar zatayi kuka,kallonta yayi kadan tare da cewa ashe kina da tsoro?ina kika samo kawa? Shukura tace malamar mu ce Aunty Zahra tana so na nima haka baka ga yanda takeso na ba, Hmm ki dai bi a hankali da kawaye musamman irinsu Ahleef ya rasa furta.

Shuru ta masa tana tsoron Umma ita dai, muryarsa ta tsinta yace naje gidan dazu Ai na fada mata sarkin tsoro,Murmushi tayi tare da cewa tsakanin ni da kai wa yafi tsoro kai,Dariya yayi lokacin ya tuno da Aljanun gidansa,katafaren Building dinsa yayi parking ma'aikata sai gaisuwa suke kwasa,Har Shukura ake gaisarwa Oga yazo da kanwarsa,Office dinsa ya bude suna shiga tare da ita sai kallon tsaruwa da haduwa Take sai kamshi tare da sanyi ke tashi, saman wata 2seater lafiyayya ta fada kai tare da kwanciya,Abinci yayi Order a kawo a katafaren wani eatery na manyan Masu kudi,Shukura gajiyar schl tasa Bata surutu Yah Ina toilet ya nuna mata can ciki ta dauki schl bag dinta yace toilet din zaki tafi da wata schl bag kuma,Ajiyewa tayi sannan ta bude ta cikin Hijab ta dauki pad dinta zaraf ta boye ta tafi toilet abinta,Dariya kawai Ahleef yayi kadan dama ya ganeta tun a mota Sabo da shi yana iya gane mata shi yasa yace kar ta shiga da bag Sabo da ganin kwakwaf.

tana shiga taga toilet neat sai ta sa key ta kulle tayi wankanta tas tare da maida kayan jikinta ta shirya Kanta,kafin ta fito kuma su Niima sukayi knocking Sabo da an santa shi yasa aka kyaleta ta wuce Direct wurin Boss,come in Ahleef ya furta cikin daddadar Muryarsa,Hafcy ce a gaba tana baza kamshi sai Niima,yana ganin Hafcy ya kara tsuke fuska,zama sukayi babu wata gaisuwa sai Sannu da aiki suka ce masa bai ko amsa ba yana ta rubuce rubucensa tare da daga waya ko kallonsu bai sake yi ba,Hafcy kuwa sai gyara kirji akeyi ana rangwada,Niima tace takardun Momee na kawo,ba tare da ya dago ba yace ajiye a table,tana daukowa Shukura ta bude toilet tare da fitowa daga ciki sanye da uniform dinta amma kowa ya kalleta yasan tayi wanka yanzu,Kallonsu tayi kawai duk Sun tare sit din zaman sai kawai ta zagaya kusa da Ahleef tana wata shagwaba kamar yarinyar Yah a ina zan zauna ni ? Da murmushi ya kalleta yasa hannu ya jawota ta bayansa sannan ya mike yace zauna a kujerata ki karasa aikin,takardun ya Nuna mata anan zakiyi ta Marking da biro tace na gane,Kallon Niima yayi tare da cewa bata documents din tasan me Zata yi.Shukura kuma kamar gaske sai jujjuyawa take a kujerar tana musu wani kallo tana aikinta da ya nuna mata, kamar hoto haka suka zama, shi kuma ya shige toilet zaiyi Alwala.

Gyaran Murya Shukura tayi tare da cewa keep it On the table cant u hear a simple English,ta kalli Hafcy tare da yin muryar Wanda ba bahaushe ba ko turanshi (turanci) babu? Nace a ajiye min a Table,Niima ranta ya gama jagulewa Ahleef ya yarfa ta a gaban frnd dinta Hafcy ma haka ranta ya konu ashe Niima aikin banza ce a wajensa amma ta Bata lokacinta,Shukura ta karo karfin AC taci Gaba da abinda takeyi ba tare da ta kallesu ba tace pls zaku iya tafiya i have done with u guys,Ahleef yana jinta yana ta dariya a toilet,Chewgum ta bare ta jefa a bakinta sannan ta jawo wardrope tare da ebo kudi 20k ta mikawa Niima take ths i know shi kuka zo nema Ko? Niima ce ta fara Mikewa a fusace Zata mari Shukura Ahleef ya fito tare da buga mata tsawa are u crazy kizo har Office dinta zaki Mareta Who the Hell are u, How Dear u,Niima tace Amma kasan kudin ubanmu ne ba naka ba,da bazar mu kake rawa,da ba a San asalin ka bane sai kace zaka bude mana ido,kai har kana da bakin magana marar asali tsintacce kayiwa iyayenmu asiri ka mallakesu harda kawo mana karuwarka gida ashe anan kuke sheke ayarku, bari su Momee su dawo wlh sai ka bar mana dukiyar mu,Hafcy tace ke Niima iya bakinki wannan yafi karfinki kuma ni a haka nake sonsa shine dalilin kulaki da nayi amma ni nafi karfin kawance dake wlh zaki zageshi shi yace a bashi dukiyar,Shukura ce tace Enough ku bar mana Office, Baraki ma ai iyawa ne wasu basu da darajar da zaiyi dasu, kun bada mata wlh get lost, Hafcy ce ta nuna Shukura da yatsa zamu hadu dake zaki maimaita kalamanki, ae din anji badai ya Sonki kuma bazai so ki ba Shegen kai kamar kwallon goruba, Kwafa Niima tayi Suka fita kuwa ba tare da sunce komai ba, Kujera Ahleef ya fada zuciyarsa tana masa radadi,Shukura ta fahimci hakan sai ta dawo kusa dashi,tana Bashi hakuri duk da Bata san labarinsa ba amma sai taji tausayinsa.

Yaya ta furta a hankali,kallonta yayi yana murmushin karfin hali yace dauko abinci gashi can kici,kafada ta makale ni tare zamu ci, lafiyayyun abincin ta bude tace dole suci tare haka suka ci abincin tare tana masa surutu har ya nemi damuwarsa ya rasa karshe ya karasa aikinsa ya sauketa a gida Bayan ya siya mata abubuwan ci iri iri, tana fita tace Yaya Bye banda tunani pls, I will try my Best inshaallah ya furta yana murmushi.

Hafcy tunawa da tayi da bukatar dan uwanta Mubaraq shi yasa taki yarda suyi fada Da Niima,kwanaki na ja Shukura yanzu ta kara gogewa tare da wayewa kuma hankali takeyi sosai Sabo da kulawar da su Umma ke kokarin yi akanta,ta iya kwalliya tare da girke girke abin ba a cewa komai, Ahleef kullum sai dai ya fake da Farhan yace Shine saurayinta.
Yau Momee da Abba zasu dawo Nigeria,gaba daya Sun tafi Airport Ahleef shine gaba kowa murna yakeyi,Alhmdllh Sun sauka lfy ana ta murna da ganin juna,Tattarawa sukayi aka tafi gida gaba daya,Washe gari Ahleef da kansa ya gabatar Umma, Baba da Shukura wajen Momee da Abba,Momee da fara'a cikin mutuntuwa ta amshesu Abba ma haka dama Momee tasan Shukura sabo da haka hira ta dinga janta dashi,abu daya ne ke damun Momee yanda taga tsantsar kamar Ahleef dasu Umma.

Sati biyu da dawowar su Alhji Baban su Hafcy ya samu Abba a Office kan maganar Auren Ahleef da Hafcy ko Zahra, Abba ya tuno rashin tarbiyar yaran sai yace ba damuwa indai Ahleef yana so shi bashi da Matsala amma bazai masa dole ba, zai tambayeshi yaji.
Yau Maman su Hafcy taje gida wajen Momee suna ta hira kamar abin arziki sai kuma ta fara kawo mata gulmace gulmacen Ahleef tana so taji ya suke da Momee Amma Momee Bata yarda tace komai ba duk kuwa da yawan zuwan da takeyi gidan.

Mubaraq yau shine ya kawo Hafcy wajen Niima,Sai da Hafcy ta gama abinda zatayi sannan ta fito zasu tafi Niima ta rakata har mota,Mubaraq a hankali yake dan janta da Hira Hafcy tana dariyar da ita kadai tasan nufinta tare da cewa Sister ga yayana da alama yana ciki a kular min dashi, Mubaraq dan gayu ne sosai ya iya wanka,Niima taji yana birgeta sosai Bata wani ja masa aji ba ta amshi soyayyar sa hannu biyu sukayi exchange na phone Number,suna Hira Shukura ta fito daga part dinsu Zata shiga wajen Momee tasha wankanta,Mubaraq ya ganta Gaba daya ya rude a ransa yana so ace ta zama matarsa,Niima na gabansa amma hankalinsa na kan Shukura Niima sai ta ji haushi kamar ita ba mace bace tana gabansa yana kallon wata can,da kyar ta danne fushinta har suka tafi,yau kuma Ahleef ya dawo gidan da zama Sabo da Abba ya matsa akan lallaai ya dawo gida..
Kullum yanzu Niina sai ta kai karar Ahleef da Shukura wajen Momee,ta kulla sharri tace Sun mata wani abu, tun Momee bata yarda har ta fara yarda ganin yanda Ahleef yake share Niima,shi ya jawo yanzu ta fara ja baya da Ahleef, Shukura kuwa kiri kiri yanzu Momee take nuna mata rashin Kauna,sabo da Me mutane suna cin arzikinsu suna zaune lfy Sabo da samun waje sai su dinga wulakanta Masu gida ita Baza ta yarda da wannan ba.

Tunda Ahleef ya dawo Shukura ke gyara masa daki,Haka abinci ma sai jefi jefi yake cin na Momee Umma ke dafawa dashi ta bawa Shukura ta kawo watarana har su Momee suna Ci Sabo da Umma karshe ce wajen iya girki,Shi yasa take kara Jin haushi kuma ta gaji to abun bazai yi kyau ba.
Tun safe yau Shukura tana farkawa tayi mika tare da cewa yau mugunta nake ji duk Wanda tsautsayi ya fada masa shi zanyi wa ba ruwana.







AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO






16-20








Official







By
AsmaBaffa








MAMAN FAHAD and HADIZA MUKTAR ga page naku ina Godiya.


MARCYCOOL jinjina me tarin yawa.








Shukura tuni tayi Sallar asuba wanka tayi ta fara kalailatar Shiryawa kamar Zata je party,Umma tana palo tana kallo Ahleef ya shigo da sallama dauke a bakinsa,a'a sannu da zuwa karaso mana ka zauna,murmushi dauke a fuskarsa sai da ya duka har kasa cike da girmamawa ya gaishe da ita kana ya zauna suna hira jefi jefi,jira yake yaga ta ina Shukura Zata fito,sai gata ta fito sanye da Arabian Gown fitted black me duwatsu tayi kyau sosai musamman da tayi acuci tare da tayi Rolling mayafin,ido biyu sukayi da Ahleef ta saki murmushi ya kashe mata ido daya, tana so itama ta kashe nata bata iya ba sai fari tayi farrr da ido, murmushi yayi tare da dauke kansa daga gareta, Umma ce ta kawo masa abin ci da sha,wata yar aiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login