Showing 81001 words to 84000 words out of 100341 words
fadin kujiye mun yara da iyayi...
A tare suka kama haba suna dariya sukace seku matan aure ....muma de nan da wata biyu ne ..
Haka suna ta tsokanar junansu ta haye sama ..
Dama duk da basa shiri aman kullum seta gyara mishi dakin shi .....kafin sallar magarib ta gama kominta tayi wanka aman kuma tana da yakinin baze shigo yanzu ba dan tunda abun ya faru baya dawowa da wuri..
Ta dauko wayarta ..da kamar ta kira se kuma ta fasa ..can de tura mishi da text nin inze shigo ya taho mata da garin kwaki irin nan ranan dan yau shi babyn ka keson ci...
Lokacin daya karanta har yaso yayi forget da ita to amma se yaji baze iya ba musaman dayaji tace babyn shi..dan haka ya biyo mata dashi ..
Bashi ya shigo gidan ba se goma ..lokacin har ta fara baccin anan palon ..
Ya so kyaleta se kuma ya tada ita ya bata garin ...
Kin karba tayi se ma zuba mishi ido datayi kamar yaune ta fara ganin shi duk yayi yar rama ...shima kallonta yake ta dan rame da ga wuya aman kuma kirjinta da bayan ta bulbul da su ..
Ya sauke ajiyar zuciya yace sakonki ne amsa..
Kin karba tayi cike da shagwaba tace to wa kakeso ya hada mun ne ..
Girgiza kai yayi dan ya lura yau rigima takeji ..bece komi ba ya tashi yayi kitchen dan kamshin turarenta fizgarshi yake.....
Hada mata yayi ya bata ....
Tana kalloshi tace to waze feeding dina ..
Abun nan fa baby ka ne kesan sha fa..
Zama yayi kusa da ita ..ai kuwa ta dane cinyarshi ta bude baki ya samata ...haya yayi ta bata a bakin
Kallonta yayi yana shafa kanta yace baby nane kade . ke ba naki bane
Kanta ta kwantar a kafadarshi tace nawane mane...
Ajiyar zuciya yayi yace pls Wife ki aje rigimar nan muyi renon cikin nan cikin so da kaunar junan mu ..wly ina son yara dayawa kuma kinga ke kade nake dashi ..na rigaya dana rufe pls ki bar cikin nan ki haifa mun shi..ina matukar kaunarshi
Wani kallo tayi mishi tace hum kace haka mana. .ko ka manta waccan lokacin kace daga wajen yarinyar daza aura kake ..shine kuma zakazo kana mun dadin baki ..
Ajiyar zuciya yayi yace keman kinsan na fada ne dan naga ko zaki sauko aman bazan iya kara aure ba .....
Tana hawaye tace to ai kuwa ka cutar dani ranar dan tun lokacin bacci bana iyayi senaga shigowar ka ..
Share mata hawaye yayi yace am sorry wify ni ma se bayan na fada na san ban kyauta miki ba ..kuma nima ai ba wani bacci nake ba ..kullum cikin dare sena bari kinyi bacci nake shigowa na ganki ba karamar azabtuwa nayi ba ..
Maysam tace baka kaini ..dan nayi missing dinka alot ..pls kayi mun alkawari komin rintsi baza mu sake yin nisa da juna ba. ..dan bazan iya rayuwa ba kai ba ...
Suka rumgume juna yace i promise you..
To ya zancen cikin ne ya shafa shi..
Hannunta ta dora bisa nashi tace ina sonshi nima dan duk abunda kake so ina son shi dama tsoron haihuwa ne nake ..kaga gani karama kada naje na mutu ko kuma nayi yoyon fitsari na tsufa da wuri kace bakayi dani..
Dariyar farin ciki da murna yayi yace ..to ai mutuwa tana bisa wuyan kowa kuma da kike zancen tsufa ..so nawa kike son na gaya miki badan jikin ki nake sonki ba....ki kwantar da hankalin ki kin rigaya da kisamu Murad ..
Dariya tayi tace am sorry too da duk irin maganganu danayi maka ...bazan kara ba in sha Allah ..
Rumgumeta yayi yace dama ni ba rikeki a rai ba ..to wai tsaya ma shekarunki nawane..
Tana turo baki tace saura wata ukku nayi 17..
Cike da tsokana yace yawwa shiyasa naga yarintar tayi yawa..
Bubbuga kafa ta fara ..tace kajika ko
Da sauri yace desole wify yanzude a bani abinci naci yunwa nake ji se mu shiga ki nuna mun irin missing din nawa da kikayi ...
Dining suka nufa tana fadin ni bawani nuna makan da zanyi tunda kai ma bakai missing dina ba nima to banyi ba..
Dariya yayi yace to yar rigimata to ai ni missing din ne danyi baya misultuwa ne..
Maysam tace daga yar reno na dawo yar rigima kuma...tana fadar haka tana serving dinshi
Bayan ta gama ta shiga feeding dinshi cike da soyaya kamar yanda suke da .....yace to ai ke din ce kullum da kalar rigimar da kike bullowa...sosai yaci abuncin dan rabonshi dayaci kamar haka har yamanta duk da tana yi mishi kullum ta aje ..to ai ba abinci kade yake da bukata ba har da kullawar ta fimishi komi ma
Koda suka gama tare sukayi wanka...wasan ruwa kam sun shashi kamar kananan yara ga cikinta ya taso masha Allah dan ya kusa wata biyar ....
Suka fito kowa shi ya shirya dan uwanshi ..sannan suka bi lafiyar gado .yau kam abun ban sauki dan Maysam ce manager ...,director,kuma actor principal ..๐...Murad kam dan kallon ya zama ....ina gani haka na rufe musu kofar dan gudun gardama....๐dan fa inaga kwana sukayi suna abu daya kowa yna nunawa dan uwanshi irin missing din da yayi ....
Tun lokaci suka sake shimfida sabuwar soyyaya wacce tafi ta dama ....ko tari tayi zakaga Murar ya. Wani lalace wurin tambayar mi take so .ina kema ciwo....tun tana jin kumya da mamakin abun dan ko gaban su Mariam ne babu ruwanshi ..har ta dena ....
Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin kwanciyar hanki da kaunar juna..
Yau kuma suka zana exam din su wanda har sun fara shirye2n koma warsu ..Murad ma permission ya nema a wajen aikin shi suka bashi.. yayinda mall din shi ya damka su a hannun wani manager dake mishi aiki dan ya yarda dashi kuma komi ze ringa turo mishi ta internet dan yaga yanda komi ke tafiya....danharda Mark za suzo ..dan aurenshi nan da wata ne shima ..suma su Mufeeda haka..
Niger
Yau kama duk inda ka wulga a masarautar zakaga anata shirye2 bangaren Murad kam komi seda sarki yasa aka sauya musu da daki aka gyara tsarin gidan..
Fulani kam ta saka ana shirya musu abinci iri daban2 ..
Malam Musa kam baki har kunne yar lelenshi zata dawo ..banda Murza da bakin ciki kamar ya kasheta dan ta rasa hanyar da zatabi ta cutar da Maysam din ..ga shi yanzu Musa baya barinta fita ..bare taje ta aiwatar da kudirinta..
๐น๐น๐น. ๐น๐น๐น๐น
Ana gobe zasuzo sukaje ya nuna mata mall din duk sunan Murad ne ajikin su ..yace su zabi duk abunda suke so ..nan sukayi wa yan gida tsaraba dan harda su Mufeeda...
Washe gari jigin su ya daga
A jirgin da ya saya na can za suzo dan su Momy su ganshi ...
Suna cikin jirgin Maysam ta rike hannushi me zoben tace yaya ka tuna mun da munje na nuna maka nawa zoben dan kaga da gaske nawa yafi naka kyau..
Dariya yayi yace inSha Allah ..Allah de ya kaimu lafiya nima ai na matsu dana ganshi dan saboda na tattance wani abu..
Seda suka sauke Mariam a Maradi tukon jirgin ya sake dagawa su iso Zinder...
To nima bari na daga nawa jirgin haka ko๐.
Love you allโคโคโค๐
Fasma ce ๐(FASSOUMA)
[18/08 ร 00:27] FASMA๐: ๐ *STAR WRITER'S ASS* ๐โจ๐
( _Home of spรฉcial ๐ก&extraordinary writers_ )
๐น๐น *SANADIN ACCIDENT* ๐ฅ๐๐น๐น
S.W.Aโ
๐ณ๐ชStory&Written
by
*FASMA* ๐ณ๐ช
Dedicated to all my fans๐โค
๐
ฟ103__104
```Manzon Allah (SAW) yace''idan na umarce ku da wani abu ,to ko zo dashi gwargwadon ikonku''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi```
[17/08/18 a 23:01]
Wajejan sha biyu na rana jirgin su ya sauka a zinder ...zo kaga murna a masarautar musaman wajen fulani da m.Musa dazega tilon y'arshi bayan kusan shekara guda ...bakin nan har kunne sab'anin Murza dake ta yake ..bata gama shiga bakin cikin ba seda taga Maysam tare da Murad ga cikinta daya dan taso ..har mumurza ido take wai ko mafarki take (ni kuwa nace mutum da matarshi to miye na wani mamaki tunda de badan ya kalleta a ka aura mishi itaba)...take ta ayyana wani mummunan kudiri a ranta...har da wani murmushi mugunta tayi
....fada suka fara sauka ..suka gaisheda Sarki ..cike da murna da d'auki yake amsawa bare dayaga Maysam da dan cikinta ..dadi ya gama mamayeshi ..ze samu jika
To hakan ne ma a bangaren M.Musa dan yayi murna ba kadan da ganin yar shi ta kara girma tayi bul2 alamar hankalinta a kwance yake ga kuma albarkar aure ....
Addu'a sukayi ta musu tare da saka musu albarka ....dagan nan bangaren fulani suka zarce ..itama tayi farin cikin ganin su ..ai kuwa Maysam na ganin Momy ta makalkale mata ta shiga zuba mata shagwaba...ita kuwa se lallabta take bare da taga cikin ya fara tasowa sosai taji dadi ...tace babyna mi kike son ci ne..?
Tana dariya tace hadin boss zansha Momy....
Momy batayi nauyin baki ba tace miye kuma wani hadin boss...
Maysam tace Momy ai shi yaya ya sanshi kawai ki sashi ya hadamun ..dan dama cewa yayi ai da zarar mun dawo ze dena mun wasu kana nan hidimar saboda bayi da dogarai ..har da yar kwallarta
..
Murad dake kallon su tun dazu bece komi ba se yanzu da yace pls Momy ki rabu da ita rigima ne kawai take ji...
Can de fulani dataga abun bana karewa bane tace su tafi su watsa ruwa se suci abinci ..in su huta daga baya sa yi hirar...
Maysam dakinta na nan bagaren fulani tayi niyyar shiga ..dan yanzu tana bala'in kunyar fulani bazata iya binshi ba a gabanta ..
Shima da sauri ya sha gabanta yace miye kuma haka my wife .kin fa sani na saba da jikin kusa dani ..ina shakar daddanan kamshin nan naki..ya kama hannunta yace mutafi can inda zamufi sakewa kinga nan Momy nanan ....kuma zan hada miki hadin boss kasa2 yake mata maganar aman ba karamar kunya ya bata ba dan se gani take kamar fulami na jinsu ..dan haka seta saci kalon fulani se taga hankalin ta baya ma kansu dan haka cikin sauri sum2 ta fice ..shima Murad ya mara mata. Baya..harda yar rawarshi
Duk abunda suke fulani na lure dasu kuma taji dadin hadin kan da suka samu tare da kaunar junan su ..nan ta kara yi musu addu'ar Allah ya qara basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba...
Suna kuwa zuwa ta aza mishi rigima dole ya hada mata dama ya taho mata da garin tun can...tare suka yi wanka ..sede tun kafin su kwanta aka fara kiran sallar dole yayi alwala ya fito masallaci itama tayi tata nan gida tukon suka bi lafiyar gadon....
Haka suke kullum a tare makale da juna ko a gaban fulani be hana wa ya nuna mata soyyaya itade ji take kamar kasa ta tsage ta shige dan kumya shi kuwa ko a kwalar rigarshi ..
Fulani ma kam se de ta kau da kanta daga wata rashin kumyar tashi .....
Bayan sati da dawowar su suna palon bangaren su ..Mysam dake zaune a cinyarshi tana zuba mishi kukan shagwaban da bashi da dalili ...can ya kalleta yace to ki nutsu muyi wata magana..
Tsayar da kukan tayi ta tattaro hankalinta gaba daya wajenshi..
Gyaran murya yayi yace ya zancen zoben ki ne naji ki shiru ne...
Dafe goshi tayi tace laaa Muradina ai na manta da shi aman bari naje na dubo shi dan yana dakina dake bangaren Momy...
Murad yace mutafi to na raka..ki
A tare suka shiga dakin ..aman sukayi ma zoben neman duniya basu samu ba...ita kam har ta gaji dan neme2 da tayi..
Kamota yayi ya zaunar yace ta bari shi ya ci gaba danema ..aman de kin tambbata anan dakin yake ..
Tana meda numpashi tace ee to ina de kyautata zaton anan din yake sede bana tune inda na saka shi ne
Ci gaba yayi da ne ma aman shiru...
Can sega fulani ta fado dakin jin sukurniya a dakin ..turus tayi ganin Murad da kanshi ke neme2..
Tace son lafya kuwa...
Jiki a sanyaye yace Momy zoben wife muke nema ne..
To amemakon ka saka kuyangi suyi se kai da kanka ..
Momy baza ki gane ba ..zoben ne ai bana so wani ya ganshi kafin ni..
Girdiza kay tayi da abun nashi se shi......tafiyar ta tayi ta barsu nan..
Jikinshi duk yayi sanyi dan yaso yaga zoben nan yau..aman dole ya hakura ..
Maysam tace am sorry hubby na baka wahala..ina ga fa na barshi a Maradi da mukayi patyn mu na karshe ina ga yana can ..
Ajiyar zuciya yayi yace shikenan ki shirya se mu tafi sati me kamawa ...cike da murna tace to dama kuwa har nayi kewar su Mufeeda..
Aman kuma ganin damuwa a fuskarshi yasa taja shi zuwa bayin dakin dan duk ya hada zufa abunka ga wanda be saba wahala ba..
Wanka suka yo ..tanata janshi da hira ko ze saki ...ta koyi nasara har da dariya ya shigayi yama manta da wani zobe ....nan tashiga yi mishi cakulkuli suna ta dariya abunsu...daga nan kuma wasa ya fara canzawa a zafafefe Maysam ke aikawa Murad da sakon ni..(kai yarinyar bakida ta ido fa๐
.).na so yau na doko muku aman se rasa ta ina zan fara dan yarinyar nan ta fice tunani na ..ina ganin haka na canza takuna na ja musu kofa .dan pratical se manya ..
...
Sede Kash basu samu zuwa a satin ba dan asibityn na nan masarauta suka dinga samun emercency kuma duk na fanin shine ....ga doctor din me kula da wurin baya nan ..dole tasa ya kama aiki har zuwa lokacin dawowar doctor din..dan clinik din tasu tafi sauran kayan aiki .shiyasama duk wani emercency daya gagari sauran se aturo su nan...haka ya hakura kullum cikin buzy yake ..ga kuma rigimar Maysam a gida... ..itace goyo ,kokuwa ta aza mishi kukan se yayi mata doki ,kai shirme da rigima iri2 take mishi ..
Seda yayi sati biyu doctor din ya dawo ai kuwa a washe gari suka daga se Maradi .fulani kam tayi fada a cewarta zasu wahalar da cikin ...kuma ga bikin Mahmud aman jin acan Maradin za'ayi komi.....kuma taga Maysam ta nuna tana son zuwa dan aure su Mariam saura one week .na Mufeeda kuma ..kwana goma ..seta kyalesu...
Ba karamar Murna sukayi ba da ganin junan su ba...
Wani abun mamaki be huce zoben dabaya nan ba ..shima duk sun burcike dakuna sun bar kuyangi da aiki amam babu zobe ...Maysam har da kwallarta ganin ta batar da zoben.....kai daga karshe ma Murad hakura da zoben yayi ..tunda daman da kamar wuya ace na sweetbabyn shi ne..shiyasa ya rarrasheta aka bar zancen shi
Maysam tun zuwan su ta shiga hidimar bikin Mariam da dan cikin ta se shiga da fice suke itada Mufeeda ..in sun mata magana tace to suwa zasuyi in bata kama ba..
Se kuma dare in yayi ta addabi Murad da jikinta ciwo yake mata dole se yayi mata massage..shi kanshi wani lokacin mamakin kanshi yake yanda yake biye mata ..(hum macen kenan Murad๐)
Har lokacin kuma Mark be taba zuwa ganin *zab'in iyaye*(littafin my my Fatima yar kasarmu๐) n shi ba ..yaude Dadyn shi ya ritsa shi ..tunda yake ta mishi fada be dago ba se yanzu .dayashiga bawa dadi hakuri.hum wai kunsan waye Mark kuwa?
Ku biyo ni de
..dole yaja Mahmud ya rakashi ..da yake ya dawo shima ...dan Murad yana can yana fama da Maysam dake dan zazzabi gajiya
Mark ke jan motar dan shi ya san gidan......koda sukazo sukayi horn me gadi ya bude musu kofa ...
Shi de Mahmud ya cika da mamaki dan yasan san nan gidan su Mariam ne tripleM...aman se beyi magana ba
Mahmud yace to ka kirata ta fito mana..
Ya tsine fuska yayi yace nifa banida numberta hasalima rabona da ita tun tana yar mitsitsiya da ita ...
Ya kuwa kwashe mishi da dariya...yace kana da aiki kam
Suna fito wa daga motar akayi sa'a sega wani kaninta yazo ze fita..dan haka suka aikashi ciki ...
Iso akayi musu anan palon ..ummanta da yayunta ne a palon dan haka har kasa suka gaishe su..sanan wata kanwarta tayi musu rakiya bangaren baki...
Mariam kam tun lokacin da taji wai Ma'aruf yazo ..se ta tsinci kanta cikin bakin ciki dan aganin ta ai reni ne wanan ace se ana sati sauran aure sannan ze zo ..badan ummata bace ta gaya mata da bame sata fitowa..
Wani katon hijab ta saka babu ko kwalli a idon ta ..yayunta na mata magana aman ta kyallesu ga babu su Mudeeda sun tafi bare su rakata..dole ta fito ta shiga palon da sallama ..kanta a kasa tunda ta shigo dan bata ma son ganin shi..ta gaishe su
Mark kam tunda tayi sallama ya zuba mata ido ..miyan bakinshi sun kafe..
kuma daga shi har Mahmud babu wanda mamaki be kusan kashe shi ba..yama kasa magana dan duk gani yake gizo ne take mishi ...shi kuwa Mahmud mamakinshi dan yana labari soyayyar su ta can england
Mahmud daya lura da haka se shi ya amsa ta tare da fadin tripleM ykk ya shirye2.
Da.sauri ta dago idonta dan ta gane muryar Mahumd ..aman abunda ta gani ya kara bata tsoro ...sororo take kallonshi shima haka ..
Mahmud yayi dan murmushi tare da tafa hannushi. Firgit suka dawo da tunanin hucin gadin da sukayi. ..kowa yana jiran bayani daga bakin dan uwan shi..
Shikam daya ga abun bana karewa bane se yace to Mariam ga abokina Ma'aruf Elh Ma'azu kuma dan abokin abbanki kamar yanda kika sani kuma shine wanda ze aureki ...
A tare suka sauke ajiyar zuciya ..aman kuma sun kasa magana ..se sakin murmushi suke akai2 ..
Mahmud yace to ni ina mota idan kun gama kurmaci se ka zo muta fi..
Yana fita Mark ya matsa kusa da ita ..yace lovely ta kinga wani okon Allah ko?Alhamdulillah ashe addu'ar mi bata fadin ba ..shiru tayi ..yace baza ki mun magana ba ..se lokacin ta dan saki..nan fa hira ta barke har sun manta da wani Mahmud bare su tuna da ba a daura auren su ba ..hirar masoya kawai suke sharba..
Har goma da wani abu shima seda Mahmud yayi mishi magana ne kamar kar su rabu haka suke ji ..
Ai