Showing 144001 words to 147000 words out of 183527 words

Chapter 49 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

331

uku cif sukai kafin Bena ta fara motsawa a hankali tana kokarin Bude idanuwanta ga kanta kaman zai fashe sbd nauyi da tsananin ciwo.

Sosai ta Bude idanuwanta suka Bude daidai ta tashi daga jikin Anne tana kallan Annen taga lafiyarta kalau ta mayar da kallanta cikin tsananin bugawan zuciya kirjinta har amsa sauti yakeyi sbd mummunan tsoro da firgicin Daya cika zuciyarta.

Tsoron leqa fuskarsa takeyi ta kalla sbd takasa yarda da Abinda idanuwanta ke ganar mata.


"Ya...yaa BILAL".....Ta furta cikin yayyankewan kalamai da tsoron Dayake Neman juya kanta da cikinta Daya kulle waje Daya take ta sake zubewa jikin Anne ta sume a Karo na biyu sbd Tama rasa Gane inane take tsakanin duniya da lahira.

Bai tsayaba sake waiwayowa yayi ya kalleta Yana ci gaba da tuqi sbd komin dare Abuja yakeson Isa a ranar.

Zuwa wannan lokacin Anne hankalinta Neman sake juyewa yakeyi sbd ganin Bena na mutuwa tana tashi ahakan itama bacci ya dauketa abinka da Wanda ba cikakke.

Tafiyar awanni ce ta wuni Daya ta kaisu Abuja sai Daya gansa cikin garin Abuja dasu ya sauke numfashi tararda ajiyan zuciya me qarfin gaske kafin ya tinkari anguwar Daya sauka bayan dawowarsa Nigeria kwana uku dasuka wuce.

Wani gida ne me kyan gaske da tsari sosai irin ginin turawa me kyau sosai Amma ba mahaukacin girma sosai.

4 bedroom apartment ne Dayake cikin estate Amma still kowa da gate dinsa da harabar ajiye motacinsa kaman biyu haka.

Parking yayi ya sake sauke ajiyan zuciya tareda hamdala da adduar isowansa lafiya dasu Annen.

Bude kofan baya yayi daidai lokacin Anne ta farka itama Bena lokacin ta sake Bude idanuwanta ta kallesa idanuwanta na Neman sake shiga mummunan hali yayi saurin Kiran sunanta tareda matsawa baya Dan taga tsayinsa da kyau shi din ba fatalwa bane
Shine a Raye gabanta.

Tana ganin Hakan jikinta ya dauki mummunan rawa zuciyarta na kokarin Faso kirjinta idanuwanta na sake rinewa zuwa jajir ta fito motar rawar qafafunta na qaruwa bakinta cikeda tsoro da fargaba tareda tashin hankalin amsar tambayar Datake bakinta tana son furtawa tsoron amsar na Neman gigita kwakwalwanta.

Bude bakin tayi tana sake damqe hannuwanta dake kakkarwa tana kallansa ta furta

"Ina....su..mayyahhnmu?
Itama...tana..ray.....

Maganarta Bata gama fitowa ba aka Bude kofar qayataccen palon sumayyah ta fito da gudu wata 'yar dattijuwa na bayanta da sauri tana Kiran sunanta,
Bata tsaya koina ba sai jikin Bilal din ta maqalqalesa tana dariyar farin cikin ganinsa kyakyawan fuskarta na Wani irin sheqin Hutu da zallan farin cikin asalin kyakyawar rayuwa.

Rungumeta yayi da kyau jikinsa Yana juyowa zai Kalli benazir da Anne sai yaga babu ko dayansu
Da sauri ya Maida kallansa qasa sai kawai yagansu a qasan duka sume.

Cikin sauri da tashin hankali ya Kalli dattijuwar data biyo sumayyah yace

"Momyn Abdul riqeta Jata ki mayar da ita ciki kada tashiga tsoro ko firgici zanji dasu idan sun samu kansu sai akawota ta gansu."

Gyada Kai momyn Abdul tayi tareda kamo hannun sumayyah zata Jata sumayyahn ta maqalesa tana girgiza Kai alaman bazataje ba.

Shaf fuskarta yayi tareda hura mata iska a fuska ahankali take ta lumshe idanuwanta ta sake sa momyn Abdul ta kama ta sukai ciki batareda tama lura da Wainda ke gurinba tinda ba cikakkiyar lafiyar hankali ne da itaba.

Suna shigewa ya su kuya ya fara daukan Bena yakai ciki kafin ya dawo momyn Abdul ta dauko masa Anne wadda batada jiki ko Wani nauyi da zaa rasa iya daukanta.

Kai tsaye daya daga cikin dakunansu dake gidan suka nufa dasu suka Kwantar ita Bena Yana ajeta tana farkawa a gigice ta tashi zaune jikinta na sake daukan rawa da fizga ta sauko gadon tana kallansa hawayen na bushe mata Basa iya fitowa da rawan baki ta sake maimaita ambatan sunan sumayyah tana rarraba idanuwanta inda zata ganta.

Ganin halinda take ciki bayan an sanar dashi batada lafiya sosai Daman can ya sakashi saka momyn Abdul rirriqeta Yana kokarin Kwantar mata da hankali suyi magana a tsanaken Amma Sam ta fita hayyacinta Neman zaucewa tayi sbd ayau mummunan ranar baqin cikin rayuwarta,
Ta Gane miji Daya suke aure itada sister dinta tsawon shekaru da Basu ganta ba har sun cire Rai daga rayuwarta tini, a ayau din ma an rabota da Zuciya da ruhinta Amnah da dadynta sannan ta fito babu Abinda idanuwanta ke Gani sai matattun da suka Fi shekaru da rasuwa,.Tayaya hankalinta zai dauki wannan lamarin duka a lokaci Daya Rana daya.

Sosai jikinta ke jijjiga tana girgiza Kai tareda rintse idanuwanta gam tana qin budewa sbd kanta bazai dauka ba zafi qwaqwalwanta keyi, zaucewa takejin tana Neman Yi.

Ganin mummunan halin data shiga ya sakashi sakinta yabarwa momyn Abdul ita ta riqe da kyau yaje har bedroom dinsa inda ya wuce sumayyah a palonsa zaune tana kallan cartoon harya wuce ya fito Bata dago ta kallesaba sbd idan tana kallan cartoon babu Abinda take sake iya kalla sai an kashe tv din.

Yana fitowa dakin da Bena din take ya nufa da sauri cikin alluran Sumayyah ne da itama duk ranarda ta dawo hayyacinta haka take rikice musu da tambaya da son komawa gurin Bena da Annensu taka zata fara jijjiga tana Neman mace masa sai yayi mata allurar take kwantawa duk jikinta ya sake tayi bacci tana tashi shikenan zata tashi kalau Saidai lafiyarta dataqi dawowa daidai duk yawan Da yayi da ita na qasashe a tsawon shekarun ya kasa samun cikakkiyar lafiyarta ta dawo lafiyayyar sumayyahnta ta baya.

Yana Isa yayiwa Bena alluran wadda take bana cutatarwa bane take jikinta ya saki tayi sanyi ta silale a kan gadon a hankali take bacci ya dauketa.

Ajiyar zuciya dukkaninsu suka sauke shi da momyn Abdul.

Mayar da kallansa yayi kan Anne da itama Sam ko matso jikinta bayayi yace momyn Abdul ta tsaftace ta zai kira likita yanzu yazo ya dubata ita.

Ficewa yayi daga dakin Yana sake sauke ajiyan zuciya sai alokacin ya samu Kansa ya wuce dakinsa Kai tsaye yanajin gajiya ma tana Dan taso masa sbd tsawon rayuwarsa a jirgi yake yawo Bai iya Tina wen last yayi tuqi me tsayi irin wannan din sbd ko yau din Daya Isa jirgi ya hau ya Isa can sai Kuma gashi ya juyo baiyi Shirin juyowa a yau din ba sbd abubuwa da dama dasuka kawosa.

Yana shigowa sumayyah dake Kallo har lokacin ya kalla ya qarasa gurinta tareda sauke ajiyan zuciya ahankali ya rankwafo yayi kissing forehead nata ahankali,.dagowa tayi tareda Dan juyowa ta kallesa ta saki murmushi me kyau Daya sake qarawa fuskarta kyau Shima murmushin ya sakar mata ya Dora bakinsa kan lips nata Suma yayi kissing ahankali kafin ya miqe ya juya ya nufi bedroom dinsa yanajin koyaushe son sumayyahnsa sabo yake koma a ransa fatansa dai Allah ya Bata lafiya suji Dadi kaman kowanne ma'aurata da suke rayuwa duk da ahakan ma son juna sukeyi sosai,shi kadai ne Wanda ta sani matsayin uwa,Uba,miji,Dan uwa,aboki hakama masoyi.

Sam Bata yarda Yana barinta sai daqyar da dubara yake fita kullum tinda suka samu kansu a rayuwar kwanciyar hankali ta iya su Biyun yake kulawa da ita sbd tinda ta farfado bayan tsawon lokacin data dauka a coma,
Ta jima sosai kusan shekara a coma kafin Allah yasa zata tashi ta tashi saidai ba acikin hankali isasheba haka suke rayuwar har yanzu dasuka dawo Nan din.

Yana shiga bedroom wanka ya fara tubewa yayi da ruwan dumi kafin ya fito ya goge jikinsa da towel jikinsa ya Dan sake sosai daga gajiya Dan haka Yana shiryawa cikin qananun designers kaya marasa nauyi ya fito palonsa yayi sallah tareda sumayyah wadda bataiba,
Magrib da ishai da baisamu Yi ba kan time yayi suna idarwa yayi adduoinsa sumayyah nayin duk Abinda yayi tana murmushi sai da suka gama ya janyota jikinsa tareda zare mata hijabin sallanta ahankali Yana kallan fuskarta itama shi take kalla tana murmushi tace

"Kaima kana Jin yunwa ko?
Ni dai inason zanci abinci da yawa."

Ajiyan zuciya ya sauke tareda Jan hancinta ahankali Yana shafan fuskarta dake sake kashesa da sonta kullum yayi kissing gefen fuskarta ahankali cikin nutsuwa da sanyin sauti yace

"Zaki ci abinci?
Me kikeso momyn Abdul ta kawo Miki?
Kin Tina sunan Bena da Anne???

Shiru tayi Jin sunayen a cikin kunnuwanta sun Bata Wani sautin Daya Isa harga zuciyarta ta dago ta kallesa tana lafewa jikinsa batareda ta iya cewa komaiba.

Shima shiru yayi kafin ya dagota daga jikinsa suna miqewa tsaye ya kama hannunta cikin nasa suka fito main sitting room na gidan ya nufi dining da ita suka zauna.

Sai alokacin jikinta da yayi sanyi ya hau murna ganin Abinda takeso ne duka su snacks sai pasta wadda takewa cin shedana har ta Koya masa matiqar zasuci spaghetti to Rabin cin duk lalata ne.

Cin abincin suka hau Yi sai a lokacin Dr din Daya kira yace masa ya iso.

Momyn Abdul ce ta shigo dashi tai masa jagora har dakin da Anne take kwance kan gado bayan ta Dan gyarata.

Dubata sosai likitan yayi ya tabbatarda zuciyarta da komai nata Yana Aiki kawai dai shock be dayayi mata yawa ya sakata Suma.

Ruwa ya daura mata Dan taimakawa saurin farfadowanta kafin yabar maganin da zaa sakawa raunikan jikinta Daya Gani wainda na mummunan dukan da Ababa yayi mata ne na bankwana.

Bayan tafiyarsa daga Anne har Bena kowanne na daki daban daban gyara musu kwanciya momyn Abdul tayi ta rufe kowanne kafin ta jawo musu dakunan ta fito ta nufi nata sbd dare da yayi sosai.

Sumayyah da Bilal kuwa tini suka wuce dakinsa Wanda yake nasu su Biyun sai Daya taimaka mata gurin wanka Dan Daman shine kullum yake taimaka mata da wanka sbd Bata iya Yi da kanta jiqo jikinta takeyi har kanta da kayan jikinta shiyasa tinda sukai auren tsawon shekarun shine yake mata wanka da komai sai idan zai fita Aiki momyn Abdul ta kula da ita wadda itama Momyn Abdul din sun Dade sosai tareda ita sulaiman ne Mai napep dinsa yakai masa ita qanwar mahaifiyarsa ce Kuma mahaifiyar Nafisat Nanny din Amnah anintacciyar me aikin Bena.
##MAMUH#




*_Arewabooks@Mamuhgee_*
83
Kwanciyarsu sukai hankalinsa na kwanciya da dawowan su Bena rayuwarsa da sumayyah sbd idan har yanda wasu likitocin suka fada ne dawowar wainda ta rasa rayuwarta zai iya dawo mata da hankalinta daidai cikin qanqanin lokaci koma lokaci Daya yasaka yake Jin damuwarsu da quncinsa na rashin lafiyarta tsawon lokacin Dan haka a yanzu kam yakejin lokacin warkewar matarsa yayi.

Gyara mata kwanciya yayi a jikinsa kafin ya miqa hannu ya kashe musu wutan dakin Yana lumshe idanuwansa tareda kokarin Tina gwarwarmayar daya Sha a baya daga lokacinda ya bar gida.


Babu wanda ya farka a cikinsu kaf wainda sike gidan sai da safiya tayi sosai,

Bena ce tafara farkawa ta Bude idanuwanta dasukai mata nauyi sosai tana Jin kanta na Dan juyawa ta dafa ta tashi zaune daga kwancen datake tana kallan inda take.

Lumshe idanuwanta da sukai nauyi da ja tayi tana kokarin motsawa ta sauko Amma jikinta gabaki Daya ya mutu batajin karfinsa ko kadan kaman wadda akaiwa duka ko Wani allura.

Qafafunta ta zira qasa ta saukar tareda kokarin miqewa tsaye ta daddafa bango ta Isa bakin kofar dakin ta Bude ahankali ta fito tana tafiya kanta da Dan juyawa.

Motsin dataji a hanyar dining ta nufa batareda tasan inane take nufar ba.

Sumayyah ce da momyn Abdul ke zubawa ruwan tea Dan baa barin tana hada tea da kanta sbd ruwan zafin kada ya mata illa dokan Bilal ne.

Sumayyah dataji motsi tahowa itama dago kanta tayi ta Kalli hanyar idanuwanta a Bude hakama fuskarta dauke da murmushi da farin ciki duk tinanin Bilal ne ya fito.

A cikin idanuwan junansu idon kowaccensu ya sauka,

Cak Bena ta tsaya rawan qafafunta na qaruwa kaman yanda bugun zuciyarta ya tsaya cak wannan lokacin.

Sumayyah kuwa kafe idanuwanta tayi kan Bena tana Dafe kirjinta ahankali dataji Yana harbawa kadan kadan yana qaruwa.

Bena na ganin Hakan take ta fahimci halinda sumayyah take ciki sbd a duniya ita kadaice tafi kowa Gane lafiyan sumayyah da Anne hakama rashin lafiyansu.

Wasu zazzafan hawaye ne da tinda masifun rayuwarta suka fara saukan mata jiya Bata samu ko digon hawaye sun zo mata ba sbd radadin masifun sai wannan Karan dataji suna gangarowa daga idanuwanta tana rasa Gane wane yanayi ne a cikin zuciyarta,
Zallan farin ciki ne ko tsoro da fargaba ne¿

Takowa ta ringa yi ahankali tana nufo sumayyahn wadda hawayen Bena suka sauya buguwan zuciyarta kwata kwata sbd tini kanta ya fara juyawa fuskar Bena na dawo mata cikin Kai da hawaye kala kala da kukansu na baya.

Benazir na qarasowa Bata tsaya komaiba ta rungume sumayyahn data miqe itama tana kallan Bena har lokacin kanta na juyawa sosai.

Cikin tsananin Kukan Daya tarwatsa zuciyarta me qunci da tsima Rai ta ambaci sunan sumayyahn Wanda yayi daidai da fitowan Anne itama daga dakin tana dafa bango ahankali ganin inda take da Neman Bena.

Ganinsu ya sakata tsayawa cak itama tareda tsirawa fuskar sumayyah idanuwanta tana tinanin kenan jiya a hankalinta da gaske taga sumayyah,
Ta dauka cikin haukarta ne taga sumayyahn na mata gizo kaman yanda taga Safnah tai mata gizo shekaran jiya da jiya a gidan Ababa.

Sumayyah Datake rawan jiki sosai tana Neman rikicewa da runguman da Bena tayi mata tana ambatan sunanta suna hada Ido da Anne ta qarasa rikicewa gabaki Daya tafara jijjjiga tana kafe idanuwanta akan Anne benazir na Jin Hakan itama nata jikin ya hau rawa, Anne data farka cikin hayyacinta itama kansu tayo tana Taya Bena taro sumayyahn jikinta sbd zubewan Datake Neman yi.

Fitowan Bilal ya ga Abinda yake faruwa da sauri ya qaraso tareda daukan sumayyah wadda ta zube jikinsu kaman ba Rai jikinta idanuwanta a rufe koina jikinta na rawa sosai.

Kai tsaye dakin dake kusa Wanda Anne ta kwana ciki ya nufa da ita ya Kwantar sai alokacin ya lura da yanda jikinta ke rawa sosai da sauri ya fara girgiza ta Yana Kiran sunanta da karfi Yana cewa ta Bude idanuwanta.

Momyn Abdul dataga halinda sumayyahn take cikin damuwa da tashin hankali ta kallesa tace yayi mata alluranta mana.

Girgiza Kai yayi Yana kallan Bena da Anne da Suma suke cikin girmamammen tashin hankali da tsoron Abinda yake faruwa yace bazai mata ba yau tinda wainda take shiga wannan halin sbd su yau din suna tareda ita Yana fatan qarshen wahalansu ne yazo yau din.

Benazir ce ta hawo gadan itama ta kamo fuskan sumayyahn tana Kiran sunanta da qarfi muryanta na rawa,
Anne gabaki Daya ta kasa yarda da duniyar dasuka tsinci kansu a yanzu,
Shin duniya suke kokuwa lahira suka hade dasu sumayyahn,
Ita dai a halin yanxu data ganta tareda yaranta biyu a gabanta ko lahirar ne batada damuwa bare baqin ciki Dan kuwa rayuwarsu ta duniya sai dai suce Allah ya Basu ladan Ibadan daukan qaddarorin da sukaita Yi.

Bilal da duka zuciyarsa da kirjinsa suke tsalle Yana kallansu Yana jira da fatan daga yau idan ta gansu kada hankalinta ya sake juyewa ya tsaya daidai Dan bazai sake mata allura ba inshallah ahaka yakeson ta samu sauki da ganinsu.

Anne ma hannu takai ahankali ta dafa sumayyahn tareda Jin hawaye sun gangaro daga idanuwanta na farin ciki da tausayin kansu batasan lokacinda ta zube jikin sumayyahn ba ta rungumeta da qarfi ta qanqameta tareda fashewa da kuka me sauti tana Jin tsananin so da kaunar 'yarta na dawo mata sabo fil sbd sun cire Rai daga rayuwarta tintini.

Kukan Anne ya saka sumayyah bude jajayen idanuwanta da suka sauya take ta Kalli Anne hawayen nason ciko idanuwanta Wanda ya saka Bilal Jin zuciyarsa na Neman bugawa sbd fargaba da matsuwan son ganin reaction nata sbd tsawon shekarun Bata taba Kuka ba bare hawaye Wanda Hakan ke nuni da Bata hankalin nata Amma yau ganin hawayenta na Neman sakasa Kuka Kai tsaye.

Momyn Abdul ma ganin hawaye idanuwan sumayyah ya sakata fashewa da kuka kawai tana kallan Bilal Wanda hawayensa ke gab da gangarowa.

Benazir ma datake Gane sumayyah ta dawo daidai tin Abaya idan taga hawaye a fuskarta ne tana ganin hawayen ta batasan lokacinda itama ta fashe da kuka ba Wanda ya saka sumayyah fashewa da kuka take itama tana kallansu har lokacin Bata gama dawowa daidaiba Amma tabbas Bena da Annenta ko da can ko a halin ciwonta Bata mantasu Bata Dena sonsu Bata Dena jinsu tsakiyan ranta.

Fashewan kukan sumayyah ya saka Bilal fashewa da kuka mara sauti Wanda ya saka momyn Abdul zuwa gurinsa ta dafasa tana Dan bubbugasa alaman rarrashi da taya murnar farin cikin wannan Rana me dinbin tarihi a rayuwarsa sbd soyayyan sumayyah a ransa Wani Abu ne da momyn Abdul Bata taba Gani ba, mutumin dazai iya baro gida,iyaye da danginsa da gata da daulansu ya zo ya Gina tasa rayuwar daban sbd kawai kulawa da macen dayakeso Kuma duk shekarun Nan a cikin rashin cikakken hankalinta.

Duk Wanda ke dakin Kuka yakeyi tsawon lokaci kowa baya iya magana suna kukan rage baqin ciki da quncin rayukansu na baya tareda farin cikin rayuwar dazasu sake ginawa a tare yanzu.

Sumayyahn ce tafara shiru daga kukanta jikinta na Neman sakewa sai alokacin suka saketa suna kallan Bilal Wanda ya fita ya dauko mata Wani magani da sauri ya dawo ya saka mata bakinta tareda zuba mata ruwa daqyar ya samu ta hadiye maganin ta silale jikinsa idanuwanta na rufewa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu a tare kowa idanuwansa na kanta cike da so da kauna da kulawa.

Bayan tayi baccin sai alokacin suka zazzauna jigum jigum kafin Bena da qyar ta lallaba ta shiga toilet din dakin tayi wanka sbd ciwo da tsamin da gabobinta sukai na wahala Dan haka tana shiga toilet din ta sakarwa kanta ruwa ta fashe da sabon kukan Datake riqewa cikin ranta na tata quncin zuciyan.

Wane tsaka me wuya ta samu kanta aciki?
Menene makomar tata rayuwar data auren Dayake kanta?
Ta Ina zata fara tinanin kowace iriyar rayuwa batareda shi da Amnah a cikinta ba?
Wannan sabuwar qaddarar tata me nauyin gaske ce data hadata auren miji Daya da Safnah,
Gashi idan ta lissafa daidai itace ta haramta garesa Koda su Safnah da Ababa Basu koreta ba sbd ta tabbatarda zamansa da Safnah bayan tarewan bikinsu sunyita samun muanalan aure....

Rintse idanuwanta tayi tana durqusawa qasa kukanta mara sauti da tsananin qunci na qaruwa.

Ta jima a cikin toilet din kafin ta fito tana sakawa ranta cewa dole ne yanzu tayi kokarin yakicesa daga zuciyarsa sbd yariga ya haramta gareta matiqar 'yar uwarta na Raye.

Bayan fitowanta Anne datai zugum itama cikin Nisan tinani dagowa tayi ta Kalli benazir din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login