Showing 81001 words to 84000 words out of 96510 words

Chapter 28 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

256

Bata a Baki da kansa tana ta bashi dariya da hirar kuruciyar ta, Bayan sun Gama, shiri sukayi sun dau wanka kamar baza a mutu ba suka fita yawon zaga gari abinsu gwanin Sha'awa da birgewa.








Ayi min hakuri Fans wannan Novel din bana bada page da wuri wasu Abubuwa ne suka rikeni in busy ne sosai,Dan Allah kuyi min hakuri da afwa da kyar nake samun time na typing.







AsmaBaffa
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







71-75






Official







By
AsmaBaffa











Ahleef Yan London sun kwashe 2wks a garin suna zuba amarci kafin suka tafi Russia sun kwashe 1wk sannan suka wuce Saudi nan suka Iske Baba da Umma Sunyi Ibada sosai,sai kyau da haske da suka Kara tare da Yar kiba kowa ya gansu yasan suna Jin dadi,Shukura tana ta siyayya Ahleef Yana kashe Mata kudi sai abinda take so, Bayan sun Gama aikin hajji Su Umma suka dage zuwa Nigeria,Ahleef kuwa Shukura ya dauka suka wuce Dubai abinsu, Baba da Umma suna hutawa suka tafi Niger a jirgi wurin dangin Baba sada zumunci,can ma Sunyi Mamakin ganin Baba,domin tunaninsu baya Raye sai gashi ya kawo Musu ziyara tare da kyautuka na alheri, sunji dadi sannan Ya Basu labari dansa Ahleef, satinsu biyu sannan suka dawo Abuja cike da murnar ganin Yan Uwa.

Bayan 3weaks Su Shukura jirginsu ya sauka a Nigeria,Murna take faman yi zata ga su Umma, escort din Ahleef ne suka dauko su daga Airport zuwa gida, Umma da Baba ma murna suke sosai da dawowar yaran nasu,Shukura jikin Umma ta lafe sun Dade suna Hira har Ahleef tare da cin abincin Umma me Dan Karan dadi sannan suka wuce hadadden part dinsu cike da kaunar juna.

Niima ciki ya Kara girma sai fama take da laulayi, Momee kullum sai ta zubar da hawaye musamman yanzu da suke cikin talauci kudi ya Kare karaf,abincin da suka siya ma sun cinye Babu sai kadan,kudin cefane Babu shi kullum shinkafa fara da Mai suke ci abinda ya rage musu kenan, tuni suka daina girki da Gas sai itace ko coal,kamar kullum yau sun tashi sisi babu ko na Koko Basu samu ba sai taliya suka dafa suka ci da Mai,duk sun rame Sunyi Baki lalacewar tayi yawa ma,Babu Wanda yake taimaka musu,tunaninsu don sun tuba ga Allah shike Nan baza a jarab cesu ba sai gashi sunga ba Haka bane, wahalar tayi musu yawa yau Momee da kanta ta shirya tace Niima ku kula da gidan Bari naje wajen Farhan ko zan samu tallafi,Latifa tace Allah yasa a Dace Amma da na biki ko zanga Farhan naji sanyi, Momee tace to zo mu tafi,a gurguje ta gyara Fuskarta tare da yafa mayafi tabi Momee suka Shiga Napep suka nufi gidan Su Farhan.

Suna Shiga lokacin Farhan ya fito yaci wanka zai fita,Yayi mamakin ganin Momee da kanta,ya kallesu duk yaga sun lalace sun fita daga hayyacinsu da gani suna cikin wahala.
da sauri ya Isa wajen Momee tare da gaishe ta kamar yanda ya Saba, ta amsa fuska cike da annuri sannan ta fara karanto Masa matsalarsu ta Kara bashi hakuri sannan tace Dan Allah ka hadani da Ahleef ko ba komai zamu roki gafararsa tare da Matarsa.

Farhan ya tabbatar su Momee Sunyi Nadama,Latifa tana gefe ta wani rakube a bango kamar munafuka sai kallon Farhan take ba ko kyafta ido, Farhan Yana kallonta ya lura da abinda take suna hada Ido ya zabga Mata Harara tare da Jan tsuka kadan ya turo Dan lips dinsa gaba kamar yanda Mata sukeyi,Latifa tana gani sai ko ta bangale da dariya tana yaye Baki, fuska ya Kara tamkewa.

Farhan Yana kokarin bawa Momee Number din Ahleef sai ga Ahleef tare da escort dinsa sun shigo da motoci gidan,Momee Baki ta bude ganin motocin da Bata taba gani ba masu shegen kyau da tsada,Latifa kuwa ta ma manta a Ina take kamar Yar kauye Haka tabi motocin da kallo.

Da sauri suka budewa Ahleef mota ya fito cikin Shiga ta alfarma,tuni kamshi ya cika gidan,Yana fitowa ya Mika hannu tare da fito da Shukuransa cikin rantsatsiyar Shiga kamar zasu je gidan shugaban kasa,sun wani Kara ja da kyau,Momee da kyar ta ganesu,Haka Latifa ma Baki bude take kallonsu,Ahleef kuwa Bai kula dasu ba tunaninsa Yan maula ne.

Momee da sauri tace Dana Ahleef, Latifa tace ya Ahleef da karfi, Jin Muryar da ya sani da sauri ya juyo kallo daya ya ganesu, kafin yayi wani taku Momee tazo ta durkusa tana bashi hakuri harda kuka, Latifa ma Haka, Nan Momee ta fara bashi labarin duk halin da suke ciki da abinda Mubaraq ya musu etc.
Ahleef yace ba komai Momee Ni baku min komai ba Allah yafe Mana Baki daya,Shukura tana gefen Ahleef ta kankameshi Haka ta gaida Momee a ladabce, Momee ta kalleta da Faraa sannan tace ki yafe Mana Shukura mun zalunce ku,Shukura ta kalli Ahleef sannan tace Ni dama na yafe muku tuni ban rikeku a Raina ba,Ahleef yace kije Gida Momee zanzo anjima,Latifa tayi sauri ta bashi address din gidan da suke sannan suka tafi gida gwanin tausayi,har Sunyi Nisa Shukura tace kasa a kaisu gida a motarka,Nan ya bada Umarni driver dinsa daya yaja mota ya dauki su Momee ya maidasu gida,sai murna suke tare da bawa Niima labari itama sai dadi take ji zai aureta kwana Nan.

Shukura wurin Maman Farhan ta wuce,Ahleef Kuma ya tsaya tare da abokinsa suna tattauna magana kan su Momee, Farhan ya bashi labarin halin da suke ciki, Kuma gidan Dana maka waya ka siya shine nasu Momee, Ahleef ya tausaya musu kuma yasha mamakin karewar dukiya me tarin yawa Haka.haka Hukuncin Allah yake ko nawa ka Tara a duniya sai Allah yaso zasu zauna,komai kudin mutum idan Allah yaso ka talauce Dole su Kare Babu abinda ya gagari Allah har kaji mutane suna ai wane shi da talauci har abada,sai idan Allah baiga dama ba.

Wurin magrib Shukura tana wajen Maman Farhan tare sukayi girki suna hira,Mama tana Kara koya Mata dabarun rike me gida da yanda zata gyara kanta sosai,wasu Tsumin ta bawa Shukura iri iri da yanda zata dinga amfani dasu,har sukayi Sallar Isha Ahleef Bai dawo ba sun fita tare da Farhan.
Faskekiyar wayarta Shukura ta dauka tare da Kiran Ahleef, bugu daya ya dauka can kitchen ta shige sabo da tana kunyar Maman Farhan, kashe murya tayi tare da narkewa a hankali tana Shagwaba tace My Hero na gaji kazo mu tafi gida pls, wani yarrr yaji jikinsa ya amsa sabo da yanda tayi maganar,cike da so yace sorry Honey I wll be on my way soon, minti nawa zan baka? 10mnt Zaki ganni ok? Kai ta daga kamar Yana ganinta sannan tace to Allah kawo min Kai lfy sannan ta kashe wayar,har tazo bakin kofa zata bar kitchen din,Ahleef ya kirata back,ta daga taji me zai ce, tana dagawa yace na manta ban fada Miki ba? Tace mene fa? Albishirinki? Tace goro Fari Kar,tana jira taji sai yace I LOVE U SO MUCH, wani sanyi da sonsa ya Kara ratsata tayi Murmushi cike da farin ciki tace Love u much more, u are my World and u make me complete, sannan ya kashe wayar,sai ta sake kiransa again yayi picking tace missed u missed ur everything,Ur hand fit in mine just wanna sleep on ur chest sweety, Honey Zaki sa na kasa driving kina kashe min jiki, dariya sukayi gaba daya,Farhan Yana gefe Yana jinsa lokacin Kuma Niima da Dan cikinta tirtsitsi tana motar zasu kaita gidansu, su Momee tuni Ahleef ya musu kyautar gidansu back dama shi ya siye gidan.

Niima kamar tayi kuka taga yanda Ahleef suke ta diga love da Shukura baya kallon ko wacce mace sai Shukura, a ranta taji tsanar Shukura marar adadi ta kamata,Latifa da Umma su tuni Driver ya maidasu gidansu tare da kayansu.

Bayan sun ajiye Niima a kofar gidan suka juya sai gidan su Farhan,Maman Farhan tana mamakin Shukura yanda ta kasa zaune ta kasa tsaye ita mijinta ta Matsu ta gani kusa da ita, Dan yanzu Shukura tafi sabawa da Ahleef ko yini cikakke Bata iyawa ba tare da ta ganshi ba.

Tana Jin karar motar ta yafa gyalenta, sai gasu sun shigo,Maman Farhan tace Kun dawo kenan, wannan duk ta kasa sakewa baka Nan,Murmushi Ahleef yayi Yana kallon Shukura ta kasan Ido, a fili yace Haka takeyi ai da a Office nake ma da tuni taje, Farhan yace ki daina yarda Mama munafuki ne shima shine Dan anace Baya iya yini sai yasa an daukota, dariya Mama tayi tace to Dan sa Ido,Shukura tayi luf Wai kunya takeji,kallonta Ahleef yayi tare da cewa tashi mu wuce Madam,ta kwashi kayanta da Mama ta Bata sukayi musu sallama sannan suka fita,Shukura tace Ina escorts? Na sallamesu Ni zanyi Driving idan Kuma kina bukatarsu ranki ya Dade sai a kirasu sai abinda kike so, hararar Wasa ta watsa Masa suna nishadi suka wuce gida.

Suna Isa gida Umma tace Kun Dade yau,Ahleef da Shukura suka nemi wuri suka zauna a Palon Umma, Baba ma Yana nan, Ahleef ya kwashe komai da ya sani game dasu Momee ya sanar dasu sannan yace Umma yanzu Niima tana Nan da cikinta, gidan ma Allah yasa Ni na siya yanzu na bar musu shi kyauta,sannan kudin da Abba ya bani Wanda suke Usa an hanasu to nayi waya dasu nace a Basu na bar musu kyauta tunda Allah yasa sun iya business tun farko suja jari su juya kudin suna Samun na cin abinci,Sannan Niima Na Sa za a Bata aikin Gomnati su dinga yi tunda Ina da hanya Kinga ya Isa su rike kansu, Sai Latifa a nema Mata University taci gaba.

Albarka su Baba da Umma suka dinga sawa Ahleef yayi kokari da wani ne manta alkhairi zaiyi yaki tallafa musu, Ba komai Umma ai ko ba komai Momee uwata ce,ta rikeni Amana da Abba ko sabo da wannan ai bazan watsar dasu ba,har abada Ina ganin mutuncinta,dama Niima da Latifa sune suka Bata komai to Suma ga inda ta Kare musu. Allah ya kyauta yanzu idan Niima ta haihu sai Kuma tayi aure idan taga zatayi cewar Umma, Ahleef yace ai Momee tace aurarsu zatayi Baki daya Bayan ta haihu tayi istibrai, Farhan ma ya samu matar da zai aura Fatima kawar Shukura ce schl dinsu daya,Amma Wai wajen babansu yaje Kai Masa sako anan ya ganta,manya har sun Shiga zancen,Shukura ta kwalla ihun murna tace Fatima tawa dai Dana sani? Ahleef yace ae itace,yau Munje wajenta kawai naga Ashe itace ma, Umma tace Alhmdllh, Baba ma Haka yace Kinga kawa da kawa ga aboki da aboki,dariya sukayi Baki daya,Shukura sai murna take.

Umma tace Amma zaka dinga zuwa wajen Momee din taka kana gaisheta kamar da,Ae Mana, tace zata zo Wai har gida ta baku hakuri ma, sannan Niima zata zo Wai tayi sati daya anan gidan sabo da karfafa Zumunci,Umma tace Wlh mu ba komai mun yafe tuni ai.

Nan take Shukura ta hade fuska tunowa da tayi ai Tsohuwar budurwar Ahleef ce zai iya komawa yaso Abarsa,Kuma ance indai son farko ne ba a mantawa ko mutum ya tsufa soyayya zata iya tashi.

Kishi ya kama Shukura ta kasa Control a fusace ta mike ta nufi part dinsu,mamaki ya kama Umma da Ahleef,Baba Murmushin manya yayi yaje gano tuni,yace jeka Ahleef matar taka fa tayi fushi,Ahleef yace to me akayi Mata,Umma tace jeka wlh ka lallasar min yarinya ta.

Hankalin Ahleef ya tashi Shukura tayi fushi Bai San me akayi Mata ba,da sauri yabi bayanta,tun kafin ta Isa part dinsu ta fara rusa kuka, bedroom dinta ta shige tare da Sa key ta zauna dabar a kasa irin zaman Yan bori tana ta kukanta,Ahleef ya karaso da sauri ya Murda Handle Amma kofa Gam Gam,yace ki bude me ya faru,ko Baki da lfy Dan Allah ki bude Honey duk ya tashi hankalinsa.
Taki yin magana Kuma Bata bude ba kukanta take rerawa, magiya da rokonta ya Shiga yi idan baza ki bude ba to ki fada min me yake faruwa? tana shesheka tace Bayan kishiya kace zaka yi min, Ahleef Baki bude yace Ni din? Yaushe nace Haka? Yana mamaki tace ae ai Naga take takenka kuma wlh Allah indai kace Haka Ni Kuma sai ka sake Ni,Haka kawai za a kawo min jaraba gida a Jaja min cuta,Dariya ma abin ya bawa Ahleef Bai gane kan Zancen ba, yace Wai meke damun kanki ne? Ae kace Haka Mana ka zageni kaji dadi ai Dole kace min Haka tunda kaga wacce ta fini Kuma wlh baza ka dauko cuta a jikinta ka shafa min ba.

Salati Ahleef yaja shi bai San kan zancenta ba,tace idan shegiyar Nan tazo part dina wlh Allah da Kai da ita sai na yanka ku, Ahleef sai yanzu ya gane Niima take nufi ya Shiga sheka dariya yace to bude dai ki fito muyi zancen, da kyar ya roketa ta bude tare da fitowa, yasha mamaki ganin Fuskarta kamar an watsa mata yaji tayi jajir ga Hawaye ta ko Ina duk ac din dake gidan ta hada zufa.

Hannunta ya ruko ke yanzu Akan wata Niima kika Bata fuskarki Haka? Hawaye ya Kara shararo Mata tace gashi Nan yanda kake fadar sunan ma da dadi kake tsarawa kace NIIMA Mana Amma sai kayi iyayi kasa kalkala,Ahleef ya danne dariyarsa ya kumbura murya da Bakinsa yace to NI'IMA tace ai dai baka birgeni ba Tunda sai Dana fada kayi,yace muje nayi Miki wanka jiba yanda kike zufa Akan kishin banza,ai kinfi karfin kiyi kishi da Niima kucaka,Dariya Shukura tayi tana share Hawaye Wai taji dadi yace Mata kucaka.

Ya zura Mata Ido ya hango yanda take murna,Murmushi yayi tare da daura ta a cinyarsa yace to me zanci da wata Niima me katon goshi Bayan ga Shukura Balarabiya,Shukura ta Kara wani shigewa jikinsa tana Jin dadi Yana ta kushe Niima itace a sama, yace Shugabar Matana na aljanna Hurul ein,a aljanna ma sai abinda kika ce, Shukura tayi dariya tace Idan na Shiga Aljanna shuuma zan zama,Ahleef ya fara dariya,tace kasurgumar Yar giya zan Zama a aljanna kullum Nasha nayi tatul, Dariya Shidai Ahleef kawai yake na labarin Shukura sai da ya gaji sannan ya dauketa sukayi wanka suka kwanta suna hirarsu ta masoya bacci ya kwashesu me dadi.

Bayan sati biyu su Momee komai ya Dan fara gyaruwa suna Dan Jin dadi komai ya fara zamar musu Normal Ahleef ya gama musu komai Kuma Yana zuwa akan lokaci, yaune Kuma Niima ta hada kayanta ta nufi unguwar su Ahleef, da kyar masu gadi suka barta ta Shiga sai da ta Kira Ahleef a waya sannan ta samu aka bude Mata kofa, wani maaikaci ne ya rakata part din Shukura,Ahleef Yana Office Amma ya kusa dawowa Shukura tana Bed room ta Gama tsantsara masa girke girke masu dadi, tayi wanka tana tsane ruwan jikinta taji Sallamar Niima, Jin mace ce sai ta sakko daga sama daure da guntun Towel Fari ga karami a hannunta tana tsane ruwan gashinta, lekowa ta fara yi kadan ta hango Niima zaune, karasa sakkowa tayi tana tamke fuska Amma ta danne kishinta da Faraa ta tarbeta suka gaisa, Niima sai kishi take na Shukura tana wani Shan kamshi,Shukura ta Dan zauna kadan sannan ta kawo Mata kayan ci Dana sha.

Tana zuba Mata juice Ahleef ya Danna Door bell ya dawo, cike da Shauki tace Hero ne? Yace yeah Honey I'm Back, kofar ta bude a hankali cikin takunta na Jan hankali, Bai San anyi bakuwa ba ya daga Shukura sama tana Masa Oyoyo ajiyeta yayi tare da rungumeta a jikinsa suka fara kissing din juna sunkai 5mnt sannan Shukura tace muje ciki Mine.

Zai zame Mata towel tace akwai fa bakuwa a Palon Nan baka ganta ba,sai lokacin yayi tozali da Niima tana kallonsu kamar Mayya ko kyafta ido Bata yi,kishi ji take kamar ta kashe Shukura ta huta.

Da kyar ta iya gaida Ahleef,ba tare da ya kalleta ba ya amsa sannan ba kunya ya tsuguna yace Honey hau muje ki min wanka, bayansa Shukura ta haye kamar yarinyar yaye tana Wasa da gashinsa tana cewa Unique I love u, ta juyo ta kalli Niima dake Shirin kuka sabo da kishi, Shukura tace Bari mu sakko pls baza mu Dade ba wanka kawai zan masa.

Niima kanta ta dauke gefe tare da goge kwalla a boye su kuwa tuni ma sun bace Basu San tanayi ba,Niima tana Palon tun tana sa ran ganin zasu sakko Shuru kamar an shuka dusa, saida suka Gama Raya sunna sannan suka sake wanka tare da shiri ka rantse party zasu je suka sakko kasa, Allah sarki Niima sai gyangyadi take yi bakinta cike da yawu na laulayi HHH.

Ahleef ya kalleta kadan baya Jin tausayinta ko kadan gashi ta Sa Yar Jakarta a gaba, Shukura tace sannu mun barki kina jira, Baki cike da yawu Sautin maganarta baya fita sosai tace Bha..Bha...komai,Bhani...yedha( Leda) idan kina dha yita(ita) Shukura tace ai yawu Zaki Tara a ciki? Niima ta daga kai, No Ni Mijina abinci zai ci tsakani da Allah kyankyami gareshi bazai iya cin abinci Yana hangoki kina Tara yawu a Leda ba,Ina laifin ki na Shiga toilet, tsaya a raka ki wajen Umma ita zata Miki dabarunsu na Mata sai kiga yawun ma ya daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login