Showing 21001 words to 24000 words out of 100341 words

Chapter 8 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

918

ya washe wasu hakoranshi yace ai yanzu aka fara mu gama da wannan se musan yanda zamuyi dashi nan gaba...


Wajejen uku na rana waziri ya turara hayakin a kofar shiga lambu sannan ya kasa ya tsare ya hana kowa shiga. Ya zauna nan yana gadin wurin


Har lokacin isowar yarima murad tareda dogarai da kuyangi ...

Shikam waziri ya zube nan yana kwasar gaisuwa tare da zuba mishi kirarin da be kai zuciba...

Hannu kawai yarima ya daga mishi ya sa kai ze shiga lambun



To fa fans ya kuke ganin zata kaya??asirin nan ze kama Murad kuwa??



Fans ku kara hakuri dani ayukane sukayi mun yawa da zarar komi ya lafamin zaku ringa jina akai2 kuma mai yawa in sha Allah

Nice taku har
kullum๐Ÿ‘‡




Fasma ceโœ
[24/4 22:12] Fasma๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช



Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค

๐Ÿ…ฟ 35--36


```Manzon Allah (SAW) ya ce "lallai su malamai magadan sune Annabawa ,sun gadar da ilimi,duk wanda ya same shi ya samu babban rabo "
Bukhari ne ya rawaito shi.```




Hannu kawai yarima ya d'aga mishi yasa kai ze shiga lambum...

Amma me se kawai yaji kamar a mafarki ana kwala mishi kira seda gabanshi ya bada ras jin wata murya me shige data babysweet dinshi na kiranshi da Yaya da sauri2 cikin zafin nama ya juyo se kawai ya ga yar qauyen nan ce Maysam wani turnikeken bakin ciki yaji ya rufe ya kuwa d'aure fuska tumau ...

Cikin sauri dogarai da kuyangi suka zube nan suna Allah ya huci zuciyar ka yarima dan sarki jikan sarki ...blabla dan kuwa ranshi yayi matukar baci


Itama Maysam data kula da haka se taki isawa wajenshi ta zube daga inda take tana Allah ya huci zuciyar ka idan ranka ya bace.dama Fulani ce take neman ka yanzu..

Gadan2 ya nufota
Ai kuwa tace kafa minaci ban baki ba ta zabga da gudu se bangaren Fulani ....

Ranshi in yayi dubu ya bace kamarshi ace an aura mishi wannan yar shilar banda shirme kauyenci yarinta babu abunda ta iya shi walahi yaga ta kanshi banda auren dolen da aka yi mishi a memakon a samu babbar yarinya wacce tasan ciwon kanta koba komi zata iya fidda shi kumya cikin abokanan shi se kawai a aura mishi wannan aba... shifa yanda take gudu kamar ba Gimbiya matar yarima dan sarki ba ...mtss yaja dogon tsaki
Harze shiga lambun se kuma ya tuna da tace Momy na nemanshi...se kawai ya juya ya nufi bangaren Fulani fuskar nan ba annuri..


Takaici be gama kasheshi ba seda ya tarar da Maysam tayi daidaya a cinyar Momy se kwasar firarsu suke kamar ba surukai ba ..kwafa yayi tare da zama gaishe da ita kawai yayi ya ci kip...

Murmushi Fulani tayi tasan wannan bacin ran har da kishin Maysam data kwanta a cinyar sa.....

Maysam kuwa da tun shigowarshi taki ta kalleshi ma bare taga irin mugun kallon dayake watsa mata..

Fulani tace Murad2

Da sauri ya d'ago kanshi yana kallonta

Tace ya maganar karatun Maysam ne ??ka b'ullo da zancen kuma kayii shiru gashi har kana shiryen2 tafiya ...

Dan sosa kai yayi yace tana nan Momy..

Nasan da haka inaso nasan wacce makarantar ka zab'a mata ne? ?

Shifa beyi wannan tunanin ba ....yace Momy nace ba da wai a sakata a makarantar kwana ..

Waro ido tayi tace ban gane makarantar kwana ba...kada ma ka tada zancen nan dan me martaba ma baze amince ba..

Maysam ma seda ta tashi ta zauna tana wuwurga ido amma jin abunda Fulani tace yasa tasaki ajiyar zuciya ..


Murad ya marerece fuska yace haba Momy miye aibun makarantar kwana kuma fa ta nan kusa wato ta birnin MARADI za a sakata ......idan bata ganinku zata fi zagewa tayi karatu kuma makarantar ta Abba Mahmud ce ..

Jim Fulani tayi kamar me tunani

Da sauri yace kin kwantar da hankalin ni zan sanarwa da me martaba ...

Nan ta dan saki sukaci gaba da hirar su ..

Maysam de badan taso ba tade yi shirune kawai..



Yayi tsaye ya faki idon Momy ya zabga ma Maysam mugun kallo yace Momy a bawa yarinyar nan tea takawo min ina b'angare na...kan tace wani abu ya fice abunshi


Seda cikinta ya bada kululu jin Fulani tace ta shiga cuisine ta d'ako tea ta kai mishi..

Ita baza ta iya yiwa Fulani gaddama ba bare tace a 'a bazata jeba

..ba yanda ta iya haka ta d'oko ta nufi bangaren gabanta na bada fat2.....a ranta tace yau kuma ko wace muguntar zan tarar duba da irin kallon kad'e dayake mun yau kam seta Allah...

Ta jima nan tsaye taga tana b'atawa kanta lokaci se kawai tayi karfin hali ta shiga. ....





๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน



A bangaren waziri kuwa ba karamin bakin ciki yaji ba ga maganin duka ya turara wai dan ya kama Murad sosai har kwalla seda yayi saboda takaici Maysam kam ya tsine mata yafi cikin kwando ..


Haka ya lallab'a jiki ba karfi ya tafi bangaren Madina wacce take jiranshi tun tuni tana so taji in maganin yaci...

Nan ya labarta mata itama jitayi kamar ta mutu dan takaici tace wai wannan wace irin jarabace haka ..amma ba komi ka saci jiki yanzu ka tafi wajen Murza inda akwai ragowar maganin ta baka idan kuma babu to ta kwatanta maka wajen Boka se ka tafi ko zuwa gobe ne....

Nan waziri ya saci jiki se likitar da Murza take ya koyi sa'a Malam Musa baya nan...

Murza kam har tafisu shiga damuwa .jin wannan zance ..ta shiga tsine ma Maysam tare da surha mata zagi da kyar . tayi mishi kwatance. wurin Bokan.. ya tafi da yar murnar shi...


Je vous aime mes fans โคโค๐Ÿ˜


Fasmaโœ
[27/4 00:07] Fasma๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช


*Ban manta dake ba yayata takai na SARAH ina alfahari dake* *Allah ya bar kauna da zumunci ina yinki irin sosai dinnan* ๐Ÿ˜โคโค๐Ÿ’‹

*Up up up STAR .W.Aโœจ โœ hakika ina* *alfahari da ku yan kungiyar mu musamman ma*
*Antyna Momyn Mufeedah* ..๐Ÿ˜
*Hadjara (Arfat)* ๐Ÿ’‹
*Mimsqueen* โค
*Ummu Usmane* ๐Ÿ˜˜ *(i miss you keda* ๐Ÿ‘‡)
*My in-law Queenbaby* ๐Ÿ‘ธ ..
*Allah ya qara hada kammu ina kaunar irin totally dinnan* ๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜.


Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค



๐Ÿ…ฟ 37--38


```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya na daga alamar kyawun musulunci mutum ya bar bin duk wani abun da bai shafe shi ba "
Tirmizi ne ya rawaito shi.
```





A bangaren Maysam kuwa tana shiga falon da sallama a bakinta amma setaji shiru wata hamdalah tayi tare dasakin murmushi jin dadin dabata taras dashiba isa dining tayi ta aje mishi tea din sum2 cikin sauri tayi hanyar futa amma mi se taji yace ke zo nan...

Dan danan dariyar jin dadin data ke ta gushe ta tsaya cak ta kasa gaba kuma taka sa yin baya ...

wata uwar tsawa ya daka mata dan tsoro bata san lokacin data zube nan ba dan kafafuwanta gaza daukar ta sukayi dan ta razana sosai ...da rarafe ta isa inda yake tuni har kwalla ta cika mata ido. Tayi kalar tausayi

Se kawai yaga kamar sweetbaby shi idan tayi b'anna wato idan tayi laifi ko kuma idan taji tsoro ....

Runtse idon shi yayi wata zuciyar tace ka tausaya mata mana ko dan tana kama da babynka...

Wata zuciyar tace mishi a a kada ka raga mata ai dan tana kama da ita ne ma ya kamata ka bata wahala kamar yanda take ba zuciyarka duba da tun da tashigo rayuwarka ta tado maka da ciyon daya dade da warkewa ....beyi wata2 ba yabi umarnin zuciyarshi ya zare belt dinshi ya zula mata daya yace wannan na qara hawa cinyar Momy ne

seda ta gantsere saboda zafi.

Ya dadage iya karfinshi se qara mata ...
Mi Maysam zatayi da gudu ta shige jikin shi ta cukukuye shi

Wani mayan shock yaji gaba daya jikinshi ya saki yayi tagal2 suka zube bisa kujerar palon ...

Maysam wacce tun dazu idonta ke rumtse se yanzu ta bude su jin sun zube ..

Waro idon tayi ta kama bakinta ...

Shi kuma gogan sandarewa yayi sakin baki da hanci yayi ya zuba mata ido bako kiftawa itama Maysam din kasa janye idanunta tayi dan ta tsorata jiran hukunci kawai take

Sun jima a haka ita tana son tserewa amma gogan ya kasa ya tsare ya riketa da hannushi ...kuma ya fada kogin tunani.....

Mutsu2 da take ya dawo dashi da sauri ya tureta taee da hankada ta lokaci guda kuma ya daka mata tsawa ta fice mishi a daki ..

Gaba daya ya gigita ta ..tama rasa ina ne kofar fitar seda taga ya taso ya nufo ta cikin tsawa yake fadin "je dis sors de ma maison "

da gudu ta fice kan kace mi har ta isa bangaren Fulani se haki take ..nan kofar palon ta tsaya tana meda numpashi seda taji normal tukon ta shiga "heureusement"(luckily) Fulani bata palon direct room din ta tashige a ranta tayi hamdalah da Allah ya kubutar da ita a hannunshi da taci na jaki yau ta shafa bayanta tace nasan kila da ya qara min wata da bayan nan ya gama moruwa.....


A bangarenshi kuwa rasa abunda yake mishi dadi yayi kwata2 yarinyar nan ta haddasa mishi fadawa tunanin babynshi a ranshi yace kai dolema na kaita school gobe2 nan ko zanma dena ganinta kwata2...yaja dogon tsaki mtssss



Washe garin kuwa suka kama hanyar Maradin dayake tun a daren ya sanarwa Fulani da me martaba a cewarshi wai an tsere mata a karatun dan haka gwara ta tafi kota cin munsu

Tun adaren tashirya kayanta tsaf akwati ukku manya komi na bukata ta dauka wanda kuwa bata da se gobe yarima ya kaita shopping .

A shopping dinma tsayawa tayi bata dauki komi ba seda taga Murad yayi mata jan ido tukon ta dauki mai da turaruka shima bawai dan batada suba aa kawai dande tsoran fadan yarima

Shikuma wurin kayan ci ya tafi yasa yaran wurin suna jidowa kamar madara lipton Milo etc...komi a wadace ya saye dan Momy seda tayi mishi kashe kwakwara kafin su fito

Haka ya biya kudin aka jida musu a motar da kuyangi duke suka fice se Maradi.

Yana tuki a ranshi yace ya akayi bega yarinyar nan ta dauki pad..wata zuciyar tace mishi peut etre (may be) bata faraba ma..yace amma walahi angama dani (jifa to mi ruwanka ciki kawai iyayi๐Ÿ˜œ)

Juyowa yayi yana kallonta ..ita kam se sharara bacci take ..besan lokacin dayace bacci nayi miki kyau...se kuma yace to mi ruwana ciki..tsuka yaja ya cigaba da tukinshi...(kadeji da gulmarka ehe)

Tafiyar awa ukku sukayi suka iso wani shago ya shiga ya sayo mata simkin pad din gabad'aya...

Har llokacin bata farka ba..
Wani haushin ta ya karaji

Tana baccita me dadi cike da mafarkai masu dadi taji saukar ruwan sanyi a fuskarta firgit ta bude ido kamar zatayi kuka amma ganin dodonta ne seta sadda kanta kasa..

Suna isa makarantar dayake abun na sune nan aka cicika komi ya zuba kudin shekarun shidda dazatayi wato secondary
da kudin furniture dana uniform duka komi ya biya

Har dakinta kuyangi sukakai mata kayanta ......daza su tafi da kyar suka rabu da kuyangin...barema da jakadiya rumgume ta tayi se rusa kuka take...
Lallashin ta tayi tace kiyi hakuri naso zama nan kai hatta fulani taso a baki koda kuyanga dayane amma yarima yace aa a barki ai school kikazo ba hutu ba .shiyasa nakeso kidage kiyi karatunki banda wasa..kada kiyi kuka kijawa kanki ciwon kai dama gana safe dakikayi wajen rabuwa da fulani...

Share hawayenta tayi tace shikenan zan baku mamaki in sha Allah ..

Yarima murad seda ya biya gidansu Mahmud ya gaisar da iyayenshi sannan suka kama hanyar komawa


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



A bangaren su waziri kuwa samako yayi ya nufi wurin boka amma har yamma be samu wajen ba ya gaji likis dole ya hakura ya dawo gida

Ya labartawa Madina komi wani bacin rai taji tace mu bari har murza taji dan sauki se muje ta nuna muna amma kada ya fice satin nan dan asabar din nan ze koma England nan da 6 jours kenan......

Kuma wani babban bakin ciki yau yayi tafiya shida kucakar matarshi abunda ya kullar dani ma shine da kanshi ya jasu ashe dana sani da munyi anfani da wanna damar mu qara cire musu burki..
bansan da tafiyar ba seda zasu tafi shima a bakin jakadiyata naji koda na fito tuni har sun bar cikin fadar ..takaici kamar na mutu...

Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba..


Love all fans๐Ÿ˜โค

ceโœ

Fasma
[28/4 23:10] Fasma๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช



Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค



๐Ÿ…ฟ 39--40


```Manzon Allah (SAW) ya ce "Duk wanda yake so a bashi tsawon rai,a kara masa yalwar arziki,to yabi iyayensa kuma ya sadar da zumuntarsa "
Imamu Ahmad ne ya rawaito shi.```





Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba.....

Madina tace Allah ya kasan yaron ne taurin rai ne dashi
(Hum to lokacin mutum beyi ba taya ze mutu inba jahilci ba irin naki๐Ÿ˜hum)



๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

Maysam kam koda akayi mata interview se suka sakata a js2 a memakon js1 dayake Allah yayi ta brain ..basuba ni kaina taban mamaki amma wannan kadan ne daga ciki baiwar da Allah yake bawa tsirakun mutane...


Dakin da aka kaita gado ukku ne a ranta tace kenan mu ukku ne a dakin nan kodan kayan dataga kusa da gadajen ya tambbatar mata da hakan...

Nan ta zaune ta rafka tagumi tana tunanin rayuwarta .....tace ko yanzu Abbana miyake??ko yaci abinci??ko ya tafi kasuwa ...i miss you Abbana.....
Se kuma tace Allah sarki inna Murza ko ya jikinta yanzu ???

Sekuma ta tsallako tunanin Fulani ai kuwa nan shar3 hawaye ya fara zarya a kumatun ta tace har na fara kewarki Momyna hakika kin cancaci yabo baki sanin ba amma kika sani a jikin ki har kika auran danki kwaya tal ..kin nunamin so, kauna inasonki sosai fulani Allah meyin yanda ya so *Sanadin Accident* na samu Momy na fita daga kangin wuyar Murza ....Allah ya saka miki da alheri...tana haka se kuma tunanin yarima Murad ya fado mata tace shin ko ya isa gida yanzu? ??ko ya ci abinci??ko miyake yanzu se kuma ta saki murmushi wanda ni kaina bansan ma anarshi ba .....se kuma naga ta tsuke fuska tace mi nawa nayin tunanin shi mtss banda mugunta da keta mi ya iya da wata fuskarshi me kyau ......yana wata tafiyar shi ta takama kodayake yarima ne dole yayi .........haka ta lalace tana ta tunanin ta data tuno wannan se ta tuno wacan..

Dafa tan da akayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunani .....

Firgit ta juyo taga waye...

Wasu yan mata biyu ne baza su fuce sa aninta ba ..

Wanda ta dafa ta ta sakar mata murmushi tace ya haka kedaya kuma kina tunani

Itade da ido ta bisu
Tace ""je suis Mariam Moctar ...

D'ayar ma tace nikuma Mufeedah Muhammad ......kefa? ?? Suka fadi a tare jin bata ce musu kala ba

Tace nikuma Maysam Musa by name..

Wani aji kike cewar Mufeedah ...

Js2 ta fada a takaice...

Waro ido sukayi a tare sukace ashe ma ajin mu daya ....sekuma suka shiga murna

Nan sukayi dan sabo har suka qara gaya mata sharrudan makarantar da yanda suke gudanar da karatun daga takwas na safe zuwa daya na rana school ne daga ukku zuwa shida na yamma islamiyya ne.....

Haka kuwa akayi ukku nayi suka saka uniform na islamiyya suka fuce harda Maysam din dayake kama daga furniture, uniform duka a school din ake baka....


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน


A bangaren oga kuwa bayan ya koma gida gaba daya ya tsinci kanshi cikin kunci ..besan ya akayi ba amma kwata2 a ranar be runtsa bacci ba ya na rufe idanu se kawai yaga fuskar Maysam ..shi kade se juyi yake yana tuna scene dinsu na jiya ..yaja tsaki yafi cikin kwando ..ranar kam se barawan bacci ne ya saceshi abunda ya jima beyi ba kenan tunanin wani abu ya hanashi bacci shiyasa tsanar Maysam ta dada ruruwa a zuciyar shi...


A bangaren Fulani ma se taga yau gidan yayi mata fadi da babu Maysam dukda basu wani jima tare ba kuma ga kuyangi dasu na debe mata kewa amma Maysam ta daban ce a wajenta..


Washe gari kam sukuku Murad ya tashi har seda Fulani ta tambayeshi ko lfynshi amma se ya fake da kanshi yake mishi dan ciwo..(hohho su Murad manya)



Maysam kam cike da zumudi ta tashi tun wuri tayi shirin ta na school uniform din ba karamar karbarta yayiba rigace har guiwa da wando har kasa ruwan toka se dan baby hidjab fari tas ..nan ta fara bubude kayayakinta ..dan ta samu ta karya ..ita kanta ta yaba da sayayyar da Murad yayi mata dan kanyan sunyi yawa ma a cewarta .....can ta hango katan abu ta janyo shi taga an rubuta Pad sanitary .....ta dinga jujuyashi a ranta tace komiye wannan kuma oho ..haka ta mishi wuri ta aje sanna ta jere kayanta tsaf cikin wardrobe dayake ba wani girma ne dashi ba dan kahaka sauran kayan ta bardu nan cikin bags...
Haka suka nufi aji su ukku bayan an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login