Showing 96001 words to 96510 words out of 96510 words

Chapter 33 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

253

jira yaji result duk hankalinsa a tashe,Magunguna doctor ya rubuta musu sannan yace Shukura ta fito su tafi an sallamesu Amma Nan gaba zata Fara zuwa awo, da murna ta fito,Ahleef tunaninsa Doctor ne sai ya fara ganin Shukura ta fito Doctor Yana bayanta.

Farin ciki ya lullubeshi Likita ya Masa bayanin komai Ahleef sai da yayi sujjadar Godiya ga Allah,Yana ta murna Shukura ta samu ciki,itama Murna takeyi suka tafi sai da ya tsaya ya siyo magun gunan sannan suka wuce gida,part din su Umma yaja ta suka Shiga,Umma tana kitchen taji Shugowarsu ta fito tana cewa ku Kuma daga Ina ko anguwa zakuje? Ahleef Yana Murmushi tare da Sosa Kai yace daga asibiti muke mararta ya fara ciwo so muna zuwa Ashe ma Wai ciki ne da ita har wata biyu, Murmushin Jin dadi Umma tayi tace Alhmdllh Allah ya raba lfy,Shukura kunya ta kamata duk ta kasa sakewa. Baba ne ya fito da niyyar fita sai yaga su Ahleef a zaune suna kallo a Palon Umma, gaisawa sukayi ya zauna sukayi Yar Hira sannan ya fita, Umma bin Bayan Baba tayi a compound ta sanar Masa Shukura nada ciki,Murna ta kama Baba shima Addua ya kwarara sannan ya fita cike da farin ciki.

Shukura tana zaune ta zame tare da kwanciya saman cinyar Ahleef suna kallonsu Yana shafa gashin kanta Umma kuwa tana kitchen abinta.

Ahleef a hankali yace na kusa Zama Dad,Yana shafa cikinta,Shukura ta dago kanta suka hada Ido tayi Masa wani fari da Ido tare da kashe Masa Ido daya a hankali tace karfa Umma ta fito zamuji kunya,tashi to mu tafi part dinmu baza a takura min ba,Kafada ta make tare da cewa nakiya kamshin girkin Nan nake son Shaka Kuma so nake ta Gama naci sabo da tun yanzu shaawarsa nakeyi, Murmushi yayi to Bari na koma Office dama ban Gama abinda nakeyi ba,dariya tayi tace ai ka dawo kenan yau sai Kuma gobe idan Allah ya kaimu, cike da Murmushi yace kin Gama maidani Mijin tace ko Honey? Yatsunsa take Wasa dasu ta danyi dariya kadan, har Umma ta shirya Dining ba tace su suci ba suka koma Dining suka zuba abinsu suna Santi suna ci sai da suka ji su dam dam sannan suka tattara suka koma part dinsu tare da bude sabon shafin soyayya suna ta jiyar da juna dadi.

Bayan wata biyu bikinsu Niima da Latifa Yana karatowa,lokacin kuma Ahleef ya Kai Shukura Private University dake garin Abuja tana zuwa hankali kwance,yayin da cikinta ke Kara girma. Shukura ce ta dauki nauyin gyaran jikin Niima da Latifa,Ahleef Kuma shi ya musu kayan daki na gani na fada,Mubaraq matukar Dana sani yakeyi da yarsu an haifeta Bata hanya me kyau ba,Niima ma Haka kamar auren Igbo ko Yoruba sai an haihu sannan ayi biki aje da Dan dakan daddawar Miya.
Haka suka hakura da juna za ayi aure da dadi ba dadi a rufawa juna asiri.













AsmaBaffa
COPY BY ZAINAB BUTALAWA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login