Showing 135001 words to 138000 words out of 183527 words

Chapter 46 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

356

Gane taqamaimai me take nufi sbd rashin yarda da Abinda kunnuwan nasu ke ji musu. Meya hada DD da qwayoyin drugs Kuma?
Bai taba muamalantar su ba rayuwarsa,
Sam shi gyangyamin irin wainnan abubuwan ma yakeyi sbd lafiyarsa,
Yaii ma kaman zai kashesa yake masa bare qwaya,ta na wannan zancen ya fito?
Dd babba Daya kasa yarda ko fahimtar Dr
Ashley din sosai ya Dan gyara zama ya kalleta yace
"Yanzu dai baa tabbatar ba tinani kukeyi right??
Yes Sir" ta fada a natse tana fatan suka tinaninsu kada ya zama gaskia.
Gyada Kai yayi a natse yace

"A bari ya farfado zamuji meya samesa da sauran abubuwan da maganar gwajin ya biyo daga baya."
Gyada Kai tayi itama tana sake Basu tabbacin inshallah zai farfado lafiya for now dal.
Juyawa tayi tayi sauka zuwa office dinta su
Kuma suka kwasa zuwa dakin DD din Zeenah da dd babba Kuma Bena suka nufi dakinta.
Sosai ta wahala Dan haka fuskarta tayi fayau kaman wadda ta wuni a ciwo bacci yakeyi na wahala da azaba ga zazzabin gaske a jikinta
Daya dauki dumi sosai.
Shiru sukai kowa da Abinda yake ransa yana tinani.

Zeenah kasa Dora zancen cikin Kansa a takeyi wai Bena Bata taba sanin kowane namili ba sai yau,
To ya Akai ta samu cikin Amnah har ta haifeta?
Bangaren su umme ma tinanin suka shiga da damuwa duk da kaf acikinsu babu Wanda ya kama maganar wai qwayoyin maye a jikin DD sod sunsan ba Abu me yiyuwa bane Dan haka
Basu damu da wannan ba sai fatan su farfado kawai su samu lafiya daga shi har Bena din wadda itama Umme tinani ne kala kala cikin kanta game da cewan Bena Bata taba sanin kowane namiji ba sai yau da DD ya sameta a macenta.
To meye Hakan yake nuft?
Idan ana fada musu wannan zancen kenan so ake a fada musu ba Bena ce ta Haifa Amnah ba kokuwa?
Duka kowa Tara tambayoyinsa yayi cikin zuciyarsa da Kansa ya danne har asamu lafiyar su Bena din a koma gida aji gaskiyar kowa daga bakinsa, dashi da ake cewan akwai maye a jininsa da ita da akace budurwace bayan babu wadda zata taba sanin namiii har ta haihu komai shekarun da zatayi Bata sake kwanciva da Wani namiiinba bazata taba hadewa ba kaman budurwar da Bata taba sanin namijinba kwata kwata.
##MAMUH
#DBENA
#LOVE
#ROMANCE
#ABABA

* _Arewabooks@Mamuhgee_*
77
Koda gari ya waye labarin kwanciyar DD kaante da Bena Asibiti ya yadu a family din kaantes na kusa Dana nesa Dan haka wainda suke kusa tini suka fara zuwa dubasa.
Dd babba Yana komawa gida ya saka Abbakar a Hana labarin fita ko kadan sbd tinda Doctors suka fara maganar zargin qwaya a jininsa yan labarai suna ji zasu yada labarin mutincinsu da sunansu zai tabu hakama Shima DD din nasa mutincin da sunan zai iya lalacewa a idan mutane da Manyan gasa abokan huldarsa Dan haka a Hana ko kalma Daya fita ta cewan ma
Yana Asibitin kwance ba lafiya.
****Safnah da momy Suma kwanan zaune sukai a dare babu Wanda bacci ya gifta idanuwansa,
A zaune qyam suka kwana |do Bude cikin taraddadi,tashin hankali da zaquwa suka Kai har safe suja jiran ta inda labari zai dawo musu.
Babu Allah a cikin ransu suna zaune Akai sallar Asuba aka gama Basu tashi sunyi ba Safnah idanuwanta sunyi Wani jajir da kumbura sbd kukan baqin ciki da zuciyarta
Datake Jin ta qarasa bushewa Dan kuwa wallahi bazata yarda tayi biyu babu ba a yanzu da suka Kai wannan matsayin na Bena ta Riga halasta ga DD kaante.
Sai da gari yayi Shar har karfe 8 Saura basuji
Wani bayani ba suka tashi sukai sallah
Suna gamawa ko addua Basu tsaya Yi ba suka mige Safnah tafara kaida kawo hannuwanta na rawa zuciyarta na qara konewa da bushewa tareda daukan zafi tana rasa ta inda zasuji meyake faruwa.

Momy kuwa babban tashin hankalinta da zafin da kanta ya dauka har Wani hayaqi takeji kaman Yana fitowa kunnuwanta na Abinda zai iya biyowa baya idan su Bena Basu mutu ba.
Komai ya taru ya lalace musu a mummunan yanayi da hanya mara bullewa matiqar su
Bena suka rayu,.
Qarshensu ne zaizo a wulagance su rasa komai su qare inda basason garewan sbd komai a fili zai iya bayyana,
Na farko rashin mutuwar su na nufin zaa gano akwai qwayoyin drugs a jinin DD harma da cocaine suka hada duk suka zuba masa Dan haka akwai babbar matsala idan ya rayu,
Na biyu ma Bena idan ta rayu Hakan na nufin dole Safnah zata bar DD Wanda barinsa shine zai Tona ya bayyanarda ita din ba 'yar bulama bace haka zalika mutuwar hajiyarsa zata iya dawowa sabuwa ga Rabi tasan sirrinsu suna bugatan itama aikata inda bazata zata tafi da sirrin a cikinta har abada ba dawowa.
(100
Dan haka rayuwar su Bena itace qarshen tasu rayuwar.
Wani mummunan zufa ta share tareda kallan
Safnah wadda itama momyn ta Kallo tinani da momyn takeyi shi takeyi sak.
Babu Wanda ya iya cewa komai sbd babu me nutsuwa ko hankalin furta kowace kalma saisun ji labarin halin da ake ciki.
Har kusan goma na safe ba labari Dan haka
Safnah data kasa zama tana tsaye Tim asubar ta dauki wayarta ta saka Kiran umme Kai tsaye zuciyarta na harbawa kaman zata fado. Momy na Jin ta saka kira ta sa a speaker tayi tsit ko numfashi batason ja sbd fargaban
Abinda zasu jl.
Sai da wayar ta kusa yankewa Umme ta dauka tareda sallama a natse cikin sanyi.
Wani busashen yawu Safnah ta hadiye tareda
Bude baki tana Dan dedeta muryanta dake kokarin yankewa tace
"Ina kwana Umme?
Ya gida yasu Zeenah?
"Lafiya kalau Safnah,ya gidan ya momynki?
Lafiya kalau Umme,Daman Umme nace D kunyi magana dashi kuwa?

Wayoyinsa duka Basa zuwa na kira Naseer
Shima tasa a kashe banajin nutsuwan zuciyata game da rashin samunsa Umme.
Numfashi me dumi Umme ta sauke sbd sai alokacin ta Tina ma Safnah ma nada haqgi akansa Daya kamata tasan meya samesa Dan haka ta Dan sake yin sanyi a natse tace
"Safnah wIh hankula ne suka dauku sbd tashin hankalin da aka shiga na Abinda ya samesa shiyasa aka Manta shaf baa nemeki an sanar dake ba,
Yana Asibiti Tim tsakar dare jiya shi da Bena
Basu da lafiya arziki sukai wuta ta so kama gidansa dake highbridge Kuma ba.
Umme Bata garasa ba Safnah ta Yanke jiki ta zube qasa idanuwanta na juyewa.

Momy ma zubewa qasan tayi tana Neman somewa Amma tayi qarfin halin daukan wayar da Safnah ta saki ta Dora a kunnenta muryarta na yankewa da qyar ta iya cewa
"Shock ya saka Safnah sumewa itama gatanan zuwa zata kawota Asibiti"
Ko amsata Umme bataiba ta kashe wayar tareda migewa tana Gani dishi dishi sbd tsabar tashin hankali ta nufi dakinta a rikice ta janyo drowan gefen gadonta ta Ciro wata allurar jininta Data ke Jin kaman ya Haye zuwa 200+ take tayi wa kanta tana zubewa qasa tana fidda numfashi da sauri sauri Dan dawowa daidai.
Kusan fiyeda Rabin awa ta dauka kafin ta dawo daidai ta tashi jikinta na fizga da tashin hankali da baqin ciki ta nufi Palo Kai tsaye kitchen ta nufa ta dauko ruw ta zubawa
Safnah wadda koyaushe ta some kaman wadda ta mutu take.

Safnah na farfadowa momy ta kalla itama momyn ita take kalla tana cewa
Tashi mu fara kokarin hada kan Abinda muka samu dole mu bace bat mubar qasar gaba
Daya wIh bazanje prison ba.
Cikin bagin ciki da rasa abin fada Safnah tace
"dan munie prison mun samu sassauci da sauki kenan,
Kin manta momy kisa fa mukal,
Hajiya fa muka kashe,
Kina tinanin Dad zai gyale mu ne?
Su kaantes kina ganin zasu bari ko prison din akaimu?
Wih kashemu zaayi kisan wulaqanci Kuma,
Bazan yarda naje prison ba yanzu bare lahira lokacina baiyib,
Muna guduwa ba wahalar bincike zaa Gane mune mukai komai muka gudu Dan haka wIh Neman mu bazai musu wuya ba.
Idan Bena sungi mutuwa to dole Bena tabarsa bari na har abada ta Hakan ne asalina zai rufu
Kuma ta Hakan ne DD da kaantes bazasu taba samun nutsuwar yin bincike sosaiba a komai zasu mayarda hankali gurin Nemanta da tinanin inda ta bace bat babuta ba labarinta har abada haka zalika DD dole nice zanci gaba da zama matarsa.
Jajayen idanuwan momy ta zubawa Safnah tana juya zancen cikin kanta to Amma ta
Yava zasu batar da Bena tinda shegiyar taqi mutuwa a Karo na biyu.
"Kasheta zamu sake Vi" inii Safnah da idanuwanta suka gama rufewa fiyeda kowane lokaci sbd yanzu sun Kai karshen karshe na idan suka rasa wannan Karan to sai lahira ko prison.
Katseta momy tayi cikin zurfafa nata tinanin tace "Bazamu kasheta ba sbd munyi na farko babu nasara,
Munyi na biyu ba nasara
munayin na ukun Nan to tabbas babu shakka kamamu zaayi a saukake.
Shiru Safnah tayi sbd kota yayane dai dole sai sun samowa kansu mafita kafin DD ya farfado duk da Kila zai iya kwana biyu Bai dawo daidaiba kuma zaiya farfadowa kowane lokacin Dan haka Basu da lokacin batawa har mummunan kaddararsu tazo ta samesu suna
zaune.
Tinani suka fada cikin tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya da gangar jiki kansu kaman zasu kama da wuta sbd tension.
Safnah ce tinanin da Abinda taketa gujewa yaketa dawo mata cikin Kai Wanda ko sunan ta fada cikin kanta bugawa kan yake Neman Yi sbd tsoro da firgici me tsananin gaske hakama zuciyarta sunansa kawai Neman tsayawa bugawa takeyi Dan duk yanda takai ta goge a duk Wani aikin rashin Imani har gobe Ababa tsoronsa da shakkarsa a cikin jininta yake ba ita kadaiba dukkaninsu yayansa.,
Ababa sunansa kadai jikinta rawa yake dauka idan ta Tino Amma Kuma tana ganin lokaci yayi da zata Kai Kanta gabansa,
'Idan har zai iya sauya sumayyah data mutu da Benazir ya boye mutuwarta ya bayyanarda benazir matsayin wadda tayi cikin shege ta haihuwa duk akan kudi gashi kudin kaantes dinma dayake Jira ba samu zaiyiba sbd Anne data lalata masa komai Bai saniba tarko sukai masa da zai Kamasa a lokacinda baida gurin tsira.
Dan haka lokaci yayi dazai San Abinda su
Anne sukai masa,
Yasan babu Abinda zai same daga kaantes,
Zasu basa kudin da ko Basuyi yawan Wanda zai samu a Kaantes ba ta xasu kusa sbd ya hade a cikinsu ya tsaya tsam ya Hana bayyanar Safnah 'yarsa ce kota halin Yaya.
Momy shiru tayi lokacin da tagama sauraran
Safnah da wanna sabon plan din nata da tabbas ko ita da batasan Ababan ba tana Jin tsigan jikinta tashi a duk lokacinda Safnah take fadar halayensa da taurin zuciyarsa cikin tsoro da kyarma.
Idan har yanda Safnah ke fadan Ababa Tim baya haka yake to shigowarsa cikinsu komai zai tafi musu a daidai sbd da alama zaifi su sanin hanyoyin kawowa Kansu nasara,idan ma dukiyar Bulama yakeson a raba daidai dashi bayan sun kammala qwashe komai zasu raba din matiqar xai fiddasu a cikin motsalan dasuke ciki dumu dumu,
Haka zalika shine kadai yakeda mukullin juya rayuwar Bena a duk yanda yaso sbd Annenta
Datake hannunsa wadda zata iya Koma akanta,haka zalika su Kuma kaantes yanzu
Bena ce mukullin dazai iya juya raywarsu da ita sbd tsananin son Dasuke mata hardai yanzu da zasusan ba itace ta haifi Amnah ba.
Momy da lamarin da tsarin sukai mata shegen
Dadi ta saki Wani dariyar samun sanyin zuciya tace
"Idan ba Bai yarda ya dawo cikinmu an samar da mafita ba to Shima watan tonuwar nasa asirin ne ya tsayu,
Daga lokacinda kaantes suka gama sanin ba
Bena ce ta haifi Amnah ba to alokacin zaayi tariyar zancen yanda yayi ha'incin sauyawa
Amnah mahaifiya Yakuma rusa rayuwar
Bena,haka zalika jinin sameerah a hannunsa yake Dan haka daki day zaa Bamu a prison.
Cikin zurfafa tinani da 'dacin zuciya Safnah
tace

"Ababa babu Abinda bazai iyaba akan kudi,
Jin Abinda su Anne da Bena sukai masa zaisa ko bamu buqaci Basa kudi ya fiddamu a wannan halinba zai iya kashe mana Bena har lahira cikin sauki.
Amma a yanzu banason Bena ta mutu sbd
Anne,
Amma dole zata bar rayuwarmu data DD har abada.
##MAMUH#
#ABABA
#SAFNAH
#MOMY
#SHEGU/MATSIYATA

78

Guraren 11 Bena ta farfado ahankali jiki duk babu qwari hakama dumi ne a jikinta sosai.
Umme da Zeenah harma da Siyam da mum
Khadija ta Gani a dakin Dan haka ta fahimci a inda take wato Asibiti.
Abinda ya faru da rayuwarta a wanni kusan goma Sha Wani Abu da suka wuce ya sakata
Jin kanta na juyawa tareda jikinta dake sake daukan dumi na zazzabi da gabobin jikinta dake ciwo har okacin.
Mayar da idanuwanta tayi ta rufe ahankali tareda Jin hawaye masu dumi sun gangaro gefen idanuwanta Wanda Hakan ya saka su
Umme sanii ta farka Dan haka cikeda kulawa
Umme da Zeenah data taso suka fara Yi mata sanni kafin su mum Khadija Suma daga baya sukai mata suna tambayarta jikin nata.

Bata iya magana ba bare amsawa sbd kunya
da ciwon da jikinta keyi tareda azabar Dan
stitches dinta dake mata zafi sosai ya sata ko
kasa dagowa ta kallesu.
Ganin Hakan ya saka Umme kallan mum
Khadija tace bari su koma daga qaramin
Sitting room na dakin na nan Asibitin su Bata
Daman wanka da Dan gasa ilkinta ko zata sake.
Harda Siyam suka fice Zeenah kawai aka bari
ta taimaka mata tashi zaune jikinta zafi sosai.
Bayan tashinta zaune kasa daurewa tayi duk
da yanayin Datake tanason jin waye ya kawota
Asibiti sbd idan Bata manta ba Shima D baida
lafiya kafin tarayyarsu Duk da dai ya nuna
mata alamar lafiyarsa Kalau da wanna abin
dayayi mata.

Har zata tambayi Zeenah din sai Kuma ta kasa sbd harda itama yau kuniyarta takeji sbd
Bata saniba ko sunsan Abinda yayi sanadin zuwanta Asibitin.
Ahankali take tafiya jiri na Dan Neman dibarta dole Zeenah ta sake kamata ta Rakata har cikin toilet din ta hada mata ruwan zafi Dan gasa jikinta ya warware da kyau dakuma shiga cikin ruwan.
Fitowa Zeenah tayi ta barota cikin toilet din tareda janyo mata kofa.
Ruwan zafin da lallaba ta shiga tana rintse idanuwanta sbd radadin azaba da Kuma in datakeyi kaman kanta zai fashe sbd ciwo.
Shiga ruwan ta daure tayi tareda rufe idanuwanta tana kokarin Tina abubuwan dasuka farun Amma ita kanta da kanta kunyar tinawa takeyi Dan haka ta tattara tinanin ta danne a zuciyarta ta samu tayi wanka ta gasa ilkinta da kyau ta Dan ji jikin ya saki ta fito, babu kowa a dakin sai Zeenah wadda ta ajiye mata kayan da aka kawo mata daga gida kan gado tareda undies da body mist kawai me tsadan gaske.
Pant da halfvest data kama mata kirji ba sosai ba ta saka kawai sai doquwan free rigan
English material me tsada da rashin hayaniva ta saka tareda garamin hula sai alokacin tasamu sauke sallar Datake kanta da rashin sanin inda kanta yake yasa bataiba.
Tana idarwa tea kawai Zeenah ta hada mata lokacin su Umme suka dawo su Mum Khadiia zasu mata sallama su wuce.
Ya jiki suka sake mata kafin sukai sallama sika tafi. Daqyar take iya Shan tea din sbd cikinta dake matse batasan Shan komai ga Kuma zazzabin
Datake ji har Time din.
Bayan tea dagyar Umme ta sakata dole cin pepper soup din Naman rago daya dahu sosai yayi mugun laushi.
Tana gamawa ba jimawa ta amayar dashi tas
Wani sabon zazzabin na sake tsananta gareta.
Likita aka kirawo tayi mata wata allurar tareda daura mata ruwan da baa daura ba tin farko.
Rufeta Zeenah tayi cikin sanyin jiki da tausayawa suna murnar ta farfado sauki zaizo
Kuma sai gashi ta sake birkicewa
Umme ma zuwa yamma hankalinsu va tsananta tashi sbd dai har lokacin DD Bai farfado ba,
Suma likitocin Basu dauka zai Kai wannan lokacin Bai farfado ba Dan haka Suka hau dubaru da duba Abinda zaisa ya farfadon.
Can gida ma daga dd babba har dad kaante da sauran family hankalinsu ya fara tashi sbd rashin tashin DD din.
Haka aka hanye wunin tass aka kwana a tsaye babu alaman zai tashi tini Umme da Zeenah suka Sha Wani irin Kuka idanuwansu sukai luhu luhu sbd Kuka,
Shi Kansa dd babba ba garamin tsoro zuciyarta ta riska ba da wannan Lamarin dake
Shirin faruwa dasu,
Me Hakan ke nufi?
Daman ana samun haka ne daga kwanciyar aure? Bena dake fama da kanta boye mata Akai baa fada mata halinda ake ciki da DD din ba ita
Kuma ciwo da kunya ya hanata iya tambayar
Yana Ina.
Safnah tin Rana ta iso Asibitin itama Tasha kukan rashin tashin mijinta har sai dare Umme ta sakata tafiya gida dole sbd dd babba yace babu me kwana da DD din idan ba Naseer ba.
**Bayan komawar Safnah gida da daddare kasa zaune tayi ta kasa tsaye tana cikin toro da firgici tareda bugawan zuciya akan haduwar da zasuyi da Ababa washe gari,
A duk lokacinda ta Tina da goben zata tsaya gaban Wanda tasan baya yafiya sai taji toro na Neman gigitata,
Jin takeyi kaman zai mayar da ita kajin gidansa ya rufe,
Badan Abinda suke so din ba a ynzu shine last mafita da hope dinsu da har abada babu Abinda zai maidata ko hanyar gidan bare iya tsayuwa a gabansa da sunan magana.
Firgitata ma lamarin ke Yi duk bayan tinani.
Momy data ga irin mummunan tashin hankali da tsoron me tsanani Datake shiga akan tinawa kawai da Wanda zasu gurinsa ta ringa
Bata qwarin gwiwa akan cewa yanzu babu
Abinda Ababa zai iva Yi mata sbd ba Safnar baya bace baiwarsa Kuma dabbarsa,
A yanzu ita Safnah bulama ce, tana kudin da zata hanasa zaman lafiya da kwanciyar hankali idan taso Dan haka babu Abinda zai lyayi mata a yanzu.
Shiru kawai Safnah tayi tanason dilmiya a maganganun momy Amma zuciyarta na sake tsayar da ita waye Ababa,duk kudin da zasuyi tsoran takunsa kawai ma a cikin jininsu yake da bazasu taba iya gogewa. Amma dai Abu biyu ne a yanzu a rayuwarta,inma ta dake ta tinkaresa ta Siya yancin kanta daga garesa tareda bayyanar masa da bugatansu,
Inma Kuma su zauna Jira sunaji suna Gani su gama yawo qarshensu yazo, Dan haka ta zabarwa kanta tinkarar Ababa su fuskanci juna,
Zata fara Sivan 'yancinta daga garesa kafin gabatar da komai.
Washe gari a matse dukkaninsu suka kwana suka tashi sbd rashin sukuni da fargaban ko
DD ya farka,
Matigar ya farka Basu samu mafitaba to fa sunansu matattu tinda komai ma bincika zaa fara Yi a gano.

Momy tafi Safnah matsuwar su hadu da
Ababa sbd tarin Abinda take hangowa Safnah
Bata hangosu matiqar Ba siyi gaggawan ganin
Ababa ta yanda idan Bai amince musu ba sunada sauran time na harhada abubuwansu su gudu.
Safnah kuwa har lokacin zuciyarta cike take da tsoro da fargaban mahaifinta.
Karfe goma daidai lafiyayyar motar Safnah tayi parking kofar gidan Ababa Wanda hannuwanta gabaki Daya rawa sukeyi sosai hakama zuciyarta Neman Faso kirjinta takeyi.
Kallanta momy ta juyo tayi a hankali tareda tsayar da idanuwanta kan Dan siririn zufan
Daya tsiyayo mata daga goshinta ya gangara zuwa wuyanta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login