Showing 60001 words to 63000 words out of 100341 words

Chapter 21 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

926

wayar Maysam tayi ..duk se yaji babu dadi ..wata zuciyar tace mishi yo semi in ta kashe wayar ...ai k
duk lefin kane dan kana sakar mata fuska ne har taga damar renakai . kawai abunyi anan ka shareta..kai mima ze hana ka tafiyar wajen su Momy ....

Yana ta wasi2 ...can shi kade yace kai baze yiyu ba .....

Kiran sallar farko a kunnen shi ..tun da ya tashi yake ta danna mata kira amma har lokaci a kashe ..zuciyar shi ta raya mishi kawai ya iske ta school din mana..ya kuwa yi na'am da wannan shawarar..

Karfe bakwai da rabi ma acan tayi mishi ..amma cikin rashi sa'a har sun tafi daya iso ...ranshi in yayi dubu ya bace ..ya shiga motar shi yayi gida dan shiryowa office.....yana tafiya yana jan tsuka tare da buga sitiyarin motar shikade yake fadin zamu hade ne ...se kin san ni kika kashe wa waya...


A bangaren Maysam kuwa tun tashita asuba su Mufeeda suka fahimci tana cikin damuwa ..kwata2 yau bata walwala.....komi cikin fada take yinshi

Kuma gashi ta matsa musu kan su shirya yau bus din wuri zasu shiga ..ganin yanayinta yasa basuyi wata gadama ba suka shirya ...su aka fara kaiwa wajen dasuke pratical din.....


Bayan sun iso ..suka jata can wani gu inda babu sauran dalibai ....tsakiya suka sakata a tare suka dora hannuwansu a kafadarta ....
Suna kallonta Mariam tace what happen to you Maysam ?ko wani a cikin mu ya bata miki rai ne?

Mufeedah tace haba Maysam kada ki dau halin da naki ba ...tun tasowar mu muna tattala junan mu ..pls muna me baki hakuri inhar mu muka miki wani abun...ki sani komi yayi zafi maganin shi Allah. .ki yawaita fadin innalillahi. Wa inna ileyhi raju'un ...
Kuma ina me kara baki hakuri ..

Da sauri Maysam ta rufe mata baki da hannun ta ..kamar me jira kawai ta fashe musu da kuka ..

Cike da mamaki da tsoro suke kallonta ..a tare suke fadin inna lillahi.....miyayi zafi hakane wai Maysam tuni suma idon su har ya ciko da kwalla suka ce pls say something mana .....


Da kyar cikin gwanji kuka tace yaya Murad ne yayi mun kishiya.. .

Duk se suka ji wani mugun tausayinta ya dirar musu se suka rumgumeta suna lallashi ..

Mufeedah tace haba tripleM nasan kishi halas ne kuma mun san yanda kike son mijinki amma kiyi hakuri kuka bana naki bane. Lokaci yayi da zaki fuskanci miji ki ki bashi kulawar da gatan da kowani namiji ke samu..yanzu da da badaya bane ...kinsa ciwon kanki ....
Mariam tace sanna shawara da zamu baki anan itace anan shine kiyi koyi da kishi irin na matan Manzon Allah(SAW) bawai kizo kiyi ta wani tada jijiyo yin wuya ba ki tada hankalinki ki tadawa mijinki shima ....
Sanna kisani cewa su maza an halasta musu da su auri mata 4 in de har zasuyi adalci a tsakani ....Shi aure ana yinshi ne saboda asamun nutsuwa na sani kishi dole ne amma bana hauka ba. ....

Mufeedah ta kara dace wa. Kuma shi namiji inde har yayi niyyar yin auren shi to kisani ba wai fadanki da maseefar ki ,ko fushinki ze sa ya fasa ba dan a lokacin giyar amariya na layi da ,,in kinga kinyi nasara da wa'inan to dama Allah can ya nufa ba matar shi bace..dan namiji in...ko kuma inkiyi wasa ma ya tsinke taki igiyar..dan dole se kin kauda idonki daga wani abun dan gujewa duk wata fitina..

Mariam tace ina me baki shawarar da kiyi zaman amana tsakanin ki da kishiyar ki ,,dan kuwa kota cuceki Allah baze barta ba .....

Mufeedah tace sanna ki kasance macen da akullum zata ringa tunatar da mijinta kan yayi kokari ya ringa kwatanta adalci ..bawai ki zamo wacce tana kallo mijin ta baya yin dede a tsakanin ku ba amma ki kasa tunatar da shi kai har ma wai ki zanki gani ko yafi sonki ko kuma kina takamar wai ke wace abace ..to kisani duk abunda kayiwa wani to kai ma kada ka cire tammahani wata rana se am maka. ..sanna ki sani fadar ma'aiki SAW ne ke cewa
```Duk wanda yake da mata biyu se ya karkata wajen daya ya bar dayar ,,to zai tashi ranar alkiyama barin jikinsa daya a karkace''(Ahmad)...```

Tace shin zakiso kiga yayaki a haka ne duk ikirarin dakike cewa kina sonshi?

Nan sukayi ta tausarta har taji komi ya fice har da su dariya databawa suke.....
Yau kam saukar wuri sukayi dan sha biyu ma a school tayi musu...

Mufeedah tace Maysam na baki shawara mana ..
Mize hana ki kaiwa yayanki ziyara office yau ..tunda kin ga yaushe rabonki dashi kawai ki mishi suprise yau..

Mariam ta ce brain dinki naja fa..
Maysam tace to karatun yau din fa?

Mufeedah tace kuje ku biyu kawai ni se na tsaya na dau karatun in kun dawo sena koya muku...

Haka kuwa akayi bayan sallar la'asar su biyu suka shiga taxi tare da gaya mishi adress din Likitar da Murad ke aiki..

Suna nan tsaye a harabar likitar dan basu san wa zasu tambaya ba ...
Can suka tsikayo Doc Mark ...ganinshi da kayan doc yasa suka tsayar dashi...

Sallama sukayi mishi sannan suka gaidashi. .cike da fara'a ya amsa sanna Maysam tace mishi Doc Murad muke nema...

Kallonsu yayi da kyau yace yanzu kam ba lokacin visiting bane sede ku b secretair dinshi sunnan ku gobe se ku dawo...
Har zasu ...se
Mariam tace haba Maysam muda ba marasa lfy ba kawai kice ace mishi kanwarshi tazo na tabbata in yaji kece barin mu zeyi..

Ai Mark najin sunan yace kutsaya bade kece matarshi ba...

Cike da kunya ta ga mishi kai ..
Da sauri ya ce to muje na kaiku dan inyaji labarin kunzo nace se gobe nasan babu me rabani da shi se Allah..yana yi idonshi akan Mariyam kyar..

Itakuwa duk tabi ta tsargu da kallon Allah ma ya temaketa hijab dinta ya fice mata guiwa....

Yana gaba suna biye da shi har kusa da kofar office dinn..

Nan yace to ga office din nan.....Maysam tace mutafi Mariam...

Murmushi tayi tace nifa ..kawai ki shiga ina jiranki anan salon in shiga ku manta dani....nan tasamu waje ta zauna Mark ma kuwa yace kwarai kuwa to ni bari na zauna na tayaki hira ko...

Itade tayi mishi shiru ...

Ganin maysam ta doshi office din yasa na matsa kusa da ita.. ..

Kwankwasa kofar tayi ..amma shiru tasakeyi nan ma shiru kawai se ta murda ta shiga abunta
A cikin bureau di kuwa lokacin Yana tattare kaya dan ya kasa sukuni kawai gwara yaje yaga maysam....
Jin an shigo yasa ya kalli kofar yaga waye ya shigo mishi bada izini ba..
Zumbur ya tashi tsaye ganin wata tsaleliyar budurwa mai kama da yar gidan momyn shi.sak..sake baki yayi yana kallonta se kuma yaga tayi mishi kama SWEETBABYN SHI..

Maysam kam da gudu tazo ta rungumeshi har saida suka fada kan kujerar dan babu zato ..tace yayana i miss you much cike da murna.....

shi gogan ya zaci ma ko gizo ne take mishi harda dan mitsine kanshi yayi dan ya tabbatar ...shi kasa magana ma yayi , ganin bai ce mata komi bah kuma taga alamun mamakine ya cikashi


Tana turo baki Tace haba yaya wai kai bakayi kewana bane da ko magana ma bazaka mun ba..kokari tashi tayi ...

Ya kuwa kara matseta da kyar ya tattaro miyen bakinshi yace haba yar gidan momynta ni kuwa nayi missing dinki ba kadan ba..

Tunda yafara magana ta kafe bakin shi da ido (tofa Maysam gake ga bakin ci da biredin lol) ..shiru sukayi su duka kowa ya tsurawa bakin dan uwan shi ido...kowa yana zancen zuci

Ita fadi take'' je t'en suppli embrasse moi'' yayana ..ohh ni ya Allah kasa yayi kissing dina yanzu..

Shima Murad anashi bangaren fadi yake miyasa bakya son inyi kissing dinki ..a gaskiya baki mun adalci ba ..ki barni kona second daya ne mana pls...

Be ankara bah babu zato kawai saรฏ ji yayi ta game bakinshi da nata wuri guda tana tsosar abunta kamar ta samu alewa dan zuciyar ta tabata wannan shawara cewa ga dama ta samu kada ta bari ta subce mata....

Murad kam duk da abunda yake so ne amman se yaki mayar mata da martani ...

Can da taji ba ansa ta sakin bakin tana kallonshi..

Murad ya wani yamutsa fuska yace nide2 bana son wannan abun,kawai se ayi ta durawa mutum miyau gashi ma bakin ma se zafi yake mun..

Se lokacin ta tuna abunda ta taba fadi mishi wanccen lokacin a ranta tace ya rama kenan...


A fili kuma se tace Shitttt tais toi et embrasse moi ( niko nace su Maysam yaushe kika kangare kika fitsare har haka...๐Ÿ˜ณ)

Daurewa yayi duk da
shock din dayakeji tun lokacin data rumgume shi amma ya fara mata wani salo na daban kissing din juna sukeyi har sai da taji abun yana so ya huce gona da iri sanna ta janye jikinta ta koma dayar
Kujerar dake fuskantar shi ta zauna tana meda nufashi

Shima kallona ta yakeyi

Can Tace yaya ya kk?ya aiki


E shi saรฏ yanzu ma ya lura da kayan da ke jikinta after dresse ce baka tayi roling kanta da dan kwallin kayan kare mata kalo yayi yace ba tare da ya ansa mata ba yace tsaya ma bade da wa inan kayan kike fita ba?
Duban kanta tayi tace haba yaya miye laifin kayan nan ?
Besan lokacin da yace kin kasheni ...Kina Matar aure aman kifito bรข hijab da nikaf da safa?da kaji yanda yake maganar kasan ranshi ya fara baci ..
Tayi rau2 da ido kamar zatayi kuka..

Kauda fuskarshi daga kallonta..


Dan ta kawar fa zancan tace Kash yaya na manta fah ba nikade bace tare da kawata Mariam nake..na barta waje ita da wani doc

Ayya to tashi mutafi nima na tashi ai....

Har yakai bakin kofa ya juyo yace yauwa na manta ai de kinsan ba haka mukayi da ke ..ba ko?..seda nace ban lamunta ba da kiyi waya amman dan kin renani harda su facebook kike to bani ita nan ma...
Marerecewa tayi tace haba wly Mahmud tsokanar ka kawai yakeyi ni babu wani su facebook din dana keyi ...tace kuma gama wayar ka duba ka gani.

Se lokacin yayi ajiyar zuciya ..yace shikenan na yarda da ke ...

Se kuma zancen makarantarki ..kisan de banida ra'ayi amma kika ketare dan tamakar ban isa da ke ba...to kuwa kima rubuta ki aje bab...

Da sauri ta turashi tz gamashi da jikin kofar tasa hannunta ta dafe kofar..

shi kam ikon Allah yake kallo ..
Tayi kalar tausayi ido cikin ido tace haba yayana kada kamun haka na kwallafa rai a karatun nan kuma wly saboda kaine kawai zanyi medecine fannin zuciya ..dan nasan irin kulawar da zanki baka nan gaba...kada ka hanani cika burina pls..

Tunda ta fara magana yaji tayi mishi kwarjini ..shi fa wani lokacin ma besan donmi yake kasa cemata a'a ba..kuma gashi ta cika shi da mamaki wai saboda shi to taya akayi tasan inada ciwon zuciya?ma

Se kawai tsintar bakin shi yayi da fadin shikenan amma da sharadi...

Na aminci kafinma naji miye sharadin..

Zaki dawo gidana dan kina matar aure zamman hostel be dace dake ba ..kai duk ma diya mace be dace ba in ba ya zamo dole ba kuma ma bare a kasar nan..

Seda ta bari ya gama tace ok yaya duk yanda kace haka za'ayi..

Ganin yanayin ta ya sauya yace miye kuma..?

Maysam tace yaya kawaye na fa .tare muke tun muna can.kuma dayar ma budurwar Mahmud ce ...

Ke bason wasa fa da gaske budurwarshi ?

Wly yaya da gaske nake...

Murad yace kice na samu abun tsokana..to yanzu de ba wanna ba se ku dawo ku duka ukku se ku zauna a bangarenki ....kuma yar uwar zamanki anata bangaren ko?

Wani kallo take binshi dashi hawaye har sun fara mata zarya tace wai dan Allah kenan da gaske de kayi aure?

Murad yace.


Washhhh typing akwai wuya fa๐Ÿ˜ฅkuyi manage




Fasma๐Ÿ–Š(yar mutan Zinder)
[03/08 ร  23:18] FASMA๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*Allah abun godiya dama haka Fans din book din nan kukeda yawa ..kai amma na ji dadi sosai fa ina alfahari daku .ina ganin comment dinku...Allah ya bar kauna me dorewa ina yinku irin more totaly din nan*๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜โค...


_My Arfat ina kika shigene kwana biyu ....i miss you so mush...ke da my in Law xaynap queen_ ๐Ÿ˜ฅ๐Ÿ˜


Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค


๐Ÿ…ฟ85__86






```Manzon Allah(SAW) yace ''wanda ya aibanta dan uwansa da wani aikin zunubi to ba zai mutu ba har sai ya aikata irinsa.
Tirmizi ya rawaito shi``` .






[03/08/18 ร  23:01]Murad ya sa hannu ya goge mata hawayen dake diga daga idon ta yace haba yar gidan momy ina miki kallon jaruma kada kiba mata kunya mana ...kina yiwa kishiya kuka tun bakiga kishiyarba...

Itade kallonshi take tama rasa mizatace.

Ya sake cewa koda yake ma gwara kiyi kukan ki dan amariyata Allah ya zuba mata hallitar kyau gata fara ..hancin nan zurat dashi uwa uba kuma ga diri me dan banzan daukan hanka..

Da sauri ta rufe mishi baki da hannuta ta rumtse idonta se kuma ta fashe da wani sabon kuka tana fadin A'uzubillahi minna shayd'anin rajim Allahumma ajirni fi misibati wa.......

Kallonta yake cike da tausayawa yace nine kuma shaidanin yau..

Ba tare data bude idonta ba tace pls bani hanya na futa ..

Ze sake magana ..ta bude idonta wanda yayi ja tace pls in har ba sokake zuciyata ta buga lokaci guda ba to kaban hanya na futa...

Ganin yanda idonta yayi wani ja besan lokacinda ya rumgumeta tsam a jikinshi yana fadin am so sorry i dn't mean to hurt you yana jin yanda zuciyarta ke bugawa da sauri2 ya kata matse ta sosai

..wasu ajiyar zuciya Maysam ta shiga saukewa a jere har de tajita ta dawo normal...raba jikinta da nashi tayi . tace pls mutafi Mariam na jirana ...

Babu gadama ya bude mata dan yana gudun ya barko wani abun..

Zaune ta tarar da Mark se zuba zance yakewa Mariam ..ita kam tayi mishi shiruuuuu...

Isowa tayi suka sake gaisawa tace da Mariyam su tafi...

Mark yayi saurin cewa na gani fa pls ki ban numb kawarki tunda ita taki ta ban...

Maysam tace aaa da garaje bada number ta dan an yi mata miji gaskiya

Mark ya wani waro ido yace anyi mata beko ne?
Maysam ta girgiza mishi kai .

Yace Alhamdullilah tunda de haka ne ki bani kawai allura cikin ruwa me rabo ya dauka

Maysam tace kasan de neman aure kan aure bashi da kyau ko?

Kafin ya bata amsa Murad ya iso yana wani hade rai... ..
Suka gaisa da Mariam

Maysam na Ganin bakin Murad yana motsi da alamu wata magana zeyi ya sa ta tari numpashin shi da fadin am so happy yayana na yarda kai kaifi daya ne baka magana biyu na gode da barina da kai in cigaba da karatuna a hostel you are the best ta fadii tana dariyar yake ..and pls mutafi ka sauke mu kada magarib ta tarar damu anan..

Kamar bugun Wata guduma ,haka Murad yaji magagannu ta a ranshi yace mi yarinyar nan ke nufi ne?dago kai yayi ya kalleta ..,ta kuwa faki idon su Mariam ta zabga mishi harara..

Waro ido yayi yanamata kallon zamu hade ne..

Ita ma tamishi kallon se mi in mun hade dinn...

Babu yanda ya iya haka ya kaisu ..a mota ma yi tayi kamar babu wani abun daya hadasu..se zuba zancen take tana dariya abunta
Amma tana fakar idon su se ta zabga mishi harara......


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

A bangaren Madina kuwa da Murza basu san wainar da ake toya ba dadin rayuwar su suke ji karansu suke ci babu babbaka ..Murza an murje an wanku dan ko banza bata aikin komi kuyangi kemata ga ci da sha masu dadi ....


Su Fulani kam suna nan suna shirya yanda zasuyi su tona asirin su Murza ...Mahmud yace mize hana musa ka camera a ko ina na gidan dan komi mutum ze fada ba llale bane a yarda amma in ka a zahiri dole koma waye yarda.

Fulani tayi naam da shawarar nan sede matsalar anda zasu yi a saka a dakin madina ba tare da sun ankara ba ...dakin Murza bazasu sha wuya ba da kusan wuni wurin Madina take....
Dan haka suka yanke da asa a gidan Murza da gidan Murad duk da bayan nan ..dama nan bangaren fulani..
Sosai suke yin komi a tsanake cikin taka tsan2 da kada asamu matsala...Mahmud shike kan gaba..dan haka kullum Fulani cikin yi mishi addu'a take .. ...
๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

Suna iso wa suka yi musu sallama suka shigewar su hostel abunsu


Da kaga Murad kasan yana cikin damuwa haka ya juya suka koma shida Mark..shikam se zuba mishi zancen Mariam yake

Su kam isowar su kenan aka fara kiran sallar ...bayan sun sauke farali ne Maysam ke sheda musu Murad ya yarda su koma su duka ukku can gidanshi da zama se yana kawosu duk safiya makarantar ...

Ba karamar murna sukayi ba tare da cewa tayi mishi godiya kafin su mika tasu godiyar....

Wanka ta shiga tayi tare da doro alwala ..ana fara kiran sallar isha'i ta gabatar...

Se kuma Mufeedah ta gabatar musu da abun ci data dafa musu ...amma Maysam kikam tace bata jin yunwa ..har suna tsokanar ta da mi yayan ya bata ne ....
Itade dariya take musu aranta kuwa fadin take babu abunda ya bani se zallar bacin rai da kishi daya barni.dasu.

Bayan sun gama Mufeedah ta fara koya musu lecture din yau da basuyi ba...suna tsaka da yi wayar Maysam ta shiga kara...
Tana ganin kiran kuma tasan me kiran amma taki daga wa....har ta tsinke. ..se ana biyu ta daga ..tace salama aleikum yaya...

Sallamar kawai ya amsa yace ki fito ina jiranki .a waje.be jira mizata ce ba ma ya kashe wayar shi...

Haka ta tashi ta sauya kaya tare da daukan kayan data san tana anfani da su ta zuba a hand bag dinta..

Su Mufeedah kuwa sun zuba ido suna kallonta ...seda ta gama shirinta tsap tace to my tripleM

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login