Showing 18001 words to 21000 words out of 100341 words

Chapter 7 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

919

ta cika mata ido....

Da sauri tace dan Allah Yaya kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba. Na tuba ka yafen..

Wata uwar harara ya ban kad'a mata yace kima qara kiga yanda zanyi da ke ..ya fice abunshi.

Sum sum itama ta fito ta fice bangaren Fulani ..a ranta tace Allah abun godiya ...



Washe gari wajejen goma na safe Murad ne zaune gaban me martaba ya wani sunne kai banyan ya kwashi gaisuwa ..me martaba yayi gyaran murya yace alhamdullilah Son Allah yanuna mana aurenka ina alfahari da kai nan ya d'anyi mishi nasiha sannan yace game da tarewar matar kace ....nida Fulani mun yake shawarar kawai ka tafi da matarka can England .

Wata irin zufa Murad yaji tana karyo mishi kamar baze ce komi ba se kuma yace Ranka shi dade bawai naki bin shawararku bane amma ni aganina abarta nan se asakata makaranta tayi karatun nan

Ganin ya fara yin nasara ya ci gaba da fad'in ..because a can karatun zeyi mata wahala dade anbari ta gama koda secondary ne seta ci gaba a can din...


Ayi mini afuwa idan na fad'i badede ba

Dan murmushi yayi yace shikenan to Allah yayi mana zabi na alheri

Ameen yace sanna ya fice direct bangaren Fulani ya nufa..a ranshi yace alhamdullilah na rabu da alajakai ..amma inba abun su momy ba ina yar kauyen nan da zuwa England ....

Kwance take ta d'aura kanta bisa cinyaryar Fulani se hira suke abunsu kamar uwa da y'arta gwanin sha'awa...

Suna haka ya shigo palon ganin Maysam bisa cinyar Fulani ba karamin haushi yaji ba...ya qara daure fuska... ..gaidata kawai yayi yayi shiru se wani ku
mbare2 yake...

Da sauri Maysam tace ina kwana yaya ...

Wani kallo yayi mata na irin zamu hadu dinna..ciki2 ya amsa a takaice da lafiya..

Momy ta gumtse dariyata tace wai ni son waya tabo min kaine se gumtse fuska kake.. da safiyar. Nan


Kicin2 da fuska yayi yace haba Momyn ya zaki bari wannan tahau min cinyata

Fulani tayi dan murmushi tace yo inba abunka ba yarima ai yanzu na yayeka ka huce hawa cinya..ka girma ai yanzu kam matarka ya maye gurbin ka ..kafin itama ta haihu ta barwa baby place ko?...

Be iya cewa komi ba amma a ranshi yace wai baby ..bade da niba zakiyi ta jiran gawon shanu
Kuwa .

Maysam kam abun mamaki ma ya bata ta saki baki da hanci tana kallon wannan shiriritar


kawar da zancen yayi da labarta mata duk yanda sukayi da sarki yanzu ..

Dan jimmmm tayi kamar me tunani

Da sauri yace kuma kinga in anan take zatafi sakewa tayi karatu da kyau ..

Shikenan Allah yasa hakan yafi alheri cewar fulani...

Maysam da tun dazu take jin duk hirar se wani
washe baki take tana mirmushi kasa2 dan akwaita da son ecole

Suna haka sega sarki ya aiko kiran Fulani ....nan ta barsu palon cikin su babu me magana ...

Fitarta keda wuya ya ce kuwa ke zo nan.d....



Pls fans ku kara hakuri ina gani korafen2 ku
Kwana biyun nan ne se a hankali. Ina de barar addu'arku .....

Kuna raina fans love you
all๐Ÿ˜โคโค

โœFasma ce
[22/4 09:28] Fasma๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial &extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน


S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช



Dedicated to all my fansโค๐Ÿ’‹

๐Ÿ…ฟ 29--30


```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya ku mutane ku tuba ga ubangijinku. Na rantse da Allah ni ina tuba ga Allah a rana sau dari "
Muslim ne ya rawaito shi```





Fitar Fulani keda wuya yace kuwa da Maysam ke zonan wacce ita har ta kai kofar fita palon ganin fulani ta fita..

Jiki na b'ari ta zo ya durkusa gwiyoyin ta a kasa ta sada kai kasa tace gani Yaya ...

K'ara murtuke fuska yayi beyi wata2 ba ya dadage iya karfin shi ya rankasheta a kai yace wannan na hawa cinyar Momy nane ...ya qara mata yace wannan na gaishe nine da kikayi dan nace kada ki sake kimun magana matukar bani na baki izni ba...ya qara mata yace wannan kuma na kallona da kikayi ne....

Ze qara mata da sauri tace dan Allah yaya kayi hakuri bazan qara ba...sega hawaye shar2

Wasu biyu masu shegen zafi ya sake yimata yace wa inan kuwa na jin dadi da kikayine dan za'a sakaki makaranta tare da ban hakuri da kikayi yanzu ya hankad'eta yayi ficewar shi ya barta nan se kwasar kuka take...

Ta jima nan taga ba sarki se Allah ta lallashi kanta ta tashi ta shige room tana me ayyana abubuwa da dama...

Sarki ma kuwa maganar karatun ce yayi wa Fulani ta ko yi na'am ganin irin farin cikin da Maysam tayi lokacin da yarima ya sanarwa musu yanzu...



๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน


A b'angaren Murza kuwa Madina tasa aka yi mata kiranta ...tana dari2 tsoro duk ya cikata ta amsa kiran dan duk a ganin ta wuyyar da tabawa wa Maysam ne za 'a hukuntata


Amma me jin irin mugun nufin Madina da waziri akan su Maysam din har bata san lokacin da wata bazawarar dariya ta kufce mata ba ta kuwa gyara zama tana sauraron su daga nan itama ta ta karkace kai ta sanar musu irin yanda take yiwa Maysam har zuwanta wurin boka seda ta sannar musu

Madina tayi wani murmushi tace shikenan fad'uwa tazo dede da zama in lokaci tafiyarku kauye yayi zan turo miki da kudi kisa bokanki yayi mini wani aiki....


Murza se wani wangale baki take taji zancen kudi...

Haka suka yi ta tsara makircinsu ...

Murza jitake kamar ta zuba ruwa a kasa tasha jin za akashe mata Maysam ..sun jima sannan taron makircin ya qare kowa ya kama gaban sa ...


Sha biyu na rana dede aka maida su Murza kauyensu cike da murna dan kuwa Madina ta saki mata kudi a zuwan ta kaiwa boka ayi mata aiki akan Marud da Maysam ...zuwansu keda wuya ta kuwa haura hann se wajen boka yankan wuka dayake bata tarar da Malan Musa ba.....

Zaune take a gaban bokan se wani hangame baki take tana watsa wasu jan hakoranta...nan ta fad'imi shi yanda suka tsara na akashe su ..

Buga kasa da tsubbace2 yayi kamar na wancan lokacin ...

Ya dubeta yace wannan yara da taurin kai suke dan kuwa ajalinsu ba anan kusa ba yake abunda zan iya yi muku anan shine kawai rabashi da iyayenshi da matarshi kai dama masarautar baki daya duk da aikin ba karamin aiki bane dan se azubadda da jini ma..

Ko ajikinta Murza tace babu matsala a zubar ko na waye inde bukata zata biya ..nan ta zube mishi rafar kudi wanda ita kanta bata san adadinsu ba a ranta tace nikam kudi be daman ba inde Maysam zata dawama a wahala...se wani murmushi take...

Wani magani ya bata cikin wani tsumma yace a turara a wurin da aka san ze ketara .....

Yana ketarawa yanda hayakin yabi iska haka shima in ya bar masarautar baze sake waywayen su ba har se in ku kuka bukaci dawowarshi........

Ta karbe magani ta fito har da yar rawarta ta kama hanyar gida.....

ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta jikake ragajaf ta zube kasa wanwar...




Kuyi manage da wannan ๐Ÿ˜๐Ÿ˜Š


Fasmaโœ
[23/4 00:38] Fasma๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _๐ŸกHome of spรฉcial &extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน


S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*Ina maqiyan Murza ku fito wannan page* *din takuce .....ku fito ku kwashi shoki fa ....lol..* ๐Ÿ˜๐Ÿ˜œ


*Ban manta dake ba my dear Hadjara* ( *Arfat.)..ina godiya da qaunarki Allah* *ya bar qauna da dankon zumunci...ina yinki sosai ...* *littafinki "AMEMAH " yana wuta๐Ÿ”ฅgaskiya* *yana fadakardamu da nishadantar damu Allah ya* *qara basira da zakin hannu Fans kada kubari a baku labarin* *littafin Amemah dan gaskiya ya hadu sosai* โค๐Ÿ˜



Dedicated to all my fans โค๐Ÿ’‹



๐Ÿ…ฟ 31--32



```Manzon Allah(SAW) ya ce "wanda duk ya yarda da cewa ALLAH shi ne Ubangiji,ya yarda musulunci shine addini,ya yarda MUHAMMADU(SAW) manzon ne to wannan ya dandani zakin imani "
Muslim ne ya rawaito shi``` .




Ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta ji kake ragajaf ta zube nan kasa wanwar ...

Ta kuwa bare baki iya karfinta ta saki wani runtamemen ihu sakamakon wani bala' in zafi da taji a kafafunta ...tuni ta sume dan zafi ..kan kace mi a ka kwasheta akayi likita baban gari dake kusa da su ..amma mi daga nan ma aka turasu babar likita ta birnin Damagaram har lokacin da suka isa bata farfado ba..

Nan likitoci suka bata taimakon gaggawa .....sukayi mata allurar bacci dayake dare yayi daman ..

Dreban daya kade ta ne bayan sun koma kauye yaje ya sanarwa da Malam Musa ...be wani daga hankalinshi ba yade ce Allah yabata sauki..



Washe gari wajejen goma na safe ta farka da kadan2 take bude idon ta harta bude su ware ..dan motsa kafafunta tayi aman se taji kamar babu su ..dan danan gabanta ya bada fat .....da sauri ta yunkura zata tashi aman ta kasa ..se kawai ta fara ihu.....

Sega infirmieres"likitoci " sun shigo da gudu da kyar suka samu tayi shiru tace miya kawoni nan ne.

D'aya daga cikinsu tace ina kyautata zaton Accident ne kukayi wanda ya hadasa miki karaya har biyu a qafar dama se kuma qafar hagun da aka cire miki ita saboda gaba daya kashishuwan wajen sun ratatake babu damar dori dole seda aka cire ta


Wani ihun kururuwa da ta saki se da ta firgita su ta dunga ihu da fuzge2 kamar sabon kamu...

Wata nurse tace haba baiwar Allah kamata yayi kiyi hakuri kiyi hamdallah daba duka bane aka cire miki ko kuma ma da kika rayu baki maceba

Haba ina Murza bata ma san tanayi ba ganin abun bana qarewa bane yasa suka mata allurar bacci tukon suka samu lfy..

Se sha biyu Musa yazo likitar ..nan docteur yayi mishi bayani halin da Murza ke ciki..

Banda girgiza kai babu abunda yake....
Ya na fitowa daga office din doctor direct chambre "daki"da Murza take ya shiga wanda yayi dede da farkawarta ...

Ta bare baki zata fara kururuwa yace ke dakata bakida hankaline ?ko baki san nan likita bane da akwai marasa lfy?to walahi kiji da kyau inde kika ci gaba da wannan ihun naki to ina me tabbatar miki gidan Mahaukata zasu kaiki..

Tsit kakeji Murza tayi se wani mazurai take..

Nurse suka shigo duka dan duduba ta suka bata magani tasha ...(su Murza an zama me kafa
daya๐Ÿ˜๐Ÿ˜....)


Kafin sati ya zagayo har ta fara jin sauki ....

Labari na kaiwa ga Maysam ta kuwa bi ta tada hankalinta ta ringa rokon Fulani ta barta taje ...
Da fari Fulani ta kiye mata ganin duka ma yaushe akayi aure harda zata fara futa amma irin addabar tata da tayi setace shikenan jeki tambayo mijinki inhar ya barki sekizo mutafi tare dan ban yarda da Murza ba..

Jin haka yasa Maysam ta bata rai tace haba Momy (haka itama take kiran Fulani yanzu) miye na wani tambayyarshi kawai muyi ta fiyarmu..a zahiri kuwa tsoran zuwa idan yake take..

Fulani tayi dan murmushi tace baki san mace bata futa seda izinin mujinta ba?..duk macen da ta futa bada ixinin mujinta ba to tana cikin tsinuwar malaiku .ne har ta dawo
Nan tayi tajan hankalinta....

Maysam tace shikenan bari na tambayoshi to ta fice daga palon

Fulani kuwa a ranta ba karamin dadi taji ba ganin yanda Maysam din ta dauketa kamar mahaifiyar ta...


Seda taje bangaren nashi tsoro ya kamata nan ta fara wasisin shiga..ta jima nan se kawai tayi shahada ta shiga..

Zaune yake bisa doguwar gujera a palon ya mak'ala ecouteur "earpiece "a kunne se wani karkada kafa yake...

Tun lokacin data shigo fitinenen kanshinta ya sanar mishi da zuwanta amma se yayi kamar besan da shigo warta a..

Itama tunda ta shigo kallo daya ta mishi ta kauda kai ..

Ta jima nan tsaya tana tsoran yi mishi magana tajawa kanta rankwashi dan bata manta dana waccen ranar ba..

Ta kusa rabin awa tsaye sekuma ta samu waje ta zauna a kasa ta sada kai


Ganin haka yasa ya tashi ya zauna yace ke dabbar inace daba zakiyi sallama ba ...kuma ki wani zo kisani gaba bako gaisuwa ke gaki ishashi ko? ...

Itade batace komi ba a ranta tace kai wannan mutumun komi zakayi baka yi mishi dede..

Shifa yace kada na sake gaisheshi ..amman yau kuma yana fada akan gaisuwar..

Abunda ya harzukashi menan jin tayi mishi shiru ya ce ke yaki nan na tatakaki..

Maysam da shegen tsoro har kwalla ta cika mata ido ta miki ta fara tafiya kamar hawainiya ..

Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata. Ai kuwa bata san lokacin daya gurfana a gabanshi ba.

Yace....

Sorry fans nida kaina nasan yanxu banayin typing me yawa kuma ina ganin korafe2 ku banaki d'auka bane....de kuna muna uzuri ..am buzy kwana biyun nan ne..

Love you all fans irin sosai din nan ๐Ÿ˜โคโค



Fasmaโœ
[23/4 23:03] Fasma๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*Fans na Sanadin* *Accident ina jin dadi yanda kuke nuna qaunar ku ga littafin nan ** *mussaman yan group din*
*MEERAH FANS
ZURI'ARMU FANS2*
GENTLE LADIES* H
FATIMA(A'S)H*
*ETC ..
*Ina godiya* *hakika ina alfahari daku ina jin dadin yanda kuke bibiyar book dina* *Allah ya bar zumunci* ๐Ÿ˜๐Ÿค je vous aime my fansโค๐Ÿ˜๐Ÿ˜



Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค


๐Ÿ…ฟ33--34


```Manzon Allah (SAW) ya ce""Allah ta'ala yana da sunaye casa'in da tara,wato dari badaya,duk wanda ya haddace su, to lallai zai shiga Aljanna "
Bukhari da Muslim se suka rawaito shi.
`







Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata ai kuwa bata san lokacin data gurfana a gaban shiba ..

Yace ke wai mi kika d'auki kanki ne??ee..ya kuwa kai mata rankwashi a kai ze qara mata da sauri tace yi hakuri yaya kaifa kace kada na sake yi muka magana in har bakaine ka bada izinin haka..ba..

Wani kallo ya watsa mata yace ohoo๐Ÿ˜ฎ kuma shine kika zo kikayi mun kikam kamar wani dogari kin wani zura min ido kamar manya ya kuwa dungure mata kai yace to wai ma miya kawokine? Iye me kama da aljanu

Baki na karkarwa muryarta har sarkewa take tace da......ma2 innata ce ba ta da lafiya shine Momy tace nazo na tambayeka zamu tafi ganinta..


Mi kikace???Momy komi ne?? ..ya sake rankwasheta ya kama kunnenta ya murd'e harda ciza leb'e yake dan mugunta seda ta saki d'an kara yace wannan Momy nace ni da sweetbaby na kadai in kika kuskura kika sake kiranta da Momy tooooo yayi kwafa tare da sake mata kunnen .. ....yace kuma ni ina ruwana da fitarki tunda ba d'aureki nayi ba??(umm umm Murad to๐Ÿ™ƒ)
Yaja dogon tsaki Mtsssss KE SORS DE MA MAISON VITE2


Qafafunta har hadewa suke wajen sauri ta fice a dakin seda ta fita ta sauke wata nauyenyar ajiyar zuciya tana luliya kunnen a ranta tace shi wanna wai hannunshi baya gajiya da mugunta ne..? Amma de kwanda shi da Murza ..


Bayan fitarta ya lula kogin tunani yace kai ya zamo dolema na koma England wajen aikina dan kuwa inde har ina tare da yarinyar nan to kuwa seta saka tsohon ciyona tashi ..ba damar ya tabats se yaji mass shock koda kuwa mugunta ce ze mata da zarar fatar su ta hadu to se yaji..gwara ya tattara yanashi2 ya tafi kafin ta bullo mishi da wani
aiki (umm su Murad manya๐Ÿ˜๐Ÿ˜œ)


tare suka tafi da Fulani lokacin Murza anji jiki duk da taji sauki amma tayi yar rama...

Irin yanda ta dinga tarerayar Maysam ke kace ta sadudane ita ko da ga ranta tana ta kisima abubuwa da dama ..dan har yanzu bata bar munmunan qudirinta akan Maysam ba..

Ita kuwa Maysam yarinta me dadi ganin yanda Murza take yimata yasa ta dan saki jikinta se dadi takeji wai yau ga Murza na mata magana me dadi ba hantara harda tafawa..


Itade Fulani kallonsu take amma bata yarda da tuban Murza ba.....

Nan kuyangi suka shishigo da kayan marmari da abinci iri2 ..

Murza har wani lashe lebe take dan kwadai taga abubuwa..

Basu jima sosai ba Fulani tace su tafi ..

Maysam badan tasoba sedan batason yiwa Fulani gaddama..

Tundaga wanna lokacin kusan kullum se Maysam tazo ganin Murza i zuwa yanzu ta saki jikinta sosai da ita...ita kuwa Murza se dariyar mugunta take kasa2..tana fad'in shigo2 ba zurfi shegiya me kama da aljanu..ai sena rabaki da wannan mijin zakisan ni Murza yar bala'i ce( Allah de ya shirya)






๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน




A bangaren su Madina kuwa Lokacin da sukaji labarin Accident din da Murza tayi waziri ya garzayo a b'oye...

Nan ta bashi kullin magani tare da gaya mishi yanda za'ayi dashi...suka kuwa sheke da dariya kamar ba a likita suke ba...nan ya sake zube mata wasu kudin tare da alkawarin zasu na kula da ita a boye har ta warke garau dan suci gaba da cin karen su ba babbaka..

Lokacin da waziri ya kaiwa Madina wannan labari ba karamar mjrna tayi ba harda d'an taka rawa tayi..

Nan suka tsara yanda zasu turara hayakin....waziri yace kinsan shegen nan.akwai shi da son zuwa lambu bayan la'asar ..kinga se a turara a hanyar..

Wani murmushi Fulani tayi tace aikin ka na kyau kaga yanzu karfe biyu kenan nanda awa biyu komi ya kammala...shege inbe mutu ba ma to mu kawar dashi daga masarautar..kaini dama haukatar dashi tasa akayi ..

Waziri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login