Showing 99001 words to 100341 words out of 100341 words

Chapter 34 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

945

akayi sunana ya koma Murad..kuma wani lokacin zakiji su Mahmud na kirana da MΒ² to shima yana nufin MUJAHEED & MUNIRA kar yanda yake a cikin Zoben mu

Wayyo dadi kashe Maysam kai ita bata masan dami zata saka mishi kan irin son da kaunarta ta da yake dan ta tabbata ko makawa babu yafita sonta .....

Bayan wata shida naga su Mufeedah se jan kafa ake don cikin su ya shiga watan haihuwa ....ai kuwa cikin satin su duka biyu suka sambalo yaran su duka maza zo kaga Murna wajen su Mark baki har kunne ..dole anan akayi sunan dan ana tsaka da school babu damar komawa gida....a tsakanin su sukayi yar walimau se yan Uwa da suka zo daga Niger dan sunan ...anci ansha kowa yana cikin murna da jin dadi yara sunci sunnan kakkaninsu na wurin uba dan Mahmud sunanshi MUBARAK yayinda dan Mark sunan shi MANSUR ..inka dauke Maysam dake kwance ba lafiya ...har su Maryam na tsokanarta wai kode wani ciki ne ....

Batade ce musu komi ba dan ita kanta abunda take zargi kenan aman dan ta kwantarwa da kanta hankali se ta ce ai tana shayarwa kuma ma ai malaria ce....


Kai abu de kamar wasa jiki yaki yin sauki shide Murad ya gane komi sede yana son tabbatarwa dan haka yau tun safe suka jeya gwadata..ai kuwa abunda fulani ke gudune wato de Maysam na dauke da cikin wata daya da yan kwanaki ....Maysam suman tsaye tayi ..bazatce bata son cikin ba aman duka duka ma danta watanshi shida ace kuma yanzu tana da wani cikin ...

Murad kam Murna kamar mi ..ya kalleta yace ya naga bakya murna ne da cikin ko bakya sone..
Da sauri ta girgiza kai sega hawaye shar3 tace yanzu duka ma fa Muhammad watanshi shida ace nayi mishi kane ni walahi ina tausayin shi..

Ajiyar zuciya yayi yace inde wanan ne kada ki damu ki ci gaba da bashi nono akwai maganin da zanki baku komi bazeyi ba yana cika shekara daya semu kaywa Mom Ko Momy yaye ko tunda yana cin abincishi?

Dafe kirji tayi tace baby na shiga ukku bade Momy ba dan walahi fada zatayi dan seda ta gwasileni gashi yanzu kayi mun wani cikin dama Momy ta fada..

Haba mi zeyi inba dariya ba seda yaga tana kuka da gaskenta tukon yayi shiru tare da lallabata ya kuma sheda mata se akaishi wurin Mom..


Haka kuwa akayi yana cika shekara guda lokacin sun zo gida vacation sun yanke ranar birtday zata yaye shi ..su duka ukkun ranar birtday din dayane dan haka sosai aka shirya wa wannan birtday din har su Mom seda sukazo ..anci ansha sosai .da daren ranar suna zaune a daki su hudu da cikon Muhammad din na biyar Murad ya dauko jakar kayan Muhammad ya dau keshi da ga cinyar Maysam din ya bawa Mom yace Mom ga da nan mun baki renonshi dan yau aka yayeshi ...

Ba Momy ba har Mom kallon mamaki take binsu dashi..tayide karfin halin cewa da wasa kake yaro duka ma shekara daya yau kace kun yayeshi a ina kuka taba jin haka ...

Maysam kam tuni tayi hanyar waje dan tana jin kunya dan tasan Murad se ya tona asirin...
Ai kuwa bata kai ga huta ba Mom tace dawo ki zauna ...

Sum2 kamar munahuka ta dawo ta sadda kai ..

Momy tace Murad3 walahi ka fita a ido in rufe bana son shashancin banza daga kai har ita kuruciya na damunku walahi..

Sassauta murya yayi yana bawa fulani hakuri tukon ya sanar da ita cikin Maysam din..

Gaba dayansu sakin baki sukayi suna kallon su ..Momy tace haba ni kam daman nasan za a rina koda kuka zo nayi zargin cikin to senaga ita me jariri se kuma tayi shiru da ga haka basu iya cewa komi ba se addu'ar Allah ya raba lafiya sukayi musu....


🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹
Five years later(5ans apres)


Yau ake walimar rantsar da sabbin doctarorin anan jami'ar England inda triple3 aka basu lambar yabo ita Maysam Cardiologist tayi ,Mufeeda gynecologist yayida Mariyam tayi pediatrist...aman fa abun mamaki su duka da nan cikin su kui2 kamar hadin bakin ....duk sun kara girma sun zama wasu mayan mata bulbul dasu a raina nace kai mazajenku sun iya kiwo faπŸ˜‰πŸ˜œ

Murad ke rike da yaransu su ukku babba de na gane Muhammad se kuma twinx mace da namiji da kadan ya fisu tsayi wanda naji yana kiran su MUHSIN DA MUHSANA yaran bade kyauba sun kuwa sha alkyaba .

Mark ma yana rike da yara biyu Mansur da kuma wata beauty baby me sunan MANSURA ..Shima Mahmud din yana rike da Mubarak da kuma wata baby MUSULMA..... kai yaran de kamar na sace su na gudu dasuπŸ˜†


Gaba dayan su suka tattaro suka dawo kasar su dan sunce suna kishin kasar yayinda zasu fara aikinsu anan cikin asibitin masarautar bisa alfarmar da Maysam ta roka wajen su.....walima ga garuma aka shirya musu wanda kuma a ranar ne za'ayi wa Murad nadi dan sarki yayi murabus acewarshi ya tsufa ya barmishi..

Tode MURAD YANZU shike mulkar garin yana iya kokarin shi ganin yayi adalci da temakon talakawonshi ...sede abu dayane yake damunshi rashin zaman gida kullum yana fada ..shikam ya fiso kullum yaji shi kusa da sweetbabynshi ..korafi kam kullum tana shanshi dan se dare yake samun sararr kasancewa da ita se kuma inya saci jiki daga fadar ya lekata..

Yauma kamar kullum da dare suna zaune suna hirar wanda duk yawonci korafin ne ita kuma tana lallabarshi ..yana famar rumgumeta ta matsa tare da nuna mishi yaron su da suke kallon tv..dan muskutawa yayi yayi kasa da murya cewa yaron nan fa suna san shiga hakki shi..dariya tayi tace kadeyi a hankali dan yaron nan wayo ne dasu ..ba jima ba ma suka yi bacci anan dan haka ta kira bayin suka kaisu dakunan su ..komi suka kashe suka shiga dakunan yaran suna tofe su da addu'a sannan sukayi nasu dakin seda suka kimtsa komi suka bi lafiyar gado ...kamar wani abun arziki Maysam tayi firgit ta tashi zaune . .shi kanshi Murad din seda ya tsorata yace wife lafiya kode haihuwarce?

Girgiza kai tayi tace a'a. Daman wata tambaya nakeson yi maka ne ...

Umm yace dan yana wani shahsafata ..

Maysam tace wai dan Allah dole ne seka kara aure ?dan naji cewa wai sarki dole ne ace akkala yana da mata biyu kwalla harta cika mata ido ..

Murad dake kokarin kwantar da ita yace pls ki bar maganar nan waya fada miki ne. ..

Maysam tace a'a nide ka amsa min tambayana ..

Shi abunma dariya ya bashi yace a'a ni kam banida ra'ayin mata biyu ke kade ma kin ishen kaina baze iya daukar hayaniyar mata biyu ba ke ke kade ma a matsayin biyu kike da Swetbaby da Maysam dita sede ko kwarkwar zanyiπŸ˜ŽπŸ˜ŽπŸ˜….

Zumbur Maysam ta mike tace what ?

Yanda tayine seda gaban Murad ya yanke da sauri yace share zancen nan wasa fa nake miki ke kade ma kin isheni rayuwa so pls baby mu bar maganar nan haka ..kinga wani ikon Allah babyna SANADIN ACCIDENT na rasaki kuma SANADIN ACCIDENT na kuma samunki dag haka ma kina ba kanki amsa cewa dan ni akayi kuma nima haka kai Allah abun godiya daganan kuma Murad ya shiga koyar da ita sabon pratical ina ganin haka nace to nima baru na barku haka ya isa ko .. Se min hadu a sabon littafina me zuwa SO SOON insha Allah..

TAMMAT ALHAMDULILLAH . anan na kawo karshen wannan littafin kurakuren dake cikin shi Allah ya yafe min..

For correction or comment:+22799951593

Godiyar DA gaisuwar ban girma zuwa ga :
Yayana MUJAHEED
YAYA HAYAT(admins of admins)
Ya AHMED GUMEL
YA YUSUF
IBRAHIM ABDOURAHAMAN
AA DBOY
ZAHRA
HADIZA TUNAU
MAMAN SHUREIM
MAMAN AFNAN


BAN manta da kuba

*RAMATOU,LITTLE BALKISSA,SAMIRA,ZARA.DIZO,SARGA,N.FATCHIMA,SARAH,SUMMAYYA,MAMAMAN SS,MAMAN IMAN,UMMI,DALA,HAFSAH NASSIR,RAMATOU &FATIMA MUNICIPAL,SAFARA,KADI,NAFISSA,SALAMATU,HALIMA,FATIMA HASSAN,HAJO,MEENA,SUMAISU,DR FATEE,GARKUWA,UMAIMA,ZAKIYYA ABDULKARIM,SALIHA,ZEINAB SULEMAN,HASSAN,SAKINATOU,MAMAN ISLAM DA DJAMILA,MARYMA,AYSHA,HAIRAT,MAMAN JANNAT,UMMU AIMAN,PRETTY.IRSHAM,MAMAN JIDDA,AISHER DZ,DADY'S GIRL,ETC...*. kai masha Allah kunada yawa fa wanda basu ji sunan su ba kumun afuwa kuna rai ina yin ku irin more totaly din nan❀😍😍😍😍😍😍😍

Subahanakallahuma wa bi hamdika Ashhadu an lailaha illaha iila anta astagafiruka wa atubu ileyka...

Ni FASMA NACE INA YINKU ❀❀❀..
TAKU HAR KULLUM FASSOUMA YAR MUTAN ZINDER.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login