Showing 57001 words to 60000 words out of 100341 words
gida amma ciwon kamar karashi ake ...
Ba bu zato yaji bakin shi yana abaton addu'a wanda rabon daya ce yayi addu'a kai koda bayan salla ne to ya manta...
Kan kace mi bacci ya sure shi ..bashi ya farka ba se wajejen sha biyu da rabi na rana duk wani iri yake jinshi kamar wanda iska zata dauke shi yake ji fayau2 kawai....ganin lokacin sallar Juma'a yayi dan haka wanka yayi ya fice Masalaci duk da akwai yar tazara dashi da masallacin. Amman har yanzu kan be bar mishi ciwon ba...
Tunda sheik din ya fara huduba jikin shi yayi sanyi duk se yake jinshi imcomplete kamar wanda ya rasa wani abu a rayuwar ya ke ji dan akan yin biyyaya ne ga uwaye...ake hudubar..
Haka jiki ban kwari har akayi sallar ..suna gamawa mutane suka fara tafiya dan ba wani yawa ne da su ba daman...
Amma shi Murad nan ya tsinci kanshi da ya zauna ...yana yiwa fiyyenyen Halitta SALATI ..
Mark dake share guda yana kallon shi duk mamaki ya cika shi ...duda yasan wannan al'adar shi da Murad ce in akayi Sallar juma'a nan zasu zauna suyita istigifari tare da salatin Nabiyi ..to aman fa shi Murad ya dade da fasata ..dan ana gama sallar yake tafiyar shi...
Be gama tsinkewa ba seda yaga an tada sallar la'asar anyi shi da Murad din dan ba kullum ba yake ziwa masallacin ma agida yakeyin sallar shi...
Shi kam Murad tun da ya fara yin Salatin ya ji zuiiyar shi ta nutsu ..wani rin nishadi yake ji yana bin duk illahari jikinshi
Kasa hakuri Mark yayi ..bayan sun gama sallar ya matsa kusa da Murad din yayi mishi sallama nan suka gaisa ciki da fara 'a Murad din yake amsawa ..
Mark de ya boye mamakin shi dan ba kamar kwanakin baya ba da sama2 suke gaisuwar ma..
Nan Mark cikin dakewa yace yau fa duk kawani sauya mun ...
Murad yace mi ka gani ne.....
Mark daman kamar jira yake nan ya kwashe komi ya fada mishi har da zuwan Mahmud din da yanda sukayi dashi ...
Inna lillahi wa inna.ileyhi raji'un ... A bunda bakin Murad ke memetawa kenan .....
Be gama tsinkewa ba seda yaga babu numb familyn shi ko daya a wayar shi ...
Mark yayi karfin halin fadin ai ka canza layi tun da dade wa....
Hawaye kawai ya shiga zarya a idon shi yama rasa abunyi ya kuma rasa miya sa shi yin haka gaba daya baya iya tuna komi......
Mark daya fara dan zargin wani abu se yaji tausayin shi ya kama shi dan shi dama yasan da walakin goro cikin miya ...Murad dayake tsananin son familyn shi aman farat daya ya yanke duk wani contact dinshi da su ...
Nan Mark ya shiga yi mishi Nasiha tare da jan hankali kan ya rike addu'a don ita ce takobin mumuni....
Daga haka Mark ya bashi shawara ya kirayi su fulani yanzu ..
Kallon agogon hannushi yayi ya ga hudu na yama kenan yanzu goma na dare ne a can ..
Amma duk da haka ya danna number fulani dan ya haddace ta a zuciyar shi tun da dadewa...
Lokacin fulani tana shirin fita zuwa wajen sarki..kiran ya shigo..
Ringing a na biyu ta daga duk cike da zumudi dan taga number england ta aza Maysam ce ta ari wayar kawayen ta kira...dan haka tana dagawa ta fara da fadin asallama yar gidan Momyn ta .....
Murad daga can a ranshi ya shiga dan tunani nan da nan zuciyar shi ta fara aikin zut2 dan tuno mata da Maysam...katse shi fulani tayi da fadin hello..
Cikin da sanyi jiki zuciya na mishi fat2 ya amsa sallamar tare da fadin Momy nine...
Wani farin ciki marar misultuwa ya ratsa zuciyar fulani ...tace son kai ne...
Cike da kwarin guiwa jin bata dau abun da zafi ba ya ce nine Momy ..dan Allah ku yafe mun wly basan miya sa man ba yana fadin yan kuka..
Godiya ta shiga yiwa Allah (SWT)daya kubutar mata da son dinta ....dama ai addu'a bata faduwa kasa . kuma ```Manzon Allah (SAW) ya ce'' idan zakayi roko ,to ka roki Allah ,kuma idan zaka nemi temako ,to kanemi temako a wurin Allah.(Tirmizi)```
sanin bayin kanshi bane yasa tace na yafe muka daman can ban rike ka ba ...nan ta shiga yi mishi nasiha da ya rike addu'oi dayin sallar nafila..dan ```Manzon Allah (SAW) ya ce''Addu'a itace ibadah (Tirmizi``` )
Sosai zuciyarshi tayi wasai ...sun jima suna wayar sanna ya kashe tare da fadin se zuwa safe ze kirayi Sarki dan har sha daya tayi...seda safe sukayi wa juna tare da gaya mata gashi nan cikin satin nan in Allah ya yarda.....cike da murna kamar karsu kashe wayar ..har ze kashe se kuma ya sake fadin Momy ina Yarinyar nan take ..
Ganin dare yayi Fulanin kar sarki ya jita shiru dan ita keda duty yasa tace tana nan she is fine tana can tana wurin karatun ta...
Bakinshi yayi nauyi tambayar a 'ina se kawai ya kashe kiran ..
Fulani dan murmushi tayi tare da fadin ni kam ido ne nawa...
Yana kashewa ya dannawa Mahmud kira ...
Ringing biyu shima ya daga duk jiyake su Mufeedah ne shima...
Amman mi se yaji muryar Abokinshi wanda ko cikin dubunan jama'a ze iya sheda ta..
Cike da zumudi yace M2 kai ne ko kuma kunuwana ne suke mini gizo...
Murad yace nine aboki pls kayi hakuri da abunda....
Be gama ba Mahmud ya katse shi da fadin ai komi ya fice a kiyayi gaba de...shima de nasihar rike addu'oin tsari na safe da yamma yace ya rike kamar yanda fiyyenyen Hallita ya umarce mu da yin su...(suna nan cikin HUSNUL-MUSLIM)..
Murad yace hakika ka cika aboki na kwarai Allah ya bar kauna da zumunci masu dorewa...
Ameen ya amsa ..
Se kuma Murad ya ce kenan de yar gidan Momy bata ci jarabawa ba ko kuma fasa yi musu tsallaken class din akayi ne dan na tambayi Momy tace tana can wurin karatun...
Mahmud yace ita kuwa suka samu dan har da mention excellent SANADIN haka har gwanati ta tura su karatu England itada kawayen ta ...
Yan zu haka suna can. enland...
Tunda Mahmud ya fara bashi labari yake jin dadi har lokacin daya ce mishi wai sunan nan england sannan hankalin shi ya tashi wani irin bacin rai da kishi suka da baybaye shi wanda acewarshi martabar aurenshi yake karewa..
Cike da masifa irin tashi yace What?da Izinin wa?...waye yayi mata jagora batare da izini naba?ya ci gaba da fadin jinake na jima da gayamata cewa bazan barta tayi karatu anan ba......?
Mahmud shima daya kai kololuwar bacin rai yace..
The more you comment ,the more i typing..๐๐.
Bazan gajiya da fadi muku ina yinku irin totaly din nanโคโค
Fasma ce๐
[31/07 ร 23:35] FASMA๐: ๐ *STAR WRITER'S ASS* ๐โจ๐
( _Home of spรฉcial ๐ก&extraordinary writers_ )
๐น๐น *SANADIN ACCIDENT* ๐ฅ๐๐น๐น
S.W.Aโ
๐ณ๐ชStory&Written
by
*FASMA* ๐ณ๐ช
*Alherin Allah ya kaimu muku a duk inda kuke aminan kwarai MOMYN HADJIA & MY AISHA (NANAS)ina jin dadin shawarwarinku da nuna kulawarku a gareni Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa a gaskiya ina yin ku* ๐๐โค
__ban manta dake ba Garkuwa ina jin dadin yanda kike bibiyar littafin nan Rabbi ya bar zumunci......_ ๐โคโคโค
_Fans ban manta daku ba kusan ina yinku irin totaly din nan har kullum_ โค๐
Dedicated to all my fans๐โค
๐
ฟ 81__82
``` ```Manzon Allah (SAW) yace''kowane abu me sa maye haramun ne.
Muslim ya rawaito shi
```
[31/07/18 ร 22:23]
Mahmud ya kai kokokuwa bacin rai ..ya ce to Momy da Sarki suka bada izini..........
Jagora kuma da kake wani tada jijiyoyin wuya nina na mata shi ...,,
Sanna da kake batun ai tasan bakada ra'ayin tayi karatu acan .to mu aljanu ne da zamiyi aruwar sanii komi kake nufi tunda de mu baka taba fada mana bz.....da kaji yanda yake maganar kasan cinkin bacin rai yake yin ta.......
Se kuma jikin Murad din yayi sanyi yayi ajiyar zuciya yace sorry aboki ba haka nake nufi ba cikin sassauta murya yayi maganar
Mahmud ya sauke ajiyar zuciya shima ya ce shikenan amma a tari gaba ...cike da tsokana ya ce kawai kishi ya wani rufe maka ido har baka san maganar dakake fadi ba..
Ya leman kuwa yace kishi fa?ni ba wani kishi kawai ina son kare martabar aure nane...
Dariya Mahmud ya yi daman yayi zaton abunda ze fadi kenan ....
Nan Mahmud ya gaya mishi komi game da makarantar har sunan ta ...
Shi kanshi besan irin yana yin da yake ba yana de amsawa da to...
Shi kuma Mhamud dan ya kara har zukashi ya ce ..bari na baka number ta dan kada kasha wuya. .
Wani yawu me dacci ya hade yace Mahmud kun kashe ni yanzu har da waya kuka bata ..fadi yake kamar zeyi kuka ..
Mahmud ya kwashe da dariya ..seda yayi me isar sa har Murad ya hasala dan haushi ....yace se anjima..
Da sauri Mahmud yace kenan de baka bukatar number ko...to seda safe...
Da sauri yace bangane ba bana so ..?kaji na fada da bakina ne...kawai kaban in zaka ban kasa2 yake fadin kawai ana so a bata min yar renota a wani zo harda bata phone. To wai ma itada taje karatu miye na wani bata waya.
Mahmud daya jishi yace da kuwa kasani iphone7 ce..
Kamar zeyi kuka yace wly kun gama dani ina yarinyar nan ina iphone7 miye laifin ki saimata touch ligth ma.....
Mahmud daya samu abun tsokana yace kai har da fa Whatsapp ,twitter,facebook etc ..duk ta iya kai tama kware yanzuu...in fada maka kuwa
Katse kiran kawai yaye ba tare da ya anshi numb wayar ma tuni zuciyar shi tashi bugon zut3. Banda huci babu abunda yake .Mark da ke kusa dashi ya dafa shi yace be carefuly .mana..bawani abun tada hankali bane kayi hakuri duk da banji miya ce ba amman ina so kabi komi a sannu.kada kayi saukin yanke hukunci cikin fushi daga baya kayi da na sani....nan yayi ta tausarshi har yaji sanyi a ranshi ...basu fita ba daga massalacin har seda suka gabatar da sallar isha'i sanna suka komo kowa ya nufi gidanshi .. ...
Yana nan kwance bisa makalelen gadonshi har wajejen sha biyu na dare amma ya kasa bacci kai alamun jima be jiba kawai duk maganganun Mahmud ne ke masa yawo a kwakwaluwa ..kasa hakuri yayi ya kalli agogo yaga sha biyu har da minti 5. .dan haka ya danna mishi kira dan yanzu yana da yaki nin sun idar da sallar asuba acan..
Lokaci shi kuwa ya dawo daga masjid kenan yaga kiran Murad ..seda yayi murmushi dan yasan mussababin kiran .....
Yana dagawa yace kai wai har yanzu bakayi bacci bane ko kuma tunanin yar renon naka kake....
Seda ya ja tsaki yace ni ba wannan nakira ka fadamin ba ...number zaka bani ..kuma harry up ina da abunyi..yana wani basarwa wai dan kadama yaga damarshi....
Mahmud yace ka biya tukon....
Kamar ya shiga wayar yake ji yace wai kai wani irin dan rainin wayo ne ...yace ka fada ko nawane kasan de zan iya saye ko?...
Yace amma de kasan number nan zatayi tsada ko ?dan kuwa me wayar....
Da sauri ya katse shi da fadin ''je t'en supplis''' kaban number nan ..wai mi natare maka ne a rayuwa da kake son yi mini katsa landa haka ne .....
Mi Mahmud zeyi inba dariya ba yace shikenan bari na turo maka..
No kawai ka gayan yanzuu....
Number ya bashi yana fadin ka gaida mun yar renon taka..
Katse kiran kawai yayi dan yaji haushi ba kanan ba ....
Yana bashi ko save dinta beyi ba ya danna mata kira.....
Haba yaya Murad sha biyun dare ne fa. ...ai lokacin Maysam ta kai goma ma na bacci....
Seda yayi mata missing call 5 bata dagaba ...
Murad ba uzuri nan ya fara fadin zamu hade ne inba ma raini ba ina kira kiki wani dauka....tsaki daya ja yafi a kirga ..haka ya kwana da kyar barawon bacci ya kwashe shi...
Washe gari Tun tashinta da asuba taga miss call 5 amman dataga sabuwar number se bata meda kiran ba kai daga karshe ma kashe wayar tayi dan yau wani pratical zasuyi kuma abayan gari sannan ba'a barin su suyi waya shi yasama basa fita da ita duk ranar da zasuyi...
Murad kam yau har makara ma yayi salllar asuba seda gari yayi dan haske ya farka a gurguje yayi sallar yayi shirin fita . amman kafin nan ma ya mata kira yafi akirga yajita swich off....tun lokacin zuciyar ta fara lugude....ya na fita direct hanyar dazata kaishi makarantar yayi dan yau ko office baya jin ze iya tafiya..kira yayi ya sanar da Mark cewa baze samu damar zowa ba.....
Cikeda zullumi ya isa makarantar ..be tsaya wata2 ba ya shige wurin shugaban makarantar ..dayake bawani boyayye bane dan haka tarba ta mussama shugaban yayi mishi.
Nan yayi mishi bayanin abunda ya kawo shi.
Babu mata lokaci shugaban ya fara bincike...
Can yace ai kwarai a nan take karatu su biyar gwamnatin kasar Niger ta turo su...amma yanzu basa nan sun fita bayan gari yin wani pratical...kuma gobe ma can za su tafi...
Ranshi in yayi million ya bace..amma se ya danne yayi mishi godiya tare da fice wa .....ranshi inba suya babu abunda yake ..a ranshi fadi yake dole ma ta bar makarantar nan .....
Su Maysam basu suka dawo ba se wajejan shida na yamma . duk sun galabaita......
Suna zuwa ta kunna wayarta da zumar yi wa fulani shagwabar wuyar dasu sha yau...
Gefe daya kuma Mufeedah ce ke soyewar ita da Mahmud ....yanzu kam ba'ace wa komi dan sun shaku da soyyarsu.. Can yace wai ina kanwata ne.
Gatan nan kusa dani kona bata ne..
Ee yace..
Bayan ta bata suka gaisa ..yace wai mijinki ya kiraye kuwa jiya....
Dafe kirji tayi ta wani waro ido kamar yana ganinta tace wayyo na shiga goma . kadade fa shine ya kirani jiya .......
Tace ya Mahmud kace tawa ta karemun dan naga number england ce sede ban kawo cewa shine ba shiyasa ma ban mede kiran ba...
Mahmud yace ki kwantar da hankali ki ..nan ya bata labarin duk abunda ya faru jiyan.
Wani uban tsale tayi ta dane bisa kan Mufeedah tare da wani ihun murna tace kai Alhamdullilah ..lallae Allah abun godiya ne. ...
Cike da murna da zumudi har jitake kamar tayi fiffeke ta ganta kusa da yayanta..
Wayar ta bawa Mufeedah tashige bayi abunta ..se taji ma duk wata gajiyar da suka kwaso ta tafi ..fuskarta banda annurin murmushi babu abunda take. ..
Suna zaune suna wani dan exercice su ukku.....lokacin har goma tayi dan haka suna gamawa kowayi shinfidar shi dan bawa gangar jiki hakkin ya...
Lafiyar gado suka bi ....can se wayar Maysam ta shiga tsula kara...
Da kamar bazata dagaba dan har bacci ya fara dibanta...
Amman ganin number jiya ce yasa ta wartsake tana mutsitsike ido..tare da zubawa wayar kallo kurr
Kasa dauka tayi se wani waro ido take kamar wanda tayiwa sarki karya.....
Can de tayi shahada har ta kusan tsinkewa ta daga ...
Da farko yayi niyyar yima mata masifa ..aaaman mi ..tana doka sallama yaji shi har cikin kokkon brain din shi. A take yaji ranshi yayi sanyi ...muryarta kade data daki dodon kunneshi seya ji ta mishi kwarjini ....yaji baze ma iya mata masifar ba..
Seda ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa sallamar ..
Tofa ita kam har seda ta wani lumshe ido jin muryar shi dan ta sheda Muryar....
Tace yaya ykk?ya two days?ya aiki?ya fama da jama'a?
Wannan karon shima lumshe idanun yayi har besan lokacinda murmushi ya subuce mishi da fadin haba duk wannan question din wacce zan ansa ne ?dan ayanda take wata maganz kasa2 ko su Mariam da suke daki daya basu jiyo ta ba
Kamar tana gabanshi ta wani turo baki tace duka.....
Jin shiru yace ..to am fine ...komi Alhamduliilah...
Tunda ya fara magana tayi shiru a ranta fadin take masha Allah ...yaya bade dadin Murya ba ....ko dayake ma ai daga bakin nan tafito wanda nakeji kamar na saka a biredi na cinye shi .... .(๐to mikike jira๐คจ)
Katse mata tunanin yayi da fadin haka mukayi da ke ne?jinake na dade da cewa bazakiyi karatu a England nan ba?kuma nace ba yanzu zaki fara aiki da waya ba amma sedakika amsa ko? to wly..
Da sauri tace haba yaya na ..yaushe rabon da ka ganni,ko kaji murya ta ma seyau dana ke daukin ka seka shiga yi muni fada...ta fada cike da kissar kamar zatayi kuka. ..ta cigaba da fadin kuma wly ni duk agajieye ma nake duk bacci ne tak ado na....pls yaya kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba...am so sorry..
Duk se yaji ba dadi ya tausaya mata yace shikenan bari na barki haka amma fa make sure zamu cigaba da maganar nan gobe....
Da sauri tace kada kashe wayar nan ni ban gaji da hirar ba...
Yace to ai nima ban gajin ba se de zanje aiki gobe kuma kema gashi pratical zaku ....
Har zasuyi sallama yace yauwa daman dan na fada miki yanzu kina da abokiyar zama dan nayi aure.da...
Bata bari ya karasa ba ta kashe wayar tare da sakin wani kuka kasa..2...
Yau itama kam bacci se barawo ne ya saceta ..dan maganar wai yayi aure se dawoma ta take.....
To fa๐ณ๐ณ๐ฑMURAD aure yayi kuma ๐ค๐ค๐๐
Kenan de Maysam anyi mata kishiya๐
...kai abun nann yayi mun...๐๐๐๐
Ina yinku irin sosai din nanโค๐
Fasma ce ๐(yar mutan Zinder๐)
[01/08 ร 23:12] FASMA๐: ๐ *STAR WRITER'S ASS* ๐โจ๐
( _Home of spรฉcial ๐ก&extraordinary writers_ )
๐น๐น *SANADIN ACCIDENT* ๐ฅ๐๐น๐น
S.W.Aโ
๐ณ๐ชStory&Written
by
*FASMA* ๐ณ๐ช
Dedicated to my SAMBABY๐โค
๐
ฟ83__84
```
Manzon Allah (SAW) ya ce''kunya tana daga cikin imani''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi```
[01/08 /18 ร 22:58]A bangaren Murad shima beyi wani bacci ba. .nan zuciyar shi ta fara cewa why2 zaka fada mata nee.....ganin baze iya jurewa ba yasa ya danna mata kira amma har tagama ringing ba'a daga ba ...kai daga baya ma kashe