Showing 114001 words to 117000 words out of 183527 words
turo mata numbernsa a Karo na farko data taba samun numbernsa bare kiransa a wayanta.
Kira uku tavi Bai daga ba da alama yasan numbern tata Dan haka itama aje wayar tayi tana cire maganar daga ranta.
Gurin dd babba taie tai masa bayanin zancen murmushi kawai yayi yace
"Ki shirya kije ki dubo Annenki kawai karki je aikin bari sai kinsake magana dashi, Bazan masa magana ba kiyi magana
Dashi zuwa gobe ko anjima idan kin dawo daga gurin Annenki ki samesa gidansa na highbridge kuyi magana."
To kawai tace Amma bataso Hakan ba hasalima bazata sake nemansa ba.
Shiryawa tayi itada Amnah da Nafisat dake kulawa da ko saka talkalmin Amnah suka fita.
Shopping sosai suka fara yiwa Anne kafin suka wuce gidan saidai murnarta komawa ciki tayi sbd tararda yau din jikin Annen ya tashi
Sam bata Wani hankalinta sosai ganinsu ne ma ta Dan Yi kaman ta dawo daidai sbd Bena cikin tsakiyan ranta take.
Hande duk Abinda zuka zo dashi karbewa tayi tace sai Ababa ya dawo abasa kafin ya bawa
Annen Abinda zai Bata da Kansa Bena Bata damu ba Dan haka ta zauna ta yankewa Annenta farce dasukai tsayi,
Ta kunce mata Kai ta wanke mata tas tareda taimaka mata da kanta tayi mata wanka tas
Nafisat kuwa dakin ta sakata ta gyara tayiwa
Annen wanki duk da sun siyo mata sabbin kaya Amma duk hande ta karbe sai Ababa ya dawo.
Abincin lafiyayyan dasuka zo dashi Daman sbd Annen suka fara barinsa mota Bena ta saka Nafisat ta dauko hande na ganin babban basket zata amsa Bena tace Mata abincin
Amnah ne Batacin komai sai shi.
Dole hande ta bari sbd duk masifar Ababa ya
Hana a taba Amnah wadda itama ta Dan yinsa sbd Yana sonta.
##MAMUH#
#DBENA
#LOVE
#TOO HOT
* Arewabooks@Mamuhgee.*
65
Pepper soup na qatan catfish ne da Kuma white rice da aka dafa tareda veggies sai sauce na kidney qanana aciki,
A cikin dakin suka zauna Amnah na jikin
Nafisat tana Bata da spoon abaki ahankali ita
Kuma Bena tana bawa Annenta cikin tsananin kulawa da soyayyan mahaifiyarta me tsanani.
Saida ta tabbatarda Annen ta Koshi kafin ta
Bata fruit drink me mara sanyi Tasha tukuna
Nafisat ta tattara kayan ta mayar basket ta
Maida mota.
Har yamma tana gidan tana jiran dawowan
Ababa taso rokonsa yabata Daman kai Annen taga likita Amma har magrib Bai dawoba Dan haka Suka tafi Annenta na kallanta kaman zatai Kuka, Itama Saida tayi hawayen kafin ta iya tafiya tabar Annenta.
Gida suka koma Kai tsaye daki ta shige sbd ranta ya gajule da yanayin Annenta Kuma gashi dd babba Yanata tausanta sbd matigar ba asirin kafin da Ababa yai mata a karya ba ko sace ta Akai kokuma akai dole aka dauketa zata iya ransa ranta sbd Hakan Sai Kuma idan shine da Kansa Ababan yace ta tafi yayi freeing dinta.
Data shige daki bayan tayi sallan magrib kasa rige kukan Datake dannewa tin a gaban Anne tayi ta fasa kukan a hankali tareda cusa kanta cikin qafafunta.
Amnah data shigo ta taddata tana Kukan qarasowa tayi ahankali ta shiga jikinta ta lafeta tareda yin shiru sbd Bata taba ganin Mummyn nata na Kuka ba. Saida Bena tayi kukanta me isanta hardana DD
Daya da Abinda yayi mata da radadin kishinsa
Datake ta dannewa duk sai datai kukansu
Daman suna ranta danqare.
Wata alwalan tayo tareda wanka tazo tayi sallan ishai tana gamawa a daki Nafisat ya kawo mata yoghurt a glass cup Tasha ya isheta ta kwanta tareda cewa batada lafiya
Zazzabi takeji sbd tasan Hakan ne kawai zai saka abarta taji da Abinda yake cin ranta da ruhi.
Daga Zeenah har Umme sin shiga damuwan rashin laflyan nata Amnah kuwa sukuku tayi sbd Daddyn da Mummynta sune walwanta,farin cikinta da rayuwanta.
Da daddare Shima Bai shigoba sbd Bai sauko ba,
Washe gari ma Bai shigoba ya tafiyarsa office.
Safnah gantalinta Bai bari tasan Bena ta dawo ba sai data kwana biyu tukuna sbd kullum
Bata wuni gida idan ta fita sai dare.
Dd babba taje ta gaida harda yimasa girki na musamman
Baya cin girkin kowa yanzu saina Bena Amma
Bai nunawa Safnah din ba ya saka mata albarka tareda godia.
Qin zuwa sashen Umme tayi tinda taji Bena ta dawo Dan haka ta sake haukacewa tareda mayar da hankali ga Jan hankalin mijinta
Wanda haryanzu suke yanda suke.
Bena kuwa cikin kwana biyu ta shiga Wani mummunan halin sanyi da damuwa, Sam ta
Dena zaman Palo sai ta tabbatarda lokacinda bazai shigoba take fitowa ta zauna cikinsu
Umme Zeenah ma aikinta baya barinta zama gida sosai itama Kuma.
Amnah halinda mummynta take ciki itama ya taba ta Sam ta Dena walwala da Hayaniyan yarinta Datake sosai ta sauya.
Shi Kansa a kwanakin gabaki Daya ya sauya baya cikin walwala ko sakewan, koyaushe ransa ba Dadi a hade fuskansa take
Duk sai abin ya sake taba Amnah Takoma kaman iyayenta ba walwalan.
Shine yafara kokarin dawowa daidai sbd
Amnah data fara harda rashin lafiya sbd Bata
Saba da qunci ba batama San Saba.
Duk yanda ya sauya Yana shigowa yanzu kullum Bena Bata taba yarda ya ganta ba gabaki Daya ta kaucewa duk Abinda zai hadasu. Amnah idan zatai vidcall dashi barin dakin takeyi hakama idan har taji alaman Yana bangaren Bata fitowa saiya tafi.
Babban Oarin kame kanta ma harda matarsa
Bata shaawan haduwa da ita Sam bare shi.
A haka suka share kusan sati biyu
Duk lokacinda matarsa akace ta shigo Bata fita sai ta fice hakama Shima duk akace
Yananan Bata fitowa din.
Dd babba idanuwa ya zuba musu hakama umme sbd batasan meke damunsu ba kowannensu Kansa ya dauki zafi,dad kaante kuwa baimasan meyake faruwa ba.
Yau Zeenah bazata office ba hutawa zatayi
Dan haka Suka shirya itada Bena din suka fita outing ko kansu duka zai sake. Sunyi shopping sosai sunci tsadaddiyar abinci a restaurant na kaantes hotels and suites daga Nan sukas shiga VIP saloon and beauty parlor dake cikin kaantes hotels and suites din.
Ba Wani gyara dasuke bugata sbd kusan duk sati zuwa sati biyu saisunzo gyaran Amma tinda sun shigo Basu fitaba saida suka sake shiga Akai musu manicure and pedicure dasu
gyaran Kai da sauransu.
Suna fitowa Bena tace Zeenah ta ajiyeta
gidansu zata duba Annenta
Bayan sun Isa Bata bari Zeenah ta shiga ba tace ta tafi kawai idan ta gama zata kira
Abbakar ya turo driver ya dauketa.
Hakanan Zeenah ta barta ta wuce Amma taso duba Annen itama Amma Bena da dubara ta hanata sbd Bata son a ga Annenta cikin halin Datake ciki.
Yau dinma Bata tadda Ababa ba Dan haka gyara Annenta tayi fes ta sake tsaftace mata dakinta tsakan gidan kaman bola sbd babu me shara sai Anne ta Dan dawo daidai tayi musu shara
Shi girki kuwa yanzu Ababa kusan kullum na
Siya yakeci lafiyayye hande ma wataran na
Siya wataran Anne keyi idan tana daidai, Annen ce kawai kusan yunwa tafara shigowa cikin ciwon nata sbd saisun rage suke Bata.
Ganin Hakan sai Bena ta kawo Mai Aiki gidan ta ringa shara da wanki da girki Amma wahala tasaka me aikin kwana daya tayi ta gudu,
Bayan ita wata ta sake kawowa itama kwananta biyu ta yiwa Ababa Satan da Saida
Bena din tayi masa ranko Kuma ya Yanke babu me aikin da zata Kuma kawo masa gidansa daga lokacin.
Ana gama sallan magrib akazo daukanta ta koma gida.
Wanka tayi ta saka straight pencil Sisley doguwan Riga me laushi data kwanta jikinta gabaki Daya bawai matsewa ba.
Qaraman hula ta saka tareda ziro slippers tana fitowa palon Yana shigowa Shima sanye cikin black Ralphs da slippers na chanel fuskansa fresh Yana fidda Wani kwarjinin da sirrin kyau
Bata dakata ba ta juya kawai zata nufi hanyar kitchen babu tsammani ya riqota sbd ya kasa
Hana kansa barin ta tafi.
Baya ya dawo da ita bayanta ya jingina da kiriinsa gamshinta ya shiga hancinsa take ya rufe Ido Yana son magana ta kwace iikinta a hankali tareda yin gaba ya rigota kenan
Amnah ta shigo palon daga dakin Zeenah tana Ana gama sallan magrib akazo daukanta ta koma gida.
Wanka tayi ta saka straight pencil Sisley doguwan Riga me laushi data kwanta jikinta gabaki Daya bawai matsewa ba.
Qaraman hula ta saka tareda ziro slippers tana fitowa palon Yana shigowa Shima sanye cikin black Ralphs da slippers na chanel fuskansa fresh Yana fidda Wani kwarjinin da sirrin kyau
Bata dakata ba ta juya kawai zata nufi hanyar kitchen babu tsammani ya riqota sbd ya kasa
Hana kansa barin ta tafi.
Baya ya dawo da ita bayanta ya jingina da kiriinsa gamshinta ya shiga hancinsa take ya rufe Ido Yana son magana ta kwace iikinta a hankali tareda yin gaba ya rigota kenan
Amnah ta shigo palon daga dakin Zeenah tana Owacewa Bena ta hau Yi fuskarta ba walwala
Bai ce mata komaiba ya dagata cak zuwa bedroom dinta ya Bude ya shiga tareda tura kofan kafin ya jiyeta tareda jinginar da ita jikin kofan yayi manneta da kirjinsa ahankali.
Idanuwanta dasuka qi kallansa ya kalla tareda
Kai bakinsa kan fatan kunnenta cikin qaramin sautin Daya saka gashin jikinta gabaki Daya migewa yace
"Kukan me kikeyi kullum?"
Dumin numfashin bakinsa ya sauke direct cikin kunnenta tareda maganarsa Dan haka gafafunta sukai Neman saki zatai qasa ya zagayeta da hannunsa Daya tareda matseta da kyau jikinsa Yana lumshe fararen idanuwansa tareda zira Kansa wuyanta ahankali ya Shaqi qamshinta da qarfi.
Da gyar ta iya Bude baki muryanta ba sauti sosai itama ta furta
"Ka sake ni please"
Kansa dake cikin wuyanta yasaka maganarta shiga kunnensa Shima direct tareda dumin numfashinta Dana haka gabaki Daya ta qarasa kunnasa ya dago a kasalance ya Kalli fuskarsa tareda gangarawa da idanuwansa bakinta zuwa wuyanta da Kirjinta da rigar ta kwanta ta lafe.
Kunnenta ya fara sakar kiss me sanyi ahankali kafin ya sakarwa wuyanta tukuna ya dago ahankali ya kama bakinta da nasa wannan
Karan tare suka fara kissing juna cikin sanyi ba da zafi ba.
Baa taba kissing nasa ba sai yau din sbd duk kisses din dasuka taba Yi shine yake kissing nata Bata taba kissing nasa back ba sai yau
Dan haka kissing din na yau yafi kowanne shigarsu da tsimasu.
Ita kanta batasan tafara kissing din nasa ba sbd daga ita har shi sunyi kewan juna sosai batareda sun San Hakan.
Sake matseta yayi jikinsa tareda daukanta suka nufi couch har lokacin bakinsu na hade tini wayarta da hularta suka watsar jikin kofa
Ya zauna tana kan gafafunsa Yana Jin notin
Kansa suna kuncewa Daya bayan Daya,
Rigar jikinta ya Zame Daga sama zuwa ilkinta
Takoma daga ita sai hot red strapless bra data sake gigitasa ya shafo cikinta Yana zuwa kiriinta Yana Jin bazai rige Kansa ba.
Kirjinta ya dawo da Kansa da baki ya fizge bra din Daman Ba hannuwa ne da ita ba bare Wani qarfi sbd bras masu tsada basuda Wani qarfinauyi bare takurawa.
Jikinsa ta shige sbd rabata da bra da yayi shikuma Hakan ya kunce masa last notin
Kansa Daya rake Dan haka ya ringa kissing fatar jikinta Yana cakuda ta.
Bai taba samun Kansa a cikin wannan halin ba shi dayayi rayuwar turai da yanda yakeso bare ita data taso a killace cikin Cage Dan haka cikin zazzafan shauqi suka samu kansu da Wani irin crazy romance Daya kaisu wata rayuwar ta tsakanin so da kaunar juna batareda baki ya furta ba.
Migewa yayi tsaye da ita zai nufi lafiyayyan gadan dakin ta fizgo nutsuwanta tana sauke numfashi ahankali ta Bude idanuwanta dasukai nauyi ta kallesa tareda dakatar dashi tana nuna masa kofan da Akai knocking
Ahankali Wani irin zazzafan numfashi ya sauke me zafi kafin ya iya datakar da Kansa Yana kokarin daidaita Kansa ya saketa
Ta sauka jikinsa ahankali tareda Maida rigarta ta tana kasa kallansa ta nufi Kofa ta dauki wayarta da hulanta dake gurin tana juyowa ya taso ahankali idanuwansa jajir ya fice daga dakin.
Zeenah dake buga dakin sbd Daman tinanin
Yana ciki Dan Amnah tace daddynta na bangaren
Kasa binsa da Kallo tayi sbd ganin yanda ya fita fuskansa a hade.
Shigowa tayi dakin tana kallan Bena data kasa kallanta itama tana kokarin danna wayarta.
Akan bra din Benan dake qasa yashe idanuwanta suka sauka tana ganin Hakan ta Hana murmushinta fita tayi kaman Bata ganiba tafara tambayan Bena Abinda ya kawota Kasa amsata da kyau Bena tayi Zeenah na
ganin Hakan taji haushin kanta dataxo daidai
wannan lokacin da Bena dinta zata samu
Karne Virginity din DD kaante.
Zeenah na fita toilet Bena ya shiga tayi wanka
ta fito tayi sallan ishai da Kai tin dazu Basu
saniba
Daqyar ta iya fitowa cin abinci sbd har lokacin
jikinta a mace yake suna gamawa ta koma
daki ta Kwanta.
Washe gari da sakonsa ta farka na cewa
Takoma Aiki Dan haka cikin murna ta da farin
ciki tayi Shirin office ta fice.
Acan ya wuni gaf da magrib ta dawo sbd tarin aikin data tarar office dinta.
Tana yin parking harabar gidan ta fito mota daidai lokacin Safnah itama motarta ta shigo
tayi parking me aikinta na bayanta ta fito
idanuwanta suka sauka akan Bena data wuce
batareda ta tsaya kallanta.
##MAMUH#
#DBENA
#LOVE
#ROMANCE
#TOO HOT
Arewabooks@Mamuhgee_*
66
Dummmmm kunnuwan Safnah sukai mata jinsu na daukewa ahankali tana Jin maganar
Rabi me aikinta Sama sama dake tambayanta ko lafiyanta kalau.
Bata iya Jin me take fada daidai Saida garamin jiri me juyar da Kai ya dibeta Rabin tayi saurin tareta tana kallanta cikin tsoro da mamakin meya sameta a take.
Idanuwanta dake Neman hada mata hadari hadari ta sake budewa da kyau akan Bena wadda ko mutuwa tayi aka binneta ta kwana kabari aka fitar zata Gane itace wlh,
Benazir 'yar uwarta jininta ce ta Gani takuma tabbatarda ita din ce idanuwanta har Wani rawa rawa sukeyi gurin kallanta harta shige
Take Wani jiri me qarfin gaske ya kuma dibanta gafafunta na kakkarwa ta kasa dagawa da Kanta kaman makauniya Rabi ta kama hannunta zuwa bangarenta.
Suna shiga Palo ta tsaya sbd Bata ganin komai sai duhu duhu ganinta Yana rawa cikin masifa da tashin hankalin da Bata taba saninsa ba a rayuwanta..
Harshenta karyewa yayi tana son tambayar
Rabi wacece wadda suka Gani din Amma batada hali sbd karshenta dake sake karyewa hannuwanta duka na jujjiga ta Ciro wayarta
Bata Gani sosai daqyar ta iya Gane numbern
Momynta ta saka kira sai alokacin ta zamu qarfin halin fizgo magana bakinta da cewa
"'Waye,waye...wadda.muka.gani"
Ko gama rufe baki bataiba da kalaman data kasa hadawan
Rabi cikin tashin hankalin da tsoron meyake
faruwa ta katseta da Bata amsan cewa
"Aunty Bena ce,dayan Matan Sir DD,maman
Amnah 'yar marigayi Sir Bial."
Sankarew Safnah tayi a gurin komai nata na tsayawa cak harda numfashinta da gyar ta iya kemo Kalmar "bana Gane komai me kika fada?"
Cikin tsoro da gara shiga firgici Rabi ta Bude baki ta sake maimaita mata bayanin tana gama maimaitawa
Duhu ne ya rufe idanuwan Safnah gabaki
Daya sai ganinta Rabi tayi ta Yanke jiki ta Fadi a gurin Sume babu inda yake motsi a jikinta
Kuma daidai lokacin Momynta ta daga Kiran
Safnah din Daya shigo wayarta tafara Kiran sunanta sbd Jin ba magana.
hun Kuka Rabi ta sake jikinta na daukan rawan toro itama tafara Kiran sunan Safnah din cikin fargaba da rashin sanin meyake faruwa.
Jin Rabi na Kiran sunan Safnah cikin Kuka da tashin hankali ya saka momyn kashe wayar cikin faduwar gaba da shiga nata firgicin.
Kiran wayar tayi tareda micewa daga zaunen datake palonta ta shige bedroom dinta tareda rufe kofar
Rabi na daga wayar cikin masifa tace
"Ke banasan hauka da jahilci ki nutsu ki fadan meyake faruwa ne?"
Hadiye toro Rabi tayi cikin Dan daidaita kanta tace
"Aunty Safnah ne ta Suma Kuma Bata motsi
Sam harda numfashi ma batayi."
Wani mummunan yawun tashin hankali momy ta sauke tareda Jin itama nata jikin na Neman daukan rawa idan Safnah ta mutu yanzu ai ita Kuma ta shiga uku da sauran bugatoci da burikan da Bata cimmawaba.
Migewa tayi daga zaman datai bakin gado tace
"Akwai Wanda yasan halinda take ciki ne?"
"Ah ah" Rabi ta amsa tana waiwayawa duk da palon a rufe yake.
"Ki Jata ki Kai daki kada DD ya dawo ya sameku a Hakan karki bari kowa ya sani ganinan zuwa yanzun Nan."
Kashe wayar tayi tareda daukan key din motarta da mayafi ko handbag Bata tsaya dauka ba ta fito hajiya Bata sani ba ta fice daga gidan tana Hana kanta daukan duk Wani negative tinani.
Cikin mintina qalilan ta Isa kaantes sbd gudun data zabgo Amma tana shigowa anguwar ta rage gudun kwata kwata a natse ta shigo da motarta har ta iso gate aka Bude mata ta shige tinda ansan mahaifiyar Amaryar Sir DD ce
A natse tayi parking harabar gidan ta farko sbd duk bako baya wucewa da motarsa gate na biyu saidai ya ajeta a na farko masu gidan ne kawai ke wucewa gate na biyu suyi parking motocinsu acan.
Bayan tayi parking hakanan ta tilastawa Kanta nutsuwa da kamun kan dole tana Amsa gaisuwan securities harta shige gate na biyu ta wuce zuwa bangaren dazai kaita bangaren
Safnah.
Tana Isa ko knocking bataiba ta Bude kofar ta shigo Kai tsaye dakin Safnah ta wuce ta taddata har lokacin Bata farfadoba da alama idan baa taimaka mata da gaggawa ba zata iya macewa ma Kila a Hakan.
Ruwa ta fada toilet da kanta ta debo tana fitowa ta zuba mata su tana Kiran sunanta cikin mamakin Abinda yake faruwa da zai sakata shiga wannan halin.
Cikin mummunan hali ta sauke ajiyan zuciya a fizge tareda Bude idanuwanta idanuwanta da sukai jajir take sbd mummunan tashin hankali da masifar datafi mata rayuwar gidan Ababa.
Kasa motsawa tayi tana Neman sake somewa a Karo na biyu momy ta saka hannu biyu tayi mata wata irin jujigawa tana cewa
"Ke kimun bayanin meya faru ne kina Neman sakamun hawan jini da wasi wasi da firgici"
Rabi momyn ta kalla tace ta fice daga dakin ta dawo da kallanta kan Safnah dake magana ita Daya kaman ta zauce a rikice tana sake tsinkewa da lamarin ta sake jijigata ta kira sunan cikin tsawa da babban tsoro tace
"WIh zan taflyata na barki koma wace masifar kika debo ta tsaya kanki."
Kuka Safnah ke nema ta fasa ko Abinda ya danne kirjinta zai fada Amma ta rasa Dan haka ta dago idanuwanta dasukai jajir ta Kalli momy bakinta na rawar fita hayyaci tace "Momy Bena matar D itace Benazir yar uwata, uwa Daya ta haifemu,
Uba Daya ya haifemu,Nono Daya muka
Sha...itace matar Dawood, itace wadda aka fara daura masa aure da ita, itace uwar Amnah yar Bilal dasuka Haifa ba aure.…...Somewa ta sake Yi a Karo na biyu momy da tayi mutuwar zaune itama kusan somewan take Neman Yi Saida Rabi tashigo Jin shiru ta debo ruwa ta zuba musu hankalinta na sake tashi tareda shiga tsoron lamarin Dayake faruwan.
Suna farfadowa sai alokacin Safnah ta Dora hannu Akai zata fasa ihu da kukan balai da masifar Datake ji cikin zuciyarta
Momy da itama duka jikinta rawa yakeyi ta rufe mata baki da hannuwanta biyu tana jijigata