Showing 42001 words to 45000 words out of 96510 words

Chapter 15 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

241

kirki ce kuma me hankali,

Momee ce ta matsawa Abba lallai yayiwa Ahleef aure ba tare da ya zabo mace da kansa ba, Abba ganin Momee tafi son Ahleef akan kowa yace to yanzu wa kika zaba masa Zahra ko Hafcy ? Momee tace gwara Hafcy itace babba kuma tana da hankali tunda kusan kullum sai tazo gaishe da ni kuma ta tabbata Ahleef bazai tsallake zabinsu ba, Abba yace Kece baki San yaran ba amma ni na Sansu basu da tarbiya ko kadan, Momee tace tunda kace haka to a kyale su ga Islam kawar Latifa,Hmm wannan yarinyar nasan Mahaifinta Sam basu da hankali suma ga asiri da bin malamai,Momee tace to ni dai bazai auri wata Shukura ba kawai ni zan zabo Masa cikin dangina,Abba yace ki dinga tunani Wlh Sabo da abinda zaije yazo,kinyi abin alheri kin rike yaro da Amana amma kina so ki rushe ladanki,gashi kin jawo har Su Saudatun Sun bar gidan,zansa Securities su gano min inda ya maida su su dawo gidan mu zauna tare amma ni Shukura Baza ta dawo ba tunda Bata neman zaman lfy kuma Baza ta auri yarona ba,kai Abba ya girgiza kawai,Yanzu ma yau ta dukar min latifa ta yaga mata uniform,Abba yace tayi dai dai sanda ita Latifan tayi mata ai sharewa kikayi ko ita Bata da daraja ? Ko ba mutum bace ? Da ai na kowa ne kuma bar ganin kamar Bata da gata itama da baiwar da Allah yayi mata,Maganar aure ni ban yarda da zabinki ba ki zabo wata indai basu da halin banza zan daura Auren yanda kike so,Momee tace ga yar kawata Hajiya Binta kasan tana da budurwa mate din Niima,ae to dama dama su amma itama yar Tata ai ba wata ta kirki bace,kullum yarinya gantali itace yawo kasa kasa amma tunda kina so zamuje ayi tambaya asa ranar biki duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki,Momee tace na yarda hakan,Sunan yarinyar Nafeesa sai ka sanarwa Ahleef Umarni ne ba shawara ba Nima idan yazo zan fada masa da kaina.

murmushin takaici Abba yayi kawai ya fita,Momee kuma ta sa Securities su gano mata inda Shukura dasu Umma Suke zama,su dawo dasu Saudatu gidanta amma Shukura su saceta su kaita wata State din kawai su barta a can yanda kafin ta dawo ko Ahleef ya ganta an daura aure shike nan dole su hakura da juna.

Bell aka buga ta tashin yan schl,Shukura ta fito kenan taga Niima ta fito daga mota Zata je staffroom da Sauri Shukura ta tafi da gudu ta yiwa Niima wata wawar bangaza sai da takalminta me tsini ya Gurde ta, ta fadi kasa kashin Niima ya goce ihu ta fasa kafin kace me Shukura tace na rama nima ta fice daga schl din da gudu,tana fita Securities da Momee tasa suka damke Shukura tare da dannata a mota ta karfi tana kuka da zullo,Ahleef ya zo shima a motarsa tun daga nesa ya hango yanda aka kakaba Shukura a mota ta karfi amma kamar Masu aiki guards din Momee,kafin ya gama tunaninsa motar ta bacewa ganinsa tuni,yabi bayansu amma ina bai kamasu ba tuni Sun bace,kamar zaiyi hauka haka yaje schl aka tabbatar yanzu ta make Niima ta fita da gudu,Latifa tana kuka ta kama masifa wannan tsinanniyar kake nema kalli yanda tayiwa Auntyna,Ahleef bai san sanda ya kwadawa Latifa mari ba tare da cewa ni sa'anki ne ko Shukura saarki ce da zaki zageta,tsaki yaja ya bar schl din zuwa wajen Momee Direct.

Yana shiga ya iske Baba da Umma har an dawo dasu part dinsu na da, Yasan ma Momee ce itace tasa aka sace Shukura kenan.

Shukura kuma tana mota Suna zuga uban gudu da ita,ta kalli Wanda ke kusa da ita tace nasan hanya ai idan birnin sin zaku kaini zan dawo ne, Kai Driver karo karfin ac nan Sabo da naji dadin kallon garuruwa a hanya,Daya a cikinsu ya mika mata Maltina gashi ance kar mu barki da yunwa,karba tayi tare da cewa lallai tafiyar nan zatayi dadi musamman ma idan kun siyo min tsire ina ci,a hanya suka tsaya aka siya mata su tsire da sauransu,tana washe baki tace yawwa, Driver yace amma Yarinya kina da kwadayi wlh, kyaleni naci kunga ko da na mutu sai a kaini kabari da Nauyina ba a kanjame ba, naje lahira bulbul dani,dariya sukayi Gaba daya.

wai ku wannan dalilin ne ya sa zaku saceni ? Me nayi ? Ina zaku kaini ? Ni wlh Ahleef dina Nake son gani,dan Allah ku kaini muyi Sallama,yanzu hankalinsa zai tashi,ga Umma da Baba kuma na bar wayata a gida sai ta fashe da kuka har ta basu tausayi ma,suka kara Siya mata kayan dadi amma Sabo da ba kwanciyar hankali kasa ci tayi duk zalamarta tunanin Ahleef kawai takeyi har bacci ya kwasheta.










AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







21-25







Official







By
AsmaBaffa






JIN DADI SABO FANS ga page naku again ina godiya.









Basu tsaya da Shukura ko ina ba sai wani kauye can Cikin Igbo Land dake Anambra state,tana Bacci dan rashin tausayi suka shafa mata wata powder Wanda ko ta tashi Baza ta iya tuna daga ina take ba sai bayan 1mnth ko wks lokacin kuma tuni anyi Auren Ahleef shike nan ko ta dawo a banza,su kansu sunji tausayin Shukura,daya cikinsu yace gaskiya ban yarda da garin nan ba rashin imanin yayi yawa is better mu kaita kasar Hausawa tunda idan ta tashi Baza ta iya tuna komai ba, wasu ciki sukace a kyaleta kawai haka sukayi tafiyarsu zuciyoyinsu cike da ta tausayin Shukura dake kwance gefen titi,kasar arna ba me taimako Ko kulata basuyi ba kowa harkar gabansa yakeyi,har dare yayi sai da 9pm tayi sannan ta farka,ta kasa tuna Komai,yunwa ke cinta kawai sai ta fashe da kuka ta rasa daga ina take ina take yanzu.

Kusan Ko yaushe yankin can kudu ruwan sama ake musu,yanzu ma ruwane ya tsuge baka ganin komai sai yan gidajensu tsalli tsalli kowa yana gidansa,zagaye suke da gonakinsu duk ko ina abin tsoro,ruwa ke dukanta sosai gwanin tausayi,kuruciyar Shukura sai ta zauna wai wanka takeyi a ciki kowa sai yayi tunanin Hauka ce ta mata sabon kamu,sai da ta gaji ta nufi wani gida kusa da ita taje ta dinga rafka sallama,wani murjejen kato ne wani dunkulelen gardi ya fito dauke da kafceciyar addarsa kugunsa daure da wani bante ba Riga, yaren igbo yayi mata cewar lfy ? Daga ina take tayi saurin bashi amsa kafin ya yanke mata kunne daya, Shukura kuma ba ajin yaren sai turanci shi kuma a kauye yake bai iya turanci ba,zancen kurame tayi masa ya bata wajen kwanciya da kyar ya gane,sai ga wata narkekiyar dattujuwa da daure kirji ta fito tare da tambaya lfy, Mijin nata ya bata labari,tace to kwana daya tal Zata yi ta bar musu gida,da zancen kurame suka fada mata,ta bisu cikin akurkin dakinsu matar ta bata zani da wata t-shirt ta canja kaya,na jikinta kuma ta shanya su,Sannan ta dan dunkule gefen wata tabarmar kaba,ta kwanta,mutanen Sun San ba bacci takeyi ba kiri kiri suka kama baje harka Shukura sai Nishi take ji da gwalangwalan dinsu,ita Bata gane me sukeyi ba.

Haka Shukura Ta kwana da yunwa,da sassafe matar tace to gari ya waye ta bar musu gida Idan ta Gama,Alwala da sallah shukura tayi tare da adduoi sannan ta duba taga matar ta fita kawai ta bude wata tukunya da taga matar tayi girki, ta samu egusi soup da sakwara taci ta koshi Ta gama kenan sai ga matar ta shigo ta tarfa Shukura tana cinye musu abinci,da gudu ta fita sai gata Sun dawo da mijinta tare da wasu narka narkan Maza kowanne dauke da Adda,Suna cewa Sun kama barawo dodo zasu kaiwa jininta,da gudu Shukura ta fita tare da banke na kofar tayi Gaba da matsiyacin gudu,su kuma suka rufa mata Baya da addarsu Allah yasa ta maida kayanta jikinta,har bakin titi suka rakata amma Sun kasa kamata sai hakura sukayi dole.

Ahleef bedroom din Momee ya shiga tare da sallama Gaba daya a firgice yake,Murmushi Momee tayi tare da cewa Son lfy na ganka haka ? Cike da girmamawa ya samu waje ya zauna sannan cikin tausasa kalamai Momee ina Shukura ? Momee nasan ke kika sa akayi kidnapping nata,pls Momee Idan bakyaso na kulata wlh na hakura ki dawo da ita kar rayuwarta ta cutu tana ya mace yarinya kamar wannan, nasan Halayenki Momee uwace ke ta gari wacce tasan darajar dan Adam,Murmushi Momee tayi Bata boye masa ba ta sanar dashi abinda tasa ayiwa Shukura,Karshe kuma tace kaje gidan Hajiya Binta Kawata ka nemi yarta Nafeesa ku daidaita ko 1mnth baza ayi ba za ayi bikinku,Abbanku ma ya Sani zai fada ma, kuma zan sanarwa Saudatu da Baba,wannan yarinya kwadayayya wacce Bata kaunar zaman lfy, ina kaunarka Ahleef baza ka auri waccar yarinyar ba, wlh Momee ba sonta nake ba kawai taimaka mata nayi,zan yarda ku aura min ko wace amma pls Momee ki dawo da ita ko wajen danginta a maidata,ko ki fada min State din da kika sa aka kaita,Tabe baki Momee tayi karshe tace wlh Baza ta fada ba kuma Baza a dawo da ita ba kuma ka sake naji zancen wurin Abbanku sai ranka ya baci.

Momee ya kyale kawai ya fita da sauri bai zarce ko ina ba sai wajen su Saudatu da Baba ya sanar musu komai,Umma ta shafa sumarsa tare da cewa yanzu Sun fimu iko da kai kayi halacci kayi musu biyayya da shi kadai zaka saka musu sannan ka dage da addua kawai.
Godiya yayi musu ya wuce wajen Farhan tare da bashi labarin komai Farhan ma nasiha yayi masa kan yayi biyayya kawai,amma banji dadi ba a rasa wacce za a baka sai Nafeesa yarinyar da kullum tana titi yau wannan kasa gobe ma waccan kasa tana barikinta Momee batayi tunani ba,yanzu zancen da nake maka saurayinta wani dan china ya dauketa Sun tafi Korea idan ta dawo kuma ta fake da Business,Wlh ni ko Bed bazan iya hadawa da ita ba cewar Ahleef, Farhan sai dariya yake masa.bayan kwana biyu Ahleef ya tambayi securities na Momee wanne state suka kaita ? Amma sai suka ki fada Momee ta hanasu wai,dole ya hakura ya koma addua.

Ahleef bai taba tunanin haka ya damu da Shukura sai yanzu, ba wai So ba kawai birgeshi takeyi sannan da tausayinta da yake ji shi yasa ma ya shiga wani hali a kanta,kwanaki kadan kowa yasan Alheef yana da damuwa,Komai gagararsa yake yi har Office ma komai a hanun Secretary ya barshi,baya murmushi Ko Kadan ya gama fita a hayyacinsa,bashi da aiki sai tunanin Shukuransa yana tuna yanda suka zauna tare gida daya tana masa kuruciya iri iri,haka ma yake tuna murmushinta tare da dariyarta,bata fushi Sam,watarana idan ya tuna yanzu tana can maybe rayuwarta ma ta lalace har kwalla yakeyi,ga Auren Nafeesa da Momee tace dole ne domin Abba har sunje sunyi tambaya tare da sa ranar aure nan da 1mnths,Abba baiyi da ka ba saida ya tambayi Ahleef idan baya so Baza ayi masa dole ba, ganin Momee tana so kawai sai yace yana so,amma Momee anan tayi son kai,lokacin da Niima taki yarda da Auren Ahleef ai Bata yi mata dole ba, gashi kullum a kawo samari take amma bata ce komai ba, shi kuma Ahleef ganin tun yana jariri ta raineshi tasan bazai mata musu ba tunda bashi da gata sai su shine ta nuna son kai akan Shukura tayi fada Da yaranta,Tana son Ahleef amma akan Shukura ta jefashi wani hali kuma babu alamar fasawa.

Hafcy kuma sunji Ahleef zaiyi aure bakin ciki ba Wanda basuyi ba karshe ko wacce tace Baza ta hakura ba sai Sun tabbatar an fasa wannan aure sai Sun tarwatsa komai,Mubaraq bai samu shiga wajen Niima ba, wani yaro take so Wanda da Auren wuri tayi sai ta haifi kamarsa.

Baba da Umma suna zamansu lfy da Momee ba wata matsala tana kyautata musu sunyi kyau tare da murjewa. Sunji ba dadi da za ayiwa Ahleef Auren dole amma basu da iko a kansa dole sai dai kallo gudun kar su yi butulci shi yasa suka sa ido.
Amarya Nafeesa kuwa tunda taji Ahleef Zata aura take sheka uban murna kamar ta zunguro lokacin, Ango ko zance baije ba baibi ta kanta ba.

Makarantar su Shukura sunji labarin barin gida da tayi Latifa ta Baza cewar ta tafi yawon karuwanci.
Kamar Kullum Ahleef kwance yake saman lafiyayyan Bed dinsa yana faman tunanin Shukura bai ma san ya fara hawaye ba, Momee ce ta turo kofar a hankali,da sauri ya goge ido tare da fara baccin karya,Momee ta juya tuna ninta Bacci yakeyi.Tana barin dakin yaci gaba da tunaninsa wanda kullum karuwa yakeyi baya sauki,Harkar bikinsa kuwa Farhan da sauran frnds su suke komai.

Shukura tunda arna suka kifota da Adduna Bata tsaya ba sai da taje jikin wani gida shima a kauyen,Wani dattijon iyamuri yayi mata turanci Hey! Young Lady where are you going ? Whats Happening ? Shukura tana haki tace i need a help,wasu ne suka saceta amma ta manta inane garinsu,mutumin yace ta suje gidansu yana da mata sai ta zauna zuwa kwana biyu dodon tsafinsu zai fadi garinsu,Matarma me kirki ce ta bawa Shukura wajen kwana da abinci kalar nasu,tace amma da Snail tayi miyar,Shukura tace ko bera ne a ciki Zata ci haka bare wani snail, dare ya tsala gari tsit Mutumin ya sadada a hankali ya kwanta a bayan Shukura kamar matarsa yana mata goge,tana farkawa ta tsala ihu yatashi a guje zai koma wajen matarsa,matar kuma taji ihu ta fito a guje sukayi karo da kai gwaraf,sai Ihu suka koma daki Gaba daya,matar dama tasan halin mijinta, Washe gari kuwa da sassafe matar tace Shukura ta bar mata gida Zata kwace mata miji.
tafiya Shukura ta dingayi a hanya har ta hadu da wani matashi tace ya taimaketa ita yar arewa ce, nan take ya kaita inda Zata hau mota,Ba Bata lokaci ya sata a motar Anambra City tare da fada mata yanda zatayi,ya biya mata kudin motar sannan ya bata 3k,ta dinga zuba masa gidiya sannan suka wuce tana mamakin ashe a ko ina akwai mutanen kirki.

Me taxi ne ya sata a Motar Kaduna state da kyar ma suka dauketa kudinta bai kai ba, wani bahaushe dan cirani Wanda shima Kaduna zaije shine ya cika mata kudin motar.
sun sha tafiya sai cikin dare suka sauka a Kaduna lfy,Matashin yace to shifa kauye zaije a kauye yake,Shukura tace dan Allah ya taimaka ya tafi da ita gidansu can kauyen kaduna saceta akayi kafin ta gane gidansu sai ta tafi,Matashin yace ba damuwa muje,taji dadi tace ya sunanka ? Yace Jamilu ke kuma fa ? Shukura ta furta sannan suka shiga motar kauyen.

Jamilu neman kudi yake zuwa Anambra dan cirani ne,iyayensa Sun rasu kakanninsa suna raye su suka rikeshi har ya girma suke tare gida daya,baiyi karatu ba Sabo da rashin Gata shi yasa yake tafiya neman kudi.
Dattijon me Suna Malam Hari zaune yake kusa da matarsa Rahina suna hira a tsakar gida sai ga Jamilu da Shukura Sun shigo da sallama,Ko zama Jamilu baiyi ba ya sanar dasu abinda Shukura ta fada masa a kanta,babu wani damuwa suka tarbeta a mutunce,Tun Bata saba dasu ba har suka saba da juna ci sha da komai suke Bata duk da cewar na kauye ne Shukura Bata Jin dadinsa Sabo da ita ko a kauyensu ma cimarta dabance, sati daya Kakan Jamilu wato Hari yace tunda har tana iya tuna garinsu a kauyen Jos to zai Bata dubu uku kudin mota,baza su iya riketa ba dan Adam abin tsoro ne,Rahina ma tace wannan gaskiya ne ta tafi wurin danginta amma a kyaleta zuwa sati biyu ko uku.

Sati biyu tsakani Shukura ta koma Normal ta tuna Ahleef da Abuja da komai ma,ta dawo Hayyacinta,matsalarta daya tunanin Ahleef daya addabi ranta ba dare ba rana,yanzu ta tabbata Son Ahleef Ya kamata sosai,tun bata yarda ba har ta yarda,tana tsaye cikin daddazon mutane a kauyen mata da maza ana wasannin gargajiya,sai kallonta akeyi a kauyen anga kyakyawa,tunawa tayi yau rabonta da Abuja 3wks kenan karfa Ahleef yaje ya manta da ita ya auri wata,kara ta saki kowa sai da ya firgita ana kallonta ta dafe bakinta da hannu tare da tsayawa cak,sai ji akayi tace Ahleef zai so wata,sai ta fara falfala sauri kafin kace me ta koma gidansu Su Jamilu tace Zata tafi ita gida, Rahina tace ta bari sai gobe amma fafur Shukura tace tafiya zatayi, kakan Jamilu ma ya hanata tafiya yace ta bari wani satin zai kaita Abuja da kansa,ba damar tayi musu kuka kawai ta fashe musu dashi.Shukura Bata san ma bikin Ahleef saura kwana bakwai ba.

Kullum Shukura kuka takeyi ba ji ba gani Bata iya cin komai ita sai ta tafi tun Su Jamilu Suna Bata baki har suka kyaleta,Malam yace 'yar nan kudi nake jira na samu sai mu tafi,Cikin sheshekar kuka Shukura tace ni a kyaleni a gani ko ba sisi sai na koma Abuja ko da Allazi wahidin ne,dariya su kaka suka dinga yi, Shukura tace kaka wajen mijin da zan aura fa zanje, So kuke yayi sabuwar budurwa ina nan,Rahina tace oh yaran yanzu ba kunya,Shukura tace yo ke kaka me kuka iya a soyayya, Kin taba zama kamar yini daya kinyi tunanin Malam Hari? Rahina tace mu da ake mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login