Showing 75001 words to 78000 words out of 183527 words

Chapter 26 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

313

yace

"Zan baka blank cheque lissafinka yafara daga naira milayan 100 zuwa sama ka rubuta nawa kakeso ka kawon 'yata da kanka yau"......

Wani jiri ne ya dibi Ababa ya zubar qasan palon gaban DD din batareda ya sani ba sbd kudin Daya fada shi Koda an auri yar tasa Bai taba lissafin zai samu kudin zasu Kai miliyan darin ba bare zuwa sama.

Zufa ne ya tsatsafo masa ta ko Ina ya karye Yana tsiyayo masa,

Kasa dagowa yayi ya Kalli kowa sbd yaqin dayakeyi da zuciyarsa da hankalinsa dake Neman gushewa akan Jin kudin,
Rawa hannuwansa suka dauka yayi saurin zirasu cikin babbar rigarsa kada a gani asan gushewan hankalin Daya samu na 'dan lokacin.

Girgiza Kansa ya hau Yi Yana Hana kansa bayyanarda halinda yake ciki
Amma idan har wannan kudin zai iya sakasa haka hakama Idan DD kaante zai iya bayarda wannan kudin kaman ba komai bane to idan ya auri yarsa yaya kenan?
Abinda zai samu zai zama nin ba ninkin wannan???
Hummmnn ya sauke numfashi a boye tareda yaqar zuciyarsa ya dago ya Kalli dd babba da Suma duk suka rasa abin fada sbd Tim farko kowannensu yasan waye Dawood da raayinsa da kalan yanayin rayuwarsa,
To Amma a yanzu dukkaninsu suna buqatan 'yar dake hannun Ababan Dan haka suna buqatan sacrificing wasu raayoyinsu Dan samun Abinda suke so da buqatan kaman yanda dd babba ya sauke nasa tsananin raayin.

Ganin kaman Basa hayyacin fahimtar Abinda yake fada ya juya yabar palon may be idan Basa ganinsa su kawo Wani tinanin na Abinda zai yiyu.

Yana ficewa Ababa ma Dayake ta yaqi da zuciyarsa gurin Hana kansa karban kudin Dawood kaante din ya fice zuwa gida Yana hada hanya zufa na sake jiqasa.

Bayan barin Dawood da Ababa palon dd babba Kai tsaye Kiran Umme yayi a waya wadda itama take matse da akirata din Jin zuwan Ababa kaantes taji ya aka Kai karshen magana Dan Bata hayyacinta matiqar ba gabanta taga 'yar Bilal dinta Kuma jikarta ta fari ta dawo ba.

Lokacin da tashigo palon Kallo Daya dd babba yayi mata ya dauke Kai sbd ganin yanda gabaki Daya ta fita hayyacinta sbd ciwon rashin 'danta,
Kaman wadda take kwance jinyar watanni Takoma idanuwanta kuwa sun kasa hucewa daga munin kumburin da sukai na kukan data kasa denawa har yau din na rashin Bilal da tsananin buqatan 'yarsa ta dawo gunta.

Cikin nutsuwa da sanyin jiki dd babba ya Bata tabbacin 'yar zata dawo hannunsu Amma sai idan ta saka Dawood amincewa da auren mahaifiyar babyn wannan shine sharadin Mahaifin maman Babyn idan ba Hakan ba a gobe zai tafuyarsa Subar garin gabaki Daya.

Hawaye masu dumi ne suka gangarowa ummen sbd lalata rayuwar 'danta da ake magana a maimaikon 'yar Dan uwansa da suke buqata su dukan,

Auren Sbb dole ne garesa Badan raayinsa ko buqatan Hakan yake ba Amma ya amince sbd ita Dayake son farantawa Amma tasani Wanda bayason hada ko muhalli da kowa har iyayensa ansamu ya aminta zaiyi aure yanzu tin baayi ba ana sake kawo masa Qarin mace ta biyu.,

Yaya Dawood zaiyi da auren mace biyu lokaci Daya?
Tako wane saqo anshiga haqqin rayuwarsa,
Amma Kuma Tayaya suna Kallo zasu rabu da 'yar Bilal ta tafi tabarsu kaman yanda Bilal ya tafi yabarsu da gibi me girman gaske a zukatansu.

A Karo na biyu zata sake zama uwa Mai son Kai ga Dawood Dan kuwa zata sake shiga rayuwarsa da Qarin wata macen.

Hannu takai ahankali ta share hawayenta tareda jinjina Kai tana Bada tabbacin zata gwada shawo Kansa akan maganar auren.

Miqewa tayi ta fito Kai tsaye part din Bilal da DD din yake ta nufa zuciyarta na karyewa.

Tana Isa a Palo ta taddasa zaune Yana amsa wayar Naseer a hankali Wanda ya kira akan yazo daukansa yau zai koma gidansa.

Jin qarshen wayarsa na tafuyarsa dazaiyi yasaka ummensa kasa riqe hawayenta suka gangaro tayi saurin sharewa da hannunta.

Zaunawa tayi gefensa tareda kasa juyowa ta kallesa sbd kunyar rokon da zata yimasa a Karo na biyu.

Idanuwansa ya dago ahankali ya zuba mata ya karance yanayinta tsaf tsawon mintina kafin ya Dan dauke idanuwansa Yana ajiye wayarsa dake hannunsa gefensa ya kalleta cikin nutsuwa yace

"Umme idan kikace nayi auren Nan Hakan na nufin Zaki janye wancan maganar auren na farko,
Na baki zabin duk Wanda acikinsu kikeso ki zaba Daya zan aura kowace a cikinsu".

Yana fadan Hakan yayi mata shiru sbd babu Abinda zai qara Akai,
Maganar zasuyita Janta ne har sai waninsu ya samu ciwon Daya shigesa na damuwa da maimaicin Abu Daya Wanda Sam Hakan baya cikin Abinda yake buqata a rayuwarsa.

Shiru ummen tayi tana kallansa da idanuwanta dasukai laushi sbd a cikin Biyun yanzu babu Wanda zata iya zaba tabar Wani.

Ajiyar zuciya tayi ahankali sbd da Bilal dinta na Nan da duk bazasu shiga wannan tsaka me wuyan ba daga ita har Dawood da zaa aurawa mata biyu duka badan Yana sonsu ba.

Miqewa tayi ta fito Bata iya zabar ko Dayaba a zancen ta koma part dinta tana shiga tinani da damuwan Tayaya ma zata iya kallan Dan uwanta da hajiyarsu ta fada musu Dawood bazai auri Sbb ba wata zai aura?

Wannan maganar kadai zata iya shiga tsakaninta da Dan uwanta da hajiyarsu komai ya lalace a zumincinsu.


Dad kaante ma da Kansa yaje yayo magana sosai da Dawood din Amma Sam raayinsa ya kasa sauyuwa Saida dd babba ya rokesa a matsayin shine zaiwa alfarmar Benazir,
Idan ummensa ta rokesa ta zabar masa Sbb shikuma ya rokesa ya zabar masa benazir Dan haka Suka sakasa a tsakiya sbd sune mafi soyuwa a ransa su Biyun sai babyn da ayanzu tin batazo hannunsa ba yake jinta cikin ransa ta maye gurbin da Dan uwansa yabar masa.

Tinda dd babba yake babu Abinda suka taba ganin ya kwantarwa Kai sai wannan buqatan tasa ta auren Benazir wadda ta saka kusan sauran yayansa sanin halinda ake ciki.

DD kuwa daya gama fahimtar babu Abinda zai sauya tinanin su dd babban daga maganar auren dole ya amince sbd yasan auren sbd 'yar dasuke buqatan karba zaayisa hakama bayajin zai iya kallan matar da Bilal yagama mallaka a matsayin tasa matar,
Bama zai iya saka kalman aurenta cikin Kansa ba sbd Dan uwansa musamman da haihuwa a tsakaninsu.


A cikin Daren zancen yarda da auren isarwa Ababa,
Da farko kasa yarda yayi da Abinda dad kaante ya kirasa ya sanar masa akan zuwansu Neman auren 'yarsa gobe Saida ya kashe wayar ya sake dubawa yaga tabbas sunan dad kaante ne suka gama magana a lokacin.

Sakin wayar yayi tareda zubewa qasa da sauri yayiwa ubangiji sujjada ya taso ya fito zufa na tsinke masa ya tsaya tsakar gidan ya kwada sunan benazir wadda ke daki zaune tana bawa baby Madara.

Jin Kiran Ababa ya sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta sanyi da faduwar gaba ta miqe ta fito kanta a qasa ta tsaya gabansa daga nesa kadan rungume da babyn.

Anne ma dake dake rakube zaune fitowa tayi gabanta na faduwan ta tsaya gefen benazir.

Hande ma da sauri ta fito tana tsoron idan ba mutuwa benazir din tayiba itama yake wannan ihun Dan kuwa benazir na mutuwa wannan Karan zaucewa Ababan zaiyi.

Tinda aka haifesu shekaru masu yawa benazir Bata taba ganin murmushin Ababa akansu ba Dan haka daidai lokacinda ya kalleta ya saki murmushin baya tayi ahankali qafafunta na Neman sarewa da tsananin tsoro da fargaba tana sauke Kanta qasa.

"Benazir kin cika mun burina na shekarun Dana debo Ina wahala daku,.

Kallan yarinyar hannunta yayi yaji zuciyarsa na sake sanyaya da farin cikin ganin wannan ranar
Yace

"Sunan benazir sunan sa'a ta ne a yanzu Dan haka itama na saka mata BENAZIR sbd idan Kuka je Tako ina sa'a tayita fasomin ba kakkautawa,
Aurenki zaa taho nema gobe a satin Nan zaa daura Miki aure.

Anne data ji saukan zancen har cikin zuciyarta ta rintse idanuwanta a hankali tana tilasatawa zuciyarta karban zancen da sanyin farin cikin dole.

Follow me at mamuhgee Arewabooks ko VIP for more pages
09033181070
#MAMUH#
#BENAZIR
#DD KAANTE
#HOT HOT
#MARRIAGE
#LIFE
#DEEP

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
43
Benazir Bata iya dagowa ta kallesa ko Annenta ba sake Yin baya tayi ahankali ta dafa bango idanuwanta na kasa taro ruwan hawaye sbd takai matakin da ko kukan yanzu Bata iyawa Amma dai zancen har lokacin jinsa takeyi kaman almara,

Rabata zaayi da Annenta,
Ya Anne zatayi rayuwa babu kowannensu,
Sameerah ta rasu, Safnah ta tafiyarta, sumayyah ta rasu
Ita Kuma yanzu gashi zata tafi tabar Annen da sunan aure,

Bata tausayin kanta sbd babu inda bazata iya rayuwa ba komai tsanani da wahala da rashin kauna hakama batada sauran Jin feelings a zuciyarta dama rayuwarta gabaki Daya da zata ji komai na duk abinda zata tarar a rayuwar da mahaifinta ya Saidata Akai.

Ababa cikin farin cikin dabai taba Jin irinsa ba ya tinkaro Benazir ya karbi babyn hannunta Yana mata wasa baki a washe Yana saka mata albarka harma da rungumeta Yana Jin kaunarta Mai tsanani wadda yake ganin kaman ta kudin dazaiyi ne sanadinta.

Hande ma farin cikin me tsanani na Jin zasu rabu da 'yar ta washe baki tana cewa

"Barkanmu da arziki daga qarshe dai zamu samu mu aurar da Daya daga cikin haihuwar Anne da babu Wanda aka amfana dashi."

Kalmar hande ta saka idanuwan Anne dasuke danne halinda zuciyarta ke ciki na rabuwa da 'yarta cikowa da hawayen data kasa barinsu saukowa ta hadiyesu suka koma maqoshinta sukai cikinta.

Benazir ma Kalmar sakata tayi qarasa silalewa ta zube qasa zaune tana rufe Idanuwanta dasukai mata nauyi.

Ababa kuwa wayarsa ta fidda babyn na hannunsa ya kira yaronsa Bilymanin yazo take ya fidda kudi ya sako aka bazama siyayya.


Har qarfe goman dare Mai saka Kofa da windows da masu Fenti na gidan Yana sakawa su benazir a dakinsu,

Tsakar gidan da waje kuwa da yamma Akai Fentinsu ba Bata lokaci.

Tinda safe masu qatuwar katifa da fanka aka zo aka saka musu dakinsu harma da labule da sabuwar Ghana must go ta saka kayansu na sakawa,
Hadda sabuwar cerpet din daki aka zo aka shimfide dakin duka da ita sbd sanyin siminti dasuke Sha shekara da shekaru kada ya kama baby benazir.

Koda karfe goma Sha dayan Rana tayi gidan gabaki Daya kaman ba gidansu ba,
Benazir da Anne suna daki zaune ko mamakin sun kasa Dan a yanzu babu Abinda zai Basu mamaki ko tsoro daga wannan rayuwar.

Sabbin kayan sawa masu kyau da maana aka siyowa benazir na jallabiya Mai kyau da yar tsada harma da tirarika masu Dan kudi.

Itama Anne an siyo mata Riga da zani na atampa ready-made masu yar tsada
Ya sakasu cin abinci duk bayan awa data saiyace su sake ci sbd so yake fuskokinsu dasuka Fi kama dana qwarangwal su Dan ciko kafin zuwansu kaantes.

Tin safe yasaka aka gyare koina aka siyo abinci lafiyayye daga restaurant me yawa aka ajiye sunta fama yimasa cin dole kafin Kuma yasaka hande da kanta ta zaunar da benazir tayi mata wankin Kai Dana qafafu duk da Bata cikin qazanta sbd sunada tsaftansu sosai kaman ba wainda ke cikin wahala ba Amma sbd muzantawa hande ce ta zaunar da ita ta Riga zuba mata ruwa tana wanke mata Kai kaman yarinya qarama.

Bata motsaba har handen tayi ta gama ta Bata Daman tashi tkuna ta miqe jiki ba qarfi tabar gurin taje tayo wanka ta dawo dakinsu ta zauna bakin katifar da tsoron Hawa ma sukeyi sbd kada baqin su tafi yace abada katifar yace sun lalata masa Dan haka yasaka ma sun kasa sakewa su hau katifar.

Mai tashafa ahankali jikinta babu me magana a tsakanin ita da Anne har tagama ta shirya cikin kayan da aka siyo din ta shirya baby bena itama cikin kaya masu kyau da nauyi na Zeenah data kawo mata shekaran jiyan datazo.

Anne ma wankan tayi ta shirya cikin nata kayan da aka Bata suka zauna daki jigum jigum kaman wainda zaayi shooting film dasu.

Hande ma fes ta shirya cikin lace Blue da fari ta fito kaman tsohuwar albarka.

Ababa kam Jin yake kaman ranar ce zaa daura auren Dan haka yayi Shirin mutinci da babbar Riga da Hula tareda Wanda ya aminta ya tayasa tarban bakin da Bada auren.


Qarfe hudu bayan sallar laasar baqin suka iso ga mamakin Ababa harda dd babba aka taho da dad kaante sai Hon kaante qanin dad kaante,

Dd babba ko auren yayansa babu Wanda taba zuwa da Kansa nemawa aure sai wannan Karan Wanda Daman alqawarinsa ne shine zai je namawa Dawood aure,
Bai samu yaje ya amso masa na Sbb ba Dan haka ya taso da Kansa Dan nema masa na benazir.

Hadda Umme da mum Khadija akaso sai Zeenah da Siyam kaante autan mum Khadija itama.

Su dd babba kofar palon Ababa ta waje aka Bude musu suka shiga su kuwa su Umme Kai tsaye cikin gidan suka shigo Dan ganin baby Benazir da mamanta.

Hande na ganinsu ta saki fuska tana musu barka da zuwa cikin girmamawa da nuna farin cikin zuwansu.

Anne ma dole ta fito tayo dakin handen sbd a can aka saukesu.

Cikin nutsuwa da sanyi tareda girmamawa ta shigo dakin ta gaidasu tareda musu barka da zuwa.

Umme Datake kallanta a natse ta hango nutsuwa da rashin son kallan mutanen Anne sai taji Dan sanyi yaqara shigarta sbd koba komai mahaifiyar benazir nada nutsuwa Allah yasa hakama benazir din.

Zeenah ce ta Kalli Anne bayan ta gaidata tace

"Benazir da baby fa?"

Cikin nutsuwa da sanyi tace tana daki bari tazo ta kawo muku 'yar.

Juyawa tayi ta fice.

Daki taje ta kirawa benazir da jikinta yagama sanyi Amma babu gudu ba ja da baya ga wannan sabuwar qaddarar Dan haka ta miqe rungume da bena a jikinta ta fito.

Tana fitowa Zeenah na fitowa daga can zata amsa waya Amma tana ganinsu ta fasa ta nufo tana miqa hannu ta karbi little bena.

Gaisawa sukai da benazir da batasan me zata ce suka nufi dakin hande qafafunta na rawa.

Zeenah ce a gaba rungume da baby ta shigo ta nufi su Umme tana miqawa Umme babyn tana cewa

"Ga benazir Nan ta shigo Umme."

Hannu na rawa cikin Jin sanyi da farin ciki Umme ta karbi Babyn kafin ta dago ta zubawa benazir data qarasa shigowa cikin nutsuwa kanta aqasa itama Ido.

Ahankali cikin sanyi da yar rawar murya benazir ta Bude baki ta gaidasu Daya bayan Daya batareda ta dago ta Kalli kowannensu ba.

Ajiyar zuciya Umme ta sauke sbd sai yanzu ne take fahimtar Abinda yasaka Bilal kamuwa da son benazir din,
Bilal na son nitsatsiyar mace Mai tsananin sanyi,
To Amma Dawood total opposite ne na Bilal anan bangaren shi baamasan irin matar Dayake so ba kokuma raayin aura,
Amma ita dai idan har wannan nutsuwar Data ga benazir da mahaifiyarta da ita to benazir din ba Abar qyama ko baqin cikin aura bace.

Kasa zama cikinsu tayi kaman yanda Zeenah taso Dan haka ta silale Takoma daki
Anne Kuma itace ta kawo musu ruwa da abin Sha harma da abinci da snacks masu kyau da akayo order acikin sabbin plates da Ababa yasaka aka siyo.

Itama tana gama Jere musu kayan ta fice sbd bazata iya tsayawa cikinsu ba.

Daki tabi benazir Suka Kalli juna Annen ta qaqalo murmushin da ko kyau baiyi mata ba sbd zamansa na qarya da qarfin hali.

Benazir ganin Hakan ta saki nata murmushin Mai ciwo Daya bayyanarda zafin quncin dake qasan zuciyarta tana nunawa Annen gefenta da hannu ta qaraso ta zauna.

Annen ce a hankali ta sauke numfashi ta Bude baki tace

"Benazir na Amince kuma nayi na'am da wannan auren da zaa dauka Miki har cikin zuciyata a matsayina mahaifiyar data dauko cikinki ta haifeki Ina Miki fatan samun sauyun rayuwa ta hanyar wannan auren,
Allah ya albarkaci rayuwar da Zaki tarar acan keda Benazir qarama hakama inshallah zanyi juriyar da banyi a baya ba,babu Abinda zai sameni sai Abinda Allah ya Riga ya qaddara zai sameni."

Sunkuyar da Kai benazir tayi kalaman Anne na sanyaya jiki da zuciyarta sbd tabbatarda dai auren zaa yimata ta tafi tabar Anne.

Numfashi kawai ta iya saukewa jikinta na sake mutuwa da sanyi a hankali ta furta

"Komai zai zo karshe Anne,
Dukkanin tsanani Yana tare da samu inshallah,
Zaki rayu kiga auren Baby benazir Anne,
Zaki rayu,wahala Bata kisa,komai zai wuce Anne.....riqe hawayen dasuka ciko idanuwanta tayi tana hanasu saukowa sbd baqin dake gidan.

Annen ma kasa magana tayi tana Hana kanta sauko da nata hawayen itama.

Sake kiransu Akai suka fito mum Khadija ta saka Benazir din zama tareda su dole suna Dan tambayanta lafiyan baby da ita kanta tana Basu amsa a taqaice cikin girmamawa.

Ahakan sukaita kokarin Janta da magana kafin aka Sako maganar Bilal Wanda ya saka Benazir kasa riqe hawayenta na rashin 'yar uwarta da hawayen Datake ta dannewa tin a daki sukuwa jikinsu duka yayi sanyi Suma hadda hawayen sbd tinanin rashin Bilal takewa hawaye.

Yanda benazir ta bayyanarda kukanta a fili na rashin Bilal ya sakata shiga ran ummensa dasu Zeenah Dan haka Suka matsu ma kawai ayi auren ta dawo cikinsu su mayar mata soyayyar dasukewa Bilal ita da baby Benazir wadda a take Zeenah ta Dora make AMNAH akan sunan benazir din da aka sakawa babyn.

Da zasu tafi kaman kada su bar mata babyn haka Suka fita suka tafi Anne naji nauyin zuciyarta na Dan raguwa sbd ganin mutanen da Bena dinta zata Yi rayuwa acikinsu.


Sun nema auren Benazir Ababa ya Basu sun Bada kudin aure masu yawa dasu sake qarawa Ababa kaunar baby Benazir,
An saka ranar daurin aure 6 ga watan Sept sati biyu masu zuwa kenan.




*******Maganar auren ta yadu har inda Ababa Bai taba tinanin zaa fada ba Jin yake ana fada,
Kullum sai ya saurari redio da kafofin yada labari Dan kawai sauraron sunansa a cikin sanarwar daurin auren duk da kullum zuciyarsa quna takeyi idan ya Tina mace biyu zaa daurawa Dawood din lokaci Daya Amma tinda dai tasa zata shiga baida matsala hakama Amnah zata sa a Fi fifita benazir akan dayar tinda ita Amnah kowa na sonta.

Sati na zagayowa Akai yankan sunan benazir Amnah Wanda Akai a sirrance batareda ma kowa yasaniba,

Har lokacin Dawood Bai San waye benazir da zai aura ba hakama sunanta takamamai ya kasa riqewa sbd ko maganar ya dakatar da ayi masa buqata kawai a daura auren yarinyarsa ta dawo hannunsa qarqashinsa.

Ranar da Kai sunanta a ranar Zeenah tazo ta dauki Amnah taje da ita kaantes.

A ranar DD yafara ganin ta a hannunsa ya zubawa fuskarta Ido babu Abinda ta baro na Bilal,
Wani irin feelings ne na soyayyar Uba Mai tsananin gaske yaji yanawa babyn,
Shi baya ko daukan Yara sbd Basu damesa Sam baya ma Wani San

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login