Showing 54001 words to 57000 words out of 100341 words

Chapter 19 - Sanadin Accident Book 1 Complete Hausa Novel

Fisma   

24 Sep 2025

929

Mariam tace kai kede kawai dan yana yayankine kike wani yabonshi ..

Dariya tayi tace haba ba wani nan .gaskiya de na fada.kuma ma abokin MIJINA NE


A tare sukace miji๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ...

Tace ai koda na shigo makarantar nan da aurena ...kuma wannan wanda yazo lokacin da bani da lfy wato Yaya MURAD shine mijina...gidan nan ma nawa ne ..

Mufeedah tace amman kin san baki kyauta ba ko ace ayanda muke ki kasa fada muna kina da aure...

A tare sukace muna miki fatan alheri tare da zaman lfy me dorewa amman mu kinga tafiyar mu tunda de baki dauke mu ba da mahimmaci...suka tashi zasu tafi

Da sauri tasha gaban su tana basu hakuri kan bata yi haka ba da wata manufa kawai de Allah ne beyi ba zasu ji ...

Nan ta zaunar dasu ta basu tarihin rayuwar ta ...kan ta gama ,ita kuka su kuka ..nan suka rungume junan su ..sun jima a haka sannan Mahmud ya meda su gida ya kai Maysam airport ta dawo gida..


,,,shugaban makaranta su Maysam ya kirayi iyayen su bayan yayi musu barka se kuma yayi musu proposing din a aje musu takardun su inda rabonsu gwamnati zata iya tura su kasar waje karatu...

Da farko fulani bata amince ba amma ganin Maysam ta kwallafa rai yasa ta amince amma fa tace sede in England kusa da mijinta.

Itade Maysam burin ta ta amincen ...

Allah cikin ikonsa suka samu su duka ukkun kuma England duka aka tura su ....dadi kashe su ne kawai beyi ba ....zasu kara hadewa a makaranta daya..


Dan haka fulani tasake tutubar Mahmud da yasake koma wa England ya gani .ya kuma sanar mishi matarshi ta samu gwamnati ta turata England karatu..

Wannan karon Mahmud shi kanshi ya tsorata da lamarin ..dan Murad nunawa yayi da de duniya besan shi ba kwata2 ya manta dashi...

haka Mahmud ya dawo zuciyarshi cunkushe da wasi2 iri2 .....shi be masan ta inda ze fara gayawa fulani cewa ga irin cin mutunci da Murad yayi mishi ba......dan haka tunda ya dawo ya shiga wasan buya da. Fulani....


Ranar wata litinin ana gobe tafiyar su Maysam England dan Mahmud ya cike mata takardun ta.

Bangaren Abbanta ta nufa dan yi musu bankwana shida Murza sun jima Mallam Musa yana yi mata nasiha da kuma ta kare mutuncin ta da na aurenta ...

duk sai jikinta yayi sanyi taji kamar ma ta daina tafiyar amman tuno wa da tayi yayan ta na can sai ta samu kwarin guiwa har zuciyarta tafara azzalzalata dan zumudi ๐Ÿ˜œ

Dakin Murza ta nufa da niyar yimata ban kwana amma mi cak ta tsaya a dede kofar shiga palon banyi aune ba naga hawaye sun fara zarya a kumatunta cike da mamaki na matso na kara kunne na dan ji mi yasata kuka sai naji Murza tana waya tana fadin ee kadan ma suka gani wly ni nan zan zama ajalin Murad de Maysam (kuji fa da allah kamar ran a hannunta yake๐Ÿ™„) da ba ma rashin sa'a ba da yanzu sun dade da mutuwa ai...,

ke nifa haukata shi naso ayi yabi duniya bama a raba shi ba da dangin ba fadar madina da ga bangaren layi ,

shewa Murza ta kwasa tace wannan shine target din mu na gaba sai kinyi uwar dakina shugaba Madina matar sarki shugaban masarauta gaba daya kai ko makirar Fulani ba ta isa ta taka miki birki ba dole ne ki taka wanda kikeso a garin nan dan duk wanda yayi miki kan kara za kiyi mishi ta itace abuga dake a barki anan waziri ma yayi nashi babin an shafe shi.

Dafe kirjinta Maysam tayi cike da mamaki da kyar ta lallaba ta koma bangaren fulani dede zata shiga taji muryar Mahmud na fadiwa Fulani kaf abunda yafaru shida Murad, yakara da fadin amman fa ina ganin ba a hayyacin shi ba yake dan a gaskia wanan al'amari akwai ayar tambaya a ciki

jim Fulani tayi tana jinjina maganar sai kawa Maysam ta fado ba ko sallama tana gwanjin kuka cinyar Fulani ta fada ta saki wani sabon kuka mai cin rai cike da tashin hankali fulani ke tambayarta miya faru .?

kukan yakasa tsayawa ta shiga fadin Momy kada kiyi fushi da yayana ba laifin shi bane wly sune kuma sunce ma sai sunga bayan mu nida shi

Cike da tsoro Fulani da Mahmud sukace suwa din?
Yanzu nan naji Inna Murza tana waya da wata Madina matar sarki nan ta kwashe kaf abunda taji ta fada musu.
Mahamud dey mamakine ya cika shi har yawun bakinshi ya kafe ya rasa mi zai fadi.


Fulani batayi wani mamakiba dan dama bata yarda da tuban Murza ba kuma ta gane sare Madinar da take fadi sai tayi shiru.

A fusace Mahmud ya tashi yana fadin kafin su kasheku ni bari nakashesu ..

,dakatar da shi fulani tayi da fadin zauna muyi magana
Bayan ya zauna tayi mishi nasiha kan illar a bunda yake son aikata wa takara da fadin ''maintenant on a aucune preuve en notre disposition qui va prouver leur actes. .


Mahmud ya ce''Mais Momy ,Maysam a tout entendu non?.''


Fulani ta sake fadin''Meme si elle a tout entendu c'est sa parole contre celle de Madina kuma ma babu wanda zai yarda saboda iya makircinta dan tana gwada kamar ta goya Murad gaban mutane in baka mantaba waziri ma fa yaka yafada amma babu wanda ya yarda ....

Yanzu de mu fara da kubutar da Murad din daga baya se musan yanda zamu bullo musu....in su da adiri suka dogara to mu da Allah muka dogara

Nan Mahmud ya bada shawarar ayi ta saukar qur'ani tare da zuwa makarantu su taya su da addu'a...ya kuma cewa muma kuma zamu rage bacci mu zanki rayashi da nafilfili da addu'a ..

Sosai sukayi na'am da shawarar nan .....


Maysam tace Allah ya bamu nasara akansu..nima na samu Mijina ya dawo kusa dani..muyi....

Tsit tayi ganin irin kallon da suke mata ..
Se lokaci ta tuna ashe fa a gaban Surikarta fulani take ..ai da gudu da shige kuryar daki tana dariya ga kunya kamar kasa ta nutse ta shige ..

Dariya Mahmud ya shiga yi mata ...

Fulani na fadin yaki dawo y'a ta ai bama yar haka dake...

Amma ina Maysam ta ware ..

.nan Mahmud yayi mata sallama tare da jaddada mata gobe2n nan zesaka a fara saukar alqur'ani..sanna ya fice.

Fulani tabishi shi ma da adduโ€™a dan a gaskiya samun aboki kamar Mahmud a yanzu se an tona..


A ranar su duka ukku baccin da sukayi kadan ne dan kwana sukayi suna rayashi da nafilfili da addu'a Allah ya basu nasara akan su Murza ya kubutar da Murad da ga sharrin su ...



Love you all๐Ÿ˜โค


Yawan comment dinku shi ze bani kwarin guiwar yin typing me yawa๐Ÿ˜…


Fasma ce๐Ÿ–Š
[29/07 ร  21:44] FASMA๐Ÿ˜: ๐ŸŒŸ *STAR WRITER'S ASS* ๐ŸŒŸโœจ๐Ÿ–Š
( _Home of spรฉcial ๐Ÿก&extraordinary writers_ )


๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

S.W.Aโœ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*I miss you my Arfat and my in law Xaynabqueen ..wai ina kuka shige ne kwana biyu ...Allah de yasa you are fine* ๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜ฅ


Dedicated to all my fans๐Ÿ˜โค


๐Ÿ…ฟ79__80



```Manzon Allah(SAW) ya ce''wanda duk yayi imani da Allah da ranar lahira to ,ya fadi alheri ko kuma yayi shiru.
Bukhari da Muslim suka rawaito shi..```





[29/07/18 ร  18:40] Washe gari Maysam ta fito cikin shirin ta dan jirgin 10 na safe zasu bi . zuwa Niamey daga can kuma su daga zuwa England

Da ka ganta kasan tana cikin damuwa .,,duk ma se take ji kamar ta fasa tafiyar nan duk jikinta yayi sanyi ...gashi wanda take zumundin son zuwa England dan shi ,din ma Murza sun mishi Asiri .

Haka tayi break sokoko da ita duk Fulani na lura da ita ..dan haka seta ja ta jikin ta da nufin lallashi

Ai kuwa kamar jira take ta kuwa fashe mata da kuka.

Itama Fulani se zuciyar ta karaya duk se taji ba dadi .....
Haka tayi ta lallabata tare dayi mata nasiha me ratsa zuciya .. ..

Da kyar tayi shiru har fulani na tsokanar ta da fadin ko se ta goyaki ta ne zatayi shiru....

Nan ta kyalkayale da dariya..
Fulani tayi mata jagora fardar sarki tayi mishi bankwana ..sosai ya yi mata nasiha shima ..

Suna fitowa fulani ta. bata wata tsaleliyar waya ,,koda na leka na ga iphone,7,..zo kaga Murna wajen Maysam yau tayi waya ..dan dama Murad ne ya hana a bata ,to amma yanzu halin tafiya yayi sanadin an bata..
Fulani tace duk number kowa tana ciki na samiki..

Maysam ta kauda kai tare da fadin har ta yaya na ...

Fulani tayi kamar bata gane ba tace ai ..na samiki har ta yayanki Mahmud...

Tayi kicin2 ta fuska tace Momy ta mijina fa nake nufi ...

Fulani tayi dariya tace tofa an zo wurin masu miji manyan to har ita na saka miki...kai har da photunan shi na tura miki dan daman sun cike mun waya..

Maysam tace kai Momy kin ceci zuciyana fa da yanzu zance a turo min dan ko bacci zanyi sena saka ka photon a .. ...se kuma tayi shiru da sauri tasa tafin hannuta tana kare fuskarta dan Seda tayi maganar taji kunya amman ta mazge dayi mata godiya...ita kanta bata san dan mi yasa ba bata iya controling din kanta wani lokacin..

A gurguje ta shiga bangaren Abbata tayi mushi sallama haka ta daure ta shiga Dakin Murza tayi mata sallamar.

Kamar gaske tana wani dariyar yake wai ita dole yanzu son Maysam take ,,a zuciyarta kuwa fadi take ina nan kwanan nan zaki dawo gida kici Ubanki shegiya kullum se kara kyau take kamar yar sarkin aljanu..

Itama Maysam sakin jikinta tayi kamar ba'ta ji komi ba ..amma addu'a ce fal ranta ....


Haka suka rabu da fulani duk kwalla ta cika mata ido inda Mahmud zeyi mata rakiya har AEROPORT DIORI HAMANI na birnin NIAMEY......acan suka hadu da sauran kawayenta Su Mufeedah suma sun iso duk da yan uwansu nan suka gaigaisa ....suna na zaune aka fara kiran passengers ..haka suma su Mufeeda suka rabu da familly ,

,,Mahmud yana nan har jirgin ya daga ..

Wata yar dantijuwa. na gani ita da mijinta wacce tun lokacin da ake kiran passegers naga ta tsurawa su Maysam ido bata ko kiftawa. mijinta na mata magana aman bata ma san yana yi ba . hankalinta rankatakwab yana. Wurin su Maysam din.....Mijin ta na mata korafin su huce tun dazu amman hankalinta baya ma wajenshi shima ya meda kallonshi ya ga miyene ya dauke mata hankali haka amma lokacin su Maysam tuni sun shige jirgin ....

Suna nan har se da jirgi ya tashi naga ta sauke wata nauyayar ajiyar zuciyar...

Da sauri mijin ya kalleta yace ya akayi ne ?ko jikin ne...?

Girgiza mishi kai tayi kamar karamar yarinya tace a'a naga wata yarinya ne me kama da Baby na...

Shima ajiyar zuciyar yayi ya ce ya kamata yanzu yaci ace kin sakawa zuciyar ki hakurin rashinya ta ....shekara nawa kuma kusan kullum se kinga me kama da ita ....

Da sauri tace a'a wannan ta banbata da sauran wanda nake gani kullum..

Dan murmishi takaici yayi yace kamar kullum kenan haka kike cewa ...kiyi hakuri ki rumgumi kaddara ..idan har tana raye Allah ya bayyana mana ita ..

Ameen ta amsa amma kam ta kwallafa rai a kan yarinyar dan ta so tayi mata magana kamar yanda take yi duk wacce taga tayi kama da Babyn ta..

Sun juya da niyar tafiya ..naji Mahmud ya ce Mom,da,Dad...๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณparent din SWEETBABY ne.ashe..

Juyo wa sukayi suka ga Mahmud ne ..

Nan ya gaishe su cike da.ladabi ..

Suka amsa suna fara'a ..
Mom tace que est ce que te venu faire ici. ?

dan sosa kanshi yayi yace matar Murad ne na kawo zata fice England.....

Dad yace a'aa Masha Allah..

Mom tace kash yau ma babu rabon zanga ta ashe ko dayake fulani taso ta turota kafin ta fice to se akayi rashin sa'a muna Paris.hakama lokacin da akayi aure bama kasar..da nasan yau ne tafiyar ma ai da tun jiya zamu dawo dan naga matar d'ana..

Su Dad sukayi yar dariya sukace ai gaba da yawa zaki ganta. Wata rana

Itama dan murmushi tayi tace hakane to Allah ya nuna muna ya kuma sauke ta lfy .

Suka ce ameen...

Nan Mahmud ya yi musu sallama tare ya fice dan yana son a fara yi mishi saukar tun yau dan karfe da zafi2 ake dukanshi.

Suma driver ya huce su gidan su.

A raina na ce kenan de su anan Niamey suke. .

Ko sarki fulani bata sarna mishi ba halin da Murad yake dan bata da wata sheda .....

To daman gata da temakon talakawa dan kowani wata biyu ko ukku se an kai tamako kauyika ko Mutuwar SWEETBABY ma suna hanyar kai temako wani kauyen ne sukayi shi.
Wanna abu ba kamramin faranta ran sarki yake ba shiya sa ma kullum sonta yake kara shiga zuciyar shi sabanin Madina da ko yan Uwanta bata son temakawa bare wani ..
Shiyasa ma yanzu da sarki yaga kusan kullum se an kai wa makarantu taimakon se beyi wani mamaki ba dan shi ya aza ta sauya takun ta ne na temakon....

Har ranar suna fada da dare su ukku yake tsokanar ta da fadin wai kode dan taji labarin zeyi ta ukku ne yasa take shiga da ficen nan dan addu'ar ta amsu ya fasa auren. ..

Madina da bata san irin wannan wasan ba ta kuwa dafe kirji tace na shiga ukku . aure fa kace ka tsufan nan mi zakayi da wata macen.kuma shine ni ba'a gaya mun ba se yanzu tana wani kumbure2...


Share zancenta sukayi sema
Fulani da ta son tsokanarta kawai yake ta amshe karaf da fadin muna maraba da ita ...fatan zaman lafiya nake maka tanayi tana wani kashe me ido ..tace kuma ai har yanzu dan saurayi shatak yake ,,ni kam bana ganin tsufanshi.....

Takaici ya kusan kashe Madina daga zaunen banda zabgawa fulani harara babu abunda take ..

Sarki yace wannan haka yake nima kullum kamar yar sha bakwai nake ganin ki ...wai ma miye sirrin nan ne .um yan matana...

Fulani tayi wani far da ido ta ce to kawo kunnenka kaji..

Babu gadama ya kuwa dan karkato kunnen shi yana dariya ..

Cike da shaukin so da kaunar junan su ta kuso da bakinta zatayi me rada dan fa su sun manta da wata Madina na wurin...(kuji wani salon soyyayar tsofi ko๐Ÿ™ˆ)

Se ji sukayi Madina tayi tsaye tana fadin tsofe2 daku amman kuna wani abun kamar kananun yara ...wannan ai ko Murad baze yi abunda kukeyi ba tanayi tana dokawa fulani harara....

Fulani a ranta fadi take ...ke kike ganin mun tsufa amman ai ita soyyaya bata tsufa..(๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณto fa kunji tsofafin ko?)....

Fulani mikewa tayi tana fadin seda safen ku dan Madina keda girki yau..

Sarki yace zo ki fada mun mana kafin ki hucen ...

Fulani na dariya kasa2 ta ce to ai ya fice sede wani jikon..kuma

Kallon zamu hade naga yana jifanta dashi...

Wanda ya kara harzuka zuciyar Madina ..ta shige kuryar daki fuuuu ..tana fadin jarabbabiya kawai.macce se jarabar iya kissa mtssss.
(๐Ÿคฃ๐ŸคฃMadina kina sha'anin ki fa )


..๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน

Su Maysam sun isa England lafiya ..daya ke gwamnati ce ta tura su kafin ma su isa har an turo musu bus din dazu dauke su dan ba su kade bane suka samu promotion din ba....

Direct babbar university England aka akaisu ..nan aka rarraba musu dakuna su anan cikin hostel din makarantar...
Amman cikin rashi sa'a se ba a hadasu daki daya ba ...Mariam da Mufeedah da wata dakin su guda se kuma Maysam da wasu yan mata suma dakin su guda..

To fa nan ake yinta Maysam ganin an ware ta da su..da kyar da siddi suka shawo kan yan matar sukayi changรฉ da Maysam.ta koma daki daya da su Mariam.dadi kamar ya kashe su ...


Tun washe gari suka fara zuwa lecture dan har an fara da sati suka zo ..dan haka babu zancen hutu ma ...

Class dinsu guda wato medecine dan sunce mutuwa ce kawai zata raba su ..komi nasu iri daya ne kai har dressing dinsu ma iri daya suke yi .kuma kullum zaka gansu da hidjab din su basa yarda su fito hakanan duk da suna garin turawa....., .suna taka tsantsan da rayuwar su ...sun meda hankalin su ga abunda ya kawo su..


Ba kadan ba suke birge ba mutane da basu sha'awa dan duk gani suke trijumelles ne(yan ukku)......

Yanzu har sun cinye 1 mois da zuwa ..suna ta karatun su cikin kwanciyar hankali banda Maysam data tsanan ta tunanin ta oga Murad ...shi yasa ma basa barinta ta zauna ita daya koda da second daya ne dan yanzu zata saka photon Murad a gaba tana ta tunanin shi..tun abun baya damunsu har yazo kuma yana yi dan sunsa miyasa Murad din be nema ta ba suma kullum cikin taya ta da addu'a suke...

Yau ma kamar kullum su Mufeedah sun dan fita suka bar Maysam a daki tana dan exercice..

Amma mi ko minti daya basuyi ba da futa ta ture komi gefe ta fara sa'arta wato kallon photon..

Shigowar su kenan ...suka ji Maysam na fadin ita kade wly duk ranar da muka hade da kai ko to sena tsotse bakin nan tas ..dan gaskiya Allah yayi hallita a wurin nan ..dan lips din nan shine ake kira Kiss me babyn nan ..ita duk jitake a ranta tayi maganar

Tana kallon photon tana doka murmushi.

Mi su Mariam zasuyi in ba dariya ba suka kuwa tun tsire da ita har tasaki baki tana kallonsu dan bata san mi suke yiwa dariya ba

Mufeedah ta matso tace inda muga irin lips din nan da ake ta wani yabawa haka...

Wani waro ido tayi tace wai kuna nufin dama a fili nayi maganar nan ne..

Mariam tace a'aa a Mafarki ne..

Gaba dayan su suka saka dariya ...haka suka ci gaba da rayuwar su .cikin jin dadi.

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน. ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

A can gida kuwa sauka yi ake ba kakkau tawa ..

Haka kawai ranar wata juma'a Murad tun safe ya tashi da wani matsene cin ciwon kai ..lokacin yana likita ne dan haka ya tattara ya dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login