Showing 12001 words to 15000 words out of 100341 words

Chapter 5 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

922

take yimata har takai haka?to Allah ya shiryeki inme shiryiwa ce..

Kiraye2 sallah isha'i aka farayi ..Malan Musa bebi ta kanta ba ya fice mosque..

Tana gani fitarshi ta fad'a d'aki Maysam na sallah lokaci se jin saukar dorina tayi nan ta dinga jibgarta harta kaita kasa ..ita kukan azaba ita kukan bakin ciki..

Ta rasa miza tayi se kawai ta kama dantsen Maysam ta gantsara mata cizo har sau ukku har ta fitar mata da fata tace walahi baza ki tab'a auruwa ba ..senayi duk yanda zanyi na hana wannan ma..

Wani sabon kuka ya zo mata ta d'aga hannun da niyar kaymata mari taji Sallamar Malan Musa da sauri tace yi mun shiru munafuka sauran ki gwada wani alamu har malan ya fahimci nayi miki wanin abun (kuji fa keda yau har da cizo)...

Maysam kam kwna kuka tayi da ga bisani ta dauro alwala ta rinda jero nafilfi tana roqon Allah ta mata zab'i na alheri

Murza kuwa kwana tayi tana neman mafita shawara kawai ta yanke taje wurin boka ya hana auren tunda tasan sharri baze yiyu ba tunda sunga irin wahalar da tasha a hannuna..da wannan shawarar ta kwana

Washe gari kuwa tayi waMalan Musa karyar zuwa gidan su ta kuwa fice han se wajen boka ''yankan wuka''

To fa Fans ya kuke gani zata kasance ?Murza zatayi nasarar hana auren nan?


Yau ba yawa kuyi hakuri da wannan ..je vous aime tous❀😍


Fasma ce✍
[9/4 09:21] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
( 🏠_Home of spécial &extraordinary writers_ )

S.W.A

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ


πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

Dedicated to all my fansπŸ˜πŸ’‹

πŸ…Ώ. 19__20

Manzon Allah ( ```SAW) ya ce''babu wata musiba da zata sami musulmi sai Allah ya kankare masa wani zunubi shi da ita har ma qaya da zai taka ta sokeshi yaji zafi''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.```



Zaune take gaban wani bakin mutum ba kyan gani shi kanshi abun tsoro ne ...dagashi se d'an pante irin na mutanen da d'in nan ..kan wannan gashi buzu2 duk ya cikukuye ..se wani uban ja da hakoran shi suke da..wai shi'' Boka yankan Wuka ''

Murza kuwa ki kyenkyamin shi bata jiba ..ta zauna tana zayyano mishi duk irin abunda take bukata .....

Buga kasa yayi yayi wani d'an tsubuce2 shi ..ya jima... ya d'ago kanshi ya kalleta a ranshi yace idan na fad'amata gaskiya aikin nan baze yiwu ba tana iya zuwa wajen wani bokan yaci kud'intan a banza dan yaran da take son ayi mata aiki akansu sun riqe addini wani mugun abu baze iya kamasu ba Allah ya karesu ....

Se kawai ya kece da wata arniyar dariya yace aikin da kike so ba baze yiwu ba aure ba fashi sede a saka tsanar ta a zuciyar shi bayan auren ya saketa...

Jimm tayi tace babu abunda za'a iya yi baya ga wannan?

Wannan shi kad'e ne taimakon da zan iya yi miki kuma ko kinje wani wuri kud'in ki ne kawai za'aci..

Shikenan amma asa harda dukanta ya ringa yi...

Wata dariya ya sake yi se kuma ya daure fuska kamar bashi ba yace bakida matsala kud'inki dubu goma ne

Kud'in kawai ta fiddo ta aje ..ya bata wani kulli magani yace a zuba a abinci ko ana sha a bawa yarinyar...amma ki tabbatar bata yi bismillah ba

Se wani washe baki take ta ansa tana zuba godiya kamar kyauta ya bata ..

Cike da farin cike ta dawo gida ...ta tarar Maysam ita kad'e a gidan..

Kusa da Maysam ta zauna da sauri tayi tsaye tana fad'in inna sannu da dawowa...

Yawwa jeki tatso min nonon shanu ki kawo..

Batayi gaddama ba ta tafi amma a ranta fad'i take lafiya inna yau bata zagen ba bata rankwashen ba .....

Bayan ta kawo mata Murza tace zo zauna kusa dani ita de mamakin abun take ..
Kulli maganin Murza ta fiddo tace yauwa ga magani nan na anso miki wurin inna ta ...na tsari ne da kuma mallakar miji ..

Itade Maysam kallon ikon Allah take..

Zubawa tayi ta motsa shi tace ungo shanye shi duka

Karb'a tayi dan ba yadda ta iya tana tsoran taci na jaki in bata shaba ...

Bismillah tayi a hankali takai kwanan bakin ta ...

Murza jitake yanzu ne zatayi bismillar se kawai da karfin tsiya ta kama tayi mata d'ure(ee kin makaro Inna Murza dan tayi bismillah tuntuni😜)

Har kwarewa Maysam d'in tayi

Amma ko ajikin Murza ita murna ma take burin ta ya cika...


Ana sauran kwana goma Fulani ta turo jakadiya wacce zata koya mata tafiya dariya ,,magana da ka'idodin gidan sarautar kuyangi kuwa zasu ringa ringa bata labarai da ze sata nishad'i ..dade sauran su ..se kuma wasu mata guda biyu wanda aikin su kawai gyaran jiki ciki da waje...

Kan kace mi Maysam har ta fara canza kala fatar nan tayi laushi ga wani d'an banzan kamshi da jikinta ke fitarwa..gashintama ya qara tsawo abunka da farar fata se ta qara yin haske kyawunta da yarintar ta suka qara fitowa .duk abunda ake koya mata kuwa dan dana ta haddace su ..

Bakin ciki kamar ya kashe Murza dan ganin Maysam din ma wuya yake mata bare ma ta samu daman dukan ta sede ta shiga d'aki tayi ta rusa kuka (kujiye min
wani karfin hali)

Malan Musa kuwa yana iya qoqarin shi na gani ya fitar da y'ar shi kumya dukda Fulani tace ta dauke mishi nauyin komi ai diya za'a kowamata ba surika ba..

Yaji dad'in yanda suke nuna kaunar su ga Maysam amma ai wannan baya nufin ya nad'e hannuwa yaki yin komi ba..

🌹🌹🌹🌹.

Yarima Murad kuwa ana sauran satin ya diro ..sosai Fulani sukayi farin cikin ganinshi amma fa shi auren baya gaban shi ...har fulani na tambayarshi event nawa yake so ayi amma se cewa yayi baza'a yi ko daya ba ..a ranta tace be hakura ba kenan...

Tundaga haka bata sake mishi maganar auren ba seta nemi babba abokinshi me sunan MAHMUD ta bashi katin auren ya rabawa sauran abokanan su..shi kanshi yayi mamakin dan ko cikin wasa Murad be fad'a mishi ba..nan ya fara raban katin har abokanan su da sukayi karatu tare seda ya kaimusu...

Shi kam gogan aka ma be kawo ba kamar ba aurenshi ne za'ayi...

Haka Mahmud ya tsara event kala biyu na gani na fad'a ....ranar auren da yamma ayi walima dan ga nan kuma a fice paty da dare..


Yau har gobe daurin aure duk inda ka gilma a masarauta zakaga ana ta shirye2....

Waziri naga ya shiga part d'in Madina na kuwa mara mishi baya..zama yayi ya kwashi gaisuwa tare da zuba mata kirari...

Hannu ta d'aga dan danan kuyangun suka basu wuri...

Waziri yace na zone naji a ina muka kwana da maganar mu wacen time d'in kince mu jirayi dawowarsa ..amma naji har yanzu shiru shine na biyo sau..

Dariya tayi ta dauki apple ta fara ci cike da isa tace kada ka damu gobe yi warhaka ana ta'aziyar yarima..(se kace ran a hannunta yake)

Gyara zama yayi yace fahimtar dani yanda zan gane...

Apple d'in ta aje tace kamar kullum danake sawa a fidda mishi Birkin motarshi to yanzu ma haka zansa 'ayi kasan kuwa duk ACCIDENT d'in da yakeyi nice nake haddasa shi amma d'an jaraban yaki mutuwa ..so d'aya nayi nasara shima ba wata ta 'azo a gani bace ...
Idan kana tune shekaru tara zuwa goma da suka huce sunyi wani Accident a hanyar su na zuwa kai taimako kauyika..

Kwarai kuwa ni kuwa nake tune dashi wanda shine Sanadin da Murad yanzu kwata2 baya sakin fuskar shi bare har yayi dariya SANADIN ACCIDENT d'in ne ya fara yiwa mutane rashin mutun ci da wulakanci yade na shiga mutane..inde kaga dariyar to yana tare da makirar Uwarshi ne ....

To ai nice nasa aka datse musu burkin dan suyi Accident su miuu baki daya amma cikin rashin sa'a yarinyar nan ita kade ta mace....

Ashe kin dade kina farautar ranshi..

Wata dariya tayi tace ai huce nan tun yana cikin mahaifiyar shi naso kashe shi aman dayake me taurin kaine kamar na uwarshi se yaki mutuwa..

Dariya shima yayi yace aikin ki yana kyau Allah nuna muna gobe ..za mu kwashi shokin mutuwar shegen nan..

Sosai ma kuwa ......nan ya fice cike da zumud'i..



Zaune yake a gaban fulani se kukan shagwab'a yake kamar yaron goye ..

Fulani tace wai ni halan kuka baya maka wuyane ...daga zance shikenan se ka zauna ka azan kuka..

Matsowa yayi ya daura kanshi bisa cinyar ta yace Momy ba naki maganar ki bane ......ina tsoran wani abun ya kuma sake faruwa dani .........a duk sanda na dauki hanyar zuwa wani kyauye to kamar ina tarbar ajalina ne....a duk sanda na dauki hanyar se nayi Accident kuma ko ba'asa mu wanda ya mutu ba se ansamu rauni me tsanani ....ki duba fa na kwanan da nakayi har muka kad'e yarinyar nan harda karaya ....kaf motocin sun tsaya amma banda tawa ..ba kiga awata motar na dawoba ...lokacin dana tambayyi driver cewa yayi burkin ne ya cire alhali ana gobe tafiyar seda aka dubata komi normal haka kuma duk sauran Accident din ma matsalar burki ne...ina kyautata zaton wani ne yake son ganin bayana ...

Da sauri ta rufe mishi baki tace zato bashi da kyau ka bari kasamu preuve tukon ka fad'i haka kada nasake jinka ..Mazon Allah SWA yace 'ku kiyayi zato ,lallai shi zato shine mafi karyar zance''ruwayar Bukhari da Muslim.

Shikenan Momy Allah ya shige mana ga ..

ameen.tace..idan zaku tafi ka shiga motar Dadyn ka ku tafi tare .shikenan rigima ta qare ko?...

E yace,,se kuma yace waini Momy wace yarinya ce ma?

Shafa kanshi tayi tace yarinyar daka kad'e ranar nan itace ..matar daza aura..

Whattttttt yar qauyen nan ..qazama da'ita ?haba Momy walahi kun kare dani..

Murmushi kawai tayi tace yaro2 ne koda d'an giwa ne...


Washe gari takama samedi''saturday'' kuma ranar daurin aure tun shidda na safe aka kama hanya idan Murad ya shige motar Da Dadyn shi yake ..Waziri kamar ya hade zuciya ganin plan dinsu ya sha ruwa...aman se yayi kwafa yace ai da amariya zamu dawo dan haka a wata amotar zasu dawo ...se suyi Accident d'in ma tare su mutu kowa ya huta..

Takwas ma acan tayi musu nan aka yi musu tarba ta kirki inda kaf yan gari suka girgiza da wannan al'amari ga babu bakin magana ......

Tara(09) dede dubunen jama'a suka sheda auren Maysam Malan Musa tare da Murad Alh Mustapha ...masu murna nayi shide gogan fuskar nan ba annuri dan ma Mahmud na ta tausar shi.. Bare ma inya tuna wai shi akayi wa auren dole kuma da y'ar qauye ji yake kamar yayi fifike ya ganshi England wajen aikin shi... Haka yan bakin ciki ma nayi ..dan Murza rufe kanta a d'aki tayi ta tunga rafsa uban kuka......ho ho ho Murza se haushi .Maysam tayi miki nisa 😜😜.



Mu had'u a shafi na gaba dan jin yanda zata kaya..


Fasma ✍
[14/4 23:40] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
(🏠 _Home of spécial &extraordinary writers_ )


🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ


S.A.W✍


πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ


*Ina me bawa fans d'ina hakuri na rashin jina kwana biyu hakan ya faru* *sakamakon wani* *uzuri daya taso mini da fata zaku fahimce ni .. ..ina sonku irin sosai* *d'in nanπŸ’‹πŸ’‹*

*Gaisuwa da jinjina masu tarin yawa ga yan* *kungiyar mu na Star W.A...gaskiya ina* *alfahari da ku mussaman ma*
*Momyn Mufeeda* 😍
*Ummu Usman* 😘
*Arafat* πŸ’‹
*Mimsqueen* ❀ *Queenbaby my in-law πŸ‘Έ(i miss* *you so much Allah de yasa you are fine..)*
*Allah ya qara had'a kanmu gaba daya ina sonku irin* *totaly d'in nan..😍😘*




Dedicated to all my fans.


πŸ…Ώ 21__22


```Manzon Allah (SAW) ya ce''an halicci zuciya tare da dabi'ar son duk wanda ya kyautata mata da kuma kin duk wanda ya munana mata ''
Baihaki ne ya rawaito shi``` .





Bayan d'aurin aure me martaba sarki da sauran tawagar suka dau hanyar komawa yayinda su yarima zasu jira su tafi da amariya ...jiyake kamar ya had'e zuciya ya mutu ga tsoro duk ya cikashi tunda su sarki suka tafi yana tsoran kada suyi ACCIDENT a hanyarsu ta komawa...

Mahmud de se hakuri yake bashi yana sashi yana yin yaken dole duda ba wata dariya bace yake yade d'an saki fuskar ...zaune suke kasan wata bishiya me tarin ni'ima an cika musu gaba da kaya makulashe da fruits iri2.....

Waziri kuwa dan munafunci se yaki bin su sarki wai acewar shi shi ze kula da yarima ba yanda sarkin dogarai beyi ba kan shi waziri ya tafi da sarkin shi se ya tafi dasu Yarima Murad d'in ..amma kimimi waziri yakiya ....

Zowa yayi ya zauna a kusa da yariman ya d'anyi mishi kirari yace cikin wace motar zaka koma dan nasa a duba inkomi is mormal cewar Waziri kenan ...

Seda ya d'an dau lokacin kamar ma baze amsa me ba se kuma yace cikin bakar Prado ....

Da sauri waziri ya miki yana fad'in an gama ranka shi dade... Ya fice yana dariyar mugunta ..
Seda ya faki idon jama'a yayi kamar yana duduba tane ashe daga nan ya datse burkin motar amma ba duka ba dan kada a gane a ranshi yace ai daga kai har amariyar taka a lahira zaku angonce har wata waka yake cike da nishadi ...

Har hakurin yarima ya fara qarewa suna zaune kusan awa guda suna jira ...

A cikin gidan kuwa Mlm ne yake tayi wa Maysam nasiha bisa zaman takewar aure ...yi nayi bari na bari ....yiwa miji biyyaya binshi sau da qafa kai da duk abunda ya shafi aure ..hakkishi shi da hakkita duka seda Mlm ya fad'ima Maysam ..

Ita de banda kuka babu abunda take har shima seda ta sashi kwalla ..haka aka lulub'eta aka fito da ita ...
Ganin haka yasa su yarima tasowa dan ya matsu ya bar kauyen nan kamar yayi fuffuke yake ji ..

Already duka motocin an jere su a kofar gida...

Mahmud ne ya nuna motar da za'a saka amariyar amma mi?kimimi Maysam taki shiga motar anyi2 aman taki ko motsawa daga kofar gidantakiyi

wannan abu bakaramin b'atawa Murad rai yayi ba jiyake kamar yaje ya rufeta da duka tsaki kam yaja yafi a kirga..

Mlm Musa yazo ya kama hannun nata har zata shiga motar se kuma taja da baya mlm Musa yace haba Yar Abba ba ki gani kina b'ata musu lokaci ne...

Bata ce komi ba se kawai ta fara tafiya kowa ya tsaya yana kallon ikon Allah... Motar dake gaba da wannan prado ce itama amma fara taje ta shige ta zauna abunta ta cigaba da kukanta..

Ran yarima Murad inyayi dubu ya b'ace idon shi har sun fara canza kala zuciyar nan se tafarfasa take .dan kuwa a motar daya kad'e ta ce ranar nan taje ta shiga .a ranshi yace mi take nufi yarinyar nan ne ai de bani takeso na isketa ba ..?

Mahmud ya katse shi da fadin calme toi mana kowa yana kallonka kayi hakuri ka shiga waccar d'in mutafi dan kada mutane su fahimci cewa baka son auren kuma ma umarnin Momy ne cewa ku tafo cikin mota guda

Ba yanda ya iya tunda yace umarnin Momy ne..

Zagayo wa sukayi shida Mahmud zasu duka dan gaisar da mlm da sauri ya rikesu yace a'a base kun kai kasa ba
Nan ya d'an yi musu takaitacciya nasiha sanna yace ya damka mishi amanar yar shi ..

Sosai jikin Murad yayi sanyi ..

Murza na leke daga kofar gida se sharb'ar kuka take a rantan tace yanzu wannan kyakyawan ne mijin Maysam ga kudi ga sarauta ..kai walahi da sake wai ambawa me kaza kai..

Da gudu ta koma gida tana kukan bakin ciki da yawa sun tausaya mata dan a jiinsu kukan rabuwa da yarta ne takeyi..

Kamar da wasa ta yafo mayafinta wai itama rakiyar amariya zata babu wanda yai yunkuri hanata ta kuwa shige wata mota tayi kane2 a ranta tace ai se naga kwakwaf...

Mlm musa girgiza kai kawai yayi ya kyale tane dan yasan yanzu Maysam tayi mata nisa baza ta tab'a gigin tab'ata ba dan kuwa kafin auren ma wuyar gani take mata duda suna gida guda tayita mitar har ta gaji..

A gefen waziri ma kamar yayi kuka dan takaici Maysam ta b'ata mishi show shi har ya hango yarima cikin makara a ranshi yace aman yarinyar. Nan tacika magulmaciya.kwafa yayi yace ai yanzu aka fara
Wasan

Koda ya tunkari motar yaji zuciyar na b'aci tuna abunda Maysam tayi mishi yanzu a zuciye ya bud'e ya shiga motar kamar wanda ya aka hankad'o shi se huci yake.. Yace ke d.....

Kuyi hakuri da wannan...
Ku biyo ni dan jin yanda zata kaya ..nice taku har kullum

Fasma✍
[16/4 00:22] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
( 🏠_Home of spécial &extraordinary writers_ )


🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

S.W.A✍

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

πŸ‘πŸ‘ *jinjina gareki Momyn Mufeeda ina tayaki murna* *kammala littafi ki* *na UWAR RIKO part one da kuma fara part two hakika kina nishad'antar* *damu da fadakardamu ...Allah ya qara* *miki basira nikin banikin ...ya qara miki hazaqa da zakin hannun* ....
*Ina yinki irin sosai d'in nan ......*
*Muna biye dake se mun jiki a* *part two πŸ‘fans kada ku bari abaku labari ....je t'aime beaucoup ❀😘*


*Fans din Sanadin Accident ban* *manta daku ba alherin Allah ya kaimuku a duk ina kuke ..ina jin* *dadi yanda kuke *bibiyar* *book d'in ..Allah ya bar kauna ...je vous aime tous* *irin totaly d'innan* β€πŸ’‹


Dedicated to all my Fans ..❀😘


πŸ…Ώ23__24



```Mazon Allah (SAW)ya ce''Babu wani daga cikinku wanda aikinshi zai shigar dashi aljanna,haka nan babu wanda aikinshi zai tserar dashi daga azabar wuta ,har ni kaina sede don rahamar Allah''
Muslim ne ya rawaito shi.
```






Kamar wanda aka hankad'o shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login