Showing 57001 words to 60000 words out of 96510 words
Chapter 20 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete
shafa Mai ta shirya ta mayar ta tura,ta Kara zura hannu ta jawo a kwati ta sa kayanta ta tura ta mayar, Shukura na gefe can a kwance tana kallonta.
Yafendo ta bude kunu da kosai tace A'a yau kuma rowarce ta motsa aka kawo Dan wannan ba a ciko kwano ba,Baki ta tabe tare da kurba tace hmmm ai da akayi kunu ba irin na yaran yanzu ba,idan Dane wa zai Sha wannan kunu,Kosai ta bude da sauri ta bude Baki ta dafe kirji na shigesu sai kace jariri ne zaici Lallai Gaje ta fara canja hali Amma zata ci ubanta sai na yi maganinta a gidan Nan.
Shukura tana ji tana kunshe dariyarta,haka dai Yafendo ta Sha Kunu,ta Bude Koko taga Koko da yawa tace Allah sarki Indo mutuniyar kirki matsalarta daya ita kuma Koko Babu kauri a tsinka Masa ruwa yanzu mu a zamaninmu ka kaiwa me gida wannan ba sai kayi kwanan gidan ubanka ba ranar,Amma Allah sarki Iro na Yana hakuri,ludayi tasa ta ebo Koko ta sakeshi a kwanon tsiiiiiii tace ashasha kalli harda burbushin tokar Kara a ciki sabo da kazanta duk sai na gyara muku zama.Shukura a ranta tace Yafendo ba a iya mata Allah kyauta.
Shukura tana so ta fita Amma ba dama sabo da Yafendo ta share dakinta ta kwanta tana Jin radio su Gaje kuma suna wajensu suna girki,mazajensu Iro da Yahaya suna kiwo,wani yaro ya shigo da katon buhun mangoro a kansa jajaye nunannu Wanda yanzu aka tsinko su a sama,gaban Yafendo ya ajiye yace gashi inji Yahaya can wajen Kiwo ya bani na kawo miki, Godiya Yafendo tayi tace Kai yaro ka dinga sa takalmi a kafarka gashi Nan kazanta tasa duk ta tsatsatsage ina uwarka take da zata barka Haka,yaro dai yayi waje Yana Jin haushi,tsaki taja sannan ta raba ta bawa su Indo tasu ta ebi wata ta wanke ta zauna tana Sha sauran kuma a buhun ta tura kasan gado.
Dama Shukura yunwa ta fara cinta Yafendo ta fita wanke Mangwaro tayi sauri ta bude buhun ta ebo kusan guda goma,ta fito ta bude randar dakin ta kamfaci ruwa a wata roba me Fadi ta koma kasan gado,dake kusan komai har kayan kwanikan Yafendo suna kasan gado a wanke a shirye,a hankali Shukura take wanke magoronta tana Sha a hankali,idan Yafendo ta fita sai tayi taunarta yanda take so idan ta dawo kuma sai tayi a hankali,Yafendo taso taji kamar motsi a kasan gadon Amma sai tace Kai wannan bera da naci yake ya dameni tun rannan a kasan gado kwana Nan zan kawo Mage gidan Nan kowa ya huta.
Da Rana Shukura Bata samu taci abinci ba sabo da a tsakar gida Yafendo ta fita ci,Sai yamma ta samu ta fito daga gidan Baki daya,gidan Aishalle taje ta dauki toothpaste da brush dinta tayi sannan ta karbi rancen dari biyu wajen Aishalle wai sai Mijinta Ahleef yazo zata biya ta fice abinta da su ta siya danwake da dafaffen kwai guda biyu taci a garin sannan ta tafi can lambu inda ta Saba zuwa hutawa sai dare ta dawo gidan Yafendo,sai da ta shiga kitchen dinsu taci tuwo da Miya sannan ta shige dakin Yafendo kasan gado, sai da su Indo suka zo zasuyi Dumamen tuwo suka ga ba malmala daya,Gaje tace watakil almajirai suka sata kin San yanzu Haka sukeyi,da sunga baka kusa sai su sace ma abinci.
Kullum Shukura haka takeyi har ta kwashe sati biyu a haka Allah bai sa an kamata ba,bashi kuwa yanzu ta karfi take kwatar kudi tace ta ranta sai Mijinta yazo zata biya,haka masu shaguna ma duk taci bashin sabulan wanka da wanki da wasu abubuwa duk tace sai Mijinta yazo,Haka bangaren masu abincin siyarwa,masu tsire da kifi,har chemist taci bashin paracetamol da maganin ciwon ciki,bashin always pad ma haka,kuma ba roka take a Bata bashi ba kawai shiga zatayi ta faki Ido ta kwashi abin ta fice tace kana Bina bashi sai Mijina yazo,idan kayi magana tace zata siyeka ka koma bawanta ko kuma ta siye shagon naka.
Kwana daya tsakani Yafendo da sassafe tace yau Kwalimar karkashin gadon ta zatayi ta gaji da Jin beraye na motsi gwara taga ko mene a ciki,Katuwar sandarta ta dakko da nufin idan taga bera ta buge shi,ta bude gado sukayi Ido biyu da Shukura,Yafendo tayi mugun tsorata tunaninta gamo da aljana tayi ta fito da gudu tana Kiran Iro da Yahaya,suka raho da gudu da saddunansu,tana nuna musu kasan gado suka dage har katifar da komai sai ga Shukura Shar Shar dake tayi wata kiba da kyau sabo da ciye ciye kuma Bata aikin komai sai tunanin Ahleef dake damunta.
Yahaya yace Yafendo ai Shukura ce,zo kuga masifa wajen Yafendo kamar zata ari Baki,zagi kuwa ba Wanda Bata yiwa Shukura ba sannan tace fada min tun yaushe kike a dakin Nan,Shukura ta zauna sosai ta Basu labari kaf kan gidan Megari da dalilin da yasa har take shugowa tana kwana,Iro yaji tausayin Shukura ko ba komai yar uwarsu ce ai Amma duk gari da dangi an ki ta an kyamaceta bayan Bata da kowa sai su,Nan Iro ya roki Yafendo a barta taci gaba da zama a gidan kafin Nan gaba aga me Allah zaiyi, Duk Masifar Yafendo tana tunawa da yar uwarta Inna tace to ta yarda Shukura ta zauna a gidan su dinga kwana tare Amma sai dai ta kwana a kasa kan karamar katifarta dake gefe.
Dadi ya kama Shukura ta dinga zuba Godiya sannan taje ta kwaso kayanta na wajen Aishalle ta dawo dasu gidan Yafendo, ta fara Taya Yafendo sukayi kwalimar tare Yafendo na Masifa ta Bata mata kasan gado da kazanta duk kwallon magoro,ga ludaya duk ansha Koko da fura a zube, duk aikin da Shukura keyi Yafendo cewa take Bata iya ba ita tafi kowa iyawa.
Da dare Tare da Shukura su Indo sukayi girki a gidan na dare,Ana tsakar gida Ana ci sai Yafendo tace sanata Elrufai an bashi zaben Gomna yanzu a kaduna ko? Shukura tace ai ba Senator bane Yafendo dama Gomna ne ya Kara ci,Nan Yafendo ta ce to yar karya wa Zaki gayawa to sanata ne yanzu yaci Gomna, da shine shugaban majalisar dattijai a Abuja,Shukura tace bafa haka bane,Nan Musu yakacame tsakanin Yafendo da Shukura,Duk su Iro suka ce Zancen Shukura ne gaskiya,Yafendo kuma ba a Isa ance an fita sani ba Nan ta fusata tace to ai na Dade da sanin Gwamna ne har za a Gaya min shi Gomna ne,Ganduje na Kano ma ba ya koma ba ta dole bai ci ba aka kwace dole,kasar Nan ba wani me gaskiya duk karya sukeyi sai yanzu nake nadamar guri'a ta Dana sawa Buhari.
Baki Shukura ta tabe tace tab ni kuwa Ina Buhari sabo da shi Mijina yake so,Ahleef shi yake so,Yafendo ta durma mata dundu a baya Dan ubanki Ina kika ga auren?a Ina Mijin yake Nan aka ce ciki kikayi aka dawo dake shine Zaki ishemu dama Kawu yace Alfahari kike tayi da Kwarton ki na birni kina sonsa tir da halinki,Iro yace Haba Yafendo kufa daina Zurfafawa wlh baku sani ba ni Ina gani kamar tana da gaskiya,Yahaya ma yace a dai bi a hankali lokaci Dole zai nuna.
Megari ya Dade Yana fama da ciwon son Shukura har yanzu bai hakura ba sai ya auri Shukura indai Yana Raye liman sai zuga shi yakeyi,yayin da Shukura ta kame kanta yanzu kullum tana gida ko fita Bata yi a garin sabo da ko Ina taci bashi,kuma gashi tana tsarewa Ahleef igiyoyinsa ko ba komai ita da auranta tasan idan Ahleef Yana Nan bazai bari a dinga kalle Masa mata ba shi yasa take tayashi.
Labarin Ahleef kuwa su Yafendo har sun gaji daji a bakin Shukura Kai kaf garin Babu Wanda bai San labarin Ahleef ba Mijin Shukura na bariki,manya da Yara sun sani har dattijai in kaji yanda ake tsara kyawunsa Ana dariya suna ganin Shukura karya take, akwai wani da yazo daga Birni garin yasha dinkin Shadda Shukura tana gani cikin bainar mutane tace irin style din Ahleef na wata farar shaddarsa,tana Nan a cikin kayana nazo da ita,,shike Nan samarin garin suke layin karbar aronta wajen Shukura Ana yi musu irin dinki kusan kowa a garin kana cewa Ayi Maka dinkin Ahleef kowa yasan mene har telolin wasu kauyukan kana ce musu ayi min dinkin Ahleef style to za ayi Maka,yanzu dinkin shi ke tashe a kauyukan, Shukura ita kanta tana mamaki kowa yasan Ahleef a Baki,Ahleef style.
Kuma abinda yasa suka Kara yarda cewa Shukura da gaske take Ahleef ko dai Mijinta ko farkanta ne yanda suka ga tana sa dinkunan maza iri iri har jallabiya tabbas na Namiji ne kuma da gani mutumin me kudi ne shi yasa hankalinsu ya kwanta suna ganin Shukura zata biya su bashin da taci da gaske take.
Shukura zaman hakuri kawai take da Yafendo sabo da fadanta kuma komai baka iya ba Babu abinda zakayi ka birgeta bare ta yaba.
Ahleef kuwa tun bayan tafiyarsa yake fama da son kasancewa da Shukuransa,ya kasa komai sai tunaninta,gashi ko a waya ba ita ba labarinta kuma harda Umma sun kasa fada Masa gaskiya,Idan ya gama wa Momee komai zai dawo sai Momee ta Kara tura shi wata kasar ba tare da ta bari ya tako Nigeria ba,gaba daya ya fita daga tunaninsa ya kasa gane wa Momee,Matarsa yake son kasancewa da ita,yanzu ya tabbatar tsananin son Shukura yake ba kadan ba,Momee kam tuni ta sanarwa Abba cewar Ahleef ya tafi wani aiki kasashe,Amma Matarsa ta zabi tafiya garinsu ta zauna da Yan uwanta kafin ya dawo sabo da ta gudu ta Bata musu rai Dole zata wanke kanta wajensu,Abba yace ahlmdllh yarinyar tayi tunani,Momee tayi Murmushi tare da cewa ai tana da tunani da kaina muka je na kaita sannan akayi musu bayanin aurenta nace Nan gaba ma zakuje dasu Baba shi mahaifin Mijin nata,wlh masu mutunci sun karramamu,Abba dadi ya kamashi yace sai Ahleef ya dawo kasar idan za a dakkota sai mu taru muje gaba daya aga juna ayi abinda ya dace Allah yayi Miki albarka kema,Momee ta waya tace na gode mijina,Abba hankali ya kwanta tunaninsa abinda Momee tace gaskiya ne kuma da sanin Ahleef.
Saudatu da Baba yanzu sunga Momee ta daina musu magana Sam tsakaninta dasu sai Harara da kallon banza,ganin haka suka yanke sanarwa Ahleef zasu bar musu gida,tunda Matar gidan da alama Bata kaunar zamansu yanzu.
AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO
41-45
Official
By
Asmabaffa
Saudatu da Baba da kansu suka sanarwa Ahleef sufa sun gode da taimakonsa Amma zasu bar gida ga abinda Momee ke Musu sannan suka bashi labarin abinda ya faru na tafiyar Shukura,Ran Ahleef idan yayi dubu to ya baci kamar zaiyi hauka,Farhan ya Kira a waya ya bashi Umarnin ya kwashe su Umma da kayansu ya kaisu can Wani sabon gidansa daya siya kwana Nan me shegen kyau ba abinda Babu a gidan na rayuwa. Farhan ba Bata lokaci yaje ya kwashe kayan sawarsu ya Kai can gidan,ya zuba kayan abinci da komai sannan ya kawo masu aiki mata su biyar da maza sabo da su Umma suji dadin rayuwa a gidan girki kawai Umma zatayi ba abinda zatayi.
Sun Sha mamaki da murna suna sawa dansu albarka Babu adadi,Momee kuwa tunda taga Farhan ne ya dauke su tasan Umarnin Ahleef ne tace Umma ta gaida aisha Haka kawai tsofaffi sunzo sun rikita min gida baku San wahalar yaro ba kuce zaku Sha dadinsa.
Mubaraq yayan su Hafcy ya nacewa Niima har sai da ta fara kulashi ta karfi,tun Bata damu dashi ba har ta fara sonsa,Mama tafi kowa Murna zasu ci kudin su Momee tace saura ku Hafcy ko ke ko Zahra ku dage Ahleef ya auri daya ko zamu samu kudin da yawa sabo da shine me kudin, ko mata dari yayiwa ciki suka haife Babu ruwanmu ku aureshi kudi muke nema ba wani tarbiya ba.
Hafcy tace nima Dana yi tunani Haka na gani kawai ayi asan abin yi, tunda mun sallami shegiyar matar tasa.
Ahleef ne ya Kira Momee yace ya gama komai da Company din nasu dake kasar Japan gida zai dawo gobe, Momee cikin fada tace idan baka son aikin Nan Dana ke saka Ahleef ka fada min,gaba daya ka damu ka dawo Nigeria uban me zakayi a kasar ga aiki a Nan kaca kaca,Dan kaga bani da manyan Yara irinka shine kake min Haka, Allah sarki Ahleef baya son yaga Momee tayi fushi dashi ko ace shi ya Bata mata Rai sai kawai ya rude ya shiga Bata hakuri Yana lallaba ta sabo da halaccin rikeshi ta raineshi fiye da yaranta data haifa, Afwan Momeena what Next kuma? Wasu Kaya zaka je north Korea ka turo minsu zan bude shagon butique, da mamaki yace Momee sai na kwashe more than 2mnth a garin kin sani kuma yanzu akwai nauyi da hakkin Shukura a kaina, Salati Momee ta saki yanzu Shukura ta fini?akanta kake so dama ka dawo?
Momee Bata San Umma ta sanarwa Ahleef komai ba sai tace yarinyar kana tafiya ta tattara kayanta ta shiga duniya ba a San inda take ba,ai Abba yace kin fada Masa kin maidata kauyensu kafin na dawo,Momee tace Kai da kanta ta gudu kawai fada Masa nayi Dan hankalinsa ya kwanta,Kai wai me zaka yi da wannan yarinyar ne?Ahleef tuni ya gane Momee Bata da gaskiya ransa yayi Mummu Nan baci daba Dan kar tace ya hada ta fada da Abba ba da sai ya sanarwa Abba komai,a fili yace Momee wlh I do really love my wife,Dan Allah na dawo ko 2wks nayi sai na koma nayi Miki aikin? Momee tace Sam baka Isa ba ta datse Kiran ma Baki daya.
Baba da Umma dai suna can hankalinsu kwance Farhan ke musu komai da Umarnin Ahleef.
Shukura yau ta kwashe wata daya kenan a kauyensu kullum cikin sa Rai take zata ga Ahleef yazo Amma Shuru ,Nan kuma Megari ya samu Dangin Shukura ciki harda Kawu da Yafendo zai auri Shukura karya take Bata da wani Miji a birni,Kawu haushi ya kamashi ganinsa idan Shukura ta auri Megari taci gaba kaf garin ta ciri tuta,shi ga yarsa zata auri talaka Amma Shukura me gari Guda me fada aji me mulki, sai yace Kai Megari da girmanka da hankalinka zaka auri Karuwa? Megari yace ko a gidan Karuwai take na ganta zan aure ta Haka,Yafendo kuwa Murna takeyi ai Shukura ta ci gaba Megari Guda, Kawu yace to ya zakayi da yaron cikinta?Megari yace karya ce ba wani ciki,tana da ciki zaka ganta haka?kawai maganar mutam kauyece, Yafendo tace Bata da wani ciki Shukura fa shirmenta kawai takeyi sabo da kuruciya ko rannan tayi alada.
Megari ya washe hakoransa na cin goro.
Bayan sati biyu tuni dangi sun Gama komai za a daurawa Shukura aure da megari, zance ya baza gari,ance kar a fada mata sai an daura ta ji daga baya, Ana saura kwana Uku a daura aure Shukura taje gidan Aishalle,Aishalle tace ke kuma da kike auren me kyau a birni ya naji za a daura Miki aure da Megari,Shukura tace aure kuma? Ban gane ba kefa kin cika hauka,Dariya Aishalle tayi tace to wlh boye Miki akeyi kaf garin da Yan uwanki sun sani Amma ance kar a fada miki yau saura kwana Uku ki zama Amaryar me gari,gashi can Talliya Matarsa tayi yaji ta bar gidan ma,idan Baki yarda ki tambaya kiji,Yafendo tasan komai,har an Kai kudin aure wajen Kawu,idan kin San kina da auren wani wlh ki San abinyi tun wuri.
Ai Shukura ko Gama ji batayi ba ta fito sai gida wajen Yafendo ta fado da gudu tana Hawaye tace Yafendo me nake ji wai za ayi min aure da Megari? Yafendo tace yo tsayawa zamuyi mu kalleki ko me,kinzo sai karya kike Mijinki zaizo Yana Ina?Baki da sheda,Wanda suka kawoki sunce karuwanci kike Zaki likawa wani Dan ya aureki Kinga sun tabbatar Mana Baki da aure kuma aure kamar anyi.
Ga Dubu goma Megari ya kawo sune kudin lefenki, da Sauri Shukura ta karbi Kudin lefen dubu goma,har Yafendo tana dariya tunaninta ta yarda da auren,Sai taga Shukura ta tattara kayanta a akwatuna tas ta fito ta kalli Yafendo tace wannan dubu goman ki fadawa Megari na ranceta zanzo tare da Mijina na biyashi kudin Lefensa,da sadaki ya kawo bazan ranta ba Amma tunda kudin Lefe ne na ranta na bar muku garinku wlh Akan na auri Megari gwara na koma ga Allah banyi aure ba.
Tasa Kai ta fice sanye da hijab tana Jan akwatunanta tana tunanin Ina zata je inda Ahleef zai San tana nan.
Tana cikin tafiya sai ga Megari a saman wani tsurar machine dinsa da ciyawar tumaki a bayansa ya dawo daga gona,kallo daya ya gane barin gari zatayi,ai da sauri yaci uban birki ya dirgo daga Machine ya rike hannun Shukura Kam,tunawa da tayi tana da aure wani bakin ciki ya kamata ta dage iya karfinta ta warware Megari da Mari,idonta cike da kwalla tace Ina da igiyar wani a kaina baku da hankali ko jahilci na damunku.
Megari yaja baya dafe da kumatu Yana mamaki,tace kaja mutuncinka Ina ganin mutuncinka,ta ja kayanta taci gaba da tafiya abinta ta bar Megari da jimami duk girmansa da mutuncinsa ga mulki babu Wanda ya taba ko Masa magana marar dadi Amma wannan so