Showing 39001 words to 42000 words out of 96510 words

Chapter 14 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

238

ta bangaren Momee ta shigo tare da Cewa Saudatu kizo inji Momee,Haka kawai sai Ahleef yaji haushi da yar aikin ta kira ta da Saudatu kai tsaye Ko ba komai ai dattijuwa ce da an dan sakaya sunan.
Tsam Umma ta yafa mayafinta ta wuce part din Momee.

Shukura tace zanbi Umma wajen Momee gaskiya ban yarda da Kiran nan ba is better ayi komai a idona Sabo da Momee ta canja mana fuska kwana biyu Niima ta gama zugata, Hmm kina da gaskiya muje to,tare suka jera kamar ango da Amarya, a palo suka iske Niima,Momee,latifa tare da Abba,har Baba yana wajen.
Ahleef tare da Shukura suma waje suka nema tare da zama,Momee Bata Jin haushin kowa sai Shukura Akan yanda Niima take Bata labarin cewar kwadayi ne ya kawo Shukura gidansu,Momee kuma ta tuna tun a asibiti tasan Shukura da kwadayin abinci maybe har kudi ma shi yasa tasan yanda zatayi dole ta dawo gidansu da zama ta hanyar ahleef, Gashi Ahleef yana wulakanta yayanta akan Shukura wacce a duniya suka tsince ta,sannan ta fuskanci Ahleef yanzu yafi damuwa da Saudatu fiye da ita Wanda kwanan nan suka shigo gidansu gwara ayita ta kare kawai.

Abba ne ya fara magana Alhmdllh gaba daya gashi mun hadu,Ahleef kaine babba ta dalilinka kuma abubuwa suke faruwa a gidan nan marasa dadi Wanda bamu gane gaskiyar faruwan hakan ba, ke Niima gamu baki daya a nan fada mana abinda ke faruwa,Momee cikin fushi tace Abban Latifa ba haka za ayi ba gwara farko kowa yasan waye Ahleef a wajenmu har Wanda yake fifitawa akanmu su Sani ni bazan lamunci haka ba, nan fa Momee ta refe baki ta fara kwararo labari tun farkon batan sa har zuwa dalilin da yasa suka je gidan raino suka dauko shi har jarin da Abba ya bashi ya zama me kudi zuwa yanzu komai saida ta fada, Cikin fushi Abba yace Haba Momeen Yara ina hankalinki yake,mene na bayyana jarin da na bashi,wannan gori kika yi masa kuma shi ma danki ne kuma sai da kowa ya sheda kinfi sonsa da yaranki na cikinki,kuma jari dana bashi ki Sani kyauta ne halak malak ba bashi lauyoyi Sun sheda Sabo da irin wannan ranar dama nayi haka,nasan ku mata tunaninku kadan ne abinda zuciyarku ta baku sai ku aikata, ke ai abin kunya ne aji wannan a bakinki,halayen Niima waye bai sansu ba amma kin kasa fahimta.

Ahleef yace kuyi hakuri Abba da Momee Idan na Bata muku kuma bari na fada muku dalilin da yasa bana saurarar Niima da kuma haduwata da Shukura,Haka ya basu labarin Irin wulakanci da cin mutuncin da Niima ke masa da Wanda tayiwa Shukura iri iri, sannan ya basu labarin Haduwarsa da Shukura har zuwa yau, sai ya bada labarin haduwarsu da su Umma har Baba Bayan ya gama ya kara bawa Momee hakuri.

Saudatu tare da Baba Kuka suka fara yi,Abba yace kuyi hakuri wannan ba abin kuka Bane,Momee tace sayi Shuru tunda sunzo zasu dasa mana rashin zaman lafiya a gida musamman wannan kodaddiyar ta furta tana nuna Shukura, Shukura tayi murmushi Sabo da ita Bata wani fushi sai tace kodaddiya kamar Tsohuwar atamfa fa Momee...Babane ya Katse ta da cewar wannan Ahleef dai danmu ne na jini wlh,na dade ina bincike a kansa sabo da yanda mutane ke cewa kamarmu daya,ban fadawa kowa ba Sabo da kar ace karya nakeyi, bari nayi lokaci yayi na furta yau Allah yayi,Momee tace tanan kuka Bullo kuma ? Baba shima ya bada labarinsa dana Saudatu kaf bai boye komai ba har sace Ahleef,sannan yace abokin Ahleef Farhan shine ya sameni ya sanar dani tarihin Ahleef kaf anan na gane danmu ne, karshe Baba yayiwa su Momee Addua da godiya na rike dansu da Amana, Saudatu kukan Murna takeyi kawai,Abba yace tabbas biri yayi kama da mutum Yanzu muje asibiti ayi gwajin DNA kowa ya fita daga Zargi, Momee ta zabgawa Shukura harara sannan tace muje a duba amma wlh wannan Tunda Bata neman zaman lfy Baza ta zauna a gidan nan ba, kuma Ahleef indai har ni na raineka na Isa da kai sai dai ta koma kauyensu tunda babu dangi tsakani taje can inda ta fito kuma kar naji ka kaita wani waje ka ajiyeta wlh.

Shukura batayi fushi ba duk da taji haushi sai tayi murmushi tare da cewa Momee zan tafi dama amma dan Allah kiyi tunani akan Niima ki daina yarda da zancenta karya ta shirya miki,wani murmushin mugunta Niima tayi taci nasara akan Momee an kori Shukura,Abba yace Kiyi hakuri yarinya ki koma gaban danginki kawai yafi miki mutunci, Shukura tace inshaallah Abba ba damuwa amma bari na baku lbr na,Momee tace ba sai kin fada ba bama bukatar ji,iyayenki Sun rasu mun Sani thats all, Niima tace hakane kawai ya ishemu,Abba ya harareta tayi Shuru.

Ahleef tausayin Shukura ya cikashi ransa ya baci sosai ji yake dama shi aka kora,Da fara'a Shukura tayi musu Sallama ta fita daga palon da sauri Sabo da dab take da tayi kuka,Ahleef ya mike da sauri zai bi bayanta,Momee ta daka masa tsawa dawo ka zauna, Saudatu tace kayi biyayya itama kamar mahaifiyarka ce ta fimu iko da kai a halin yanzu,Baba ma haka yace daga nan suka dunguma zuwa asibiti,kafin su tafi saida Umma ta jadaddawa Shukura ta zauna ta jirasu kar ta tafi, tunda Momee ta kori Shukura batayi adalci ba Sam ta nuna son kai suma bar mata gidanta zasuyi su tafi da Shukura,ita kuma Shukura tasan me Umma ke shirin yi dan karta kara raba da da iyaye kawai ta shirya kayanta kala biyar da komai ta dauki kudin break dinta da Ahleef ya Bata ta ajiye a hannunta dubu goma ta zuba a jaka ta dauki katuwar Yogourt me kauri tare da soyayyun naman kaji Zata dinga sha a hanya ta ta sadada ta fito kenan suka hadu da Niima Zata fita da car key a hannunta, dariya tayiwa Shukura tare da cewa ba a ja dani yarinya, Dutse kato Shukura ta dauka tayi kan Niima dashi ta rotse mata kai,Kara Niima ta saki ta fadi sumammiya jini na zuba a kanta, Shukura tace dama na fada duk ranar da zan bar gidan nan dole sai wata ta tafi gadon asibiti, na yarda zan bar gida amma dole kema kiyi gadon asibiti.

ruwan cikinta Shukura ta taka da karfi tare da tsallakewa tayi tafiyarta ta bar gidan kawai tana goge hawayenta yanzu ta daina ganin Yayanta Ahleef,Niima kuma yan aiki Sun taru a kanta ba abinda basuyi mata ba amma Bata farfado ba,Momee suka bugawa waya,Momee ta fashe da kuka a asibiti tana ka gani ko Ahleef abinda ka jawo mana gashi nan ta kashe min yarinya,Wayar Ahleef ya karba yace a kawo Niima asibiti itama, Abba yace Good yarinya tayi daidai nasan Niima ce ta tsokaneta ai hakan yayi kyau ina ma ta karyata gida uku da kowa ya huta.
Likita yayi gwaji ya tabbatar Ahleef dane ga Umma da Baba Saudatu da Amadu kowa yayi farin ciki musamman Ahleef Farhan ma yana asibitin Ahleef yace yayi sauri yaje ya dauki Shukura kar ta tafi kafin su dawo gida.

sai da Shukura ta shiga taxi sannan ta fara tunanin ina Zata je, kawai tace a kaita tasha tana zuwa ba Bata lokaci ta shige motar Kaduna state motar Bata cika ba Baza ta tashi da wuri ba Shukura ce dama farkon Shiga motar,Lokacin Farhan kuma yaci uban birki a gidan security yace ai ta bar gidan tuni, da sauri Ya kira Ahleef a waya yana sanar masa,da Sauri Ahleef ya bar su Momee gaba daya tare da fadawa motarsa ya fusgi mota a gigice Bai tsaya ko ina ba tashoshi ya dinga bi har ya je tashar da Shukura ta shiga mota saura mutum biyu motar ta cika Ahleef yayi parking motarsa ya shiga tambayar Masu mota yana bada kamannin Shukura,Wani dattijo yace ina tunanin tana waccan yellow Bus din indai kyakyawar nan ce,Ahleef ya je motar har jikin motar ta Window ya hango Shukura ciki tana shan Yogourt dinta tana hawaye,Murmushin da bai shirya ba ya saki ta Window ba zato tana waigowa ta ganshi a tsaye,tunaninta gizo yake mata sai taga da gaske ne,Murmushi tayi masa sabon hawaye ya shararo mata,alama ya mata da hannu ta fito sai ta makale kafada,dariya yayi yana yafitota da hannu ta sakko amma sai ta makale kafada, ga Hadari ya hada gab ake da fara ruwa,Driver yayiwa magana Shukura Zata fita,tace Ni Bazan fita ba Driver,Ahleef ya zaro kudi wanda bai san nawa Bane ya bawa Driver kan ya sauke Shukura,Conductor yaga kudi a banza yace kowa ya fito dole sai Shukura ta fito ta karfi,Ahleef yace duk Wanda yake motar ma an biya masa kudin mota zuwa inda zaije ya fito da wasu kudin ya kara bawa Driver,da sauri passengers suka sauka sai Shukura a ciki taki fitowa gashi an fara yayyafi,Ahleef ganin Baza ta fito ba ya shiga da kansa ya fara miko kayanta kasa conductor ya kai jikin motar Ahleef ana dariya ana shan kallonsu,hannun rigarsa ya nade ya daukota a nutse cikin dabara suka sauko kasa,Ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya passengers suka koma motarsu,ita kuwa Shukura wutsil wutsil takeyi har ta kwace a hannun Ahleef yana Damkota tana kwacewa mutane suna kallo, Shukura ta fara ihu tans zan tara ma mutane ka kyaleni wayyo jama'a a taimakeni barawo ga dan mafiya, Ahleef shima yace kuyi hakuri kanwata ce jiya aka sallameta daga asibitin Mahaukata,tana da tabin kwakwalwa,mutane suka fara Allah bada lfy ai ga alama ma ta nuna Allah sawwake yarinya Allah baki lfy kinji.

jawota yayi jikinsa har yogourt na zubo masa kadan a rigarsa kamar zai maidata cikisa ga ruwa ana shimfidawa,daukanta yayi cak amma ta fara kokawa dashi tana wutsil wutsil ruwa na dukansu,wasu da suka fake a shaguna ta glass din Windows suke ta kallonsu suna dariya,da kyar ta kwace kanta har ta zura da uban gudu cikin zafin nama ya damkota yana dariya ita kuwa ta maida abin da gaske ta wani hade fuska,jawota yayi sosai ta fada kirjinsa ya rungumeta tsam a jikinsa wani irin yanayi suka tsinci kansu ciki musamman Ahleef bai taba Jin irinsa ba sai a jikin Shukura, a kirjinsa ta lafe tayi shuru tana shakar kamshinsa ta daina Wutsil wutsil, ruwa ya kara tsugewa a hankali ta dago da fuskarta tare da zuba masa kallo na musamman Wanda dole sai mutum yaji a jikinsa,Hannunta yarike tare da furta Muje mota duk yayaninsa ya canja,kwar jini ya mata nan take ta kasa yi masa musu ta bishi suka shiga mota,sun jike sharkaf da ruwa,motar yaja zuwa gidan su Farhan, Shukura sai fushi takeyi tana share Hawaye har suka karasa gidan su Farhan.
su Umma dasu Momee saida suka je har gidan Raino aka tabbatar da komai gaskiya ne sannan suka wuce gida,Momee ta zauna tana Jinyar Niima.

a bakin gate ya tsaya tare da Kiran Farhan ta waya,Farhan yana fitowa key ya mika masa yana tsokanar Shukura ta gudu ba sallama,wani dan karamin gida Ahleef ya kai Shukura me dauke da bedroom biyu da palo sai kitchen,ba abinda babu a gidan,gidan yasha gyara Neat dashi,kayan abinci ne kawai sai an siyo,zaki iya zama a nan ? kafada ta makale tare da cewa ai tsoro zanji ka dawo dasu Umma mu zauna tare dasu,Idan har zaku Zauna tare to Umma da Baba sunfi karfin wannan gidan sai a canja muku,baki har kunne Sabo da murna zata zauna tare dasu Umma.

har mamaki Ahleef yakeyi yanda Shukura ke kaunar iyayensa sai yaji ta birgeshi ya kara wani sonta, Daukan Shukura yayi a mota tare da kiran Farhan yaje gidan Momee ya kwaso kayan Umma,Shukura tare dana Baba ya kai can guess House nasa da suka taba zama tare da Shukura,Farhan yayi duk abinda Ahleef yace har Umma da Baba ya kaisu gidan, Momee tana gani har sallama sunyi da Saudatu amma Bata ce su zauna kar su tafi ba, Ahleef tare da Shukura suka Isa gidan,Baba Murna Umma ma haka wai Ahleef dansu ne,a palo suka zauna gaba dayansu,Babane ya fara magana Alhmdllh mun godewa Allah sannan ya bude da Addua,Yau Allah ya nuna mana ranar da muka hadu da danmu na jini,Nasiha Baba yayi sosai,Umma ma Sabo da murna kasa magana tayi,Shukura tayi Murmushi tare da cewa dama na fada miki Umma kuna kama da wani kikace kar na dameki to gashi Umma Allah kin iya Haihuwar me kyau,Dariya sukayi gaba daya har Ahleef, Ahleef yace Baba daga yau Baza ku kara aikin komai ba, Ku huta kawai,Shukura tace Yaya har girki Baza ayi mana muci dadi ba? Gaskiya Umma sai tayi girki,idan naje schl in dawo naga gida rafai wannan ai ba shawara bace,to ai banda aikin gida akace ko cewar Baba,Umma ta furta kyale ja'ira sai kin fada min ta ina kuka hadu da Ahleef da kika mana karya dan uwanki ne,dama ke yar uwarmu ce ashe bamu Sani ba fada mana muji,Dariya Shukura tayi taji kunya tace ai to boye sirrina nayi shi yasa na fadi haka Umma.Hira sukayi sosai karshe Ahleef yace zai tafi zaina zuwa kullum akwai komai a gidan na amfani,Shukura Bedroom dinta ta zaba,Umma da Baba ma haka,Baba shi kam har ya fita wurin abokansa da suke zama can Zone 11,Umma da Shukura basu huta ba sai da suka kara gyara gidan sosai duk da ba Dirty sannan suka Daura girkinsu.

Washe gari da wuri ta Isa makaranta,Latifa tayi mamakin ganin Shukura tunaninta ta koma kauye Bata da gidan zama, Kallon kallo suka yiwa juna Shukura yanzu tace ta daina raga musu ko kadan dama dan Umma take kyalewa yanzu kuma Umma ta zubar da girmanta a wajenta, Sai da ta tabbatar Su Latifa ba teacher a ajinsu ta shiga ajin da gadara,Latifa na zaune Bata san Shukura ta shigo ba suna ta surutu kawai taji anci kwalarta tare da tsarge Hijab dinta gida biyu,kafin Latifa tace komai ta wanketa da gigitaccen marin da kowa sai da hankalinsa ya dawo kansu,Shukura Bata kyaleta ba ta dauki jakar Lateefa ta zazzage komai a kasa tare da Nuna latifa da yatsa Dama na fada miki bashi kika ci,Kawayen Latifa suka taso da niyyar dukanta Latifa tace kar Wanda ya taba ta Ina zuwa ta fita da sauri Hijab din na hannunta,Wajen PC taje tare da fada masa karya da gaskiya,sabo da yana karbar cin hanci wajen Niima Yace ta bari zai dauki mataki mummuna,Nan yasa aka yi sabon Assembly, kowa na schl ya hallara yace Shukura Mohd ta fito,ba Bata lokaci ta fito ta tsaya ya zayyane abinda Latifa ta fada masa sannan yace yau zaiyi maganinta ya samu bulala ya fara tafkar Shukura sai da bulalar ta kare sannan ya mikawa malamai kowa yayi mata guda biyar biyar,Shukura tace a tsaya tana da magana,kowa yayi shuru ana jiran wata maganar kirki sai suka ji tace PC dan Allah ka kara min ko guda ashirince,banza ya mata,ya fara tafiya kenan ta kwala masa kira sir ?ya juyo kuwa sai ta zaro harshe tayi masa gwalo,Pc yace stupid Mad girl, malamai Sun gama nasu sannan yace sai tayi wankin toilet har na 1wk shine Funishment nata, Bayan ya sallami Student Shukura tace wlh sai tayi maganin Latifa da pc itama.

Bayan komai ya lafa,Shukura ce ta samu wata garkamemiyar Kusa ta lallaba wajen motar PC tana Jan murfin ya bude dama bai cika rufe wa ba idan a schl ne,mazaunin Driver ta samu tare da fasa kujerar ta zira kusar kanta ya dago sama inda mutum na zama Zata coke masa Mazaunai,bayan ta gama da sauri ta bar wajen,ana tashi PC ya fito zai tafi gida ya fada motar tare da zama a kai,kara ya kwalla tare da mikewa da sauri ya fito yana danne Mazaunansa da hannu jina ya dan fito har ya nuna a rigarsa,Shukura tana labe tana kallo sai dariya take yi,bayan motarsa ya kalla nan take ya zaro ido ganin an jiketa sharkaf da ruwa da Yogourt a saman kujera,ya tambaya ko anga Wanda yayi masa haka,kowa yace Bai Sani ba.

Latifa tana zuwa gida ta fadawa Momee komai daya faru,Momee tace lallai Ahleef ya raina ni zaizo ya sameni,Niima tace Momee ki daina bata lokaci sonta fa yakeyi zai aureta.
Dalla rufe min baki ai duk ke kika jawo da kin aureshi da hakan Bata faru ba cewar Momee amma bari yazo kafin ya fara son Shukura dole zai Auri Hafcy ko Zahra,Ke kuma ya kuka kare da Mubaraq din?baki Niima ta tabe sannan tace nifa bana sonsa Momee,Allah ya shiryeki cewar Momee.
Niima wani kyakyawan yaro wanda kwanan nan ya shiga 20yrs bai dade da gama secondary schl ba, yaro dan gayu amma dan talakawa ne futuk,Niima ta nace masa taga me kyau tana sonsa sai kashe masa kudi takeyi,sutura Masu tsada, waya me tsada,yanzu mota take son siya masa Ga kudi da take bashi ko yaushe,tun yaron baya kulata sosai ganin kudi yake kulata,yanzu kullum tana yawo dashi a gaban motarta,shi yasan ta girmeshi da wajen shekaru takwas Amma Sabo da kudinta yace zai aureta sai soyayya suke zubawa abinsu,ita tana sonsa don kyansa da iya Shiga shi kuma don kudinta,Ahleef ya linkashi a kyau da komai sau yafi dubu amma Sabo da iyayenta Sun nuna suna sonsa kuma ya fisu kudi duk ta silar iyayensu Shine yasa Bata sonsa tana masa bakin ciki da hassada amma tasan Ahleef samun irinsu sai jefi jefi.tana son yaron Abdullah amma tasan da kyar idan Momee da Abba zasu yarda ta aureshi ita kuma shi take so,yaro kuma bashi da sisin aurenta tana batawa kanta lokaci,kaf dangin yaron Haneef Sun San Niima Sabo da tana kai musu ziyara tana musu wasa da kudi kowa gani yake mutuniyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login