Showing 9001 words to 12000 words out of 96510 words
Kiwa ma wata budurwa ta bawa tace gyara naman nan ki soya min Zan baki Dari biyar,jiki na Rawa budurwa ta Karbe tayi yanda take so, ta karba tare da figawa mutanen gidan nasu sabo da bata da rowa,zama Tayi da Maltinarta a gefe tana ci tana kora Maltina sai kuma ta fashe da kuka ta tuno Baffanta da Inna yanda watarana ma abincin a baki suke bata ana lallabata taci,haka takeyi kullum barnar kudi ga Dunkuna tana faman yi iri Iri har shopping taje cikin garin Jos ta siyo cosmetics da turaruka masu kyau,abinda kawai take birge mutane dashi addini ne da ita sosai bata wasa da addini.
A kwana a tashi Dangin Baffa suka takura su ta ishesu tayi girma da yawa dole sai tayi aure ko su bata duk wanda suka ga dama,ita kuma tace ba wanda ya isa yayi mata dole,su kuma Suka ce baza ta ja musu abin kunya ba sai dai ta bar musu gida baza su iya da halinta ba, Kawunta ta samu tace Kawu kasan bana Zance bani da saurayi kuma ina so na cikawa Baffa burinsa na zuwa abuja nayi kallo kallo.
Takaici ya kama Kawu kawai ya jawo sanda ya fara zane Shukura Yana Karuwanci zaki shiga tsinanniya,sai da ya farfasa mata jiki abinda iyayenta ko zagi basu taba yi Mata ba, haka suka bi suka tsaneta a gidan da sauran dangi bata da ikon magana sai duka kuma yanzu aiki ake sata sosai a gidan kamar jaka lallai taga maraici, ko wanke wanke idan tayi To ranar da zazzabi zata kwana bata saba ba,Kwatsam sai Kawu sukayi shawara a junansu suka zabowa Shukura miji wani Me kiwon Shanu Halilu,Halilu Dan shaye shaye ga neman mata kaf garin an sanshi,Shukura bata da labari sai da bikinta ya rage saura 1wk taji ana kiranta da Amarya tana tambaya taji a garin ana ta mata dariya anga karshen iyayi da jin dadi.
Kukan Maraici Tayi tana tuna so da gatan da iyayenta ke nuna mata amma ga yanda ta koma dare daya,ragowar kudinta ta duba saura Dubu Saba'in kacal Duk ta kashesu a siyi banza siyi Wofi Trolley dinta ta jawo ta shirya kayanta a ciki kaf sauran da bata so ta barsu,Handbag dinta ta zuba kayan kwalliyarta ciki tare da kudinta ta shirya tsab,sai da ta Bari an shiga masallaci sallar asuba ta sadada cikin duhu ta bar Garin bata tsaya ko ina ba sai garin Jos ta zarce Tasha inda zata shiga motar Abuja,a Tashar tayi sallar asuba da Asuba,ta dauko Toothpaste dinta da Brush tayi da ruwa pure water,a tashar ta siyi kosai da biredi tare da shayi hadin kauri taci ta koshi sannan ta wanke fuskarta da sabulunta harda shafa powder da jan baki sama Sama,ji tayi Driver yana cewa shigo yan mata zamu wuce,da sauri ta shiga ta zauna mota ta tashi sai Abuja.
Bikin Ahleef saura kwana uku ango ba zama Sun gama gayyatar abokai,ba abinda ba a gama ba na shiri,sun narkar da kudi,Abba yana sama a dakinsa yaji ance yazo ga manyan danginsa sunzo Maza biyu da mata biyu,ya fito Sun gaisa kenan sai ga yayan Momee da kaninta tare da yayarta,abin ya basu mamaki,bayan an gaisa anci ansha,suka ce abinda yake tafe damu ba komai bane sai akan auren Niima,Gaskiya bamuji dadi ba Sam da ilminku da komai zakuyi mata auren dole,jiya taje mana Tana kuka ita bata so auren dole za ayi mata,Abba ne ya dakatar dasu yace ku bari Niima tazo shima Ahleef yazo, Nan Momee ta Kirasu a waya,5mnt dukkansu suka zo, Momee tace gata nan gashi kuji daga bakinsu,Ahleef suka kalla kai kaine da kanka kake son Niima tsakani da Allah?da Sauri Ahleef yace ae,Niima kefa?kinje kin Kai mana kukanki yanzu maimaita a gaban kowa,ai kuwa ba tsoro Niima tace uhmm... Ahmm..Ina sonsa amma bada aure ba,ni ban shirya aure ba, kuma ni bana...Mari taji Abba ya kifa mata shi,Tana kuka tace wlh ni bana son aurensa,Abba Hawaye suka gangaro masa,Momee kam dama zancen ya dade da zuwa kunnenta,a hankali tace Baban Suhail kyaleta,ai dai kin tabbatar bakya sonsa ko? Niima tace ae,Abba yace ni zaki wulakanta sai ki fada mana sabo da me? Tana kuka tace bashi da asali wa ya sani ko shege ne,Momee Kuka kawai take shekawa, Abba yana Jin haka yace Ahleef kayi tawakali kayi hakuri,Allah zai baka wacce ta fita,ke kuma baza muyi miki baki ba amma ki sani sai kinyi nadama,yan Uwansa ya kalla yace na gode kuje kawai,jiki ba kwari suka tafi,itama Niima ranta Fari kal ta koma dakinta tana bugawa samari da yanmata frnds nata waya Tana Murna suma haka.
shiko Ahleef ya mike kenan ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme,
Momee da Abba da gudu sukayi kansa ana kiran Driver duk abinda za ayi masa anyi bai farfado ba da taimakon yan aiki aka kwasheshi zuwa Hospital,Private Hospital suka tafi amma duk likitoci sunyi iya yinsu sun kasa dawo dashi yaki farfadowa,Kwana daya bai farfado ba,Momee tare da Farhan ne ke kula dashi sai Abba dake sintiri,Kwana biyu bai farfado ba har dare yayi Momee ta damke hannunsa tana zubar da hawaye Tana masa addua cikin ikon Allah sai ya fara motsi,Momee ta rungumeshi tana Murna tare da godiya ga Allah, kamar ba Namiji ba taga yana Kuka sosai,Ahleef Momee ta kira sunansa,kuka kawai yakeyi Har Farhan ya shigo ya tausawa abokinsa duk dauriyarsa gashi yana kuka akan Mace,Momee ta Tallafo fuskarsa kayi Hakuri Son wlh mu kamar iyayenka ne,karka dauki maganar Niima kasa a ranka kaji na rantse munfi kaunarka fiye da yaran da muka haifa,kuma a yanzu Niima ko tace tana sonka bazan Bari ka aureta ba tunda Tayi Ma haka Allah sai ya baka wacce tafita komai da komai, Har abada Niima tayiwa kanta,kayi tawakali jarabtarkace,Farhan ya dora da cewa Maybe ma ba alkhairi bace a tare da kai shi yasa,kuma Allah zai ma sakayya dama can ba matarka bace,Momee da Farhan tare da Abba haka suka sa Ahleef a gaba da Nasiha iri Iri,Suhail da Salman Ma haka yar auta Latifa ma ba a barta a baya ba, ita kuwa Niima yau kwana 4 kenan suna asibiti amma ko dubiya bata leka ba,Momee da Abba duk sun daina kulata har su Salman.
ganin ba Wanda ke kulata a gidan tace zataje dubiya Momee tace karta soma ganin kafarta,Ahleef Sabo da Nasiha da kula da yake Samu yaji sauki ya dan warware amma ya daina magana da kowa sai ta zama dole baifi a Rana yayi manana sau uku ba, kullim fuska a cinkushe take shi kadai yasan irin kunci da baking cikin da yake ciki.
AsmaBaffa
[7/22, 1:09 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO
4
Official
By
AsmaBaffa
Masu sharhi ina godiya wannan page naku Ne.
Tunda aka sallamosu yayi tozali da Niima Sonta ya dawo sabo ciwonsa ya tashi suka kara komawa asibiti,kwana daya aka sallamosu Duk ya kara fari ya rame,Niima sai harkarta takeyi ba ruwanta,Momee killum Nasiha da fada take masa yayi hakuri,Farhan shi ya dinga sanarwa cewa an dage bikin Ahleef sai nan gaba idan an sa Rana za a sanar mutane sunyi mamaki Wanda suka san labarin sun tsinewa Amarya ba adadi.
Ahleef ya zama kamar kurma fuska ba Rahma,Sai kallon hoton Niima kullum aikinsa Kenan,Momee tayi fadan har ta gaji,shima Abba haka,Har Saudiya Momee ta shirya musu ita da Abba tare da Ahleef suka tafi,sai da suka kwashe 3wks suka dawo Alhmdllh Ahleef ya samu afwa har kiba da kyau yayi sosai,sai rashin magana da fara'a ya dawo abin Tsoro,kwarjininsa ya Karu ya maida Hankalinsa wajen aikinsa Kawai,duk ranar da zaiga Niima to sai hankalinsa ya tashi ganin haka yasa Momee tace maza Niima ta shirya ta koma Kaduna wajen yayarta ta zauna kafin wani lokaci,Niima murna tayi zata ji dadin Shanawa da samarinta a can, Zata yi yawonta inda taga dama.
Ahleef ya riga da ya tabbatar bazai taba aure a duniya ba tunda ya rasa wacce yafi so Niima to bashi ba kara kula mata, kullum dare sai ya zubar da hawaye ya kasa hakura da Niima,har aka kwashe 3mnth a haka yake ba canji yana shan wahala.
Shukura ko da ta sauka a Abuja da yamma ta rasa ina zatayi kawai tayi zamanta a tasha a nan taci abinci har dare,sai kallonta akeyi gata da shegen kyau,a tashar nan ta kwana dake Abuja ne ba ruwan wani da wani ba wanda ya kulata,gidan wanka na mata ta shiga ta biya kudi Tayi wankanta Tayi brush tare da shiryawa tsaf ta fito ko vaseline bata shafa ba kaya kawai ta canja taja akwatinta Tayi gaba,tana fitowa gefen Titi taga wasu arnayen motoci guda biyar sun wuce da matsiyacin gudu sai ko daya daga cikin motocin suka kade wani dattijo nan take ya mutu,dattijon da dansa namiji abin tausayi yaron zai Kai 25yrs sai ihun kuka yake yayin da wannan motoci suka gangare gefen titi,mutanen suka fito,Ahleef yana motor dake tsakiya Duk escort dinsa ne,fuska ba rahma ya fito cikin takunsa kamar Sarki, Shukura dake gefe bata da burin da ya wuce taga baban wani ko babar wasu ta mutu sabo da nata Sun rasu,wajen gawar taja akwatinta bakinta har kunne sabo da Murna,yaron yana ta zunduma ihu Yoruba ne ko Hausa baya ji,Shukura ta kutsa ta cikin mutane har gaban yaron ta dinga tuntsira dariya,kowa yana kallonta gashi ko ba Dan Allah ba sai ka Kalli Shukura sabo da kyanta,Ahleef ya kalleta sau daya kirjinsa ya buga,Shukura tace amma Allah yayi muku albarka masu motoci gwara iyayen kowa su mutu a duniya nima nawa Sun mutu.
Kallonta mutane suka fara yi masu Jin Hausa suna Mamaki wasu na dariya, matashin Yoruba ya daura hannu aka yana rusa kuka yana Help me ooooo My Papa,Help me Jesus ,Oh..God Papa....yana ta sambatu Ahleef ya karasa da niyyar taba jikin Wanda suka bige da mota caraf yaji an rike masa Damtse,a fusace ya juyo da mamakinsa sai yaga Shukura ce duk da bai santa ba ya zuba mata Harara,kwarjininsa yasa tayi saurin sadda kanta kasa tana cewa Allah baza ka kaishi asibiti ba sai ya mutu shima tunda ubana ya mutu,Hannunsa ya fisge da karfi har sai da ta kusa faduwa kasa Bata hakura ba ta jawo rigarsa nan ma ya fisgeta yana bawa Guards dinsa Umarni a daukeshi zuwa Hospital,sanan aka kira Police suka shige mota suka bar Shukura da sauran mutane.
Itama akwatinta ta ja tayi gaba abinta ko ina zata je Oho. Ahleef kuwa ya cika da mamakin Irin rashin Imani na Shukura,Sunje Hospital anyi komai tare da Police,wanda ya mutu an kaishi gida tare da Tallafin kudade da kayan abinci,wanda kuma ya kade mutimin ba musulmi bane bare ace azumi ya kamashi.Abba da Momee ma duk sunje Sun kai musu tallafi,Yaron matashin ma Salman ya bashi aiki a Company nasa.
Shukura kuwa Hotels ta dinga zagawa sai da ta samu Me kwana daya dubu goma sha tara a Maitama,cikin gwarancin turancinta ta samu ta kama daki da kyar ma suka barta wai tayi yarinya,cikin dubu sabain dinta,taci abinci na dubu biyar, kamar wacce ta dawo daga kasar waje sai dai ana kallonta daga karkara tazo,kwana uku ta kwashe kudinta suka kare saura 3k Amma sai tace masu Hotel su kara mata 3days zata biya Idan ta shiga bank babu cash a hannunta kullum Bread take fita taci da ruwa ta dawo Hotel,ana haka 3days ta cika, masu Hotel gani suke kudi ne Da Shukura,da safe tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar Riga silver color,tayi kyau kamar balarabiya kuma yar birni,akwatin kayanta ta ajiye a Room dinta ko Hand back Bata dauka ba sai kudinta dubu biyu ta fito tare da sanarwa ma'aikatan cewar ta tafi bank zata dawo yanzu kayanta har Handbag suna ciki yanzu zata dawo ta biya su.
Ganin har hakorin makka ne da ita guda daya Sun San ma Hajiya ce kuma sunga yanda take wasa da kudi,Shukura tana yin nesa da Hotel din tace ruwa ta sha ta shiga taxi tace ya kaita wani restaurant mutanen wajen dama Sun saba da Shakura tana zuwa tayi musu wasa da kudi farkon zuwanta Abuja da kudinta, suna ganinta suka fara washe baki, Ta zauna duk abinda takeso sai da tasa suka cika mata table da abinci,ta ware ciki taci ta koshi karshe ta duba ta zaro 2k sai ta mayar taja tsaki ta dauko Voter card dinta ta matseta a hannu yanda za a hango kamar Atm card ne sai tace bari naje nan Opposite Bank na ciro kudi just 2k ya rage a hannuna,mutanen duk arna ne musulmi yana musu kwarjini kuma suna ganin masu gaskiya ne most of them kawai suka ce taje ko gobe ma ta kawo,aiko da gwarancinta na turanci tace OK thanks ta fita Bata tsaya komai ba ta mike layin tana tafiya,alhazawa da manyan masu kudi sai kallonta akeyi Sabo da kyau Irin na Shukura,duk motar data wuce sai ta kalleta,Tafiya takeyi tana tunani wai ina zataje ? Ina zata kwana,wata dalleliyar motace tayi slow a gaban Shakura,da sauri ta kalli na cikin motar wani jibgegen Alhaji ne kamar zai fashe sabo da kiba kansa kuma dan karami Horn ya danna mata tare da yafitota tazo,bata San mazan Abuja ba sai ta je tare da gaisheshi tun a nan yasan Bata waye ba kuma bakuwa ce ya samu banza.
yace yan mata shigo muyi magana mana,ba musu ta shiga mota,shiko farin ciki ya kamashi,yace Hajiya na ganki ne kuma naji ina sonki,gaki kin hadu gaskiya kina da kyau irinki nake mafarkin samu,murmushi tayi kawai,yace ina ne gidanku na kaiki can ? Tace nima bakuwa ce kwana nan babanmu yaci dan Majalisar tarayya muka dawo nan da zama amma ni yar kauyen Jos ce fulanin daji,Alhaji dadi ya rufeshi ya samu yar gidan me kudi nan take yace a wanne Hotel zamu hadu ? nan ta gane me Alhajin ke nufi da ita,kawai sai tace karfe 12 na dare ai zaifi Ko ? Yace ashe dai kin gane gaskiya kin hadu ta ko ina.a boye ta maka masa Harara suna hada ido ta saki murmushi,tace hmm Muje kasan layin nan zanje wani Mall zan siyo waya sabuwa,Ki bari mu hadu a Hotel Idan mun gama Jin dadinmu sai na siya miki wacce kike so me tsada,nan taga fa baza ta samu sisi ba sai yayi lalata da ita sai tace to bari na koma gida sai mun hadu ltr, ta fice a motar yana washe baki zaiji dadi yau,sun rabu ya tafi itama ta kara Gaba tafiya take a kafa gashi Bata san ko ina ba a garin kawai tafiya take.
Momee Dalilin abinda Niima tayiwa Ahleef yasa Hawan jini me karfi ya kamata ta fara cuta me tsanani tun tana boyewa har ta kasa motsi gashi lokacin su Salman Sun koma Uk sai Latifa kawai, Ahleef kuma yanzu tunda abin ya faru Sam baya zama sosai a gidan yafi zama a katafaren wani gidansa daban can wata Unguwar da turawa suka fi zama ciki,ba ruwan wani da wani,kamar malaikan mutuwa haka ya koma ba fara'a ba komai ko magana sai ta kama wannan abin ne ya damu Momee har cuta ta kamata,Abba ma Yana Tunusia bai Sani ba boye masa takeyi,Ahleef ne ya shigo da safe gidan yaci uwar wanka Cikin wani yard hadadden gaske dinkin ya masa kyau sai kamshi yake zubawa,ga wani agogo malam abin kallo,Sumar nan tasa kyalli takeyi lips dinsa yana sheki jajur dasu.
Cikin takunsa na kasaita ya shiga bedroom din Momee yana bulbula kamshi,Subhanallah ya furta hangota yayi kwance ta dafe kirji tana tari tare da haki ta rame,da gudu ya karasa kusa da ita bai ma Bata lokacin yin magana ba cak ya dauketa ya sauka kasa cikin sarsarfa escort dinsa suka figi motoci sai wani katafaren asibiti Emergency,likitoci suka rufu kanta har aka samu ta farfado sai aka canja mata daki suka ce dole sai tayi 1wk Ko 2wks kafin a sallameta,Momee tana jin dan sauki tace kar Ahleef ya fadawa kowa sai ta warke,yace to Momee Tawa Allah baki lfy tace Ameen,Tunani yakeyi wacce mace zai dakko wacce zata iya kula masa da Momee.
Shukura yau titi ta yini tana yawo ga yunwa da take cinta,tana zaune jikin wata bishiya a zaune mararta ta murda ta fara ciwo sosai take ciwo da alama Period zata fara,ta Mike a hankali ciwo na cinta Bata kula ba ta tsallaka titi sai mota ta fyallo da gudu saura kadan ta maketa Allah ya taimaketa kadan ta dan bigi Kafarta sai ta fadi can gefe,dalleliyar motar ce tayi parking wani katon arne Igbo ya fito da sauri yaga jini na bin kafafunta tunaninsa motarce ta mata rauni haka bai san period take ba dama kuma ba pad jikinta,a motar ya sata ya figeta tana kuka za'a saceta,bai tsaya ko ina ba sai asibitin da aka kwantar da Momee tasu Ahleef, sai kuwa aka rasa dakin da za a kwantar da Shakura sai dakin da Momee ke ciki suka shiga neman izini tunda daki mutum daya ake bawa.
Ahleef na zaune gefen Momee suka shiga suka nemi izini tunda dakin da aka sa Momee na mutum biyu ne normal, Ahleef yace bai yarda ba, Momee tace Son kyale a taimaketa a kawota ba damuwa.
Shukura kukan Shagwaba kawai takeyi Wanda dama ta saba,jini na bin kafafunta aka turota Saman bed har dakin,duk ta cikawa mutane kunne.
Ahleef Sam bai ganeta ba,amma kamar ya santa amma ya manta a Ina,Momee tace sannu yarinya ko cikine daita tayi barinsa Allah Sarki gata kyakyawa Mashaallah,Likitoci sukace Ahleef ya fita