Showing 138001 words to 141000 words out of 183527 words

Chapter 47 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

312

Kasa juyowa tayi ta Kalli momy sbd babu
Abinda idanuwayke Gani sani mutuwar
sameerah da kusan koyaushe take Jin kaman
itada Ababa ne suka kasheta tinda tana Kallo
lokacinda sameerah ta manta tabar dakin
hande Bude Amma tagi fitowa daga inda take
kallanta ta fada mata har Saida sanyi da iska
suka tayarda hande bacci ta cimmata a kofar
gidan da batai nasarar budewaba da wuri.
Masifu da balai da ukubar dasuka taso ciki
suka tayi aciki take tinawa tana Gani ta ko Ina
tini rawar hannuwanta ta qaru har jikinta Yana
dauka zufanta na qaruwa sosai.
Tashi hankalin momy yayi tayi saurin kama
hannuwanta tana Dan jijjjigata tana Kiran
sunanta tace
"Karki yarda ki bari tsoron zuciyarki yayi nasara
akan Abinda muka zo Yi wlh halaka Zaki jefa
mu,

A halake muke ma bari ki sani Dan wlh kowanne lokaci Muna iya zama labari gwara ki nutsu mugani idan Ababan zai samar mana
hanya me bullewa,
Ke ni wlh ko duka sai mu mallaka masa
Abinda muka samu mu fita wannan masifar idan yado daga baya mun dasa sabuwar hanyar dawo da dukiyarmu hannunmu,
Ki nutsu idan Zaki nutsu ba lokacin shiga tsoro
bane da firgici.
Wani busashen yawu Safnah ta hadiye tareda zaran tissue dake motan ta share zufanta a hankali tana kokarin daidaita kanta faduwan gabanta na Neman tsananta tana kokarin
controlling nasa.
Facemask ta Ciro a hankali ta saka tareda qatan glass ta juyo ta Kallo momy
Momyn ma ita ta kalla suka sauke ajlyar zuciya a tare kafin momy ta Bude motar ahankali ta fito daukeda qatuwar handbag dinta dake cike
dam da bundles na kudi har Dana dollar.

Makeken Chanel sunglasses ne a fuskarta ta nufi kofar shiga gidan ta shiga sai data shigo da bakin tsakar gidan tayi sallama ahankali tana kallan gidan.
Hande na dakinta tana Shan redionta Anne ce a tsakar gidan tana wankin kayan shagonsa a natse kanta aqasa.
Bataji sallamar farko ba sbd kunnuwan sun gara tabarbarewa sbd Marika datake Sha da wahala,
Tinda ta gudu dinnan aka dawo da ita azabar rayuwar gidan ta dawo sabuwa FIL batada ranar da zatace tanada sauki gareta.
Saida momy ta sake sallama da qarfi kafin
Anne taji ta dauko ta Kalli momy Wanda take kallanta cikin Dan kokarin sake fuska Dan tasan halaka suka kawo mata idan Ababa yaji
Abinda suka kawo masa.

Cire hannuwa daga wanki Anne tayi tana kallan momy tana kokarin Tina inda ta ganta sbd tabbas tasan fuskar.
Kanta ne ya Dan ringa juyawa tafara Dan girgiza sa tana kallan momy idanuwanta a
waje.
Faduwa gaban momy yayi kada haukar matar
Nan ya tashi tayo cikinta fa batareda tayi
Abinda ya kawotaba.
Momy na ganin Anne tana yowa gurinta ta sake Bude baki da garfi tayi sallama kafin ta rufe baki Anne ta ambaci sunan Sameerah tana kallan momy,
Girgiza Kai tayi tana cibaga da bubbuga kanta tana maimaita sunan Sameerah sameerah sameerah…....tana haka Hande ta fito daidai lokacinda Anne ta girgiza Kai da karfi tace

"ba sameerah ba Safnah ce,
Safnah ce,Safnah.
Momy na Jin Hakan Wani zufa ya Dan yanko mata Hande ta qaraso gurin da sauri tana riqe
Anne cikin tsawa me qarfi zatai magana Anne ta fizgi hannunta tana cewa
"Safnah ce sameerah ba,kece da Safnah.
Hande na ganin Hakan tasan abin ne yake
Neman motsawa cikin daga murya ta hau
Kiran Ababa Dayake dakinsa ya fito fuskarsa a matigar hade ya kallesu kafin ya Kalli baquwar dake tsayen tana daf da juyawa ta bar gidan kada Anne ta Tara musu mutane Yana cewa
"Uban waye yake Kiran sunan Safnah a cikin gidana?"

"Uban waye yake Kiran sunan Safnah a cikin gidana?"
Anne da kanta ke Dan juyawa Yana kokarin dawo mata da Abinda ya faru ranar tasake ambatar sunan Safnah
Ababa ya kalleta Yana Hana kansa fasa bakinta sbd baquwar dake tsaye wadda ko baa fada ba yasan itama daga kaantes take Kila sbd komai na alamar kudi sun nuna a tareda ita.
##MAMUH


79
*****
Momy ce tafara Bude baki ta gaidasa cikin
Dan kamewa sbd ganin kallan Dayake mata,
Sam bayason baqi kowanne suna shigowa gidansa sbd baya San kowa na sakawa rayuwar Dayake gudanarwa cikin gidansa Ido.
Amsa gaisuwanta yayi Yana kallan hande yace tayi ciki da Anne
Fizgarta Anne tayi tana cewa
"Muie ni wannan masifa har Ina da tsufana anbarni da aikin kulawa da mahaukaciya,
'yarki na can cikin daula tana hutawa da 'yarta tabarni da aikin kulan mara da mahaukaciyar uwa ayi magana su miqawa Ababa kudi yace na Dena damunsa da zancen Ina dawainiva da mahaukaciyar.

Daki hande taja Anne suna shigewa momy ta juyo ahankali tareda sauke numfashi me dumi da ajiyan zuciya ta Kalli Ababa suka sake gaisawa Kai tsaye ya tambayeta daga ita ba walwala a fuskarsa.
Numfashi ta sake saukewa tareda Dan gyara tsayuwa ta Bude baki tace
"Magana ce me mahimmanci da girma ta kawoni...
Akan me kenan??"Ababa ya katseta sbd bayasan kwana kwana ko batawa Kai lokaci matiqar ba garkar samunsa bace.
Sake kallansa momy tayi itama Kai tsaye tace "Akan halinda kake ciki muma muke ciki,a taqaice dai akan safnah 'yarka dakaji mahaifiyarta na fada...
Wani mummunan matsiyacin kallai ya dago idanuwansa yayiwa momy sauran annurin fuskarsa na daukewa gaba Daya ya juyo da kyau ya kalleta zaiyi magana ta Bude bakin
Jakarta nuna masa daurin kudaden dollar dake sama kafin na nairas a qasa.
Kudin ya kalla da kyau ya ga Basu kama da fake ba Dan haka ya dauke kallansa akansu ya dawo dashi kan momy suka Kalli juna ta gyada masa Kai alamar zasu iya magana yanzu.
Wani numfashi ya sauke sbd mamakin matar datasan kudi sune Abinda ke karkatasa ga wata lanqwasar,
To Amma idan Safnah data ambata tana nufin safnan data gudu daga gidansa ce tsawon shekaru masu yawa wh wannan kudin bazai fidda ita daga hannunsa ba.

Ta dawo da kanta ne a daidai lokacin da yake
Neman 'ya ko ta sata ce ya migawa yan drugs din Daya ci kudadensu sama da miliyoya
Dan haka babu Abinda zai hanasa hukunta rayuwarta mafi munin hukunci kuwa.
Palonsa suka garasa Yana gaba taba bayansa har cikin palon ya zauna a natse tareda Nuna mata guri ta zauna itama a natse tareda ajiye
Jakarta gefenta.
Numfashi ta sake saukewa a Karo na uku da ajiyan zuciya kafin ta kallesa dakyau ta tattara hankali da tinaninta guri Daya tafara da cewa
"Sunana hai Nuratu matar Alh basheer bulama,.
Kallanta Ababa ya sake Yi da sauri sbd baya mantuwa ga duk Abinda yakeso ko ya tsana ko lissafinsa ya sauka Akai,

Alh basheer bulama shine 'yarsa ta auri DD kaante Rana Daya da Benazir.
Wani tinani ne kawai yafara zuwa Kansa a take kafin ta qarasa bayanin na kishin 'yarsu ya kawosu akan tasa 'yar Amma zai gama Jin Abinda taxo dashi da inda sunan Safnah ya shiga bakinta.
Ci gaba da bayani momy tayi da cewa
"Nice momy din matar Dawood kaante Daya wadda aka daura masa aure da ita Rana Daya da Bena Kuma nice marigiyar 'yarka Safnah data bar gida a baya.
Shiru Ababa yayi Kansa na daukan caji da maganganun data fada din.

Kallanta yayi da kyau Yana Dan gyara zama yace
"Bangane marigiyar 'yata ba Kuma mahaifiyar
Matar Dawood?
Ke menene sunan Taki yar matar Dawood din??
"Safnah basheer bulama" ta fada Kai tsaye.
Ni tawa yar Datake hannunki da wane sunan take amfani yanzu?
"Safnah basheer bulama" ta sake fada Kai tsaye.
Shiru Ababa yayi ahankali ahankali zafin kansa na tashi sbd Jin sabon zancen kaman bana hankali ba, Safnah basheer bulama har so biyu a gida
Daya??
Zare hular Kansa yayi ya ajiye gefe sbd zufan da Kansa ya a Dan fara hadawa ya kalleta yace
"I dan sunan yarki Safnah bulama,tawa ma
Safnah bulama a cikinsu da waye aka daurawa
DD aure da ita??
Sake sauke numfashi momy tayi tareda gyara zama Dan Yi masa gwari gwarin zancen Dalla
Dalla tace
"Safnah 'yarka da ita aka daurawa DD kaante aure,Kuma Nima itace 'yar tawa 'yar Alh basheer bulama.,
Bayan barinta gida nice na tsinceta Kuma nice na bayyanar da ita ga Alh basheer bulama a matsayin 'yar Dana Haifa masa,
Safnah 'yarka itace 'yar basheer bulama..
Shiru Ababa yayi zuwa lokacin zafin kansa sosai yake ci ya Bude baki cikin tsananin mamaki da tiririn Kai yace
"Benazir da Safnah miji Daya suke aure kenan?
Safnan tawa yar itace Kuma ta koma 'yar Alh basheer bulama wadda aketa ikirarin babu
Abinda yakeso Sama da ita,
Auren mi Daya a tsakanin 'yaya biyu to na waye ya haramta acikinsu yanzu??
Momy da Nan takeson Akai tace
"Aurensa da Safnah ya Riga ya haramta sbd
Bena yanzu haka tana Asibiti kwance ita ya fara mayarwa matarsa."

Sai alokacin Ababa ya dago ya Kalli momy
Yana share zufansa sbd tsaka me wuyan da zasu sakasa idan akace na Bena ne zai haramta Dan kuwa shi ita Kai tsaye yake bugata a Kaantes,
Ko sumayyah ta dawo duniya yanzu akace ya zabi wadda zata zauna aciki Bena zai tsaya ta zaunu a ciki sbd itace saarsa.
Kai tsaye momy ya kalla Yace "Ina Safnah?
Girgiza masa Kai tayi tace
Ka nutsu kaji asalin Abinda ya kawoni.
Wani mugun Kallo yayi mata sbd a yanzu
Safnah yake buqatan Gani gabansa kawai yaga inda ta samu zarra da qarfin zuciyan iya barin Wani ya tinkaresa da zancensa bayan tana kusa dasu Ashe.

Zafi zuciyarsa ta dauka sosai sbd gabaki Daya zancen tafasa jininsa yayi duk Wani zafin kansa da zafin zuciyarsa suka taso.
Momy data ga yanda lamarin zai lalace batareda sunyi maganar datazo da ita ba ta fidda wayarta kawai ta Nemo recording din maganar Anne ta kunna masa tareda ajiyewa gabansa muryan Anne na fita cikin kyakyawan sauti tana fadan vanda Ababan yayi komai da yanda ya canja Bena da sumayyah dakuma gaskiyar sumayyah ce ta haifi Amnah da yanda ta fadawa dd babba komai da alqawarin da dd babba yayi make na ganin qarshen
Ababa.
Tsit palon yayi har recording din yagama playing bayan numfashinsa dake fita babu
Abinda yake motsawa a jikin Ababa, Sake kunnawa yayi ya sake saurara,Yana qarewa ya sake kunnawa har so hudu ya tabbatarda muryan Anne ce da kanta take maganar,
daidai Nan Kuma Safnah ta shigo palon Kai tsaye ta kofar waje dake kawoka cikin palon direct.
491 a
1 101
Daqyar take iya daga kowane takunta tana garasowa cikin tsakiyar palon.
Bugawan zuciyarta har ta saman kayanta ake ganinsa sbd tsananin tsoro da firgicin Dayake cikinta,
Tsayawa tayi a inda take gafafuwanta da hannuwanta na rawa ta dame hannuwanta sbd rawarsu ta tsananta.
Bata iya dagowa ta Kalli Ababa sbd Shima Wani horo ne da har abada Kila bazasu iya denawa ba saidai Nan gaba Kila idan ya shiga
cikinsu.
Tinda ta shigo ta tsaya Kallo Daya Ababa yayi mata da idanuwansa dasuka kada sukai jajir lokaci Daya da Wani irin mummunan tashin hankali bagin ciki tafasar jini da zuciya.
2 PA
Sharkaf ya jige da zufan da baimasan meyake akai Dan Adam keda irin wannan ruwan me yawa cikin jikinsa sbd har Wani tsiyaya yakeyi.
A tsawon shekarunsa baa taba Yi masa
Abinda ya jijiga duniyarsa da tinaninsa irin wannanba,
• A tsawon shekarun Nan Ashe kallansa ake tsaf Angama sanin komai gameda shirinsa,
Tarko aka hada masa mummunan da baisaniba Bai zataba saidai kawai yajisa aciki,
Duk wahala da gararin Daya ringa yi Yana kashe Kansa da lissafi da tinanin ya gama samun Abinda yakeso ranar kawai yake jira
Ashe babu ranar zuwan wanna ranar bare ya
Gani.
Lallai Anne ta demo Abinda kanta bazai iya dauka ba,
Benazir ma ta debo Abinda kanta bazai dauki nata ba bare na uwarta.
Safnah datake tsaye ya dago itama ya sake kalla da jajayen idanuwansa ya miqe tsaye ya nufeta
Take rawar hannuwanta tsananta sbd dukkaninsu da uwarsu wIh babu Wanda zai fita Basu he gasa tare ba.
Tsayuwarsa gabanta ya sakata dagowa ahankali tana fidda Wani irin zufa ta kallesa ko gama sauke idanuwanta akansa bataiba ya sauke mata Wani mummunan Marin bayan hannun Daya sakata zubewa qasa gefen bakinta Yana zubarda jini
Qafa ya saka yayi mata mugun Harbin data gangara gefe tana Dafe cikinta hannuwanta na tsananta rawa Kuma har lokacin ta kasa Bude baki tayi ihu ko Kuka, Jajir kawai idanuwanta sukai Wanda yake nuna tabbacin taurin zuciyar Datake dashi da bushewa ya saka qafarsa Daya ya take wuyanta daidai magoshinta tini tafara Shure
Shure tana Neman rasa ranta ga bakinta lokacin ya sake zubarda jini sosai sbd ba qaramin muni Marin Daya saukar mata yayi ba.
Momy dataga masifar rashin Imani Dayake
Neman daidai da nata koma fin nata sbd su a tsorace cikin rawar jiki suke komai Ababa kuwa hankalinsa kwance yake Neman kasheta har lahira babu toro ko rawar iiki a tareda shi.
Da sauri tazo gabansa tana kokarin cire
Safnah daga garqashin kafafunsa tana rokan ya saketa zata mutu.
Bai saurara Saida ya Bude baki yace

"Idan ma ta mutu ke kinada bagin ciki ne?
Tafi kowa sanin waye ni Amma har ta lya dawowa bayan ta gudu daga gareni tazo ta tsaya gabana Kuna tinanin na amsheta hannu biyu ne?
Somewa Safnah tai sai alokacin ya dauke kafarsa daga wuyanta zuciyarsa na tafasa da tsananin zafi da jininsa dake quna ya nufi cikin gida Kai tsaye dakin Anne ya nufa hande na ganin wucewarsa ta fito daga dakinta tana tambayar lafiya.
Yana shiga dakin wuyanta ya fara shagowa Bai tsaya komaiba ya janyota kaman ba mutum ba ya fito da ita har cikin palonsa ya jefar da ita gasa sai alokacin idanuwanta suka Bude cikin wahala ta Kalli gabanta tayi arba da fuskar Safnah kwance a some itama bakinta na zubar da jini.

Rufe idanuwa Anne tayi jikinta mace ta Bude ahankali ta sake dubawa dakyau taga Safnah dinta ce,
Wani nauyi zuciyarta yayi sbd idan har lafiyanta kalau ba cikin hali ne na hauka take ba idanuwanta ke nuna mata Safnah to tabbas
'yarta ce take Gani gabanta.
Kokarin tashi tayi Dan sake Gani dakyau
Amma Ababa ya shaqota tareda fizgo wayar momy ya kunna make a maganarta taji.
Tinda tafara sauraran recording din ta fahimci itace Kuma shikenan Ababa yasan Abinda komai zai iva lalacewa Bena dinta.
Duk Abinda ya shafi Bena a yanzu kaman rayuwarta yake Dan haka jikinta ya dauki rawa idanuwanta suka fara sauyawa zuwa ia sbd
Abinda ya taso daga zuciyarta na tsananin fargaba da tashin hankali.
#MAMUH#

80

Rawa bakin Anne keyi kaman yanda duka jikinta ya dauki rawa ta Bude baki zatayi magana ya dauketa lafiyayyan Marin bayan hannun daya sakar mata habo itama a take.
Bata damu da jinin dake zubo mata ba ta sake dagowa zatai magana ya shagota cikin Kansa dake Neman juyewa sbd bagin ciki da masifar dake cin jininsa da Kansa.
Hande data shigo tana sake ihun tambayar lafiya kan Safnah idanuwanta suka fara sauka ta tsaya ta duba dakyau dakyau ta tabbatarda
Safnah ce sbd kamannin Basu sauyaba duk da girma da sauyin rayuwar data samu.
Bata bi takan Anne dake Neman mutuwa hannun Ababa ba tayi kan Safnah da momy ke Neman ruwan zuba mata ta farfado a rikice take cewa "Waye wannan kamar baqar 'yar can Safnah data tsallake uwarta ta gudu ta fada duniya."
Ababa kuwa baimasan me hande ke fada ba
Jin yake baqin cikinsa na ninkin ninkuwa akan
Anne da duka Abinda ta Haifa masa babu
Abinda suka qaresa dashi sai baqin ciki da asara kan asara.
Wato ita yanxu Nan acikin hauka harta samu
Daman ganin dd babba tafada masa komai bayan algawarin dayayi na hallaka duk Wanda ya fitarda zancen Nan har Abada,
Wato shi wahalar banza ma yakeyi ya sharewa
Bena guri ya samar mata gun shiga da zama a
Kaantes qarshensa kawai suke Jira.
Tabbas da Badan Anne dake hannunsa ba da tini sun Dade da aikasa inda Bai taba tinaniba. Wane babban balai da masifar ne wannan?
Sannan yanzu wannan shedaniyar da sabuwar uwarta suna Karanto masa zancen miji Daya
Bena da safnan ke aure kenan dai a daidai Nan kowa alalensa ta kwabe masa,
Idan har tasa Alalan ta kwabe to wlh ta kowama kwabewa zatayi ta Hakan zai samu tasa mafitar fita da wannan zagayen da Akai masa sbd a yanzu kam zagaye yake baida tudin tsira.
Sakin Anne yayi tareda jefar da ita gefe ta zube tana kasa sakin ko tarin azaba sbd wahala ko fita bayayi.
Magana hande ta hau Yi tana tsinewa Safnah da gudunta da dawowanta Wanda yake sake qular da zuciyar Ababa ya kasa rige Kansa ya hada da Annen da Safnah yayi musu shegen duka Yana fatan ace Bena na gurin ya hada da ita Dan kuwa a yanzu dukkaninsu babu me amfani a gurinsa rayuwarsu da mutuwarsu duka Daya ce a gunsa Amma ko ta halin yayane sai ya samar da amfanin garshe daga gurinsu kafin gamawa da rayuwarsu.
Momy tin Datake Bata taba shiga mamaki da tsoron ganin me aikata barna irin haka babu ko shakka bare tsoro a tareda shi kaman
Ababa ba,
Su tsautsayi ne ma ya sakasu kisa Amma sun
- kasa samun kwanciyar hankali tin ranar har yau din Amma ga Ababa Yana taka wuyan mutane kaman dabbobi ko ajikinsa idanma zasu mutu rufesu zaiyi babu Wanda zai sani
Kuma yaci gaba da rayuwarsa hankali kwance.
Hande ce ta janyo Anne da kanta ya juye ta fito da ita tsakar gidan ta wucewarta dakinta,
Itama momy jiki na rawa da tashin hankali da toro ta fito da Safnah tsakar gidan ta debo ruwa daga Anne har Safnah din ta ringa zubawa a tare kowannensu na sauke ajiyan zuciya suna motsawa ahankali.

Tana ganin sun farfado tayi kan Safnah dake tashi zaune ahankali tana kasa iya juyowa ta
Kalli mahaifiyarta dake Jin jiki sbd bazata iya hada Ido da itaba.
Anne da Bata hankalinta batama tsaya kallan su Safnah din ba ta tashi zaune tana Sosa bakinta Daya fashe ta nufi dakinta Dayake a hargitse kaman na mahaukaciya ta shigewarta tana shiga ta zauna tana qanqame jikinta sunan Bena kawai take kira.
Safnah kuwa momy kamata tayi hande na zaginsu da tambayar gidan ubanwa ita
Safnah zata koma Kuma?Amma ko kallanta momy bataiba sbd Jin takeyi kaman ta fasa kan shegiyar tsohuwar da garamar pistol din
Jakarta.
A bayan mota ta saka Safnah dake Jin Wani radadin zuciya da zafi,
Ko radadin jikinta bataji saina zuciyarta dake tafasa,
Wih bazata ci wannan dukan a banza ba batareda sun samu Abinda takeso ba,
Idan har ta rasa DD to sai Bena ta rasa DD itama.
Koda suka Isa gida ko dressing din ciwonta gin bari tayi a kira likita yayi mata zafi sosai zuciyarta ke mata tanajin qunci.
Momy kuwa Jin tayi lamarin Ababa ya Bata toro sbd wannan ko su zai iya kashewa akan zafin zuciyarsa da nasa buqatan.
Har dare yayi zuciyar Safnah Bata Dena radadi ba gashi tanason zuwa Asibiti gurin DD Amma ba Daman zuwa sbd raunikan dukan Ababa da zaa fahimci duka ne take bare tace accident.
Dan haka dole karya tayiwa Umme cewan batada lafiya sosai itama a kwance take sai gobe zata sake dawowa Asibitin.

****Familyn kaantes kuwa duk inda hankalinsu yake ya tashi suna cikin mummunan tsaka me wuya da tashin hankali da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login