Showing 48001 words to 51000 words out of 183527 words

Chapter 17 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

345

wadda itama sumayyahn take kallo idanuwanta na cikowa da hawaye masu zafi da radadi.

A tare hawayensu suka gangaro daga idanuwansu batareda kowannensu ya iya cewa komaiba sbd sun Kai matsayin da basa buqatan Bude Baki su fada quncin ransu saidai hawayensu su isar da sakon.

Ahankali Benazir takai hannu ta dafa na sumayyah suna sauke qaramin numfashi a tare.

Shiru ne ya ratsa dakin tsawon lokaci Babu mai iya magana acikinsu suna jiran tsammanin Ababa jikin sumayyahn Babu qwari ko kadan.

****A gida Tin bayan fitarsu hande taga Anne na Neman shidewa ta debo ruwa Kofi daya ta hau yayyafa mata ba Ji ba gani tana cewa

"Benazir bazaki mace ba ki barni da Renan jikan gaban fatiha bayan na gama naki Renan nayi na 'yayanki,

Maza tashi kece Zaki Rena jikanki tinda kune kukasan ya Akai kuka somosa."

Numfashi da ajiyar zuciya Anne ta hau jerowa tana Bude idanuwanta da Dan qarfi sbd ita kanta bazata so ta mutu a yanzun ba tabar 'yayanta Harma da jikan idan yazo cikin wanna masifar su kadai tanason kayanta,jikan ma na gaba da fatihar tana sonsa ahakan tinda Allah ne ya qaddaro musu hakan Kuma sun karba.

Hande wurgi tai da kofin hannunta tana wucewa cikin masifa da cewa

"Tinda kukayo cikin nan kuka hanamu samun zaman lafiya a gida Nan,

Duk Kun zautar mun da 'da ya haukace ba dare ba Rana magana yake shi kadai da Kansa duk akan cikin nan,

Gashi yanzu Yana musu Barazanar yunwar da Babu ranar dawowa daidai idan aka rasa cikin,

Benazir aurenki dai ba Alkhairi bane ga Ababa tin kuruciya har girma Bai ganewa komai akanki ba".

Sai alokacin wasu hawaye masu dumi da zafi suka gangarowa Anne ta dafe zuciyarta Dake Neman fashewa sbd abinda takeji cikinta na tsananin qunci da damuwa.

Kasa komawa daki tayi ta rarrafa ta miqe tsaye ta Isa Inda kujerar tsakar gidan take ta zauna tana dafe kirjinta dake Dan mata nauyi da radadi ta dasa zaman jiransu har Akai asuba tana gurin zaune.

Sai da gari yafara haske ta iya daurewa ta tashi taje tayi sallah ta sake fitowa tana kokarin sake zaunawa zaman jira hande ta fito tana cewa kasheni zakiyi da yunwa kenan bazakiyi abinci ba tinda 'yarki Rai na hannun Allah.

Fasa zaunawa tayi ta nufi kicin tafara kokarin sharewa kafin tafara hura wutan aikin.

*****Ababa har qarfe goman safe Yana yawon Asibiti Neman jinin da zaa sakawa sumayyahn Amma Sam baa samu na siya ba hakama shi bazai iya qanqantar da Kansa rokan kowa jini ba.

Ransa ba qaramin baci yai ba,fushinsa sai qara Hawa yakeyi sbd ko ciwo Bai taba hanasa fita nemansa ba sai yau gashi tin asuba Yana gantalin nemawa jikan da a yanzu yafi kowa son zuwansa duniya.

Yunwa ma bayaji sbd a yau ida Bai samu jini ba dole ya Isa KAANTES su Dd babba Aturo Mai Bada jini wlh,

Yaso ya bari sai Alh Bilal ya dawo qasar ya tinkaresa Amma idan har baa samu ba gwara yaje tin wuri kar yayi biyu babu

Koda Babu me Bada jinin dai su San da cikin ta yanda ko cikin ya matu shikam zai samu abinda zai Maida dukiyar daya rasa.

Koda yadawo dakin daga benazir har sumayyahn idanuwansu a kumbure da kukan dasuka Sha sosai suna ganinsa benazir tai qasa da Kai sumayyah kuwa Dake kwace rufe idanuwanta tayi ahankali tana Jan numfashinta Dake fita daqyar.

Kallan da yayi musu yana Jin inama jinin uwarsu zaiyi da daukota zaiyi a kwashe duka jininta a sakawa sumayyahn da akeda buqatan lafiyanta yanxu.

Kokarin zama yakeyi nurse ta shigo tana fadan baa kawo jininba ana fa buqatansa da gaggawa gaskia.

Cikin takacin rashin sanin abin Yi yace

"Baa samu ba ni nawa Babu yawa bazan iya badawa ba Idan akwai Inda zaa samu na siyan bayan Nan ku fadan nawa ne Kuma nawa ne.

Da mamaki nurse dn ke kallansa Jin wai bazai Bada nasa ba bayan shine mahaifin sumayyahn kaman yanda ya fada.

Ganin kaman zata ma batawa kanta lokaci ne yasata juyawa tana cewa Leda biyu mukeso Kuma ko wanne ka tanadi kudinsa muje Akira aji idan akwai Inda muke saka ran zaa samu.

Miqewa yayi Yana take kafar benazir cikin zafi ya fice daga dakin Yana bin bayan nurse din ransa a bace Jin har Leda biyu bayan yasan jinin mutum sai yayi tsada sosai Kila.

Bayan fitarsa Babu Wanda ya iya motsawa har tsawon mintina kafin sumayyah datasan ba jinin da Ababan zai iya siya a Saka mata bare ma ta rayu,

Hawaye ne suka cika idonta tana kallan benazir data kasa kallanta sbd karyawar zuciyarta yayi yawa.

"Bena" takira sunanta ahankali da wani irin rauni tana Jin karyewar zuciyan itama dan idan ta mutu ta barsu da wahalar da taci alhakinsu.

"Bena ku yafemun ke da Anne....

Kukan da Benazir tafashe dashi ne yasata maganarta karyewa itama tana sakin kuka.

Kasa sauraranta benazir tai ta miqe tsaye tareda barin bakin gadon ta juya mata baya tana kuka mara sauti sbd harga Allah zuciyarta bazata iya daukan rashin sumayyah ba bare Anne.

Ahakan suka ringa kuka har sumayyahn ta dawo tana rarrashin Benazir a hakan sukai shiru dole

ta dawo kusa da ita ta zauna tana Bata tabbacin zaa Sami jinin da yardar Allah.

******

Ababa kuwa Inda aka Saka ran samun jinin baa samu ba take tashin hankalinsa ya Qaru Dan haka Kai tsaye ya yanke shawarar gwara ayita gaba daya bazai haukace ba a hanya gwara Suma su shigo lamarin.

Securityn Dake masa duk wani mugun bincike da boyayyan aikinsa ne ya kirasa a waya daidai lokacin da ya shiga dakinda sumayyahn take ya rufo kofa.

Wayar yakalla cikin zafi da masifar daya rasa yanda zaiyi da ita tana cinsa,

Ganin Mai Kiran yasashi furzar da numfashin bacin Rai Mai zafi ya dauka zaiyi magana aka rigasa da fadin

"Sir Bilal Kaante ya Sauka kasar yau dinnan A Lagos,

Komin dare yau zai biyo wani girjin ya iso gida".

Tinda aka fara wannan masifar sai wannan lokacin yaji wani sanyi ya Sauka cikin zuciyarsa Yana sanyaya wutar Dake cin zuciyarsa da gangan jikinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke a Fili Yana cewa

"Ayau Nima zanga Manyan kaates din da yardar Allah,

Komai na aikina ya zama shirye Ina awa biyar bakajini ba kasan abinda na fada Maka dai."

Kashe wayar yayi Yana juyowa yakalli su benazir Dake jinsa Yace

"Alh Bilal kaante ya dawo

Ayau zanje musan matsayar gaskiar wannan maganar,

Kuyi adduar komai ya tafi daidai idan ba haka nadawo kisan ku zanyi naje gidan yari Nima ba huta da masifarku data isheni.

Juyawa yayi yafice dakin batareda ya waiwayosu ba bare tinanin suna buqatan abinda zasu Dan sakawa cikinsu.

Yana fita Kai tsaye gida ya nufa Dan yin wanka ya sauya kaya zuwa shigar alfarma Dan koba komai ta yanda zasu San lafiyarsa kalau ba mahaukaci bane yaxo Yana karanta musu hauka.

*****Barinsa asibiti da kusan awa daya suna zaune jigum jigum cikin fargabar abinda zai biyo baya idan aka samu matsalar da Alh Bilal ya gaddada cikin,

Faduwan gaba da tashin hankalin dasuke ciki ya hanasu Jin yunwa,

Musamman sumayyah datafi shiga tashin hankalin me Bilal din nata zaice.

Kofar dakin nasu Akai knocking ahankali tareda budewa aka shigo cikin sanyi da nutsuwa

Take atmosphere din dakin ya sauya gabaki daya da wani irin qamshin luxury turaran _CARON POIVRE_ na DD dayake amfani dashi kwana biyu yayi tare dashi akan zasu dawo qasar tare Amma wayar sulaiman daya saka bibiyan motsin su Benazir yasashi dawowa Bai jira DD ba dazai dawo tareda su umminsu.

Qamshin yasa sumayyahn kasa gane shi dinne Kai tsaye sbd wannan ba qamshinsa bane kwata kwata da Suka saba Ji.

Ganinsa a tsaye Yana kallansu zuciyarsa na karyewa yasa daga sumayyah har benazir fara hawayen da suka kasa tantance na farin cikin ganinsa ne kokuwa na murnar sumayyahn tasamu Mai Nemo mata jinin da ake Neman.

#MAMUH#

#LOVE#LOVE#ROMANCE#DD#BENAZIR

#LITTLE AMNAH KAANTE

#ZAFIN KAI#MAMUHGEE

27

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

27

Kaman saukan ruwa Mai sanyi cikin maqoshin daya bushe da qishi haka dukkaninsu ganinsa ya sanyaya zuciyarsu musamman sumayyah data fara hawayen da bata shirya ba idanuwanta na Kansa.

Shima ita yake kallo idanuwansa na bayyanarda rauninsa da tsananin son da Allah ya Saka masa nata.

Benazir ma farin ganinsa takeyi a Fili idanuwanta na cika da hawaye sbd koba komai idan su Basu samu gatan rayuwa ba 'dan da zaa Haifa musu zai samu gatan daga ubansa idan har zai aminta dashine uba Kuma magajin abinda zaa Haifa din.

Qarasowa yayi Kai tsaye gurinta ya nufa Bai tsaya Bata lokaciba ya zauna bakin gadon ya rungumota jikinsa a karo farko hawaye na ciko idanuwansa sbd tsananin karywan da zuciyarsa tayi da ganin yananinta gabaki daya ta rame sosai ga cikin Shima yafito ana ganinsa.

Saukowa hawaynsa sukai sbd yakasa riqesu,

Yayi kewanta fiyeda yanda ya tsammata zai iya daurewa,

Ga halin daya sakata yasani zuwa yanzu Ababa ya gama hukuntar da ita Harma dasu Anne ga ciki da yanxu kam dole kowa zai girbi abinda ya shuka,

Babu maganar boyo tinda ciki baa boyesa saidai babban tashin hankalinsa da baqin cikinsa tin daga ranar da aka sanar dasu wanzuwar cikin shine tarihi ya sake maimaita Kansa akanshi.,

Tayaya familynsa zasu karbi wannan girmamman zancen dazai kawo tashin hankula da damuwa.

Shigowar nurse yasa Bilal din sakin sumayyah Yana goge fuskarsa da black handkerchief din dayake aljihun kayan jikinsa.

Qarasowa tayi tana fadan har yanxu baa kawo jinin ba sai ta mutu ne zaa fara kukan ta mutu bayan sune suke son kasheta sbd ance musu da gaggawa ake buqatan jinin.

Kallan nurse yai Yana Maida kallansa kan sumayyah Yace suje Yana buqatan ganin likita.

Juyawa tai ya kalli benazir cikin kulawa da sanyin jiki Yace mata Yana zuwa.

Bin bayan nurse din yayi suka fice daga dakin.

Duka wani bayani dayake buqata yaji daga bakin likita da nurse Dan haka take Yace a duba jininsa idan zaiyi a Saka mata.

Babban Saar dataci jininsa O- ne Dan haka Babu Bata lokaci aka hau diban jininsa a Saka mata hankalinsa na rabuwa biyu sbd baisan ta inda zai fara tinkarar su Dd babba da dad Kaante da zancen kaddarar data samesa.

Benazir kuwa kwanciyar hankali da nutsuwa data samu ta lokacin ta ganin a qalla sun samu jinin da zai taimakawa yar uwarta warware.

********Karfe hudu na yamma bayan yar tafiya Mai tsayi daga gidasa zuwa kaates Ababa ya Isa qatuwar makeken gate din kaates Wanda Saida ya daga Kansa tsawon mintina ya qarewa gate din kallo Yana mamakin Wanda yake rayuwa a wannan gidan kwadayi me ze Kaisa gurin 'yar marasa galihu.

Securities din Dake zaune a kofar gate din ya hanasa tinkarar qatuwar gate din Kai tsaye Yana Jin qarfin zuciyarsa na qaruwa Dan kuwa dole su Dd babban daya sani a jaridu da labarai su tsaya a sauraresa idan Sunki baida asara bayyanarda maganar cikin zaiyi duniya ta sani har gidan jaridu Dan kuwa tini ya tanadi makaman yaqinsa.

Ko su karba ciki ko yaja musu bacin sunan da kafin suna da mutuncinsu ya dawo daidai ba shekarun kusa ba.

Kuma ya Maka su kotu Koda sunfi karfinsa ya dai Bata musu sunan da duniya taji abinda Akai.

Tin shigowarsa anguwar securities suke kallansa Amma Babu Wanda ya kulasa tinda Basu San Ina ya nufa ba.

Gurinsu ya nufa Kai tsaye Yana Isa suka dakatar dashi daga nesa Dan basa bari ana isowa jikin doguwar katantar gidan.

Daka tawa yayi Yana kallansu kai tsaye Yace musu gurin Dd kaante yazo.

Gabaki daya securities din suka zubo masa idanuwa Jin sunan Wanda Yace yazo gurinsa.

Cikin son dakatar da koma wane irin shirme Ababan ke shirin Yi shugaban securities din fuska ba sakewa Yace

"Sir DD kaante baya qasar shekaru da dama so kabar Nan please".

Hanya ya nunawa Ababa dayake kallansa Yana Jin takaici Amma tinda Neman ganin Ddn yake dole zai sauke Kai harya samu ganinsa tukuna.

Sanyaya murya yayi cikin Basu girma a gurin aikin nasu Yace

"Officer Alhaji Dd babba dinne baya qasar?

Dan ayimun alfarmar na gansa wlh lamari ne mai mahimmcin da idan natafi yau zaa iya rasa Rai,

Kuma ran 'dan Nan dinne ne maana jininsu ne.

Wani kallo tsaf chief security din yake masa Yana son tabbatarda idan Ababan ba mahaukaci bane acikin kaya lullube.

Idanuwan Ababan yake kalla Yana sake katantar yanayinsa Dan kada su tsaya batawa kansu time da mahaukaci basu sani ba.

Ganin ana tantancesa yasa Ababa tsayawa da kyau idanuwansa na kan kofar gate din da aka wangale wata mahaukaciyar Lexus black ta fito baa ganin Wanda yake ciki sbd Nisan datake da Inda suke tsaye.

Ta gabansu motar ta wuce idanuwan Ababa kaman zasu zasu fado subi motar Dan son ganin Wanda yake ciki amma chief securityn ya hanasa ko motsawa daga Inda yake bare ya Isa gate din.

Sallamarsa sukai da cewan ya wuce daga layin gabaki daya basason ganinsa.

Qin tafiya yayi ya tsaya Inda yake Yana sake qudurcewa a ransa yafison su masa duka a gurin idan yaso dole a tsaya a sauraresa ya sake samun damar nunawa duniya dukan da Akai masa bayan anwa 'yarsa fyade so uku.

Sharesa sukai a gurin tsaye suka koma bakin aikinsu iyakaci Yana kusanto babba gate din farkon dukan da zasu masa ko haukace saita sakesa.

Gyara tsayuwa Ababa yai a gurin sbd yau din a shirye yake da kwana tsaye a gurin indai zai samu dacewa da fitowan Wanda zaisa a barsa yaga Dd babba.

Rana Ce tafara gasa Kansa yafara daukan zafi Yana tsiyayar wani irin zufa Yana jiqasa kaman Wanda ya hadiye kunama da ranta.

Sanyi da gajiya qafafunsa sukai matiqa Amma Sam bayajin zai hakura ya tafi gashi hankalinsa duk ya gama tashi zuwa yanzu Kila sumayyahn ma ta mutu da rashin jinin.

Azabar ranar wunin akansa ta qare har Rana ta fadi Yana gurin Yana zare idanuwansa da wahala ta sake rinarwa.

******Acan asibiti kuwa har aka gama diban jininsa aka sakawa sumayyah ba Ababa ba labarinsa.

Daki aka sauyawa sumayyahn zuwa sama dakunan da suke ajiye masu kudi.

Komai sake siyowa akai tareda abubuwa buqatanta dasu abinci kala kala take nurses ba kunya suka hau hidima dasu.

Wanka Benazir ta taimaka mata tayo bayan angama Saka mata jakar jinin daya.

Dan qarfi ta samu a jikinta sumayyahn kafin ta zauna da Kansa ya Bata abinci tanaci a hankali itama benazir ta shiga toilet ta watso ruwan ta shirya tin a can tafito ganin sumayyah taci abinci yanda ya Dan kamata sai alokacin itama ta daure taci lafiyayyan abincin da aka kawo musu iri iri.

Har yamma Alh Bilal Yana tare dasu cikin kulawa Yana jiran Ababa sbd ganin juna da yanxu garesu ya zama dole tinda dalili Mai qarfi ya Saka.

Dayake wayoyinsa a kashe suke Babu Wanda ya Kira nemansa bayan yasan iyayensa sun San ya iso tinda daga gida driver yaje daukansa airport Kuma daga can Nan ya ajesa.

Ana kokarin Sallan magrib dole ya baro asibitin ya nufi gida da niyar zai dawo daga baya.

Driver har lokacin Yana Nan Shima Yana jiran fitowar Bilal din dan haka Yana ganin fitowarsa ya taso daga Inda yake Zaune suna fira da wani Wanda ya sani da sauri.

Motar suka shiga kusan a tare da sir Bilal din dan lokacin ya kunna wayoyinsa Kiran Dd babba ne yafara shigowa wayarsa take ya dauka jikinsa a mace.

Kicin muryarsa ta Kai tsaye Yace yazo Yana buqatan ganinsa.

To Yace cikin girmamawa sbd yasan Shima Bai kyautaba rashin Isa gidan su San da isowar tasa.

Numfashi ya sauke zuciyarsa na tsinkewa da Neman da Dd babban yake masa dan muryarsa ba sauki Kai tsaye take.

*****Ababa babbar sa'arsa daga Allah ne kaman yanda yake fada sbd ana Kiran sallar magrib a babban masallacin kaates Dake manne da qatuwar katangar gidan sai ga fitowar tsohon daya gama jiquwa a cikin arzkin Allah da tarin Hutu da dukiya Harma da boko da ilimin addini ya fito Dan shiga sallah Kuma cikin wata sabuwar sa'ar shi dayane yau sbd dad Kaante da sauran mazan dasuke dasu a gidan sunyi tafiyan kwana daya wani mahimmin daurin auren da dole kaates su halarta.

Duk kowace Rana daidai wanna lokacin Dd babba ke fitowa sallar magrib baya taba fashi matiqar Yana qasar Kuma garin.

Ababa Bai taba tinanin zai samu dama a ranar farko ba lokaci daya ta ganin Dd babba kaante Dan haka yake sake Jin Kansa me Saa.

Da gudun fanfalaki yaso zuwa gurin Ddn Amma securities sukayo Kansa Dan haka ya jujjuya baiga ruwa ko gurin alwala ba bare shima ya fada masallacin Dan haka juyawa yayi da sauri yana Neman Inda zai samu qasar taimama Amma anguwar kaman ta kafiran turawa Babu koina a tsare.

Daqyar ya samu Inda keda yar qasa yayi taimama jiki na rawa ya dawo da gudu gudu sauri sauri yana Isa ya shige masallacin kafin securities su ankare Kuma Daman baa Hana shiga masallacin Sedai bama kowa ke zuwa ya shigaba tinda anguwar akwai tsaro ba mutane.

Ba mutane sosai Dan haka ya kutsa ya shige sahun gaba Inda Dd babban yake aka tada sallah.

Ana idarwa salati da istigfar kawai Ababa yayi ya juyo Yana Satan kallan Dd babba Dake adhkar cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin masu abin duniya.

Ahankali kowa ya fice aka bar limamin masallacin kaantes din sai Dd babba sai Kuma Ababan da bakinsa ke rawa sbd maganar Dake cinsa kada damarsa ta qwace.

Daya daga cikin securities din dazu ne ya shigo zai masa magana

Yana ganin hakan ya miqe ka tsaye ya nufa gurin Dd babba Yana miqa masa sallama da gaisuwa a tare.

Jinjina Kai kawai Dd babba yayi batareda ya amsa da Baki ba sbd Bai gama laziminsa ba Kuma Bai dago ganin kowaye ba.

#MAMUH#

#BENAZIR ABABA KAANTE

#DD KAANTE

#ZAFIN KAI

#LOVE#MARRIAGE#ROMANCE#BABY

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
28
Ganin security din na sake nufosa ya sanya Ababan zubewa ya zauna gefen Dd babba Yana sake Dan saita muryarsa cikin nuna nutsuwa da mutuntuwa ahankali Yace

"Ranka ya Dade gurinka nazo tin safe an hanani ganinka a waje na wuni tsaye har Rana ta fadi akaina,
Alhaji ka saurareni maganar danake tafe da ita Mai tsananin girma da mahimmanci Ce sbd maganar Rai da mutuwa akeyi data shafe ahalinka da nawa ahalin."

Kalmarsa ta qarshe Ce ta Saka Dd babba waiwayowa ta kallesa tinda ya fara magana bai juyoba,

"Maganar Rai da mutuwa tsakanin ahalinsa dana kaantes?

Daga Ina wannan din yake?
Lafiyayye ne ko kuwa?" Shine kallan da Dd yayi wa shugaban securities na gidan nasu kafin ya maida kallansa kan Ababa Dake a shirye qyam zantikansa a tsare tsaf cikin ransa da zai jero.

Ganin kallan da Dd ke masa yasa take yayi fuskar tausayi da bacin Rai tareda bayyanarda baqin cikin rayuwa na tareda shi kaman Wanda yayi rashin uwa da uba da kowa na duniya.

Cikin nutsuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login