Showing 87001 words to 90000 words out of 100341 words
tana saurarenshi har ya gama ...tana kuma yaba hankali irin na Mahmud tare da jin dadin kasance warshi aboki ga danta..
Fulani tace yayi mata bayani .abunda ke faruwa..
.nan ya gayamata yanda sukayi da doctor ...itama bata ji dadi ba aman ba ta tsammani Maysam zata iya aikata haka ..kai ko in hakan ne ma to dawani abu akasa..
Maysam kam kara volume din kukanta tayi tana fadin walahi Momy ki yarda dani ban sha maganin komi ba....
Ajiyar zuciya Fulanin tayi tace ya isa haka to ..na yarda dake my dauther sannan kiyi hakuri kan abunda yayi miki.kinji ranshi ne ya bace . aman komi ze zama nml ..kada ki tada hankali ki mijinki yana da saurin yin fushi kuma saukarshi ma ta kankanin lokaci ne ..ki kyaleshi yanzu har ya sauko..shida kanshi zakiga ya dawo
Rumgume Momy tayi tana sauke ajiyar zuciya ..tace walahi Momy ina son cikin nan. ..taya uwa zata iya kashe danta ..
Nan de Momy tayi ta lallaba ta ..
Momy a ranta kuwa tausayin Maysam take ..gata so young aman da kaifi tunani ..shiyasa take jinta sosai a jikinta dan tana sonta ..
To inbama rashin hakuri na Murad ba ai komi tayi se kamata hakuri da izuri ka kumsawa yarinya ciki kuma harda duka ..to dami zataji ..ne.. Allah de ya kyauta...
A ranar ma akayi decharge din su direct dakinta na bangaren Fulani ta koma dan acewarta mutumin da bayason jin muryarka ma to ai in ya ganga abun se yafi haka ..dan haka ta kudurta zata bashi space kamar yanda ya bukata ..kuma bazata kara nemanshi ba inde har bashine yazo da kanshi ba......ta sani ya kwallafa rai akan cikin nan to aman ai ya dace yayi bincike kafin ya yanke hukunci . ita aganin ta koshi ai be kaita san cikin nan ba ..dan babu wanda ya kai uwa son danta se mahalici mu ..to wai ma tayaya ze ce wai ita tasha magani zubar da ciki ..wata zuciyar tace ai dan kin nuna tun farko bakyaso ..badan haka ba ai da baze zarge ki ba..haka de tayi ta tunanin ta..
A bangarenshi kuwa se bayan yayi abun yayi nadama ..ai ko ba komi wifyn shi ce ..ya kamata yayi mata uzuri sannan ya lallabe ta ko zata gaya mishi miyasa ta aikata hakan ..se kuma wata zuciyar tace batada wani hujja .kawai dan ta bata maka rai ne.....
Se kuma dayar zuciyar tace to ai rabin zuciyarka ce kaga yanzu kasakata kuka may be ma tana can tana yinshi . ..ai da sauri ya juya ze koma se kuma ya tuna maganar Momy cike da sanyi jiki ya koma cikin masarautar..
๐น๐น๐น๐น. ๐น๐น๐น๐น
A bangaren Murza kam ba karamar murna tayi ba da taga anyi likita da Maysam dan tana labe daman .Allah2 take taji labarin barewar cikin aman setaji akasin hakan..ranta yayi mugun baci aman kuma data ga yanda Murad din ranshi ya bace se ta danji dadi2 acewarta kafin su shirya zata hada wani target din ta zubar dashi gaba daya ..inya so se ya koro ta....tun nan ta shiga tsara yanda zatayi. .
Dan munafinci so biyu tana zuwa duba Maysam da tana likitar kuma tunda aka sako su kullum.setaje .
๐น๐น๐น. ๐น๐น
Malam Musa kam da me martaba basu san wainar da ake toyawa ba ande cemusu bata ji dadi bane..kjma sun mata ya jiki
...
Bayan sati da faruwar hakan Murad yaji baze iya jure rashin Maysam kusa da shi ba....duk ya fara dan ramewa dan bawani abinci kirki yake ciba dan ya saba da nata se yake jin wannan din bashida tast...dukda kuyangi na gyara mishi bangaren aman ba kamar yanda wifyn shi keyi ba .. dan kuwa ko tsohon cikin ta baya hanata gyara bangaren tsaf ..shi kanshi ya san yayi dace da sa'ar mata ...dan haka yau tun safe wurin Fulani yaje .yayi ta bata hakuri kan sharin shedan ne hakan bazata sake faruwa ba ..sannan ya bukaci data bashi matarshi..
Fulani tayi murmushi ..tace har ka gama fushin damu kenan ....to nide bakayi mun komi ba kaje ka bawa matarka hakuri sanan intace zata koma dakinta to ni mi nawa a ciki ..kajede ka lallasheta kawai..nan tayi mishi yar nasihohi
Cike da kwarin guiwa ya nufi part din ..lokacin tana tolet ..zama a bakin gadon yayi yana jiranta ..
Tana fitowa taganshi ai kafin yayi wani yunkuri ta koma ta datse kofar ....nan ya shiga kiranta ta bude mishi aman yanda kasan bada ita yake ba..haka ya gaji ya fita..
Murad be san abun nayi ne ba seda yaga ya shafe wata guda harda kwana ishirin Maysam taki kulashi kai rabon daya ganta ma har ya manta dan bata fitowa. Se yabar bangaren ..har karar ta yakai wajen sarki ..wata rana da dare suna hirar su shida fulani kamar kullum ya shigo bayan ya kwashi gaisuwa ne ...yake gayawa sarki shi fa ya a meda mishi matarshi ..
Sarki ya kalli fulani da alamar tambaya ..wayen cewatayi da fadin mistake ne suka samu a tsakanin su ita kuma tayi fushi ta dawo bangarena ..ta kalleshi tace ko ni na rike maka mata ne..
Ya sadda kai tare da girgizawa..
Murmushi sarki yayi irin nasu na manya yace to kai son kawai kaje ka lallabeta mana..kasan su mata seda da lallaba
Yace Dady nayi fa taki hakura kawai kasa baki ta koma..
Sarki yace bazan tirsasata ba itama ya ce kuma bansan mi ya hadaku ba ..kuma ma ai ba'a gajiya da lallaba mace ..kaci gaba da rarrashin ta zata sauko bare ma su mata akwai su da tausayi da raunin zuciua....yayi kasa da murya yanda Fulani bazata jiyo ba yace bari na gaya maka wani secret irin na mu na maza yanda zaka shawo kanta cikin sauki ..
Kasa2 sosai yake mishi maganar wanda ni kaina banjiyo ba . nade ga Murad na wani sunne kai irin na inkaji kunyar nan ..yana kuma murmushi kasa2..
Fulani kam kallosu kawaitake cike da birgewa ..
Yana gama fada mishi ya mike ya fice har ya kai kofar futa Sarki yace kada kaji komi zanji da tanan din ..wuf ya fita a palon dan yau dadyn nashi ba karamar mamaki ya bashi ba ..daman tsofi ma sun iya soyyaya haka..(ni kuwa nace zauna de nan ai fulani da sarki se a hankali dan ko kallon juna suke zaka iya hango tsantsar kaunar da sukewa juna..๐..)..
Direct bangaren fulani ya fice ...lokacin Maysam zat shiga dakinta ..
Be bari ta ganshi ba ..tana shiga direct tolet tayi ..shima kuma wuf ya shigo dakin ..ya saka key ya kulle....dede kofar tolet din ya labe bayan labule dan kada ta ganshi ta koma.....
Tana fitowa ya shaki kamshin turarenshi ....har wani lumshe ido tayi dan tayi bala'i missing din turaren ...batayi zato ba taji an rumgumeta ta baya ...ta kuwa bate baki zata yi ihu da sauri ya rufe mata baki tare da fadin nine mijinki ..
Ai kuwa ta shiga kiciniuar kwace kanta. ...
Ganin haka yasa ya sake ta dan kada taji ciwo...tana kallon shi kallonirin na mi kake yi mun a daki ...
Kalar tausayi yayi yace.
To nima de nace Happy sallah my fans..
Love you allโคโค๐
Barka da sallah ..
Bonne fete de tabaski a tousโคโค๐
Fassouma ce๐(yar mutan zinder)
[06/09 ร 05:21] FASMA๐: ๐ *STAR WRITER'S ASS* ๐โจ๐
( _Home of spรฉcial ๐ก&extraordinary writers_ )
๐น๐น *SANADIN ACCIDENT* ๐ฅ๐๐น๐น
S.W.Aโ
๐ณ๐ชStory&Written
by
*FASMA* ๐ณ๐ช
*Ina me bawa masoyan wannan littafin hakuri na rashin jina da kukayi hakan da farune sakamakon exam da aayi satin daya huce ..am so sorry na rashin jina kwana biyun nan shiyasa ma zan cire labarin na rage shi dan nayi na gama dan koni kaina bana jin dadin yanda bana typing kullum.....*
*Wanda suka yi kirana da wanda suka mun text na gode Allah ya qara dankon zumunci .. Wanda kuma bansamu damar dauka ba ina me baku hakuri kun sani ina yin ku irin more totaly din* *nan* ๐๐๐โคโค
*Yan kungiyar mu ina alfahari da ku ina godiya da irin karfin guiwar da kuke bani Allah ya qara hada kanmu .ina yinku gaba da baya* โค๐๐
_I miss you a lot my in law Xaynap queen keda my Arfat da kuma Momun Mufeedah Allah yasa kuna cikin koshin lafiya.._
Dedicated to all my fans๐โค _special my zee'' Xaynab Idris ''ba shaharariya marubuciya ..kada ku bari abaku labarin littafinta dan akwai fadakarwa tare da annashuwa da ilimantarwa (kuneme shi me sunan RAYUWAR FADILA)Allah ya barmin ke_ ๐๐โค
๐
ฟ109__110
```Manzon Allah (SAW) ya ce''za a tayar da mutum akan abinda ya mutu a kai(gobe kiyama)''
Muslim ne ya rawaito shi```
[06/09/18 ร 00:10]
Kalar tausayi yayi yace haba my lovely wife ..am.so sorry nasan banyi dedeba aman hakan bazata kara faruwa ba..ni kaina bansa don mi nayi miki haka ..aman ga fuska ta ki rama marinki ko zaki huce dan na gaji da fushin nan ..
..yi tayi da daya duniya bada ita yake ba ..dan ko kallonshi bata kumayi ba ..se ma ya yan wake2n ta ma take ...
Kara matsowa yayi kusan ta ya rike mata hannu kamar zeyi mata kuka yace kiji tausayi na ciwona na gab da tashi . .ya aza hannunta bisa zuciyarshi yace ji kiji yanda take bugawa ..pls ki mun ko magana ne ko naji sassauci akan abunda nakeji ..kin sani zuciyata bazata juri rashinki ba...nayi nadama kuma lokacin idona ya rufe ne ...
Se lokacin ta dan kallo shi ..aman batayi magana ba ..setaga har ya rame kamar yanda ta rame itama ..gaba daya tausayinshi ya mamaye ta .,.jitake kamar ta rungumeshi aman se taga kamar tayi saukin saukowa ..baride ta nan kara garashi dan ko gobe kada ya kuma yi mata haka
Dan haka bata ce komi ba ta bi lafiyar gado ma....
Yajima nan yana bata hakuri sanan ya tashi ze fice ganin ko kalloshi ta dena yi....
Dafe zuciyar yayi dan wani irin zut4 take mishi๐ ....har wani layi yakeyi kamar wanda yasa wani abu dan dishi2 ma yake gani.....
Yana gab ta fita yaji Maysam ta rumgumeshi ta baya
A tare suka sauke ajiyar zuciya ...Rikeshi tayi tsaf kamar wanda akace za'a kwace mata shi ....
Da kyar ya jiyo da ita face dinshi ..sun kusan minti biyar suna kallon juna kowa yana kokarin aikawa da dan uwanshi sako ta kwayar ido..
Can Murad ya bude baki zeyi magana da sauri ta sa hannunta ta rufe mishi bakin tace ya isa haka ..nima am sorry da yanda na shareka ..ta kai hannuta wuyanshi tace duba min wanan rama da kayi kamar wanda baka cin abinci ....
Dan murmushi yayi yace to ai kece abincin nawa..ganin ki kade ma kosar dani yake ...
Idan ina tare dake bana bukatar wani abinci dan na rayu..na saka ki kade ma a gaba ina kallon ya isheni ........kamota yayi suka zauna bakin bed ya dorata cinyarshi ko nauyinta ma bejiba.....yace '' je t'aime a la folie ma princesse d'amour...ma bouche ne peut pas dire a quel point je t'aime ni mon corps ne peut pas l'exprimer .ni mon cerveau et mon coeur ne peuvent pas compter a quel point tu compte pour moi...tout ce que je sais est que je ne peux pas vivre sans toi ..sans toi ma vie n'est rien ...''
My repiration ''je ne vis que pour toi ..si tu me quitte un jour ca sera le jour de mort j'en suis sure ma douce dulcinรฉe ''
Ya kamo hannuta ya dora a setin zuciyar shi yace dama rabi ce to ina me tabbatar miki duk ranar da kika barni to nima a ranar za'a dauki gawata. .....''sache bien que ma vie ne depend que de toi.....je place ma vie entre tes mains..je compte sur toi pour ne pas la perdre...
Maysam kam tunda ya fara magana taji kanta ya kara girma ..gaba daya se taji kamar tafi kowa yin sa'ar miji a rayuwa ....idanunta banda hawaye dadi babu abunda suke ..duk setaji babu ya ita a duniarnan ....zuciyarta wasai takeji
Tace Mon bb cheri.ina kataba jin mutumin da yayi wasa da rayuwar shi ne ..idande har zan rasaka to kamar na rasa rayuwa tane .. ..ko mutuwa ina addu'ar idan tazo ta fara daukana dan nasan inde har kai ta fara dauka to kuwa ina me tabbatar maka da nima a ranar zan bika dan rayuwata batada wani anfani inde har baka cikin ta..son dan kemaka ya fice amisalta shi ''tu es ma raison de vivre''i love you more mijina
Da sauri ya rufe mata baki yace haba kibar zancan mutuwa in har muna tare dake..ya zaki kirawo mana ita
Dan murmushi tayi tace haba ''Autan maza '' ai ita mutuwa tana wuyan. ..kamata yayi duk wani musulmi munmuni ya dinga tunawa da ita akai2 akoda yaushe dan ita dole ce komin dadewa ..
nan fa suka shiga zuba wa juna kalaman soyyaya wanda ya karasa Murad jin shima fa wani ne ...bama da inta kirashi da 'Autan maza ba ..(๐ko ba haka ba my kawali rams๐. )Se yaji kanshi yayi wani kara girma ..nan suka lalace da kalanmansu...daga nan kuma ogan niya ta shiga mishi kalon nata pratical din da ta kara koyo ko tulelen cikinta be hanata yiba ..nace tab yarinyar nan tayi nisa bata jin kira . daman an jima ba'a jiba .kun sani ai nan naja musu kofar .kawai nayi gaba abuna.
Washe gari cike da farin ciki da annashuwa suka tashi ..
Har tara na safe sunan nan dakin sun kasa fitowa gaba daya ya dabaibaye ta kuma gashi ya kulle kofar...seda ta fara mishi kukan shagwaba kan ita yunwa take ji sannan ya sarara mata yace to mikike son ci yanzu na saka akawo miki shi. ..
Turo baki tayi cike da sangarta tace ni farfesun kayan cike nake son ci kuma kai nake so ka girka min ..
Wani waro ido yayi yace ni kuma. Yana nuna kanshi. ..
Noding din kanta tayi ta kuwa shagwabe fuska kiris take jira ta saki kuka..
Zama yayi ya dorata cinyarshi yace wify kin gane ni ko kunna gaz ma ban iya ba bare aje ga zancen farfesu ...
Ai kuwa bata bari ma ya gama ba ta bare baki ta shiga rera bishi kuka wanda daga ji kasan na jin dadin rayuwane..kawai
Shi kuwa ya lalace wurin lallashi . da kyar ya shawo kanta tare da cewa to sutafi can bangaren su se ya shiga kitchen din ya dafa mata yanzu nan yana shiga ze zama abun fadin cewa ga yarima me jiran gado can yana dafa abinci da kanshi . kinga kuma da bayi birjik zasu renani ne..
Hawayen ta goge tace shikenan to mutafi dan yau girkinka nakeson ci ....
Suna fitowa suka tarar da fulani a nan falon tana kallon tv...da dan sauri Maysam ta nufeta ..Murad kuwa se fadi yake kibi a hankali fa...
Har kasa ta duka dan gaishe da fulani da kyar ma ta dukan.
Fulani bayan ta amsa tace mata way ni Maysam bakya tausayin kanki ne kina cikin watan ki fa na takwas inake ina dukawa mafarin ki kasa tashi kisa mijinki ya daureni dan naga akan cikin nan komi ze iya yi cike da zolaya take maganar..
Gaba dayan su suka kwashe da dariya Maysam tace tab ai sede ya dauremu gaba daya dan kafarki kafata ......
Murad yana turo baki yace lovely wife mutafi mana kinga bakici komi ba kada ulcer yakamin ke da little babyna ....
Tab ai kam ba karamar kunya Maysam taji ba har jitake dama kasa ta tsage ta shige ...kanta a kasa ta kyaleshi ..
Ganin haka yasa yaje ya tallabota ta mike ai kan kace mi harta fice a palon tayi sid din su ..
Murad kam dariya ya shiga yi mata ..
Fulani tace bason haka fa kaga kasa dauther na taji kunyata ko .. ..
Murad yace to ni Momy minayi kuma kawai de ...
Kafin ya karasa tace jeka kada yunwar ta shige maka ita ..
Da dan saurinshi kuwa ya fice yana fadin haka ne.. fa
Fulani ta girgiza kai cike da farin ciki a ranta tace inde Murad ne zeyi rashin ta idon nan fiye da haka ma ..dan kuwa tun be girma haka ba bayajin kunyar kowa inde akan nuna soyyayar sweetbabyn shi ce sede kai da ake abun agabanka kaji kunyar.....
Sekuma tace Allah yaji kanki '' *MUNIRA''* ya rahamceki...(๐ค๐คdaman sunnan Sweetbaby *MUNIRA* kenan mujede zuwa...)
A kitchen ya tarar da ita se hada zufa take rumgumeta yayi ta baya yana shafa cikinta yace pls zoki zauna banason kina ba kanki wahala haka bayan Allah ya yaye miki ita ...duk abunda kike so kisaka bayi su miki ....
Kashe gaz din tayi dan ta gama abunda zatayi tana kallonshi tace nasan da haka aman jifa ta shafa dede wuyan shi tace yanda ka rame gaba daya ..nasan kuma harda rashin cin abinci dan kasha fada yanzu baka iya cin abinci inde har ba na Momy bane ko nawa .. ...ka barni na maka ''hangandi''(cin abinci dan yin kiba)kafin birtday dinka dan kada aga ban iya kiyo ba cike da zolaya ta karasa maganar...
Lakice mata hanci yayi yace tab ai ni kade nason iya kware warki wajen kiyo ai ko se yayi mata rada akunne wanda banjiyo mi yace mata ba yace shi kade ma ya isheni na kiyu .har na ginu..
Kirjinshi ta kaima bugun wasa tace kai ko ..ka jika da wata magana kuma ...
Ze kara wata magana tace pls yaya ni yunwa nakeji sosai da sosai fa..
Sorry yace tare da daukan kullar abinci data dafa suka fito gaba da baya ta rike kugu shi kuma rike da kullar dan gaba daya ya kore kuyangin bangaren dan acewar shi babu wanda zega shigar shi kitchen yana dafa abinci. . kuma yanzu baza ma su kara shigowa in ba aikin goge na share na safe se kuma in an kira su
Kallonta yake cike da tausayi yanda take tafiya yace aman wife cikin nan yayi miki kyau ba kadan ba ..
Murmushi kawai tayi ..a kasa suka zauna yanaci yana kuma bata a baki ..
Murad yace yauwa