Showing 51001 words to 54000 words out of 100341 words
๐ก&extraordinary writers_ )
๐น๐น *SANADIN ACCIDENT* ๐ฅ๐๐น๐น
S.W.Aโ
๐ณ๐ชStory&Written
by
*FASMA* ๐ณ๐ช
*Alherin Allah ya kaiwa masoyan wannan book din a duk inda kuke ..hakika* *ina jin dadin comment din ku kuma yana bani kwarin guiwa ...daya wa naga sakon ninku..wasu* *suna cewa ina jan aji da rai ..to bahaka bane muma muna da uzuririka a gabanmu .....Allah* *ya bar kauna da zumunci ina yinku iri more totaly din nan*โค๐๐โคโค
*Pls masu juyamun littafi ku dena bana so . ...kun san kanku base na tona ku cikin jama'a ba so tun kafin abu yayi nisa ku fasa ....*
Dedicated to all my fans๐โค
๐
ฟ75__76
```Manzon Allah (SAW) ya ce''babu d'a'a(biyayya)ga kowa cikin sab'on Allah''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi.```
Murad kam fushi ya dauka da Maysam ..ga zuciyar shi na azalzalarshi kan ya kira ta amman yayi biris da ita seda yaji ta fara mishi zut2 din nan sanna ya kira office din ..lokacin sun gama lecture kenan ...
Da sallama ta amsa .. Tu nan yaji wani mayen sanyi yaji a zuciyarshi amma wani bangare yana tunatar dashi cewa yayi fa fushi da ita .. Dan haka
Amsa sallamar yayi a dakile kamar ba shine ke daukin kiran ba.
Cikin sanyi jiki ta gaishe shi tare da tambayar ya aiki. .
Da kakkausar murya yake amsa mata fada2..
Maysam ta sake cewa yaya mi akayi ne ?ko nayi maka wani laifine,?
Cike da kaguwa cikin fada yace au baki ma sani ba shikenan..yana fadar haka ya katse kiran..
Gaban Maysam ya bada dam ta fara tunani ...ji take kamar tayi kuka dan ita bata san lefin ta ba kuma gashi shi be fada mata ba...
Har ta juya zata fita ya sake kiran dan zuciyar shi ta hanashi sukuni tana ayyana mishi cewa Maysam na can na kuka ..shiyasa ya kasa resister ya sake kira..
Tana dagawa taji shine yayi sallama bata jira taji me ze ce ba ta saka mishi kuka....
Tirkashi nan ya dafe setin zuciyarshi yana fadin why nayi mata fada gashi yanzu na sakata kuka..beyi aune ba yaji kwalla ta cika mishi ido..da kyar ya daure ya rarrashe ta ...
Maysam tace shikenan amma yaushe zaka dawo nayi missing dinka fa....
Dan jim yayi dan shifa baya ma jin ze dawo kasar..
.
Yace ni kaina bansan ranar dawowata ba kai inaga ma bazan kara dawowa ba ...
Bata kawo komi ba dan ta zaci dan ya tsokane ta ne kawai dan lokacin daza suyi bankwana ya jaddada mata baze yi 3months ba ze dawo shi ya sama bata dau abun serious ba...
Zata sake jefo mishi wata tambayyar ya katseta da fadin kin ga se anjima inada aiyuka ...be jira mi zata ceba ya katse kiran dan kwata2 ma baya son ta mishi zancen.......haka ta koma aji jiki ban kwari dasu Maheeba suka tambayeta ganin mood din ta ya sauya aman se cewa tayi ai bata jin dadi ne...
Sarki kuwa ba karamin dadi yake jiba kasancewar Malam Musa wazirin shi ...
Lokacin da labari ya isa kunnen Maysam harda kukan dadi tayi tace gashi yanzu SANADIN ACCIDENT ta samu gatan da ba kowa ke sa'an samun shi ba..da tana cikin 'KUNCIN RAYUWA(littafi na na gaba in sha Allah).na azabar Murza aman yanzu...ta samu Mahaifiya wato Fulani ..ga karatun boko da islamiyya. Gashi kuma yanzu anyi wa Abbata Waziri.ita kam in bata godewa Allah da wannan ni'imomin ba dayayi mata to mi zatayi ...har Fulani ta kiraya ta shiga yi mata godiya har seda ran fulani ya soma baci tukon ta dena..
Haka rayuwa tayi ta tafiya inda zuwan Murza ya kara sa zuciyar Madina kara yin baki yanzu bata da wani buri na taga Murad ya mutu...sabon boka ma yace mata hakan bame yiyuwa bane amma taki hakura kullum da irin plan din datake shiryawa....
Murza kam ta zama tabarya me baki biyu ko nace me fuska biyu ma ..dan yanzu tana yawon shiga bangaren fulani tana nuna mata ta shiryu ta dena abunda take alhali tsegumi ne ke kawota dan ta kai wa Madina rahoto. ..duk abunda ta gani ko taji a bangaren fulani to seta gayawa Madina shi. Amma har yanzu ba'ayi katari taji Fulani ta kirayi Murad a gabanta shi yasa suke kara jin dadi .
Basu san duk safiya se Fulani ta kirashi a waya ba ...kuma kullum seta nemi ya dawo amma se ya fara kawo mata kabli da ba'adi ..kullum cikin yi mishi addu'a take .
Ita kam Madina zuwan nan Murza yayi mata dadi tana samun information akai2..
๐น๐น๐น๐น. ๐น๐น๐น
A banagaren su Muheeba kuwa bayan sun ji sauki amma fa fuskar ta bata dedetu ba duk tayi wani tabo2 babu kyan gani ...
Kullum cikin kuka take ganin haka yasa Mahaifiyarta ta cira musu ticket zuwa wajen danginta na Ghana ..(safe journey du Muheeba Allah ya raka taki gona๐)
A bangaren su Maysam kam itada kawayenta sun dage ba kama hannun yaro karatu suke sosai....
Cikin sa'a suka kawo makin da ake so dan haka shugaban makarantar ya ce vacation din 1 month ne kawai garesu dan wani lecture za'a fara yi musu dan kada susha wuya....
Har lokacin Murad be dawo ba kullum intayi mishi zancen se ya katseta da wani zancen ........yanzu kam ciwonshi har tashi yake kadan2 dan kuwa Maysam kuka take saka mishi kan se ya dawo tayi missing dinshi ..
Shi kanshi baze ce ga taka meman abunda yake hana shi dawowa ba ...kullum cikin rarrashi yake ...Fulani ma kullum cikin bata hakuri yake....
A na sakin su Fulani tayi mata booking jirgi ta dawo gida...
Ba karamar Murna sukayi ba itada M.Musa ba da suka juna ..rasa inda ze sakata yayi ..Murza na gefe se tabe baki take tana tsuka kasa2 amma da taga Maysam ta kallota se ta fake da dariyar yake wai ita a dole nan ta shiryu ta fara son Maysam.....
Tun Maysam na dari2 da ita har ta saki jikinta kadan ..
Lokacin da Maysam ta sanarwa da Fulani yanda sukayi da shugaban ba karamar murna tayi ba dan haka tana cika watan ta fara shirye2 komawa. ..
To fa ranar wata samedi(Saturday )ana gobe komawar Maysam .....suna falon Fulani ,Maysam,Murza,da ita Kanta Fulanin ...
Hira suke wacce duk ta karatun Maysam din ce . Murza se wani tarerayar Maysam din take amma fa k'asan zuciyar bakin cikine fal dan ji take kamar ta rufe Maysam din da duka ganin irin yanda take zuba shagwabarta a cinyar fulani ..ita kuma se lallaba ta take. ...
Ganin abun bana karewa bane yasa fulani fadin bari de inkira mijin ki may be shi ya lallabaki ki barni na huta da shagwabar nan.
Gaban Murza yayi wata irin mummunan faduwa ta shiga wuwurga ido ..
Kamar wasa Fulani kuwa ta danna mishi kiran ..
Murza ta kashe kunne kuwa. ..
Bayan ya gaisheta ne ta sake tambayar shi yaushe ze dawo ..nan ya fara yi mata kame2 ..
Fulani tace to ka bude kunnuwanka da kyau kaji ina son ganin ka a week din nan wannan umarni nake baka maza2 ka taho ....
Cike da tashin hankali yace to Momy zan zo ..
Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Maysam da ta fulani tace to se kazo Allah yayi maka albarka.
Sabanin Murza datayi mutuwar zaune zuciyar ta cike da wasi2 a ranta tace daman suna waya ko kuma yau ne suka fara kawai. ..bata gama tsinkewa ba seda taji Fulani na fadin pls ka lallaba min yarinyar nan ysa duk ta hanani wali...
Shata da baki Murza tayi ganin Maysam ta karbi wayar tayi cikin kuryar daki tana dariya kasa2 ...wani dunkulelen bakin ciki taji ya to kare mata wuya a ranta tace kada fa Yaron nan ya fara son aljanar yarinyar nan......babu me bata amsa dan haka ta danne bakin cikin ta gaban Fulani ta tashi tana fadin barin koma akwai wasu ayuka da zanyi ...nan tayi ma Fulani sallama ta fice ..
Itade Fulani tana kallonta ne amma bawai ta yarda da tuban Murza ba..
Tana fita kuwa ta fada bangaren Madina ......๐ณ๐ฑ
Kuyi hakuri da wannan...
Fasma ce๐
[27/07 ร 14:25] FASMA๐: ๐ *STAR WRITER'S ASS* ๐โจ๐
( _Home of spรฉcial ๐ก&extraordinary writers_ )
๐น๐น *SANADIN ACCIDENT* ๐ฅ๐๐น๐น
S.W.Aโ
๐ณ๐ชStory&Written
by
*FASMA* ๐ณ๐ช
๐๐ _jinjinar ban girma Momyn Mufeedah ,ina tayaki murnar kammala littafinki hakika kin fadadakar da nishadan tar damu Allah yasa sakon da kike son isarwa ya isa ,Allah ya bamu ikon yin aiki da shi ke kuma Allah ya biyaki da mafificin alherinsa ,ya yafe miki kurakuran dake ciki.._
_Up.up.up๐๐muna tare dake se mun jiki a sabon littafin ki..._ โค
*congratulation my lovely sis SARAH hakika ina tayaki murna samun Bac din ki Allah ya riqa ya sa ki amfana da* *shi ....ina me kara jinjina miki .* ๐
*Ban manta dake ba kanwata ta kai na Balkissa kema ina taya ki murna samun Bepc ki matuka Allah ya rika ya sanya alheri*โค ...
*Kai da duk ma wanda suka zana jaraba wa ina muku murna tare da fatan alheri ..*
*Wanda kuma ba su samu ba ne baissent pas les bras ,du courage and wish you bonne chance* ....
_Ilou Ado Safaraou&Rabe Idi Salamatou Magaria ..les fausses jumelles ba ..ina jin dadin yanda kuke nuna kaunarku ga book din nan Allah ya bar kauna โค๐Maysam tace ta gaishe ku_ ๐
Dedicated to SARAH&BALKISSA๐โค
๐
ฟ77__78
```Manzon Allah(SAW)ya ce''Musulmi dan uwan Musulmi ne ,kada ya cutar dashi.
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Murza na fita ta fada bangaren Madina ..bakin ciki kam kamar ta mutu take ji ...
Tana zuwa ta fara zayyanawa Madina komi har da yar kwalar ta bakin rai ..
Wata zabura Madina tayi tace what?dama suna waya amma bamu sani ba ...
Tirkashi zancen dawowar shi ma bata taso ba kawai abun yi yanzu base gobe ba ki tashi yanzu ki koma wurin yankan wuka ki sanar mishi ..se kuma ki ce mishi ayi mishi asirin da ze manta da zuri'a tashi ma gaba daya ya yanke alakarshi da su ...
Murza bata yi kasa a gwiwa ba ta tashi ta fice bayan Madina ta cika mata jaka da makundan kudi...
A bangaren Maysam kuwa shagwaba wacce tafi ta Fulani ma take zuba ma Murad ..
Shi kuma se lallabata yake kan tazo mishi koda vacance din nan ne..
Se lokaci ta sanar dashi cewa ai wani lecture za suyi dan za ayi musu tsalaken ss2 ..
Shima nan ya tayata murna tare da yi mata fatan samun nasara ...
Hira tayi dadi har take tambayar shi sunan likitar dayake aiki a can ...
Sedayayi murmushi yace to keda ba zowa zakiyi ba miye na wani tambayya...
Kukan shagwaba ta sakamishi .....
Dolen shi shi ya gaya mata kai harda adress din gidan dayake.....
Sun jima suna waya cike da jin dadi ga shi kuma yace zezo cikin sati se murna ta hade mata biyu...
๐น๐น๐น. ๐น๐น
Murza ce tayi wani zaman dirshen a gaban boka Yankan wuka tana gaya mishi duk irin makircin da suke so ayi musu tare da kara jadda da cewa arabashi da famylin ma gaba daya ..
Boka ya sheke da dariyar jin dadi yace kai ina jin dadin aikin ki ...raba d'a da iyayenshi abune ne dayake bamu matukar wahalar aiki bare ma Uwa ...amma dole muke jajir cewa muga irin wanna danyan aiki ya yi tasiri badan komi ba se dan mun san yanke zumunta ma bashida kyau ,,bare yanke alaka tsakani da iyaye. ....(kuji wani shedanci ๐ค)
Dan haka muna bukatar kudi masu yawa dan asiya wa aljanan da zayi aiki jini ..,,kuma ma ba anan garin suke ba se an tafi wani gari wanda ake kira da''DOGON DOUTCHI''ake siyo su wato Aljana 'DOGUWA'....sune masu yin wannan aiki ba tare da an samu matsala ba....ya kwashe da wata dariyar hhhhhh...
Murza se wani washe baki take tace kudi ba matsala bane inde bukata zata biya ...nan ta zube mishi su..
Cike da murna da kwarin guiwa ta koma gida dan Boka ya jaddada mata cewa baze taba dawowa ba..(jifa se kace shi keda ikon duniyar๐๐๐..Allah de ya shirya in me shiryiwan ne)
Lokacin da Madina taji bayanin boka ba karamar murna tayi ba tace Mulki ne de Murad baza ka taba hawanshi ba...saura shi kanshi sarkin ina nan zuwa lokaci kawai nake jira....
Wannan kenan
๐น๐น๐น. ๐น๐น๐น๐น
Washe gari Maysam tayi tafiyar ta Maradi karatu da zumar in Murad ya zo tasan de ze je ganinta tunda ya san tana school.
Amman mi shiru kake ji kamar malan ya ci shirwa ...tun tana tammahani zowarshi har ta dena ...yau har watan su biyu ..
Bayan ta dawo gida ne kafin su koma rentren Ss3 take yi wa Fulani mitar yayanta be zo ba .har yau
Fulani ma dauriya kawai take yi...tana lallashin ta amma mamaki ne fal ranta ....da farko in tayi kira tana samun shi sede baya dagawa .,,kai daga baya ma wayar ta dena shiga..
Ta dau waya ta sake danna kiran shi amman kamar kullum bata shiga .
Maysam kam zuciyar ta banda lugudan zut2 babu abunda take mata ..se kawai ta fashewa Fulani da kuka ..
Da kyar itama ta nutsu ta shiga lallashinta ..
Dama sati biyu ne zatayi ta koma school amma duk ta wani fige ta rame Fulani kam tana tausayin ta ..ganin abun na gaba yasa tace wa Sarki tana son zuwa England wurin Murad.
Da kyar sarki ya lallabata da fadin bari Mahmud ya tafi ya gani..
Cikin satin Mahmud ya shirya ya daga se England ...lokacin da ya tafi akayi rashin sa'a Murad baya nan likitarsu ta tura su qarin karatu kasar Europe kan wata sabuwar cuta data shigowa kasar ..kuma formation din ze dauki 5_6 months....
Murad kam yana can yama manta da wasu wai su Fulani dan kuwa tun bayan kwana biyu dayin hirar shi da Maysam har ya fara shirye2 dawowa amma me kawai rana tsaka ya tsinci kanshi da son rashin dawowar . abun beyi nisa ba seda yaga Fulani tana kiran shi a waya amman ya kasa dauka...wani irin abu yake ji a zuciyar shi se kawai yama canza layi gaba daya ,,,kai da ga karshe ma dayaji tafiyar tura karin karatu se kawai ya saka sunan shi ama su son zuwa ..ya koyi sa'a aka tura sun....
haka nan Mahmud ya dawo ba dan ya so ba tun dade lfyr sa lau aiki ne kawai ya rikeshi......
To fa ๐คmuje de zuwa
Lokacin da Mahmud ya sanarwa da su Fulani se a sanan suka dan saki ransu .jin an turashi karatu ne ..
Maysam ta koma Makaranta abunta . yanzu kam sun kara girma komi na cikar budurci ya bayyana a jikin su....se wani jiji da kai suke wai su yan matan Ss3 ...yanzu kam sun kara wayo Maysam yanzu bata da wani buri na ta ganta kusa da yayata Murad .. Ga karatu suke babu kama hannun yaro ...
kullum su ke cinye ta daya ,biyu da ta ukku a ajin,,wannan abu ba karamar haushi yake bawa sauran dalibai ba dan ko wata competition se de a zaba cikin su ukku ...gaba daya kansu a hade sun shaku da junan su,,,class,diri ,kyau tsafta ,ilimi duk sun mallake su ..dan ko a islamiya ma kadan ya rage musu su sauke Alqur'ani.......
Kullum zaka gansu cikin walwala da tsokanar junan ,,,har suke kiran kansu da tripleM.. .
amman fa har zuwa lokacin su Mufeedah basu san cewa Maysam matar aure ce dan bata wani nuna musu alama ba...wani lokaci har sukan tsokane ta da fadin sun yi wa yayansu kamu ....
Itade sede ta kallesu tayi dariya..
Bayan 6 months nan ma su fulani suka dinga diba hanyar ganin Murad amma ji kake shiru ...Fulani kullum cikin yi mishi addu'a take ..
Maysam ma kam yanzu bata wani samun isheshen bacci,,,duk dare tana yawaita yin nafilfili da rokon Allah yayi musu zabi na alheri tare da karesu da duk wani me binsu da sharri mutum ko aljan.. Amma fa yanzu idonta ,kunnenta bakinta kai har ma gangar jikinta ba suda wani buri na su jisu tare da oga dan Murad ya rigaye ya koya ma ta sonshi ..dan haka ita da soyyayarshi ta girma cikin ranta ....mafi yawan cin lokaci zata dau photon shi ta saka gaba tana ta zance ita daya (umm su maysam an fada tarkon so ....sede lokaci ya kure miki๐.)
.
Tafiya tayi tafiya lokaci nata tafiya
Bayan sunyi saukar Qur'ani da sati suka fara final exam ..
Cikin ikon Allah suka gama lafiya suna jiran saka mako..
Gida ta dawo zaman jira.....
Fulani na lura da ita tun dawowarta ta kaura bangaren Murad gashi da ka ganta kasan tana cikin damuwa ...fulani kam ba karami tausaya mata ba take..bz.
Ana haka resulta din su Maysam ya fito ..gaba dayan sun ci harda mention exellente ..
Zo kaga murna wajen su
Harda wata yar kwarya kwarya walima suka shirya su ukkun ...acan gidan Maysam na Maradi akayi ta inda Mahmud ya taka rawar gani wurin yi musu komi dan ganin basu samu wata matsala ba.....
Washe garin walimar su ukku suna ta hira Mariam tace yauwa dama akwai wata magana dana ke son yi muku..
Nan suka nutsu ta ce dama abbana nane yayi mun muji ..
Wani ihu suka kwasa a tare suna fadi wai da gaske dan Allah ..
Tace ee wly wani dan abokin shi ne sunan shi MA'ARUF. Kuma a England yake aiki docteur ne...
murna fal ransu suka yi muta fatan alheri tare da fadin kice kawai da mun sha biki se England๐ ..
Mufeedah ma tace kai nima fa Maysam yayan nan naki ya fara damuna ,,..bakiga jiya daya kaini Super market siyan kayan damuka sa ....ya wani tsareni da surutu kai daga karshe ma seda yayi mun wayo na bashi number ta ..
Maysam ta kwashe da dariya tace kawai kada kija wani aji inya nuna yana so kawai ki amince Mahmud bashi da wata makusa ,kyau ne ,kudi ne,kamala ce, duk ya hada kawai ki yarda musha biki.kemz..
Cike da zolaya