Showing 69001 words to 72000 words out of 183527 words
ana cikin tsananin hali da qunci da baqin cikin rasuwar ta Bilal wadda kusan duka ta taba iyayensa da kakan nasa da basusan suna kaunarsa ba sai a yanzu da bayanan yabar musu duniyar Dan haka dukkaninsu babu Wanda yake zaune da qafafunsa a kwance suke ba lafiya hakanan ake daurewa ana karban gaisuwar daga manyan mutane da baqin dake zuwa na kusa Dana nesa.
DD kaante ma rashin lafiya ce a jikinsa sosai sbd Bilal Wani bangare ne na jikinsa da bayan iyayensa shine halittar dayafi tsananin so a duniya,
Rashin Bilal lokaci Daya ya girgiza duniyarsa da Bata taba girgizuwa ba,
Dan haka tin ranar da Bilal din Ya rasu Yana bangarensa Nan kaantes Yana fama da Kansa Shima
Sai likitan dake zuwa dubasa kullum ko gurin karban gaisuwar baya iya fitowa.
Ababa Koda ya iso baisha wahalan shigowaba sbd Abbakar dake gate Dan haka Kai tsaye Akai masa iso ciki.
A palon dd babba ya zauna cikin jimami yafara yiwa dd babban gaisuwa kafin yayiwa dad kaante da sauran uncle din Bilal din dake gurin.
Amsa gaisuwar sukai kafin Shima ya zauna cikin yan karban gaisuwar Yana bayyanarda jimaminsa harda Kuka sosai Wanda yasaka dad kaante Ganewa da shine Mahaifin yarinyar da Bilal din su ke tsananin so harya rasa ransa akanta.
Ganin suna cikin jamaa ya Hana dd babba da dad kaante tambayan idan 'yar Ababan ta sauka lafiya ita.
Ababa da Kansa ya bayyanarda Yana son yiwa ummen Bilal gaisuwa babu musawa Abbakar yayi masa jagora zuwan babban palon dad kaante aka shiga aka kirawo ta.
Zata fito DD na shigawa palonta sanye cikin black Balmain jumpsuits kyakyawan fuskarsa fresh a kame kaman baa tabawa da hannu
Duka masu masa gaisuwan Bilal din Daya shigo amsawa yayi a takaice cikin nutsuwa batareda ya tantance su waye da waye ba duk da harda mummyn Sbb amaryasa aciki.
Ganinsa yasaka Umme hadiye hawayenta tana kama hannunsa Daya miqa mata Dan kuwa yanzu shine sanyin idaniyarta.
Tare suka juya zuwa palon dad kaante suna shiga qamshinsa yafara ankarar da Ababa ba haj fatman bace kadai ta shigo Dan haka ya dago idanuwansa daidai tsayuwar DD a palon ya zubawa Ababa idanuwansa a Karo na farko Daya zubawa Wani idanuwansa Yana kallan tsaf.
Kwarjininsa yasa Ababa miqewa tsaye daga zaunen Dayake bakinsa na Tara masa yawun dazai hadiywa maqoshinsa Daya bushe sbd tabbatarda wannan shine DAWOOD KAANTE din da duniya tafi sani akan duka sauran 'yaya da jikokin gidan,Kuma qanin Alh Bilal.
Rawa hannuwansa suka dauka take baisan lokacinda yace
"Nine Mahaifin Benazir,
Yarinyar da Alh Bilal zai aura kafin afkuwan wannan kaddarar ta rashinsa"......
Daga Umme har DD a tare suka sake sauke masa idanuwansu bakin Umme na rawa tace
"Ta haihu?
Me ta..... Bata qarasa ba Ababan ya katseta da cewa
"Ta haihu lafiya ta samu 'ya mace Kuma duk suna lafiya uwar da 'yar."
Daidai Nan dd babba da dad kaante dakeson magana dashi din suka shigo Kuma a kunnesu zancen an haihun ya sauka.
Wani kukan da Umme batasan ko na menene ba ya kunce mata tana Jin bayan babyn a yanzu baby Abinda take buqatan a kawo mata tagani.
Ababa kuwa take ya Yanke shawarar benazir ce uwar yar Kuma babu Mai sanin ba ita din bace matiqar Yana Raye.
*Masu buqatan pages da Akai Nisa sosai suyi following Dina arewabooks at mamuhgee kokuma suyi joining VIP*
09033181070
09032345899
#MAMUH#
#MARRIAGE
#DD
#BENA
#AMNAH
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
39
Dd babba ne ya shigo dad kaante na bayansa suna kallan Ababan a tare sbd Jin Abinda ya fada zuciyoyinsu na karban sakon nasa da sanyi batareda sun ankare ba.
DD kuwa Dan rintse idanuwansa yayi Shima a hankali sakon na sanyaya zuciyarsa duka batareda sun saniba Dan kowa tashin hankali yasa sun manta da akwai jinin da Bilal ya bari duniya,
Sun cire Rai daga samun Abinda zai dawwamar musu da kaunarsa da soyayyar da suka kasa nuna masa sai gashi Allah ya dawo musu da jinin Bilal tsatsonsa.
Daga dd babba har dad kaante suna zaunawa kallan Ababa Dayake star kallansu Daya bayan Daya sukai
Dd babba na sake sauke ajiyar zuciya a Karo na babu adadi sbd Bayajin Dadi sosai tin lokacinda rasuwar Bilal din ta riskesu babu me isashiyar lafiya a gidan.
Ahankali dd babba ya Bude baki yace
"Abinda aka samu din lafiya take itama?"
Gyada Kai Ababa yayi cikin zumudinsa Dayake boyewa Yace
"Lafiyarta kalau daga ita har uwar"
Umme ce ta Bude baki cikin hawaye masu sanyi ta zube gaban dd babba cikin bayyanarda quncin ranta da qanqantar da kai tace
"Babba Dan Allah a kawo min Babyn Bilal ni ta kowace hanyar aka sameta Ina sonta a hakan,
Ina buqatan ta a hakan,
Zan reneta a hakan,Dan Allah kabada Daman a kawo min ita sbd ita kadai ce jinin Bilal dazata maye mana gurbin Daya bar mana....kukane yaci karfin Mai qaramin sauti da cin zuciya.
Dad kaante ma kallan dd babba yayi cikin rashin qwarin gwiwa Dana jikinsa da ba lafiyar Shima yace
"Ta hanyar dawo da ita Nan zamu ingatanta rayuwarta yanda ya dace harma da Hana kowa sanin matsayin nata tinda da Yana Rayen a yanda kayi alqawari ranar sunanta ranar daurawa iyayenta aure."
Shiru dd babba yayi Yana sauraronsu Wanda ko Basu roqa din ba a yanzu da Bilal baya duniyar bazasu banzatar da jininsa Daya qwal Daya bari ba a duniyar sbd jininsu ce Kuma itace a yanzu zata maye gurbinsa a zuciyar mutane da yawa a familyn.
Ababa zufane ya fara tsatsafo masa cikin rigarsa Yana kallan bakin dd babba yaji Abinda zai fada akan roqon iyayen Bilal din.
DD ne ya katse musu zancen Kai tsaye a natse da cewa
"Akwai buqatan Wani tinani ne Daman akan dawowan babyn hannun mu?"
Muna buqatan sai muyi nazari ne akan Hakan?
Kai tsaye daga lokacinda ya fado duniya ita din ta zama kaantes,
Akwai dalilin barinta Wani gurin ne daga lokacin da ta amsa sunan?
Shiru iyayensa sukai sbd shi Daya ne Daman yake fadan maganarsa a tsaye gaban dd babba ba acikin raini ko rashin daa ba Amma shi Sam baya kwana kwanar magana ko inane kuwa yinta yakeyi Kai tsaye ta gaskia da gaskiarsa.
Ababa kuwa Jin ana nanata maganar karban baby dai,baby dai baby dai sai kawai ya Dan gyara Yana kallan DD Da kyakyawan fuskarsa yake a kame duk da idanuwansa sun Dan fada a kwana dayan.
Dd babba cikin sanyi ya Bude baki cikin Yana kallan Ababa yace
"Kaji dai ko malam Ababa?
A kawo mana yarinyar zamu karbeta tinda dai a yanzu mutuwa ta shiga tsakani Allah beyi zamu cimma manufar hada iyayenta aure ba.
Hummmmmnnn" Ababa ya sauke Wani boyayyan numfashi Yana Jin Kansa na daukan zafi Amma dai ya daure yana daidaita Kansa.
Dagowa yayi idanuwansa taf da hawayen da baisan lokacinda ya janyosu take ba.
Cikin rawar muryar sautin kukan Dayake daurewa ya kallesu su dukan yace
"Wace jaririyar zaku karbe?
"Yar dake jikin uwarta zaa rabasu kwana daya da haihuwa?
Anyiwa "ya ta adalcin rabata da 'yartaΒ acikin wannan halin Datake ciki na rasa mijin aurenta?
Tayaya idan tayi aure Nan gaba zata kasa nunawa mijinta tana da wata 'yar a Nan?
Wannan zancen ai bazai binnu a Hakan ba,
Abar mana babyn Nima Ina kaunarta zan rungumi kaddara mu Reneta idan uwarta ta samu Muji zuwa gaba tayi aure taje da ita can sbd bazamu bar 'yar ta tashi babu Uba ba anan ne zaa San Yaya 'yar take Kuma waye ubanta Koda baya Raye,
Idan mutane suka shegantamun jika kokuma shi Wanda uwarta zata aura wataran ya sheganta mini ita nayi muku alqawarin bazan bari ba zan dauki mataki Kuma zan kula sosai da wannan babyn Amma kuyi hakuri bazan iya bari ku qwace mana ita ba a rabata da uwarta bayan wahala da gwagwarmayar da uwarta Tasha daga renon cikin zuwa haihuwarsa.
Yana gama fadan maganganunsa ya musu gaisuwar Bilal tareda sallama ya fuske ya juya Yana share hawayensa alaman iya gaskiarsa yake fada a matsayin Uba Kuma kaka.
A zuciyarsa kuwa qyam yake sbd yasan madokarsu Kuma itace ya doka Dan haka gida zai komawarsa Yana zaune zasu sake nemansa da yardar Allah.
Yana ficewa hawayen Umme suka qara gudu ta miqe tana ganin jiri tabar palon zuciyarta na nauyi.
Dad kaante ma kallan dd babba yayi jikinsa na mutuwa da zantikan Ababa Amma Kuma koma mene Suma suna buqatan 'yar ai a matsayinsu na kakanninta dasuka rasa mahaifinta.
Dd babba kuwa Jin Ababan kawai yayi Dan kuwa maganar komaima Bata tasoba yarinya bazata taba zama a wajen kaantes ba.
DD ma ficewa yayi daga palon sbd a nasa bangaren Shima yasan maganar barin jinin Bilal dinsa a Wani wajen ma har ana lissafin zuwanta agolanci tin yanzu ai baima San Hakan ba.
Babyn tagama dawowa hannunsa saidai uwar babyn ta hakura.
Ababa kuwa Yana fita Zeenah ta fice da driver suna fitowa ta karbi key tace ya jirata a hanya zataje ta dawo.
Bayan Ababa Zeenah tabi tiryan tiryan har gidansa.
Saida ta Dan jima a gurin cikin mota ta tabbatarda gidan ne kafin ta juya motarta tabar gurin.
Driver ta dawo ta dauka suka koma gida Kai tsaye gurin umme ta nufa daki ta sanar mata da ta gano gidan maman Babyn Bilal din.
*****Ababa na Isa gida shigewa yayi ya zauna palonsa ya rufe kofa ya fara warware tinani da abubuwan dake cikin qwaqwalwansa Dan ya huta shi Kansa sbd Kansa ya gama daukan zafi ya dauko maganar da baisan inda zata Kaisa ba tsakanin Ababa da Nobaba.
Amma dai koma yayane a mutu ko ayi Rai babu Wanda ya haifi wannan babyn idanba benazir ba ko duniya ma bazai yarda ta saniba bare kaantes.
Karatunta kuwa daga wannan lokacin babusa Dan kuwa haihuwa tahau kanta,
Su kuwa kaantes ba hawan jini suke fama dashi ba ko saukan jini ne bazai bayarda babyn ba matiqar bada uwar babyn zasu amsa ba.
Benazir da Anne a daki kuwa zaune suke shiru babu komai sai jaririyar dasuke lallabawa kaman Basa son ko motsata sbd so da kulawa.
A yanda rasuwar sumayyah tazo musu da har ita har babyn suka rasu da ba lallai su samu qarfin wannan tawakkalin ba Amma Suma kansu a yanzu sunsan Wani irin dangana ne da Basu taba tinanin zasu iya samu ba Allah ya Sako musu.
A jikin benazir babyn take kowane lokaci sbd ita yanzu so na tamkar itace ta tsuguna ta Haifa babyn takeji Wanda Daman ko sumayyah na Nan tasan zata mata wannan son,yanzu Abinda yasa yafi qarfi da tsanani sbd batada uwa batada Uba sai su kokuma tace sai ita tinda Anne Allah ne kawai yasan yaushe da yaushe ne take daidai bare ta nuna mata soyayyar kaka.
Saidai Abinda Bata saniba ba kaman yanda take Jin yar cikin tsakiyan ranta kaman sumayyah ce a hannunta haka Anne ke Jin 'yar itama cikin ranta kaman sumayyahnta ce ta dawo musu a matsayin jaririya Dan haka kallan 'yar kawai idan tayi sai taji zuciyarta na Neman narkewa ta fashe da kuka shiyasa take Dan dakatar da kanta tana barwa benazir sbd itace uwarta a yanzu da babu sumayyah Dan tanada tabbacin akanta benazir babu sadaukarwar da bazata iyaba a ciki gidan tinda Suma dasuke manyan tana musu tin baya.
Sai yamma Ababa ya fito bayan ya cire kayan dayaje dasu kaantes ya Sako wainda yafi sabawa da sakawa na yadika marasa nauyi su kuwa idan zasu uwar shadda yakesha harda babban Riga sbd nuna mutincin Kansa.
A tsakar gidan ya janyo kujerarsa ta roba ya zauna gefen hande da itama zamanta kenan tsakar gidan kan tabarma ta fito Tasha iska sbd Kuma ta kasa ta tsare Basa buqatan bako kowane iri ne Dan kadama a ankare da halinda suke ciki na haihuwar banza a gidan.
Ita yanzu fatanta tinda sumayyah ta rasu tabarwa su benazir 'yar so take Ababa ya samowa benazir koma waye ya daura mata aure dashi benazir ta tafi da 'yar can su qarata gidan auren a huta kada yarinya ta girma jamaa su rasa inda aka samota idan Kuma auren bazai yiyuba to gwara tin wuri ace Anne ta haihu ta yanda ko yar ta girma babu Wanda zai San shegu suka fara haihuwa a gidan Suma Dan daga wuyan dasukewa mutane ya fadi.
Shi dai Ababa duk tinanin hande nata ne kawai nasa tinanin da burin daban Kuma nasan shine magana tinda shine me Yanke yanda yakeso ayi.
Abinci yayi Kiran Anne ta fito ta kawo masa sbd Bai samu Daman cin abincin Rana ba Yana ciki Saida yagama lissafe.
Ajiye masa abincin tayi zata bar gurin ya Kalli kofar dakinsu yace
"Uwar me benazir takeyi a ciki da 'yar Amanata duk sai zafi da sauro ya cinyeta daki kaman dakin boka tsabar duhu da kaya."
Ahankali Anne ta Dan kallesa kafin ta Bude baki tace
"Idan anfito da ita waje akwai sanyi zai iya kamata"
Ajiye abincin Daya dauka zai fara ci yayi ya Kalli hande data matse fuska yace
"Wai hakane hande?"
A siqe handen tace
"Eh Amma Kuma ai da uwar datayi naqudar 'yar ce zaa ce kada ta fito dakin sanyi zai iya shigarta......
Katseta Ababa yayi Yana dire abincin hannunsa da qarfi yace
"To waye ne yace uwar datai naqudarta ta haifeta Bata gidan.?
Da sauri dukkaninsu suka miqe suna waiwaye hande cikin fargaba da tsoro Anne kuwa cikin mamaki da firgicin itama
Hakama benazir take ta fito dakin rungume da babyn Yana raba idon son ganin sumayyah da Ababa ke maganar.
Kallan benazir data fito yayi yana sake fuska sbd lissafinsa da gabaki Daya yanzune zai hau daidai idan komai ya tabbata yace
"Kunga uwarta Nan wadda tayi cikin tayi naqudar Kuma ta haihu"
Page 40 πππππ
#MAMUH#
#BENA
#DD KAANTE
#KAANTES
#AMNAH KAANTE
#SAFNAH
#LOVE/ROMANCE
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
40
Dakatawa daga dube duben dasukeyi kowanne cikin tashin hankali da firgici suka dawo da kallansu a Kansa gabaki dayansu.
Baki sake hande tace nashiga uku yau ina Shirin ganin baqar Rana,
Ciwon qwaqwalwa ka samu Ababan khairi??
Mutuwar sumayyahn ta taba ka hakane bansaniba?
Benazir ce fa a gabanka,
Gizo sumayyahn ke Yi Maka ne?
Qalu innalillahi.
Anne da benazir kuwa tsayawa sukai cikin mamaki da fargaban maganar hande kodai gizo sumayyahn ke Yi masa sbd wahalan dasuka Sha a hannunsa.
Shiru yayi musu Saida hande tagama tsoki burutsun zancenta ta saurara taba kallansa da mamakin ganin hankalinsa kwance Bai shiga tashin hankali ba.
Tattaro duka nutsuwa da hankalinsa yayi ya fara kallansu Daya bayan Daya yaga su dinma dukkaninsu hankalinsu na akansa.
Akan benazir ya tsaida idanuwansa yafara da cewa
"Ke kina son 'yar hannunki kuwa?"
Shiru sukai hande na sake shiga mamaki hakama Anne dagowa tayi ta Dan kallesa ahankali sbd Jin tambayar abinda bama sai anyi tambayar ba sbd ansan amsar.
Shiru benazir tayi tana kasa ko motsawa bare iya magana Dan kuwa fadanma tana son babyn hannunta kaman ragewa Miya gishiri ne.
Tsuke fuska Ababa yayi Yana fara hasala a siqe yace
"Ba tambaya nayi bane?kuka tsaya mun kaman wasu gumaka."
Ahankali benazir ta gyada Kai batareda ta dago kan ba.
"Bakinki Zaki Bude ki ban amsa kan na tashi na fasa bakin ki a gurin"
Cikin sanyi Kai tsaye ta Bude baki a natse tace
"Eh Ina kaunarta sosai."
Wani zafaffen tsoki ya sake Yana Hana zuciyarsa fusatan da zata sanyashi tashi yayi mata dukan fita hayyaci sbd a ciki 'yayan hudun kaf Bai qaru da komai dasu itace last hope dinsa Kuma itace wadda zata kasance mukullin samunsa Dan haka yake sake tausan zuciyarsa Yana Hana kansa Dora hannu akanta.
Bayason rufa rufa ko batawa Kai lokaci har Wani lissafin ya kunce masa Dan haka ya sake hade fuska sosai yace
"Dukkaninsu ku Bude kunnuwanku da hankalinku harma da nutsuwarku ku saurari Abinda zan fada sbd magana ce da fitarta ko bayyanar gaskiyarta daidai yake da masifar da mutum bazai iya dauka ba.,
Hande ya kalla datake kallansa a matse da son Jin meyake faruwa da Ababan ne yace
"Ki nitsu hande kijini da kyau,
Kema me ciwon qwaqwalwa ki nutsu ki Jini Kuma ki fahimceni dakyau Dan wlh kuna kaucewa magana zan dauki 'yar Nan nakai Tasha na ajiye Wani ya tsinta.
Daga yau benazir itace uwar data Reni cikin wannan yar takuma haifeta.
Anne ce kawai ta Dan kallesa sbd wannan ai maganar dazu ce ya maimaita.
"Idan nace itace ta Rena cikin Kuma ta Haifa Ina nufin babu Wanda zaisan munama da sumayyah anan gidan bare haihuwarta,
Benazir ce kawai 'yata Kuma itace wadda ta Haifawa Bilal kaante 'ya gatanan a hannunta,
Babu Wanda ya Isa yasan gaskiyar maganar Nan har sai ranar Danaso.
Wannan Karan harda benazir cikin masu kallansa Dan ita har lokacin Bata fahimci meye ainihin Abinda yake nufi ba.
Shiru sukai babu Wanda yace "toh" ko Wani abin sbd har lokacin dai ita hande kallan ya tabu take masa Anne kuwa Kai tsaye tasan meyake Shirin aikatawa da wannan maganar tasa.
Benazir ta Maida idanuwanta ahankali ta kalla sbd idan har ta fahimci inda Ababa yake Shirin dosa da zancensa itama lokacin rabuwarsu ne yazo zata tafi ta barta shikenan,
Amma a bangarenta idan har zai cusawa dangin Bilal benazir a matsayin sumayyah su amsheta da 'yarta to zuciyarta zata yarda da wannan shawarar Dari bisa dari sbd benazir taje ta samu rayuwa Mai kyau ta fita daga wannan rayuwar da saidai su mutu a wahala tinda duka 'yayanta sun mutu a wahalar sun barta.
Da wannan tinanin Anne Bata tsaya nazarin komaiba itace ta fara dagowa ahankali tace
"Na amince da Hakan".
Wata dariyar Jin dadi ya sake mara sauti Yana kallan Annen da mamaki yace
"Na buga a daidai notin hankalinki ya dawo kenan?.
Sake dariyar yayi Yana cigaba da cewa
"Kuma yaushe aka baki zabin da kike maganar kin amince?
Magana ce nayi da Wanda ya amince da Wanda Bai amince ba da Wanda ya fahimta da Wanda Bai fahimta ba duka a banza sbd magana ta zaunu babu Wanda ya Isa a cikinku ya dagata,
Ke benazir ki sakawa kanki da qwaqwalwanki kece uwa kece mahaifiyar 'yarki gatanan,
Ni bansan wata sumayyah ba anan gidan bare haihuwarta.
Hande ya kalla Yana cewa
"Hande ko ke kinsani ne?
Kinsan sumayyah a gidan Nan me haihuwa?
Baki sake hande tace
"Sumayyah a Nan gidan Kuma?
Labarin ya shude ai Kuma,
Allah dai ya Daya Miki 'yarki benazir.
Wata dariyar farin ciki ya sake Yana Maida kallansa kan Anne da jikinta gabaki yayi sanyi ya mace yace
"Kin sake fahimtar komai yanzu da kyau ko?."
Ahankali ta gyada Kai tana rintse idanuwanta dake radadin zafin Kuka Amma bayama iya zuwan.
Benazir data fara fahimtar inda aka dosa hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ahankali ta zube qasa tana sake riqe 'yar da kyau idanuwanta na sauyawa zuwa jajir itama tana kasa Kuka ko hawaye sbd tashin hankalin da Bata taba tsammani ba.
"Ki shirya kowane lokaci idan muka gama maganar manya daura Miki aure zanyi a satin Nan sbd bazan yarda a Rena yarinyar Nan ba a