Showing 78001 words to 81000 words out of 100341 words
kallonshi wurin dan ganin mitake warawa ido hakane ...ganin ZOBEN dake yatsar ne take kallo yasa yace yana da kyau ko ?
Gyada mishi kai tayi ..
Yace ko kina sone na bakishi..
A'a abun ne ya bani mamaki dan ina da irin shi ...Abbana ya banishi lokacin dana za'ayi auren mu
Kai har ma wannan rubutun M² dake cikinta ina dashi ..sede tawa tafi taka kyau da kyalli dan zinariya ne nawa..kai kuma azurfa ne ..tana yi mishi gwalo..
Mamaki da al'ajabi ya kamashi danshi yana iya cewa shida sweetbabynshi kade ne ke dasu a fadin duniyar nan ma dan kuwa shi ya saka aka kera musu su ...kuma abunda yasa yace haka can cikin zoben ba M² bane kade sunan su ne a jiki aman in baka luraba M² kade zaka gani ..yana kallonta yace ina naki zoben ne ..cike da zakuwa ..
Kai na baroshi can gida cikin kayana dan banason ya bata...
Murad yace to shi zoben naki yana rubutu ne acan cikin shi...
Girgiza mishi kai tayi tace a'a bashida kawai M² kade ajikin....
Ajiyar zuciya yayi dan dama da kamar wahala asamu me irin shi sede me kama dashi ....nan suka ci gaba da hirar su da su Mariam suka dawo sukayi mata ya jiki ..bayan Murad ya fitane suke tsokanarta kode ta sama musu Baby ne...
A ranta tace um bakusan jiyane ma aka bude hanyarba ku har ta wani baby kuke ..a fili kuma seta ce tab baby fa ni yar yarinya dani haka ..ai konayi ciki sena kara girma ..ku bakuga wuyar da akesha bane wurin haihuwa..
Suka kwashe da dariya Mufeedah tace to dai kada akwana biyu mu ganki da cikin kina wani cika bakin kin..
Kai bakinki ya sari danyan kashi wly ......nan sukayita barkon cin su hardaga baya suka koya mata darasin na yau.....
Cikin satin kam soyyayrsu suke ci da cinke kullum suna makale da juna ..Maysam ta saki jikinta kamar da har da saka kananan kayanta ..sede shima be sake gwada nemanta ba .. ..
Yau kam ta kama lahadi su duka biyun suna gida...
Maysam ta cakare ta fito da biro da kuma wata notebook lokacin yana aiki a laptop dinshi ..koda ta zo batayi wata2 ba ta jaye laptop din ta dane cinya abunta ...
Yana kallonta har wani lumshe ido yake dan turaren ta suna kashe mishi jiki .....kallonta kawai yake..yana admired dinta
Daga bisani kuma yana wani shashafa yace kullum kara kyau kike wife ..
Yar dariya tayi sekuma tayi kissing dinshi a kumatu tace nagode MURADINA ...yanzu de bawan nan ba lissafi nazo muyi...
Da mamaki yake kallonta yace lissafi kuma...
Umm tace ..se kuma ta fara yi mishi tambaya kamar haka ..shin kana da gidaje biyu A Maradi ko..,biyar a Niamey ko?
Ya gyada kai ..yace e
Ta ci gaba motar goma gareka ko?
Yace ee
Tace se kuma mall kana ukku a garin nan .da kuma hudu a zinder
Cike da mamaki yace ee
Tace da kuma jirgin ka na nan dana Niamey ko?
Yace wai tsaya a ina kika samu duka wannan bayan Mall dina nan da jirgin dana saya ko kwana goma basuyi ba kuma kosu Momy ban fada ma ba ..tayaya kika san duk wannan...
Dariya tayi tace to ai ba ina nasan su bane ..zaka tambaya mi zanyi dasu nan gaba zaka tambaya ...dan kai da kanka kayi mun alkawarin su..
Cike da mamaki yace ni kuma..
Shikenan bara na tuna maka ranar nan ne lokacin dakake amsar hakkika kace duka wannan abun ka banisu halak malak ..
Se yanzu tabbase ya tuna..yayi dariya yace to ke yanzu mi zakiyi da duk wanna abubawa...
Momy zan bawa su ..dan bansan ita waccar matar taka kyautar mi kayi mata ne ehe ...dan haka zan bawa Momysu ita tasan mizatayi da su..
Dariya yayi mata ganin kishine ya motsa yau din...
Kwantar da ita yayi a kirjinshi yana shafa kanta yace wai miyasa kike kishi da matar da bakima santa ba...
Da sweetbaby ya kamata kiyi kishinki dan ita keda rabin zuciyana kema kina da rabi...dan kishiyar da kike ta batu wasa nake miki tun wancan lokacin ..babu wani aure danayi ....ki saka a ranki daga ke na rufe kofa in Allah ya yarda dan ko nayi Allah yana gani bazan iya yin adalci tsakani ba...kai na baze iya daukan rigimar mata biyu ba ni ke din ma da za'a rabaki abani rabinki dan ke kade ma.caza mun kai kike bare mata biyu..
Wani sanyi dadine ya ziyarce ta tace har ta kara kankameshi gam a jikinta tana dariya farin ciki tace to ai ita sweetbaby bata nan taya ma zanyi kishi da ita bayan na san sonta a jinin jikinka ne yake yawo ....bazan iya yin kishi da itaba soboda kana sonta ..nima kuma duk abunda kake so nakanyi kokarkin na koyawa zuciyata sonshi ...dan na faranta maka rai...kaga ita tare na ganku bazanso rabaku da ita ba
..kara rugumeta yayi yana mata godiya ....yace to yanzu se mu fara procedure din transfert kenan...
Dariya tayi tace wani tranfer ai kuma na yafe maka su dan dama saboda kishine ...dariya yai.shikenan to ..
Can se yace kinga gift dinki ne...
Kalar tunani tayi tace a'a..
Ok to kije ki sake duba karkashin pilonki zaki gani...
Da sauri ta tashi ta shige...koda ta duba se kuwa taga wani envelop .....doko shi tayi ta kawo mishi..
Girgiza mata kai yayi yace a'a ai nakine ki bude abunki..
Ai kuwa tana budewa taga takardun gidane se key ....
Zatayi magana yace gift dinki ne ...takardun gidan wannane da kuma key din sabuwar motar da na sai miki ..kamar yanda al'adar can gida ta tanada ba ..cewa washe garin daren farko za 'abawa amariya gift na fita kumya ..naso baki taki kema washe garin to aman ai ranar tazo mun a bazata shiyasa se yau nasamu ...na baki da fatan banyi lefi ba
Cike da murna ta fada jikinshi tana me jin dadi .tace na yafe ..ai daka barshi ma dan wannan al'adane ba addini ba..
Murmushi yayi.ya rada mata a kunne cewa ina alfahari da ke babyna...ina tayaki murna kin kawo mi budurcinki na gode miki Allah ya albarkaci rayuwarki duniya da lahira...ya biyaki da mafificin alherin sa ...ina sonki wifey ta...
Tana dariya farin ciki tace na gode Allah ya saka da alheri ya kara budi ...je t'aime plus....
Sosai yaji dadin adddu'ar ....se kuma yace to muje daga ciki ki kara nuna mun godiyar ki..
Master room ya fice da ita ..na kuwa mara musu baya dan ganin wacce irin godiya ce da har se anje kuryar naki za'a yita..
Tunda suka shiga suke aikin kissing din su kamar zasu cinye junan su ..nide ina tsaye ina jira ..dan inde wanna ne naga na saba gani ..ai kuwa abu ya fara kankama suka shiga romance ..ina ganin haka na jayo kafafuna na fito ..dan kusan ita soyyayar theori suna fada ne ina sauye muku amma ita pratical ta inda zan fara ma nake rasawa shiyasa nake bar musu dakin😜.. ...tun shi Maysam ta zama yar hannu a bunka ga renonshi yasa wani lokaci babu ko kunya itake nema ..soyyaya kam da tattali junan su duk wanda yagan se sun bashi sha'awa..sun kuma birgeshi ..karfi dayaji ta medasho mrs romantico ..Mark da Mahmud kam banda tsokana babu abunda suke mishi..
Babu ruwanshi da inda suke ako ina soyyaya yake gwada mata ..rayuwa tayi musu dadi ..su duka sunyi bulbul kwanciyar hankali ta zauna musu ..
🌹. 🌹. 🌹
A gurguje pls
Bayan wata ukku
Maysam tayi wani kyau da fari na ban mamaki ..ta kara cikowa musaman kirjinta..har wani fresh tayi ...Murad kam abun nema ya samu se kwasar garabasa yake .....
Yayinda ita kuma kwana biyun nan da zazzabi take kwana ...
Se kuma wani dan banzan kwadayi abu inde me yaji2 ne to zataci shi ..kwade harda na banzan..yau ma suna zaune lafiya2 suna hirarsu irin ta masoya ..can Maysam tace my king zanci hadin boss..
Gyara zama yayi yace miye kuma wani hadin boss..?
Dayake abun na rigima ne se kawai ta rushe da kuka har da shure2 ita kawai hadin boss zataci.
Da kyar ya shawo kanta yace wai dan Allah miye ne sena fita na nemomiki shi ...
Tace garin kwaki da madara da suga kuma ba'a saka ruwa hakanan ake shanshi..
Dafe goshi yayi yace to ni yanzu a garin ina zan samu garin kwaki ..ai tana jin haka ta sake fashewa da kuka tace kenan ma baza ka samo min ba. ..wayoo Momyna ina kike ne..
Babu shiri ya zari key ya fice ..be jima ba se gashi ya shigo ..nan ya hada mata ..tana ci taji yayi mata dadi .har wani lumshe ido take.dan haka rigima ta kwanta ......bayan ta gama yace taje ta dauko hijab dinta sutafi asibiti yayi mata wani test dan tabbatar da abunda yake zargi....
Ai kuwa bayan yayi mata test din ya gano karamin cikin dake makale a mararta na wata 2 da yan kwana ki...
Tana nan zaune yashigo da test daya karbo daga lab..batayi aune ba taji ya dauketa yana juyi da ita ...
Can ya sauketa yace am so very happy today..
Tana kallonshi tace what's happen ne...kake murna haka..
Yace toutes mes felicitations na kusa zama papa ke kuma mama a takaici'' tu es enceinte de deux mois''
Wani waro ido tayi tace what ?ciki?
Yana yin yanda tayi maganar ne ya tsorata Murad ..a ranshi yace kadade fa bata son cikin ....
.
Love you all😘😍❤
Fasma ce🖊 yar mutan Zinder
[16/08 à 22:26] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )
🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
S.W.A✍
🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Dedicated to all my fans😍❤
🅿101__102
```Manzon Allah(SAW) ya ce''baya halatta ga musulmi ya leka gida ko dakin wani ba tare da izini ba.
Bukhari ya rawaito shi```
[16/08/18 à 22:00]. Cike da karkarwar baki yace ee kina dauke da cikina na wata 2 da yan kwanaki ...
Cike da dakewa tace aman de zubar dashi za ayi ko?dan ni ba isa haihuwa ba ..kuma ma karatun nawa fa yakake so nayi dashi
What ?cikin nawa za'a zubar .? Wannan bama magana bace tun wuri ki rufe ta anan ..kuma inde akan karatune sede ki fasa makarantar wly bayan kin haifeshi kya gama inde har baza ki iya ba ehe
Se kawai yaji ta fashe mishi da kuka harda dire2 ita bata san cikin nan dole se an zubar dashi..kuma makarantar ta bazata fasaba.taya ma za'ace ita yar karamar nan tanada ciki tab ..ai kuwa da sake wai anbawa me kaza kai...
Tsawa ya daka mata yace shut up ...walahi cikin nan kamar kin haifeshi kin gama ko kina so ko bakya so...
Itama cike da daga murya tace to mu zuba ni da kai ...
Fuuu ta fice a office din tare da bugo mishi kofar...
Ya mutsa gashin kanshi ya fara tare da fadin inna lillahi wa inna ileyhi raji'un.....mi yake shirin faruwa dani ne ?ya salam....
Da sauri ya bi bayanta amman kafin ya fito har ta shige taxi sunyi tafiyar su ..bin bayansu yayi shima .. A kofar gidan ya sauketa ta biyashi ta shige ...yana shigowa yaga zata shige daki da sauri ya shiga gabanta ....yace pls wify kada kin mun haka wly ina son cikin nan na kwallafa rai na a kanshi....
Maysam kam shafa wa idonta toka tayi tace bata san da zancen ba ...
Murad ya kankance ido shima yace ...dama irin son da kike tinkaho kina mun kenan?
Maysam tace babu ruwan so da kuma cikin dake jikina...ciki ne de nace bana sonshi yanzu ..ka bari sena kara girma zan haifama ko nawa kake so amma ba yanzu ba ..am so young da haihuwa....
Murad yace sukuwa suke da alaka yanzu na tambatar da dama ba sona kike ba tunda har bakya son gudan jini na ....
To ai ba cewa nayi bana so ba . a yanzu nede bana so ...
Kai.yau kam dan karamin yaki sukayi tsakanin su ..har takai Murad ya samata hannu wato ya wanka mata marin da shin kanshi seda yayi nadamar yin shi ...
Ai kuwa Maysam ta hau ta kai kololuwa ..se kawai ta dau fushi da shi ..
To da fari ya damu da fushin nata yana ta rarrashi shima kuma daga baya se yayi forget da ita...
Sede matsalarshi da ita dabata cin abinci ...yana tsoron kada yunwa ta shigeta
Seda suka cinye sati guda cur basa ko magana kai ganin junan su ma wuya yake musu dan tun safe yake tafiyarshi kuma baya dawowa se lokacin daya san tayi bacci ..su duka har wata yar rama da baki sukayi ..dan duk sun damu da junan su tsabar rigimar ta ne kawai ya jefa su cikin wannan hali.....
Yauma kamar kullum dayake abun na rigima ne ..kin bacci tayi ta zauna nan tana jiran shigowarshi ..shima beshigoba se sha daya saura..tunda ya ganta a palo yasa za ayita yau..
Yi yayi kmar be ganta ba ze shige dakin shi da sauri ta shiga gabanshi tace yau seka gayan daga ina kake ..a ina kake cika dare ....
Tsuka yayi yace da kin damu dani da bakiyi mun tambayar nan ba ...to in son sani kike to abunda bikya sone wato ina wajen wacce zan aura ne kuma nan bada dadewa ba tunda ke bakya son gudan jini na ..zan auri wacce zatayi ta haifa mun y'ay'a..ko kinada abun cewa..
Kamar saukar guduma taji zancen ...bata ce dashi komi ba ta shige dakinta ..ranar kam taci kuka...
Tun su Mufeeda basu lura ba har suka san da basa magana ..basu de tambayeta mi ya gamasu ba dan tsakanin miji da mata se Allah...su de kullum cikin tausarta suke tare da bata hakuri ...tabi komi a sannu zata ga sakamako me kyau..
Shima a bangaren shi duk yabi ya fara susucewa kamar bashiba ..ko aikin ma baya meda hankalin shi akai ..Mark shike bashi baki da yayi hakuri ....
Kai abun har ya fara taba ciwonshi ..dan haka Mark ya daga waya ya sanar da Mahmud kan ya lallabashi ko ya gaya mishi mike damunshi ..
Mahmud ya daga waya ya kirashi ..tun suna gaisawa ya tabbatar da bashida lafiya ..cike da rarrashi da dubara yace pls Murad miyasa kake son tada ciwon kane ..?mi yasa baka tausayin kan kane.. ..duba dan yanda kake shan wahala kan ciwon nan?why bazaka bi komi a sannu ba. ..ka rungumi kaddarar Allah ba....
Ajiyar zuciya Murad yayi yace dan baka san mi yarin yar nan tamun bane ...dan taga ina sonta ne na damu da ita shiyasa take mun abunda taga dama ...
Mahmud yace calme down yanzu fada mun mi tayi ma ..
Yanzu in ba ta renani ba yarinyar ta kalli tsabar idona tace wai zata zubar da cikina?.ciki nane fa Mahmud gudan jini na...?kamar zeyi kuka..
Mahamud ya dan bashi baki duk da yasan bata kyauta ba amma se ya nuna mishi da yarinta ne kawai ke damunta har take son zubar dashi ..kuma ma da tana zubarwa da tayi kawai ka lallabata da akwai abunda yasa ta fadin hakan ..nan yayi ta lallabashi har yaji ya sauko ..yayi mishi godiya kamar kullum ..suka kashe wayar..
Itama kuma anata bangaren yaude Su Mufeeda sun tusata gaba kan abunda take fa be dace ba ..ya kamata ta gyara yau har tsawon wata guda kenan fa ..itama kuma ta damu da rashin mijinta kusa da ita ....
Ajiyar zuciya tayi sannan ta sanar musu ai akan tace se ta zubar da ciki ne suke rigimar nan ...
Mariam tace bakida hankali da kike son zubar da cikin ne .....
Mufeeda taso yi mata tsiya amma ganin halin da ake ne ya sata kyaleta ...tace ke miye dalilinki na on zubar da cikin ne ..
Cike da yarinta tace to bakunga yanda ake shan wuya ne wurin haihuwa wasu fa har mutuwa suke..kuma kinga ai bankai haihuwa ba salon kawai naje nayi yoyon fitsari gani yarinya karama dani duka ma am 17 old fa..
.. Mariam tace gaskiya da kinyi wauwauta fa ..ke yanzu bakya son ki haihu a dinga ce miki mama ne..
Se kuma naga Maysam tayi dan murmushi tace ina so mana ..
Mufeeda tace kuma bakya so ace wacce er kice ..kinayi mata wanka ,wasa ..in macece kina mata kitso ne..Manzon Allah ma yana cewa ''kuyi aure ku haiyayafa dan nayi alfahari daku ranar gobe alkiyama.....shin baza kiso ki haifu ki tarbiyatar da yayanki har Manzon cira yayi alfahari dakene .
Maysam tashafa cikin tace tab ai ni kuwa nake so ..kawai de ina tsoro ne...aman kuma fa yanzu na fara sonshi kadan2..dan in naji yana motsi se ina jin dadi kuma...
.dariya sukayi sukace muma kinga zamu zama mama .tunda mu triple.zaki haifa mana baby ...
Mariam tace kuma ai ko wani me rai mamaci ne ..ba dole se wajen haifuwa ba ko yanzu in kwanan mutum ya kare ze mutu dan haka ki fidda wannan abun ma...kuma ma kin sani ko wajen zubarwar ki mutu...bama wanan ba to infa shi kade kwanki a duniyar nan..kada ki butulce wa kyautar da Allah yayi miki mana ..muatane nawa suke so amman basu samu ba ..
Maysam tace hakane kuma fa . abunda yasa ban zubar ba naga Murad yana son shi ne shiyasa ma na barshi koda zan rasa rainane dan duk abunda yake so nima ina sonshi .kawai de banji dadin rashin fahimtar da yayi mun ne...
.suna haka se ga kiran Fulani ya shigo wayarta..bayan sun gaisa fulani tace am so happy for you dauther na ashe tu es enceinte shine kuma baki taba fada mun ba duk wayar da muke yi...daga ke har mijin. Naki
Rufe fuska tayi kamar tana gabanta tana dan murmushi kasa2 ...
Fulani tace dazu Mahmud yake bani labari ..Allah ya raba lafiya ya kawo masu albarka ..
Ameen tace kasa cike da kunya..kuma taji dadi da basu gayawa fulani abunda ke faruwa ba..
Nan.suka dan tattaba hira har take tambayar ta yaushene hutun nasu...
Tace nan da wata guda ne..ta saka mata albarka sukayi sallama..
Ta juyo ta kalli su Mufeeda tace na gode muku hakika kun cika kawaye na gari ..Allah ya qara muna dankon kauna da zumunci ..a tare sukece ameen yar rigima ai yanzu seki tashi ki fara shirin tarbar yayan mu ..
Dariya tayi ta kai musu duka tana