Showing 45001 words to 48000 words out of 100341 words

Chapter 16 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

941

dariya ..

Dora kanta tayi bisa kafadarshi tare da fadin sannu da zuwa yaya...

Karan hancinta ya ja yace yauwa yar gidan Momy...

Tana dariya jin sunan daya kirata dashi ai kuwa daga idon da zatayi sukayi ido hudu da fulani .... Waro ido tayi sekuma cuwat ta yi tsaye ...ta sadda kai kasa ...

Shi besan mi ya sata yin haka ba ...se ya fara kokarin meda ita bisa cinyar ...

Nan fa ta fara tirje2 tana fadin kin ganshi ko Momy ...ni ka kyalleni..

Gumtse dariyar data taso mishi yayi ganin wai kunyar Momy takeji..

Sake mata hannu yayi ..da sauri taje kusa da Momy ta zauna kai a kasa ta kasa dagowa ..tace Momy ina kwana...

Itama fulani dariyar tayi dan abun nata abun dariya ne..tace lfy lau ya kwarin jiki ...


Murad ya ce daga baya kenan seda kika gama rashin kunyar taki zaki wani zo kisa jin kunya..
Shure2 kafa ta fara tana kukan shagwaba ..

Fulani tace a'a kyaleta daga zowa kada ka takuran yarinya...

Gwalo tashi ga yi mishi jin fulani ta goya mata baya ..yun kuri yayi kamar ze kamota ..
Da sauri tayi hanyar tolet ta tana fadin momy barin wanka ..

da sauri shima yake shirin mara mata bayan ..fulani da tayi kasake tana kallon shi ..wannan rashin ta idon har ina ....ganin fa da gaske shiga zeyi ya sa fulani tsayar dashi da fadin to barin in barmuku dakin nan ..tun kan abun yayi nisa..

Cike da shagwaba yake fadin haba Momy tayata ne fa zanyi ...saboda batada lfy ...

Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai ...

Koma wa yayi ya zauna yana ta zuba wanda duk yawancin maganar Maysam ce..

Tajima ciki har Murad ya fara korafin da mitar cewa kada fa aje ko zamewa tayi ..ko ....

Itade fulani najin shi bata tanka ba ...

Tana fitowa daure da towel dinta da hidjab .....shi da kanshi ya shirya ita...
Ya jayota ya zaunar suyi break tana kokarin serving dinsu ...Murad bako kunya ya rike hannun Maysam din yace bari na zuba mana ke da bakida lfy...

Shiyayi serving din su kuma shike bata a baki ..

Fulani a ranta tace ashe dama shakiyan cine ..zama ka iya serving din..

Ganin abun bana karewa bane se ta hau waya ..da sallama ta fara ..suka gaisa da alama de mace ce...sun dan taba hira take sanar mata da gata a likita ma matar Murad ce bata ji dadi ba .... Matar ta jajanta mata ...fulani tace yanaki jikin ...?

Tace to alhadulillah

Can kuma se ta bawa Murad wayar yana karawa bayan ya gaisheta ya shiga zuba mata shagwaba har tafi wacce yake yiwa fulani..najide ya kirata da Mom.....

Ita kuwa Mom din ta lalace wajen lallashi ...

Daga baya ya bawa Maysam wayar ya cemata Mom din SWEETBABY nace a...

Hannu na karkarwa ta amsa tana nanata sunan cikin ranta dan ita jitake yana nufin yarinyar da ze aura ce SWEETBABYN.....

Sallama tayi tare da gaisheta..

Muryarta kawai Mom taji amma seda gabanta yayi wata irin mummunan faduwa ..da kyar ta nutsu ta amsa mata ..tace ya jiki....

Tofa the same Maysam taji itama..da kyar tace naji sauki alhadulillah...

Mom tace yaya sunanki ne..

Maysam sunana se kawai ta tsinci katan ta son yi kuka wanda bata san dalili ba....

Ganin haka yasa fulani karbar wayar ..itama muryar Mom din duk ta sauya ...nan sukayi sallama ..

Murad ya goge mata hawayen da suka zubowa yace mi yasaki kuka.. ....

Babu komi kawai tace dashi

Wunin ranar anan sukayi shi...Maysam taji sauki sosai ganin Yayanta kusa da ita amma kasa zuciyar ta tana son sanin wacce ce Mom da Kuma Sweetbabyn nan....

Irin rigima ta Murad ta aka basu Sallama ya kuwa turbune sede Maysam Ta koma gidan su na nan Maradi .duk da daman wannan satin za a sake su hutun chirsmate(Noรซl)..

Fulani ma turbune wa tayi ganin in ta biye mishi suka koma gidan kada soyyayar su yasa su manta ma da ta na school.....kuma gashi tayi2 su huce tare yaki yace se ya cinye satin shi anan ...haka Fulani ta koma dan cigaban shirye2 auren ...

Murad na ganin tafiyar Fulani ya je ya doko Maysam suka ci gaba da rayuwar su irin ta yaya da kanwa masu ji da ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

Abangaren Madina kuwa taci alwashin hana auren nan tunda har waziri yaci amanar ta ....jakadiyar ta tura musamma garin su Maysam wajen Murza kan tana son ganinta..

Murza ta kuwa yiwa Malam Musa karyar za'ayi wa Maysam kishiya zata tafi amatsayinta na uwa (ni kuwa nace kode UWAR RIKO ba ..littafin Momyn Mufeeda ๐Ÿ˜)

Bangaren fulani ta sauka dan kauda duk wani shakku ..lokacin Fulani na can Maradi ma...Murza..seta saci kafa ta faki idon mutane ta shiga bangaren Madina...

Nan Madina ta kwashe duk irin cin amanar da waziri yayi musu...

Murza har kukan bakin ciki tayi wai taga samu taga rashi ..ta kuwa share hayenta tace ki kwantar da hankalin ki akwai wani sabon Boka wai shi Matsafi aikin shi shi yakan Adda ne bama wuka ba...

Madina tayi wata dariyar mugunta tace aikin ki yana kyau shiya sa nake son haraka da ke...

Kudi ta zube mata tace kuma kice a kashe mana shi ma gaba daya ..in hakan bata samu ba ...to ayi muna irin na wacen ....a tura shi can kasar da baya dawo ba... Murza ta fice ..daga nan ma wurin bokan ta fice ...kai gaskiya fa wannan yafi wacen zaman hatsabibi da shu'umanci. .....

Bayani Murza tayi mishi bayani ta zube mishi kudi.tare da gaya mishi irin aikin da suke bukata...

Wani kulli magani ya bata yace wannan a zuba akofar da shi Waziri ze tsallaka ..kuma yabata wani yace wannan kuma a zuba mishi a bun sha ....yana sha aiki ze ci dan daman kwarjini ne yake musu..

Ya basu wani yace wanan kuma a turarashi da zarar Murad ya shiki hayaki ..yanda hayaki yabi iska shima haka zeyi.....ya kwashe da dariyarr...yace ga dubara ta nunawa Waziri komi ya huce seta cuceshi daga nannnnnnnnnn..(jifa...Allah de shitya)

Cike da Murna ta kawo wa Madina wannan labari ta bata magani ta komawarta kauye cike da kayan alheri da Madina ta bata...dan har lokacin Fulani bata dawo . ...

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน ba๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
A bangaren Murad kuwa saukar QURAN ya saka ana mishi anan Maradin tare da bada kudi makarantu da massalatai dan yi mishi addu'a ganin abun akwai tambaya ciki tunda ba tun yau ba ake son ya aureta amma daya nuna bayaso ba'a matsa mishi ba se yanzu rana tsaka a tilasta mishi...shiya sa yayi haka koma de minene to yazo mishi cikin sauki....

Haka Har suka cinye satin su kullum shida yar gidan Momy...wanda yayi saura kwana takwas auren

shike kaita school ya medota ......Mufeeda da Mariam ma ba'a barsu a baya ba ..lelanta suke kamar mi..?da aka sake su ma hutu ma kamar su bita suke ji da kyar suka rabu..

Lokacin da zasu tafi so tayi taki binshi dan bazata iya jurar ganin auren shi ..amma matsa matan da yayi yasa ta biyo shi .dan dole...


Koda suka zo ma beyi wani yunkurin yin komi ba....kuma da alama ma bashi da niyyar yi

Murna kam ku san kashe Maheeba tayi ganin Murad yazo ita har ta ga an daura ..se wani d'ada'aga kai take wai ita a dole futur wife din yarima me jiran gado.


A yaune kuma Madina take shirin aiwatar da kudirin ta..


Love all fans๐Ÿ˜


Fasma ce๐Ÿ–Š
[24/07 ร  12:28] Fasma: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช



*Ho.ho.ho MIMSQUEEN hamshakiyar shahararar marubuciyar ..ina murnar tayaki karasa littafin ''KARSHEN ALEWA KASA ''hakika kin nishadan tar damu kin fadakar damu ..Rabbi ya kara miki daukaka .da Baseera tare da zakin hannu ..sosai muka ji dadin littafin nan Readers kada kubari abaku labari ...zamuyi missing dinshi ..Amma abun murna da farin ciki shine muna nan tare dake a KALAR TAWA UWAR wanda shima ya dauko dadi and other dazasu biyo baya..muna biye dake ..love you irin totaly din nan.* ๐Ÿ˜โคโคโค





Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค



๐Ÿ…ฟ69__70



```Manzon Allah (SAW) yace''kauracewar musulmi da dan uwansa musulmi kamar zubar da jininsa ne''
Ahmad ya rawaito shi``` .






Hakan kuwa akayi Madina tasa akayi mata Kiran waziri ...dede kofar shiga falon ta kuwa barbada maganin ,,,,da farko yaso yaki zuwa amman ganin in betafi ba zata iya kulla mishi wani sharrin yasa ya tafi amma a ranshi fadi yake komi za'ayi sede ayi amma bazan biye mata ba kan auren nan ...tunda aka zuba maganin aka hana kowa shigowa bare fita ....bakam2 waziri ya shigo babu wata bismillah sallamar ma se da ya tsallaka har ya tura kanshi sanan yayi ta ...(a raina nace ai kuwa hakan be dace ba kana namiji ke koma macen ..wai se ka tura kai cikin falon mutum tukon zakayi sallama..kasan a wani hali zaka tarar dashi..ne... Ko dayake may be daga wazirin har Madina basu karanci hadisin ma'aiki SAW daya ke cewa''baya hallata ga musulmi ya leka gidan ko dakin wani ba tare da izini ba..Bukhari ya rawaiti shi....
...kuma ai ita madina ta sake mishi fuska har haka)
tunda ya shigo yaji jikin shi ya saki haka ya karaso ya zauna ..

Madina ta shiga tsarashi cike da makirci da nuna cewa komi ya fice a wajenta har da nuna jin
Dadin ta ga wanna auren koma ta na goyon bayan shi kan abunda yayi

Wai shi me diya ..se kawai ya saki jiki da ita nan ya shiga ga zayyana mata yanda auran ze gudana ...

Madina daga kasa se dariyar mugunta take mishi kai daga karshe ma tace ta dau nauyin kayan dakin amariya ...
Abunda ya kara tunzura waziri da yarda da ita ....kamar gaske tasa aka kawo mishi lemo . abunka ga wanda murna ta cika shi ya ma manta da Madina ce matar Sarki ...Kawai be kawo komi ba ya bude cikinshi ya kwankwadi lemun shi .....yana gamawa sega kiran wayarshi ya shigo ...Maheeba ce da sauri wai yazo zasu kara tattauna wa ya fita tare da yi mata sallama ...


Yana fita Madina tayi wata makirar dariya tace dani kake zancen ...


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
A bangaren su Fulani kuwa ita da Sarki suna zaune suna hirar su dan tunda akayi maganar auren Murad da Maheeba ya sa Madina ta dena shigowa .akai2 ...suna tsaka da hirar Fulani tace daman akwai wata magana dana ke son muyi akan auren nan ...a gaskiya yanzu bana goyon bayan auren nan kai hasali ma nifa ban masan yanda akayi na amince ba ba ...kuma ....jiya da dare kawai nayi wani mummunan mafarki kan auren nan ...nide gaskiya a fasa tunda de ko kati ba'a buga ba bare ace garin yasan mi ake ciki ...kuma ko jiya jiya nan da safe babu irin magiyar da be munba ...kasan kuwa har kwantar da shi akayi a england ciwonshi yayi wani mummunan tashi Allah de kawai yasa da sauran kwanakin shi nan gaba ...da yanzu mun ras ...se kawai ta kasa karasa kuka yaci karfinta ..

Sarki ma hankalin shi ba karamin tashi yayi ba ..yace nima de kin sosa mun inda yake mun k'ayk'ay dan har ga Allah bazan ce ga yanda abu ya faru ba kawai de na tsinci kaina nane da amincewar auren ....amma yanzu kirawo mun shi a waya shi Murad din muji ta bakinshi...


Kallon lokaci tayi taga goma har gifta amma dayake maganar me mahim manci ce yasa kawai ta danna mishi kiran ...

Lokaci kuwa yana bangarenshi shi da Maysam se shagwaba take zuba mishi kan seya kaita shopping gobe Se burgima take ajikin shi duk ta yakuna mishi kaya..
.shi kuwa ya kyaleta ne dan yasan yanzu babu idan zashi dare ne ...kuma shi badan baze iya kaita bane a'a kawai futar ce ma baya son yi kwata2 dan baya son ya gamu da wani ma Wanda ya san zancen wannan aure ...
Suna haka kiran ya shigo shiit yace da ita ya dau kiran da sauri ganin lokaci ya san ''quelque chose ne va pas'' lamo tayi a jikin shi tana jira ya gama ta cigaba daga inda ta tsaya....

Cike da ladabi ya dauka ya gaishe da fulanin..

Bayan ta amsa tace ya zo nan fada dadyshi yana son ganin shi ....

Da sauri Maysam ta shiga ta dauko mishi wata riga .jin Sarki nason ganinshi ...kuma be kamata ya fita da rigar nan haka ba..

..lokacin data dauko har yakai kofar fita dan sauri..

..
Itama Da sauri tace yaya tsaya..

Ya tsaya tare da juyowa yana fadin minene kuma cikin fada....

Turo baki tayi tace to ba riga na kawo maka ka sauya ba..

Shi se lokacin ya tuna da rigarshi ashe duk ta yakune se kuma jikin shi yayi sanyi gani tayi fushi...karba yayi ya saka ita kuwa ta anshi waccar din tayi shigewarta wai ita nan tayi fushi...

Girgiza kai yayi ya fice dan lokacin bashi da time din biye mata...


Su biyu ne palon kamar yanda ya zata nan ya kwashi gaisuwa wajen dady ...

Sarki ya ansa cikin sakin fuska ...se kuma yace dama game da zancen auren ka ne yasa nayi kiran ka

Kafin ma yaji mi za'ace ya shiga bawa Sarki hakuri kan shifa baya son auren nan hasalima auren dole ne ake shirin yi mishi har da yar kwallarshi....

Sarki yayi jim yana kallonshi..can yace to dama dan mujine ta bakin ka ..tunda baka so baza ayi ba ..kana iya tafiya...

Nan kuma hankali shi ya tashi dan jiyake ko yayi fushi ne...ya shiga bada hakuri ..

Sarki yace a'a daman muna da niyyar fasawa ..to mun tambayaka ne dan kada aje ko ka fara sonta...

Da sauri ya kalle shi yace ..so..?fa Dady ai ni so daya kawai nayi Shima wa SWEETBABYNA.

Fulani tayi dariya a ranta tace ita kuwa Maysam din fa...kayi ka gama mude idone namu ..

Sarki yace to shikenan kana iya tafiya Allah yayi maka albarka . .

Nan fa kawai ya rumgume Sarki yana zuba godiya harda kwalar murna ...
Fulani ma ta shafi kanshi tace hankali ya kwanta ko....

Cike da farin ciki ya fice ...

Sarki ya kalli fulani yace wai ashe har haka yake kin auren nan jibi fa ko lokacin auren shi da Maysam be nuna kin amincewarshi ba haka..

Fulani tace ashede da mun cutar da dan mu da kanmu ...

Sarki yace Allah ya kara tsare mu tare da yi muna zabi na alheri aduk lamuran mu
Ameen fulani ta amsa .


Wani sauri ya ringa zunkudawa kamar wanda ze tashi sama ..

Yana zuwa ya ma manta cewa Maysam tayi hushi dashi kawai tana zaune se ji tayi yayi sama da ita yana juyi ..

Itade tana mamakin miyasa ka shi murna haka take ..

Yana sauke ta yace ''devine quoi? ''(Ci aruwa?)

Tana turo baki tayi kalar tunani ...tace na baka gari

Yace to an fasa aurena da Maheeba ....

Be gama fada bama tayi wani uban tsalle me game da ihu ta dare bisan shi tana me jin dadin wannan abun...

Nan fa dadi kamar ya kashe su ...ya kirayi Mahmud ya sanar mishi ...

Shima ba karamar murna yayi ba .

Murad yace ki shirya gobe mufita yawo ba shopping kade ba ....

E fa murna ta gamewa Maysam bibiyu ...

Can yace ta tashi ya rakata bangaren fulani ..

Nan Maysam tace bata san zancen ba ..kawai dan yayi mata wayo ne yayi tafiyarshi shi kade ya barta...๐Ÿ™„ji wani shirme....

Be hanata ba ... Ta shige dakinta na nan bangaren tayi wanka tasaka kayan baccin ta ..ta feshe jikinta da turare kamar yanda fulani ta koya mata ta nufi dakin Murad ...shi lokaci har ya kwanta tazo ta makalkale shi wai ita tsoro take ji be cema komi ba ya gyara mata kwanciya ...duk da har yau inde sun samu contact body tofa se yaji electric shok din nan sede yanzu ba sosai ba.....

Cikin dare biyu na dare Murad ya raba jikin shi da shimfidar ya doro alwala ya shiga nafilfili da addu'oi da godewa Allah kan wannan sauyi lamari daya samu .yasan daman addu'a bata faduwa kasa ..ko ba dade ko bajima ...

Wajejan uku na dare itama Maysam ganin shi yana salla yasa ta tashi ta doro alwala ta shiga nafila .

Ba su suka kwanta ba se bayan sunyi sallar asuba tare da yin azkar dinsu ....ta kuwa kara shige mishi jiki..bacci me dadi ya a won gaba da su

Wayewar gari lfy Maysam et Murad...โค


Ina masoyan Maysam ku fito mu ganku. To๐Ÿ˜..


Mi ye makomar Waziri da iyanlanshi ?kuma



Ina yinku irin totaly din nan ๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜

More you comment, more i typing ..โค


Fasma ce๐Ÿ–Š
[24/07 ร  12:28]Fasma ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช


๐ŸŽ‚๐ŸŽ‰joyeux anniversaire my sam ..wish you all the best ..que cette annรฉe soit une annรฉe de bonheur, rรฉussit et plein de succรจs.. Today is your day so profite bien.because รงa ne vient qu'une seule fois par an๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚hbd


*Ohhh Allah ashe haka masoyan Maysam kukeda yawa ...๐Ÿ˜๐Ÿ˜hakika ina alfahari da ku ..Maysam na meka dubun* *gaisuwa zuwa ga fans dinta tace tana yinku irin sosai din nan lol..Fans wly* *kuna da yawan bazan iya lissafo kuba dan se na cika page din nan .๐Ÿ˜โคโค.amma fa sako daga MUHEEBA tace kada ku sake hanya ma ta gama ku* .. *Mussaman ma ke Maman SS ๐Ÿ˜ ...Amma fa tace na gaishe mata da masoyan ta mussaman My* *Zee๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž(Zaynab Idris ba๐Ÿ˜œ) tace tana yinki* ๐Ÿ˜‚..


_Welcom back Momyn Mufeeda Allah ya kara lafy ya sa zakkar jiki ce ._ ๐Ÿ˜๐Ÿ˜
*My in law(Xaynap queen),,my Arfat,and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login