Showing 3001 words to 6000 words out of 96510 words
sosai yayi suna a duniya har yafi Daddy ma kudin,suma su Salman suna fara university aka basu nasu harkar,Niima ma haka,Momee ma haka,kowa a gidan da nasa na kansa yake amfani babu Wanda ya dogara da na wani sai Latifa yarinya,Duk gidan yan boko ne Abba kuwa dan Boko ne dan kasuwa kuma dan siyasa Wanda ya rike mukamai da dama manya yanzu haka shine Sakataran Gomnati na kasa baki daya,gidane Na Tarbiya basu da wata matsala har soyayya tayi zafi tsakanin Ahleef da Niima wacce ake tunanin aurensu kwanan nan.
Ahleef Yana da addini ga ilmi,bashi da wata matsala sai watarana yana da raini sama sama,ga Gadara da takama kuma yana fama da iyayi etc bashi da abokin da ya wuce Farhan,Farhan shima namiji ne kyakyawa halayyarsu daya da Ahleef yana da haske amma ba can ba,yafi Ahleef fara'a kawai,tun suna yara tare suka taso iyayensu masu kudi ne suma su Farhan, amma shi Lawyer ne.
ci gaban labari
Ahleef Zaune yake saman 3seater dake katafaren palon Momee suna hira sama sama,sai ga Niima ta shigo a fakaice ta watsawa Ahleef harara tana zaginsa a ranta dan Iska ya gama mallake musu iyaye,har ya zama shine me kudin ma, Inshaallah sai na jefashi a bakin cikin da zai bar gidanmu baki daya shege komai nasa me kyau kamar aljani to wlh duk kyansa bazan ji kaunarsa ba tunda ya mallake mana iyaye sunfi sonsa akan kowa.
Ahleef kuwa bai san ma tanayi ba, sai da Momee tace zauna mana kin tsaya masa a kai kamar me tunani,Ahleef cike da murna, wani sanyi ya mamaye masa zuciya ga Son Niima yana karuwa masa kullum,hannun ta ya jawo zauna yan mata ki huta,sannu,ya Office yana lallabata,ita kam aranta haushi kamar ya kashe ta,a fili kuma sai zuba murmushi takeyi.
Wata kyakyawar Budurwace yar 16yrs fara kwal kwal ga kyau kamar ita tayi kanta,komai nata ya kai karshe,duk inda kake neman kyakyawa ta karshe to kazo wajen wannan yar matashiya,dan lips dinta Pink shine abin birgewa, Girar nan me yawa, ga gashi yalo yalo ya kwanto a gaban goshinta har wani saje ne da ita yabi ta kasan kunnenta kadan,hancinta me kyau amma baiyi tsini da yawa ba,idonta dara dara masu kyau, abinda yafi tafiya da Imanin mutane shine Dirinta kyan sura ga Hips kamar an zana mata shi.
Faduwa tayi a kasa ta saki kuka me karfi tana shure shure da Burburwa,Wata Dattijuwa kyakyawa Ce cikin kidimewa tare da firgici tace Shukura? Budurwar tayi banza da mahaifiyar Tata taci Gaba da kukanta,Shukurata tashi zo ki fada min waye ya taba min ke ? Nan ma Shukura tayi mata banza sai kuka take,sai da tayi kukanta ta koshi sannan ta turo baki cike da shagwaba tace Inna.... Ba...ba.. Aishalle bace take min yanga akan ta siyo Tsire tana ci ni kuma baki bani Kudin na siya ba, Da sauri Inna ta Mike jikinta na rawa kamar uwarta ce tayi magana,Dari biyar ta dauko ta mikawa Shukura gashi maza yi shuru ki siyo kema kice,sai lokacin ta goge hawayenta kamar yarinyar yaye sannan ta saki murmushi tayi waje da sauri.
Misalin 15mnt Shakura ta dawo da tsirenta ta nemi waje can gefen rumfar dake gidan nan ta kwalawa Babatar kira Innaaa.....Inn...kafin ta rufe baki har Inna ta fito tana sauri,Shukura tace cike da Shagwaba Inna yi min fifita,Ba musu Inna ta fara yi mata fifita da mufici tana sannu ci a Hankali karki kone,Harshenta ta zaro waje tare da cewa yaji Inna fifita min Harshena,Inna tana murmushi tana kallon yarta abar kaunarta gashi tana fifita Harshe, Innaa.... Ruwa ki bani nasha, a randa ta ebo mata me sanyi,Inna bani abaki,ai kuwa ta Bata a baki ta sha,Dankwalinta ta cire ta jefar dashi,gashinta baki me santsi ya zubo a kafadarta Bata da tsayin gashi me yawa amma baza a kirata marar gashi ba, Bayan Inna ta gama mata komai ta koma tana aikinta sai ko Shukura tace Innaa... Zanyi wanka ruwan wankan ki dafa min, katuwar Budurwa amma kome sai an mata lafiyayya kuma,Baffanta ne ya dawo daga kiwon shanu,Da Shukura yayi arba nan ya fadada fara'arsa yace Autata ta kaina banga kin cakare ba ga Yamma lis tayi,tana Shagwaba tace Baffa sannu da zuwa,Inna nake jira ta kai min ruwan wankan, Da Sauri Baffa yace a kyale tuwon daren nan dan Allah azo a kula da yata yaran gari fes banda Yata,Inna ta fito ta hada ruwan wanka ta kai mata bayi,Bayan ta fito daga wanka ta shirya fes,tuwon dare ma tana ci ana mata fifita ko Inna ta Bata a baki taci Bata fiye cin abinci da kanta ba, Ko tsinke Bata daukewa a gidan kuma ta iya ko zata yi sai Inna tace a'a zata Bata jikinta,Idan Baffa yaga tana aiki to sai ya kwana ya yini yana masifa.
yau ma shukura ce ta nace sai ta dakawa Inna kayan miya,ta fara tana ta yi Sai Baffa ya kwada sallama,ganin Shukura na daka da masifa ya karasa shugowa haba Haba kashinta kike so ya karye ko kashi kike so ki buda mata, yarinya kamar Shukura nawa take da za a barta tayi daka,Inna tace nima bana son takeyi nayi nayi taki yarda,Shukura tace Inna na gaji zo ki karasa abinki dama idan da Sun kyaleta ma indai Shukurace sau biyu ma zata daka tace baza ta iya ba.
wacece Shukura ?labarin Auren Iyayen Shukura yayi kama dana Iyayen Ahleef nan gaba za muji.
AsmaBaffa
[7/22, 1:08 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO
2
Official
By
AsmaBaffa
Dan Jin dadin AsmaBaffa fans club and Duk Inda ta Fadi Fans.
Washe gari da safe Shukura tana ganin Innarta tana aiki amma ko tsinke baza ta tayata daukewa ba sai dai komai ma ayi mata,sai lallaba ta akeyi ta shirya ta tafi makaranta amma taki sai wasa takeyi gata da kokari amma bata maida hankali,Baffanta yana da burin tayi karatu amma taki yarda sam,har coper yake dauko mata tana mata lesson ana biyansu kudi har ta fara jin dan turancinta ta koreta tace zarnin fitsari arniyar takeyi bata tsarki,tana ss3 ta kusa gama secondary schl dinta duk makarantar babu me kokarinta amma babu me wasa kamarta da tsokana ga Kuka da shagwaba sabo da gata yayi mata yawa sabo da haka ma mutane da yawa Yar Gata suke ce mata,gata da kyau amma duk kyan nan babu wanda ya taba cewa yana Sonta a duniya ko a kauye kowa gani yake tafi karfinsa,ga shegen kyau ga Shagwaba Da tabara kowa tsoronta yake ji,yan mata kawayenta har addua suke mata Allah ya kawo sanadin da wata ko wani zata ketawa Shukura mutunci wanda zai karya duk wani abinda take ji dashi,samarin Garin ma har Meeting suke hadawa a boye za a samu wasu mazaje suyiwa Shukura fyade sabo da su kawo karshenta suna mata hassada,babanta duk garin babu me kudi da dukiyarsa gata ya daya tilo har birni ake kai Shukura tana cin kayan dadi.
Alhj Umaru shine Mahaifin Shukura,Iyayensa sun haifi yara da yawa amma cikin ikon Allah duk sai sun Zama samari da yan mata suke rasuwa,Har Iyayensu suma suka rasu tun Umaru na matashi,sai yan Uwa da yayan yan Uwa,Umaru ne kadai Allah ya rayashi har ya girma ya gaji dukiyar Iyayensa na dabbobi shanu da Tumaki,kaf rigar fulanin dake can wani daji yankin Plateu Jos,wajen tafiya kiwo a nan ya hadu da Matar da ya Aura Haj Bilkisu wacce a daji suka hadu fada ya barke tsakanin arnan Jos da musulmi an harbe kowa nata ita kuma Allah ya taimaketa ta hadu da Umaru ya kaita rigarsu wajen yan Uwansa daga nan suka fara soyayya ya auri Bilkisu,tare ya biya musu aikin Hajji suka je yafi sau biyar, daga nan Allah yasa ta samu ciki ta Haifi yarta Mace zukekiyar gaske ranar suna taci Shukura,wacce ita kadai suka Haifa a duniya ga rashin iyaye da yan uwa sabo da wannan sai suka dauki son duniya suka tattara shi kan yarsu Tilo Shukura,tun tana yarinya haka ta taso komai tace shi za ayi mata,yanzu zai siyar da shanu ayi mata abinda take so,makaranta kuwa a kauyen da ba yanda zaiyi ne amma da Birni yace zai kaita Private amma basa son yarsu tayi nisa dasu wani abu ya sameta,shi yasa ya barta a ta garin Kauye sai yake dauko mata Igbo cikin masu Nysc ana mata lesson yana biya yana so yarsa ta iya turanci,aiko dake makarantar kauye ba karatu haka Shukura da taimakon lesson ta iya karatun Hausa da rubutu ta iya rubutun turanci sama sama kuma tana dan ji bada yawa ba,sai ta Zama kaf garin babu kamarta,ko baki akayi ma'aikatan Gomnati Shukura ake kira tana jagorantarsu wajen karatu da rubutu,yayin da take zuba shagwaba da tabara ga sangarta harda tayi yawa,kowa bata raga masa bata da kunya ko kadan komai girmanka ba ruwanta sabo da iyayenta basa mata fada sai abinda take so,iyakaci suce bari Shukura ko Allah ya kiyaye gaba,ko Allah kyauta,bata cas bata as,sai umarni ma da take bawa iyayenta kamar ita ta haifosu komai direct zatace Inna tashi ki min kaza,Baffa yi kaza kuma ba musu jiki na rawa zasuyi mata sabo da kaunarta da sukeyi,Shukura tana da kirki idan taga dama sai ka dauka wata me hankali ce,gata da fara'a yanzu ta wangale baki,indai ba shagwabar ce ta motsa mata ba to bata fushi a duniya,zai wahala ka gane fushinta ko ranta ya baci,duk aikin da Inna keyi Shukura tana gani kuma duk ta iya kawai yi ne baza tayi ba ta saba da hutu,Haka ga son jin dadi,bata fiye cin abincin gidan ba sai Nama,kifi,yogourt da sauran kayan dadi su take ci ko nawa ne iyayenta bata sukeyi wasa take da kudi a kauyen,gata da kyauta yanzu idan kuna mutunci zata baka kudi ko kayan sawa,Sabo da Babanta Sutura sosai suke mata kusan kayanta ma duk na Saudiyya ne sabo da iyayenta kusan duk shekara sai sunje Makkah kuma da Shukura ake tafiya tun tana shekara 10 ake zuwa Makkah da ita,gashi ta cika 18 zuwanta Makkah sau 7,shi yasa ta dan waye ba laifi baza kace daga kauye take ba,bata fiye sa Atamfa ba duk kayanta na kasar waje ne kana na da dogayen riguna masu kyau ,yanzu idan Shukura taga dama sai tace Baffa a kaini Birni zanyi Kallo kallo da gudu zai ajiye duk abinda yakeyi su tafi cikin garin Jos har Mall yake kaita iri iri sabo da Umaru ba bagidaje bane shi sam yasan ta duniya,Haka suke shiga Mall suyi kauyancinsu su fito,idan taga dama tace Aje Kano,katsina,kaduna kusan da yawa state din Nigeria Shukura taje ta cikin birni yawon bude ido Abuja ce yanzu burinta,so take Baffa ya kaita yace sai babbar Sallah tazo zasu je tana ta murna bata da buri sama da taje Abuja shine next target nata,A birni idan taga abu bata San sunanshi ba sai taga dan gayu na gaske ko yar gayu ta karshe sai ta tambayesu dan Allah ya sunan wannan?idan an fada mata tace mene Amfaninsa?a fada mata tace da turanci fa? Nan ma a fada mata haka takeyi a birni bata shuru da bakinta komai sai ta tambaya amma indai kai ba dan gayu bane to ko kallonka baza tayi ba kawai ita baka waye ba kuma ba dan birni bane,idan kuwa ka sake ta tambayeka baka Fada ba zaka ci masifa da jaraba ga gori kayi magana ta tara mutane sabo Da Kuka zata sa ta fara shure shure shi kanshi Baffa da kyar yake lallashinta,Baffa ma Har mall idan zasu shiga da sandarsa yake shiga ta kiwon shanu ayi ta musu dariya amma ko a jikinsu, wannan kenan.
Baffa ne zaune kusa da Inna yace Inna ya kamata kema ki shirya Wannan lokacin mu tafi dake sabo da tafiya ta taso min zuwa birni cikin Kano zan tafi da Shukura tayi kallo Kallo kema ya dace ki bude idonki,Tsalle Shukura ta shiga bugawa tana Murna zata je Kano wannan zai Zama zuwanta na biyu kenan Kano,tace Baffa zamu je Shopirayit wai (ShopRite) take nufi,Baffa yayi dariya yana jin dadi Shukuransa tana farin ciki yace Yar Shopirayit din bantan uba Saura muje ki damu mutanen birni,dariya sukayi gaba daya tace Ai Allah sai na tambayi yan gayu sun fada min Sunan jakin Baban gida da turanci,dama na dade ina so na tambayi sunan Jakin Baban gida da turanci ban sani ba aiko wlh wannan lokacin sai na tambayi yan Birni,Baffa yana dariya yace ai da kin bari sai munje Abuja birnin tarayya sai ki tambaya a nan ai sunfi yan gayu,sunfi ilmi ga boko,da sauri tayi tafi ai wlh Kano ma sai sun sani, kuturin uba kai kaga wasu yan gayu Inna baki gani ba yanda suke tafiya kwas kwas,baku ga wani Namiji ba Allah dana ganshi fatarsa santsinta yasin kamar na Gansa kuka sulub sulub.
Dariya sukayi gaba daya Shukura tace cab Inna kinga wani da muka gani yana cin Nama a bakin titi suna Shan lemo a tasha cikin tashar Unguwa Uku ai kadanba Sumarsu tayi Ukun takan Baba Sumar nan da kake tarawa kaima ashe Baffa kaima dan gayu ne hhh sukayi dariya,Shukura tunaninta Sumar Baffa ma ta yan gayu yake tarawa bata San irin kauyencin yan Fulani bane wacce suke tarawa duguzum ba gyara,haka kuma da taga wasu a birni a tasha yan iskan tasha ne masu sa mutane a mota amma dake na kauye daban da taga na birni sai ta gansu yan gayu ne ma bata San yan jagaliya bane hh,yan Wiwi ma kuwa,wanda kuma take cewa me santsin fata Wani ne kawai fari amma ba wani dan gayu bane kawai dai yayi dan wankansa.
Yau asabar yau tun safe suka shirya tafiya Kano Baffa an siyar da shanu za aje birni harda Kudin dan karamin Hotel da zasu kama daki daya su Uku dama haka yakeyi Su Baffa an waye.
Baffa anci rawani kamar dagaci ga Sanda katuwa,Inna kuwa duk Wanda ya ganta zai rantse mahaukaciya ce sabon Kamu a haka kuma taci gayu,Ita kuwa Shukura ansa doguwar riga Baka ta makkah katuwa da ita amma ko gyale bata yafa ba dankwali kawai ta daura a kanta sai faman kalle kalle takeyi,ana mota tuni Inna bacci ya kwasheta,Baffa ma haka,Shukura kuwa taki bacci wai kallon Hanya takeyi har aka zo kano sai da ta bawa mutanen motar dariya yanda ta zura hannunta ta window tana nuna Abu da yatsa,Inna tana bacci taji Shukura ta daketa a baya tas Inna tashi...tashi...ki Sha kallo,kin gani ...laaaa....Baffa...kalli...wan can zuwan Wallahi babu wannan,na rantse da Allah ba wannan abin,ikon Allah...laaaaaaaa...kaga Baffa.... Inna...kalli katon gida,Baffa yace Shashasha Banki ne wajen ajiyar kudi,Kudine a ciki mu shiga Baffa muyi kallo,ana jin Shukura ta rafka Salati kunga tallan Sabulu,Fati Muhammad ce yar Film gata a sabulu shi yasa ta kara fari nima sai na siyi irinsa,nan ma ta kalli katon Symbol Wallahi ga Sani Danja ta karanta tace An rubuta Glo yeeee tallan layi yakeyi na waya yasin na gane.
Driver da conductor ana ta dariya har suka sauka ta cika motar ita kadai, kyan Shukura yasa duk inda suka ratsa sai hankalin alumma ya dawo kansu ana kallon kyawunta. Shukura ta gigice,ana sauka a tasha sai taga wani Zabiya fari marar kyau,duk kuda na binsa,jikinsa yayi wani rodi rodi,ga Hakoransa yellow,hanci kato muni iya muni,ta kalli Zabiya (albino) ta kara kalonsa ta sheke da dariya kowa ya fara kallonta a tashar,hankalin kowa ya dawo kanta amma ko a jikinta,tana ta dariya sai kuma ta kalli Zabiya ta rufe idonta tare da cewa wayyo...Allah ni bazan so wannan ba,Baffa ai wlh gwara a yoni baka kamar bayan tukunyar Inna akan na Zama irin wannan,ashe farin ma akwai na muni,me za aci da kai ta furta tana kallon Zabiya,jikinka kamar nama ga kuda sai Binka yakeyi,Inna tace Allah kyauta miki,yo Allah na tuba ko Aishalle karshen muni a garinmu me zatayi da kai,zabiya dai bai kulata ba,tace anji kunya ana birni ba a goge baki da Brush,kalli hakora na farare wulluuuuuu...ta ware masa hakora,ai ko aka dinga dariya ana Shan kallo sai Baffa ne ya fisgi Hannunta suka tafi tare da hawa Napep,tana shiga Napep tace ko ni sai na iya tuka wannan yar motar,jibeta yar karama,me Napep ya tsaya daukan wata katuwar mata nan Shukura ta saka rigima ita ba wanda zai shigar musu wannan katuwar ta dannemu a ciki,Baffa da Inna sabo da sai abinda Shukura tace aiko suka ce baza a dauki wata ba Shukura bata so,Me napep yace sai kun kara min kudi fa,Shukura karaf tace kaine matsiyaci kaje ruga kaga shanunmu da awaki ehe.Mai Napep ya mata banza har suka isa Hotel ya saukesu,Baffa ya shiga da kansa ya kama musu daki daya tal su Uku,Baffa yace su shigo dama Shukura ta saba tun a Hanya ta cire takalminta sabo da karta bata musu Hotel gani takeyi kamar gida Ne,Inna ma ganin Shukura tayi haka itama sai ta zare takalmanta suka fara tafiya sadaf Sadaf kamar Barayi ka rantse wani Glass suke takawa a hankali.
Inna ta Rafka magana ganin alhazawa da mata masu kudi suna Hutawa tace gafaranku dai bayin Allah, Shukura wayayya tace ke Inna nan fa Kamar Makkah ne bakya ganin wajen me kyau, nan Inna ta kwala sallama da takalminsu a hannu,shuru ba Wanda ya kulasu,Shukura tace sai kinyi kalkala Inna irin na larabawa yan gayu, Shukura ta makale murya tayi Sallama aiko mutanen wajen suka sheke da Dariya tunaninsu almajirai ne suka zo bara har Hotel, Baffa yazo ya Fara Fada haba Haba Bilki kamar baki waye ba Ashe zuwa Makkah da kuke na banza Ne,Nan suka bishi har dakin da aka Kama, Shukura tace wlh kamar a