Showing 150001 words to 153000 words out of 183527 words
haka komai tsaf yanda DD din ke bugatan toilet hakama kullum sai anwanke an sake tsaftace komai na toilet din duk da babu me shiga Amma sbd suna jiran farfadowansa kowane lokaci shiyasa koyaushe ake cikin
Shirin duk Abinda zai buqata bayan tashin nasa.
Fitowa yayi da Kansa ya kama DD din Wanda baya iya tafiya haka Suka lallaba ya shiga toilet din dashi yakaisa har bakin bathtub Daya hada ruwan dumi sosai ya kawo masa komai Dazai bugata ya Jere masa harda sabbin towels guda biyu dasu toothpaste da toothbrush na wainda yasan asalin dasu DD ke amfani.
Zare rigar patient din dake jikinsa yayi ahankali tareda sakinta qasa tareda short din Dayake jikinsa ya shige bathtub din ahankali tareda kwantawa Yana rufe idanuwansa.
Shiru yayi cikin ruwan tsawon lokaci seda ya ji jikinsa ya Dan sake sake sbd ruwan zafin dake ratsasa sosai suka sakar masa da jiki tsawon lokaci kafin ya fito cikin ruwan duk acikin sanyi ya dauki brush ya tsaya yayi brush tareda wanke bakinsa da mouth wash kafin ya koma qarqashin shower ya sakarwa Kansa ruwan zafin sai alokacin ya sake sauke ajiyan zuciya.
Yanda ruwan yake sauka jikinsa ahankali ya sakashi ahankali ya fara dawo da tinanin halinda suka samu kansu a ciki kafin shigarsa wannan halin da baisan meya samesa ba har lokacin.,
Bai iya Tino wahalar dayasha ba kafin kasancewa da Bena a yanzu iya nutsuwa da yanayin duniyar da suka kasance a tare yake
Jin feelings din da dumin numfashinsu Daya ringa fita Yana sauka a lokacin harma da
Wani girmamammen lamari Daya risketa aciki
Wanda ya sakasa sallama mata duniyarsa gabaki Daya sune yake tinawa suna dawo masa acikin Kansa,
Bai taba kusantan kowace mace ba Dan haka baisan ya ake nufin Virgin ta kasanceba Amma dai a iya abinda yaji Yakuma tarar Bena din ta sake komawa Virgin bayan haihuwan ne? kokuma bata Haifa Amnah da kanta ba?
Idanma Cs Akai mata to ya akayi Bai taba Jin dinki a Mararta ba sbd yasha shafa Mararta tin kafin su zama Abu daya yanzu din.
Meyake faruwa ne?
Shine baisan komaiba akan wainnan abubuwan kenan kokuwa dai akwai abinda ya kamata y sani dinne Bai saniba?
Wainnan tinanin sune suka cika Kansa kafin na tashin hankalin da mamaki suka biyo baya sbd sai alokacin yake tinanin meya samesa ya shiga halinda ya shiga,
Idan ya Tina daidai mutuwa yaji yakusa yi da mummunan desire da zai kira da dark desire ma sbd a lokacin da Bena batazo ba zai iya afkawa duk macen Daya samu Wanda zai iya kashe Kansa idan Hakan ba a faru bayan ya dawo hayyacinsa sbd tsananin gyanqyaminsa da raayinsa na macen Dayake so ne har cikin zuciyarsa da ruhinsa kawai zai iya kwanciya da ita shiyasa bazai taba iya kwanciya da dayan matarsaba sbd zai cutatar da ita matigar ya kwana da ita babu digon sonta cikin ransa,
Yabarta ne idan yaga bazai iya adalci ba zai sallameta taje da budurcinta ta samu Wanda yake sonta har Zuciya.
Ya jima sosai Yana San jikinsa ya Dan samu karfi kafin ya gama ya fito daureda towel a qugu ya ratayo dayan a wuyansa Yana tafiya ahankali fatarsa ta sake haske sbd kwanciyar dayayi kwana biyu yayi fayau kaman mace me sabon shigan juna Biyu.
Ko Daya fito tini Naseer ya ajiye masa kaya da underwear sabbi na sunspel masu tsada.
Jikinsa ya goge a hankali da sauran rashin kuzarinsa ya gama ya saka underwears din da saka short wando me Dan tsayi kadan da black rugbay shirt sai alokacin yayi salloli
Yana gamawa yayi adduoinsa Yana tashi ko gadonsa Bai qarasaba su dd babba suka shigo dakin kowannensu a tsanake cikin jallabiya
Dan lokacin 7 harta wuce.
Dd babba ne ya fara ware hannu cikin farin ciki me tsananin gaske ya rungumesa tareda Dan bubbuga bayansa Yana kiransa da "my champ"
Shima dad kaante cikin farin cikin ya Dan rungumesa Yana Jin zuciyarsa na sanyi sbd
Daya rasa DD Shima kaman yanda ya rasa
Bilal da shikenan baisan ya rayuwarsa zata kasanceba.
Zeenah data shigo daga baya da gudu ta garaso ta fada jikinsa tareda rungumesa
Shima rungumeta yayi ahankali Yana Dan Jin sassaucin nauyin zuciyarsa dake azabtiwa da rashin ganin wadda yakamata ya fara Gani farko farko.
Hawaye Zeenah ta ringa yi Wanda ya sakasa
Bude bakinsa dole yayi mata magana da
cewan
"Meyesa kike Kuka?
Kin dauka zan mutu ne?
Wa zan barwa 'yata da..
. Shiru yayi tareda
kasa qarasawa Yana dagowa ya Kalli su dad kaante Kai tsaye dd babba ya kalla Yace
"Bata zo bane?
Lafiyanta kalau right??
Zeenah na Jin Hakan ta dakata da hawayenta tana zamewa daga jikinsa tana Satan kallan dd babba dayace kar Wanda ya sanar masa halinda ake ciki.
Dd babba fuskewa yayi cikin basar da zancen da kulawa yace
'tama kasan batajin dadi so tana Nigera sai ta warke sosai zata iya zuwa daga baya kokuma idan mun koma shikenan."
Yanda yayi maganar yasaka DD Kai tsaye
Shima ba Wani shakka ko Wani Abu kunya yace
"Sosai ne batada lafiya??
Nayi forcing kaina sosai ne akanta har haka?
Did I really f... cikin Wani irin Jin nauyi dad kaante ya katsesa da cewa
"Rashin lafiya ne kawai Kuma ta warware inshallah."
Naseer ma Kansa qasa yayi sbd nauyin maganar DD din Wanda Sam shi bai ji Wani komaiba sbd yasan tabbas ya nuna mata qarfi tinda Bai dauka zai sameta a yanda ya sameta din ba,and baitaba dauka haka ake samun
Kai acikin wannan rayuwarba shiyasa ya kasa controlling Kansa Dan haka idan har shine ya sakata a wannan halin Yana bugatan komawa
Nigeria cikin ganganin lokaci sbd yaga yanayin jikin nata kada tanacan tana Jin jiki sosai Bai saniba.
Dd Babba Kuwa bai damuba da zancen dinba sbd yasan shi Dan Kai tsaye Daman musamman ga wadda yake Jin yanxu bazai iya controlling Kansa akan Yanda yakeji a zuciyarsa ba shikuma Daman Hakan shine fatansa.
Yanayin yanda DD yayi shiru ne Kauai ya saka dd babba Dan shiga nazari sbd idan Basu nuna masa taji sauki da gaske ba ba lallai ya zauna anan din dasuke son ya zauna ba har su fara zuwa su samu mafitan nema Bena din da qaske sbd dole zasu masa dubara abarsa
Nan su koma su kadai.
Shima DD din a natse cikin sanyi ya karanci yanayinsu Daya bayan Daya Amma Bai kawo tinanin komai a ransa ba bayan na sosai ya nunawa matarsa qarfin Daya illatata may be.
Kowanne fuskewa yayi suka danne suna sake bayyanarda farin cikin tashinsa Dan haka tini suma yan Nigeria aka sanar dasu suka samu farin cikin farfadowansa Kuma ana sake shiga fargaban bayyanarda maganar batan Bena.
Shi Kansa bai sake nuna damuwa ko Wani yanayi ba gameda maganar Bena din saima ya
Dan ringa daurewa Yana nuna jarumtar qarfin jikin Dayake samu.
Har yamma suna Asibitin anata nuna masa kulawa kaman zasu hadiyesa shi dai Bai Wani sake sosai ba sbd zuciyarsa data kasa samun cikakkiyar nutsuwa,
Hakanan yakejin Sam hankalinsa ba kwantawa zaiyiba matigar ba Bena din yaji ba.
Washe gari ahaka suka sake wuni results dinsa sun fito babu sauran drugs din a jininsa
Amma sun Basu takardar Asibiti data hukuma
Datake bayyanarda bashine yasha da Kansa ba Basa Akai Bada saninsa ba Dan haka hukuman gasar ta Bada takardarta akan idan sun koma gida Nigeria Akai binciken gano komai zasu shiga cikin zancen Wanda zaa kama da qwayoyin.
##MAMUH#
* Arewabooks@Mamuhgee_*
86
Wannan bayanin da Akai tas a gaban DD lokacinda suke office din hukumar Zurich din sai alokacin yasan haqiqanin meyake faruwa,
Wato Wani ne ya saka masa mugayen qwayoyi, to Amma a Ina?
Idan tinaninsa yazo daidai a ranar tinda gari ya waye babu Abinda ya sakawa cikinsa hatta ruwa Bai Sha ba sbd damuwa da bacin ran labarin accident din Bena haka ya tashi ta biyo jirgi baici komaiba harya sauka,
Daga airport office dinta ya fara tsayawa
Kuma anan ma baici komaiba haka ya Isa highbridge baici komaiba Saida yayi ordern abinci Wanda ya Saba cin abincinsu Daman bawai yanzune yafara ci ba,
Bayan wannan abincin baici komaiba a ranar
Kuma tabbas Yana gama cin abincin Nan yasamu Kansa a mawuyacin halin da babu
Abinda yake tinawa sai azabar daya ringa Sha a jininsa Daya ringa quna Yana babbaka, Zuwan Bena shine yabasa Iko da Daman yaqar ciwon da azabar sbd sonta Mai tsananin gaske da baimasan akwaisa a ransa hakanba shine yafi garfin azabarsa ya iya dannewa.
Shiru yayi a bayan motar shida dd babba
Wanda Shima tinanin yakeyi Yana Jin a jikinsa ko menene matar DD din Daya tanada alaga da wannan Lamarin.
Shi kuwa DD tinani ya ringayi tsakanin ordern abincinsa da kawo abincin babu Wanda yazo gidan bayan Safnah sai Bena daga baya.
Bena ta fita Sam a zancen ya cireta sbd Koda ta iso Yana gap da rasa ransa ma gaba Daya
Dan haka koma menene a tsakanin zuwan
Safnah da Wanda ya kawo abincin ne.
Batareda ya juyo ya Kalli dd babba ya Bude baki a natse yace
"'Me binciken da akeyi ya bayar?
Ansan waye ne?
Akwai Wanda zargi ya nuna?
Menene ainihin dalilin Daya Hana Mummyn
Amnah tahowa?
Shiru dd babba yayi tareda sauke numfashi
Shima Bai Kalli DD dinba yace
"Bayan matanka biyu a ranar babu Wanda yaje gidanka,
Su Biyun ne kawai suka shiga a dai time din da ake zargin daga lokacin ne koma menene ya sameka."
Sai alokacin D ya juyo ya Dan Kalli dd babba da idanuwansa dasuka qara haske sosai ya Bude baki Kai tsaye yace
"Kai ne ka Bada Daman a Dorawa BENAZIR alaman tambaya akan wanna maganar kokuwa su masu binciken ne??
Shima dd babba sai alokacin ya juyo ya Kalli
Dawood din da kwariininsa Shima ya cika masa Ido musamman da babu Annuri ko Daya a fuskarsa.
Wani lalataccen murmushi dd babba yayi kafin ya dauke idanuwansa akan DD din yace
"Kanada huija ko shedan fiddata daga zargin kenan?
"Ko menene acikin abincin danaci a ranar ko ruwan danasha suke,
Dan haka a lokacinda aka tafi gidana a in in
Dayake kan dining shine Abu na farko Daya kamata a dauka Dan aunawa."
"Kana tinanin baayi Hakan bane?
Babu abincin da aka Samu ko abinsha a dining ko kitchen koma duka dakunan gidan Dayake nuni da kasha Wani Abu ma kafin shigarka halin daka shiga.
Numfashin takaici DD ya sauke sbd Abinda ya kamata ayi bashi akeyi dinba a nasa ganin Dan haka yace
"Naci abinci a ranar Wanda nakeda tabbacin shine ya bamu wannan matsalan Dan haka zan kira securities na highbridge zasu turo footage na sake dubawa,
Idan har babu komai Dayake nuna naci abinci a gidan har shara idan an duba to tabbas fitar da abincin Akai Dan haka Wanda ya fitar da abincin shi kawai ake bugatan Gani asan inda zaa fara sauran binciken
, "
Wanna maganar tasa ta saka dd babba yin shiru Yana shiga nazari tabbas dole idan yaci abinci to meyasa zaa kawar da komai agi barin ko spoon Dayaci abincin dashi Kuma ko a sharar gidan babu inda aka zubar da komai da alama gidan aka bari dasu kenan gaba Daya.
Ajiyan zuciya ya sauke tareda kallan DD yace karya kira securities da Kansa tinda Bai gama warkewaba ya bari Ashir bello zai nemesu ya sake duba footage din dakyau ya duba Wanda ya fita da Wani Abu Dayake nuni da kayan abincin ne.
Hakan da dd babba yayi shikuma shine ya sake jefa zuciyarsa cikin zargin akwai abinda ba'a son ya sani shiyasa baa San ya shiga zancen bayan shine sosai a cikin zancen.
Shiru kawai yayiwa dd babba din har suka
Isa gidansa aka saukesu su Kuma suka Isa masaukinsu.
Baibu waya a tareda shi sbd bashine ya kawo
Kansa qasar ba kawosa Akai Dan haka da daddare har ya kwanta ya kira Naseer a wayar gidansa yace ya kawo masa waya ko iPad
Yana son magana da Amnah.
Hakan dayace ya saka Naseer fita ba jimawa ya kawo masa tasa iPad din Dan yayi amfani da ita.
A daidai wannan lokacin Amnah na tareda
Nafisat tana gyara mata kanta cikin kulawa
Kiran ya shigo.
Amnah na ganin numbers din na waje ta San daddynta ne da sauri ta tashi daga jikin Nafisat tana murna ta dauki wayar.
Kyakyawar fuskar daddynta ce ta bayyanar mata cikin tsananin farin ciki ta ambaci sunansa tana cewa
"Daddy na ya warke Allah ya karbi addua na danakeyi kullum yehhhh"
Wani sanyi ne ya shiga zuciyarsa ya Dan lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta yace
"Angel din daddy nayi kewanki"
Zaunawa tayi daga tsallan da take tana marairaice fuska tace
"Daddy nayi missing naku kaida mummy kullum bana iya bacci da daddare sbd mummy
Bata Nan,
Nidai Dan Allah ku dawo,kace mummy na ta dawo....hawaye ne suka fara gangaro mata sbd a kwanakin ba garamin kewa da guncin rashin mahaifiyarta takeji ba dagyar take iya bacci kullum haka Nan take Jin wata irin kewan mamanta tana cinta kusan kullum da zazzabin dare take kwana haka Nafisat ke kulawa da ita Sosai kaman jininta.
Shiru yayi tareda zubawa Amnah din idanuwansa dasuka saka yarinyar sake tsinkewa da hawaye tana sake ambatar sunan mummynta jiki a sanyaye.
Wani Abu ya Dan hadiye daga maqoshinsa
Daya tsaya kafin ya Dan diadaita Kansa batareda Abinda yake zuciyarsa ya sauka kan fuskarsa ba cikin nutsuwa da kulawa yace
"Angel,Ina mummynki taje ne??
Dagowa tayi ta kallesa tana sake tsiyayo
hawaye tace
"Mummy ba tana gurinka ba inji su Umme da
dad kaante hakama aunt Z tace mummy tazo
gurinka itama batada lafiya zasu warke ku
dawo tare"
Shiru yayi tsawon mintina yana shigar
da zancen Kansa kafin ya sake kallanta
da idanuwansa da zuwa lokacin sun fara
sauyawa ya sake tausasa murya cikin nutsuwa
yace
"Tinda ta taho gurina Kuma bakiyi waya da ita bane?
Girgiza Kai tayi tana cewa "kullum idan nakirata bana samu Kuma idan nace aunt Z ta bani mummy na muyi magana sai tacemun tana bacci kokuma tana sallah"
Shiru sukai dagashi har Amnah din tsawon mintina kafin ya dago ya kalleta yace ta miga
Nafisat din waya taie ta dauko littafin karatunta na Arabic ta nuna masa.
Migawa Nafisat din iPad din hannunta tayi tareda migewa tabar dakin zuwa dakin mummy dinta da gudu Dan dauko littafinta.
Tana ficewa Bai tsaya komai ba Kai tsaye cikin kamewan murya yace ta fada masa ina Bena take.
Shiru Nafisat tayi gabanta na faduwa hakama tana kasa dagowa ta Kalli wayar sbd tsoro da kwarjininsa.
Cikin Dan daga murya ya qara maimaita tambayar bacin ransa Dayake controlling Yana
Dan bayyanuwa.
Rawa hannuwanta suka Dan fara Yi murya na rawa tace
"Bata Nan"
"Tana Ina??
"Bansaniba,Amma ance wa Amnah tana tareda ku"
Shiru yayi kawai daidai lokacin Amnah ta kawo littafinta ta ringa masa bayani yana sauraranta kawai da amsa mata Amma kwata kwata hankalinsa da nutsuwansa baya Akai.
Yana gama magana da Amnah Kai tsaye
Ummensa ya kira Yana kiranta cikin murna
tahau gaisawa dashi tana Jin Dadin iinsa kaman daga sama taji yace ta Basa Bena yanason magana da ita.
Murmushin qarfin hali tayi tana cewa
"Yanzu ta kwanta bacci sbd ilkin nata Bai
gama warwareba kasan Kuma tana bugatan
samun isashen hutu Dan haka kabari
lokacinda take farke sai a kiraka.
Numfashi kawai ya sake tareda cewa shikenan ya kashe wayar.
Yana kashe wayar saukowa yayi daga
gadonsa ya zira slippers ya fito da keys na
motarsa Daya dake qasar Yana fita ya fada
motar yaja ya fice batareda Naseer da Zeenah
dake gidan ba sunsan futarsa.
Kai tsaye gurin dd babba ya nufa sbd baya bugatan Wani kwana kwana ko boye boye a sanar dashi Abinda yake faruwa bayason kayan ciwon Kai da haukan dasuke Neman manna masa Dan tini Kansa ya fara daukan zafi da nauyi.
Koda ya Isa yasan room numbers nasu Dan haka Kai tsaye na dd babba ya nufa Yana
Isa ya tadda room service zata fito Dan haka dakin Yana Bude ne Kai tsaye ya shige tana taresa ko sauraranta beyiba ya wuce zuwa quryan bedroom din sbd babban daki ne na masu kudin gaske Wanda zakaji kaman kana gidanka ne a sake.
Daidai kofar bedroom din Yana Isa ya sakata cak Jin Abinda dd babban ke magana Akai cikin waya Dayake Yi da Sir Ashir bello babban
Jami'in binciken sirri.
Bayanin Ababa da asalin komai Sir Ashir bello ya buqaci ji komai da komai sbd yanzu binciken ya shigo da mutane cikin zargi da yawa,
Matar Dawood din Safnah da mahaifiyarta na ciki dumu dumu hakama Ababa da ake zargin batan Bena dashi Kuma idan har yanada saka hannu a batan Bena shi to tabbas akwai alaqan batanta da Abinda ya samu DD.
Hakama ta Wani bangaren dole itama Bena din da Naseer zasu shigo binciken sbd Bena kadai ce ta samesa tagansa a halinda ya shiga dalilin gwayoyin.
Ajiyan zuciya dd babba yayi yafara yiwa sir
Ashir bello bayanin komai Daya bayan Daya na asalin rayuwar dasu Bena da mahaifiyarsu suka taso ciki da asalin Rabin kwakwalwan da mahaiflyarsu da sumayyah wadda itace Asalin budurwar Bilal Kuma mahaiflyar Amnah tareda yanda kaddara ta samar da cikin da renansa da yanda Ababa yarinta musu barazana a fakaice cikin dubara har suka aminta da auren sumayyah tazo ta rasu a gun haihuwar yayi canjen sumayyah da Bena tareda boye musu cewan sumayyah Bilal ne yazo ya sace gawarta da haryanzu basusan inda gawar suke ba wand yakeda tabbacin Shima wannan zancen akwai abinda yake boye cikinsa Basu saniba.
Kudin Daya ringa bawa Ababa da yanda yaketa bincike da Neman hanyar karbe mahaifiyar
Bena daga hannunsa duk ya hada ya fadawa sir Ashir bello din Yana dorawa da cewa
"Ina zarginsa da batan Bena kaman yanda nake zargin matar Dawood da saka hannu a kan duka lamarin biyu sbd kishinta hakama
Ina zargin akwai Wanda yasan me suke aikatawa idan ma suna aikawatan sbd yanda duk Abinda muke Gani akwai me bibiyab safnah din.
Idan akwai abinda DD ya taba ji a rayuwarsa
Wanda ya buga zuciyarsa Nan take yaji Yana Neman kamuwa da heart attack to wannan abubuwan Dayake ji ne a yanzu a bakin dd babba Wanda idan a gurin Wani yajisu bazai taba yarda da Hakan na faruwa a duniya ba.
##MAMUH#
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
87
Kansa kasa yarda yayi da Abinda yaji Dan haka ko ganin gabansa bayayi ya juyo yabar dakin ya fito jiri na juya Kansa sosai ya sauko qasa kaman Wanda yake cikin maye haka ya Isa motarsa ya shiga ya zauna zufa na feso masa Tako ina yanajinsa a wata duniyar ta daban,
Kansa ba zafi yakeyi ba wuta yakeci sosai da sosai,
Bena dinsa ce ake fadan ta taso a wannan rayuwar dayakejinta kaman duniyar wasu dabbobin ce ake fada?
Bena dince ta taso tana wankin wasu qattin Maza?
Bena dinsa ce ake maganar da yanzu tana hannun yan drugs?
Bena dinsa ce ake maganar ta taso cikin yunwa da wahala irin wannan da ko karensa bazai iya bari ya Rabi irin wannan wahalar ba bare ace Macen datayi nasarar da Saar shiga inda babu wata mace