Showing 66001 words to 69000 words out of 183527 words

Chapter 23 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

346

da kuka Jin ihun Ababan Yana Kiran Anne yasata fitowa daga daki a rikice rungume da 'yar acikin zanin uwarta.

Hankali tashe ya sanar da hande Annensu ta bi daji a Daren,

Hande cikin firgici tace

"Mun shiga uku da wannan qaddara,
Daga mutuwa sai hauka ga Kuma jinjirar 'ya anbarni da ita a hannu wayyo Allah mun shiga uku.

Dakin su Annen ta fada ta fizgo Benazir dake riqe gam da hannun sumayyah suna fitowa tsakar gidan ta dungura mata 'yar tana fasa kukan sun shiga uku sun lalace 'danta ya hada iri da Anne me jinin Kaddara baqa iri iri.

Qanqame 'yar benazir tayi kaman sumayyahnta ce ta qanqame
Ahankali take dawowa hayyacinta tafara Jin sama sama hande da Ababa na ihun Anne tabi daji haukanta ya tashi.

Fizgo tinaninta da hankalinta tayi da qyar tareda shiga girmamammen tashin hankali da masifar rayuwa.

Daqyar taji qafafuwanta a jikinta ta iya motsawa tafara jefa kafa koina ta samu ba nutsuwa ta nufi hanyar bangaren dabbobi Ababan dataga shi da hande sun nufa suna Kiran sunan Annen cikin mamakin ganinta zaune cikin dabbobi tana Kuka kaman ranta zai fita.

Benazir na hango Annen ta qaraso da tsananin gudu ta fada jikinta da babyn a hannu suka fasa Wani tsimamman kukan Daya taba zuciyar hande a Karo na farko.

Kuka sukeyi sosai hande da Ababa na kansu hande na fadan baa yiwa Mamaci Kuka,

Shi kuwa Ababa kokarin Ciro 'yar daga tsakiyarsu yakeyi kada a kashe masa ita
Ta Daya bangaren baya hayyacinsa Shima kwata kwata sbd rasuwar sumayyahn Neman juyar masa da Kai takeyi,

Kakkarwa jikinsa yakeyi Yana hada gumi Mai tsananin yawa.

Rikosa hande tayi tana kokarin zaunar dashi sukaji motsi can cikin gidan da sauri hande ta sakesa Dan dubowa tana shigowa tsakar gidan bataga kowa ba.

Faduwa gabanta yayi ta waiwaya ta Kalli dakin su benazir saidai bazata iya leqawa ba tayi Ido biyu da gawa Dan haka take tsoro ya Dan shigeta ta juya zata koma Ababa ya iso Yana Neman zubewa qasa sbd jiri da bushewar yawun tashin hankali.

Dakin ta sake kalla tace masa

"A dakin Nan fa Akai motsin dazu fa,
Kodai Bata rasu bane sumayy....Bata qarasa ba Ababa yayi Wani irin zabura ya fada dakin sbd tinawa da dazu kaman yaga motsawanta saidai Yana fadawa ya haska Kansa ya juye take sbd ganin wayam babu sumayyah a dakin koma me Rai koma gawarta.

Hande data biyo bayansa tana ganin babu gawar ta saki Wani gigitaccen salatin dayafi kama da ihun Daya saka Anne da benazir tasowa suka fado dakin gigice tinanin sumayyah ta tashi.

Ganin ba sumayyahn yasa benazir rarraba Ido a dakin tana Neman sake zaucewa.

Anne kuwa fadawa tayi inda sumayyahn take kwance tana lalubawa ko idonta ne Basa ganin gawan Sumayyah hannuwanta suji mata.



Sabon tashin hankalin da Basu saka masa rana bane suka samu kansu a ciki na rashin ganin sumayyah ace ta bace bat idan da Rai idan gawar.

Ababa da Kansa ya gama juyewa tsaf lokacin barin kayan gidan yafara yana Neman haukacewa ya dauko bindigarsa ya fito idanuwansa jajir baya ganin ko gabansa ya fita yafara duba zagayen da kewayan gidan da anguwar ko zai San wane balain da masifar ne ya samu Kansa,

Shin guduwa sumayyah tayi itama kokuwa sace gawarta Akai?
To waye yasan da ita da halinda ake ciki da har zai shigo gidan ya sace gawarta.


Benazir da Anne kuwa zuwa lokacin Kuka ma Wani gata da arziki ne dayafi karfinsu,
Kukan sukeson Yi Amma babu hawayen idanuwan sun bushe bayan kukan babyn Dayake cika gidan babu me iya ko motsi sbd girma da tashin hankalin lamarin.

A inda benazir take zaune cikin duhun dakin rungume da babyn da har lokacin Bata samu an mata wanka ba,
Qamshin da hancinta ya shaqar mata ne ya sakata miqewa a zabure tana tabbatarda Alh Bilal ya shigo gidan.

Fitowa tayi daga dakin Anne ma ta biyota kaman zariya suka fara ware idanuwa a tsakar gidan cikin duhu Amma Basu ga kowa ko komai ba Dan haka Suka koma bakin kofar dakin suka rakube suna jiran dawowar Ababa da Koda gawar sumayyahn ne.

Shiru shiru babu Ababa babu labarin dawowarsa Yana can yabi hanya Baya hayyacinsa gurin Neman sumayyah ko gawarta,
Tin yana yawon dubawa cikin anguwar harya fice anguwar Bai saniba kaman tsohon mahaukaci haka yakoma acikin tsakar Daren.


Hande dataji jaririyar ta kasa Dena Kuka Kuma makotan kusa zasu iya Jin kukan su San da haihuwar dole ta fito ta karbi yar ta shiga dakinta da ita acan tayo mata wanka ta saka mata kayan da Ababa ya siyo na haihuwar ta fito ta miqawa benazir ita ta sake komawa dakinta sbd sanyi illa zai mata da tsufanta.


Benazir da Anne kuwa suna tsakar gidan Basu motsaba ko Nan da can suna jiran dawowar Ababa zuciyoyinsu na Wani irin tsallan tashin hankali mara misali.

Babyn a cikin hijabi benazir ta sakata ta dunkule sbd sanyi tin tana Kuka har ta Dena tayi shiru tana baccinta da jarirai.


A rayuwarsu Basu taba shiga tashin hankali irin Daren ba,
Yanda suka ga Rana haka sukaga Daren gurin Jiran tsammanin tashin hankali,

Kiran Asuba Akai aka gama har Akai sallah aka fito babu labarin Ababa Suma babu alaman zasu motsa har gari yayi haske tukuna Benazir taja Anne da babyn a dayan hannunta sukaje sukai sallah suka sake fitowa babu me iya ko tsayuwa a cikinsu sbd fargaba da tashin hankalin.


Karfe 6 na safe Ababa ya shigo gidan ko Gani bayayi Yana kawowa tsakar gidan ya yanke jiki ya Fadi.

Hande da gudu tayi Kansa tana fashewa da kuka

Benazir da Bata gansa da sumayyah ba itama sarewa qafafunta sukai ta zube a gurin durqushe tana Neman Kuka ya taho mata ko zata samu sassaucin Abinda take ji a cikin kirjinta.

Anne kuwa a wannan lokacin Ido kawai ta zubawa benazir tana kasa motsawa bare iyayin kukan itama.



*********A Kaantes ma a tsaye suka kwana kan ummensu Bilal data rikice gabaki Daya sbd zuciyarta Datake tsinkewa tana shiga tsoro da firgici akan 'danta.

Duka wayoyin Bilal din Basa shiga hakama ga ummen asthma ya tashi gabaki Daya kaman wadda ta jima tana jinya kiransa DD keyi Yana qarawa Amma Sam wayoyin Basa shiga.

Hakan yasaka dole DD a ranar ya kwana cikin KAANTES Bai tafi gidansa ba,
Dad kaante ma hankalinsa yayi mummunan tashi shikuma dayaga baa samun Bilal din Kuma har tsakiyar dare har Asuba har safiya Bai dawoba Dan haka Suka Yanke shawarar Neman Ababa.

Zazzaune suke jigum jigum kaman gidan makoki a palon dd babba suna jiran dd babban ya kira Ababa Wanda shikuma aketa kira baya dauka.

Daga DD har dad kaante dashi Kansa dd babba harma ummensa zuwa lokacin hakurinsu yafara qarewa suna buqatan Jin komai gameda haihuwar da zuwan Bilal din dama Asibitin da suke.

Kokarin sake saka Kiran dd babba yayi daidai Nan wayar dad kaante tayi ringing cikin zaquwa ya daga Kiran ganin number sbd ko Bilal dinne Dan haka kawai wannan Karan suke Jin yanayi mara Dadi akan lamarin nasa.

A kunnensa ya Kara wayar tareda cewa hello da sallama.

Wani bayani aka fara Koro masa Daya sakasa yin shiru Yana kasa tanka kalma ko Daya sbd jinsa Daya fara daukewa kafin ganinsa.

Subucewa wayar hannunsa tayi yafara kokarin Kai hannunsa kirjinsa ya Dafe zuciyarsa Amma Bai karasa Kai hannunba ya Yanke jiki ya Fadi

Abbakar da DD sukai Kansa shi Kansa dd babba zuwa lokacin gab yake da samun attack Dan haka da sauri Abbakar ya dauki wayar dad kaante din ya miqawa Dd babba Amma ya girgiza masa alaman ya amsa wayar.

Cikin karfin hali da jarumta Abbakar ya gama sauraron bayanin da jamian tsaron suka gama jerowa ya kashe wayar zufa na tsinke masa sharkaf tareda tsananin tausayi da jimama harma da tashin hankali Amma Kuma ba dalilin boye zancen tinda dole aji,

Sauke Kansa yayi cikin raunin murya da tsananin bayyanarda damuwa yace

"Sir Bilal ne ya samu hadari motarsa ta Kone kurmus,Ansamu konanniyar gawarsa a m.....

Bai qarasa ba suka ji Wani irin Kukan Umme Daya saka kaantes din dauka tsit baka Jin motsin komai.

Mum Khadija ce matar qanin dad kaante dasuka iso gurin tare ta riqota jikinta na daukan rawa itama da mummunan labari tashin hankalin da babu wanda ya saka masa rana.

DD kuwa kasa gasgata Abinda aka fada din yayi sbd yanda jikinsa yake wata irin rawa idanuwansa dake farare masu tsananin kwarjini take sukai jajir ya fice palon da sauri ko gabansa baya Gani ya fito Ya nufi motarsa Naseer Dayake shigowa Yana hangosa ya taho da sauri ya Bude masa motar Bai tsaya cewa komai ba yace su nufi hanyar barin gari inda accident din ya afku.

Umme kuwa Wani irin Kuka takeyi Dayake tayarda tsikar jikin Masu jinta
Dad kuwa tini Akai part dinsa dashi sbd likitocin da aka kirawo har biyu da zasu dubasa Dan take numfashinsa ya tsaya.

Dd babba ma zaune yake Amma duk ilahirin hannuwansa da kafafunsa rawa sukeyi,
Zuciyarta tayi nauyi baya iya motsawa kowane lokaci attack zai iya samu Dan haka Shima take akai ciki dashi Dan jiran likita.

Zeenah dake Kuka sosai da mum Khadija harma da wasu daga masu aikin gidan suka kama Umme Akai ciki da ita,
Bata taba saka ran mutuwar danta ce ta sanyashi fita yabar gida ba da bazata bari ya bar ko kofar part dinta ba,
Irin Kukan datakeyi ne yasa mum Khadija fashewa da kukan tausayinta sbd kowa ya sheda soyayyar dakewa danta wadda ya kasa samu gurin kowa daga familynsa.



*****Koda DD ya Isa Shima Saida ambulance tazo ta daukesa daga gurin da hadarin ya faru sbd gawar Ta Kone kurmus ta yanda baa ganeta motarce kawai ake iya Ganewa itama sbd kafin konewar da alama ya daki Wani abin ne lambar motar ta fita harma da baya motar Shima ya balle ya fita.

Hakan yasa Akai saurin Ganewa aka kirasu sbd matsayinsu.

Rasuwar Bilal kaante a cikin Bata rufa awa biyu ba labarin ya bazu koina
Aka fara kokarin saka lokacin janaiza, manyan mutane kuwa tini suka fara kira da Kuma fara Siyan tickets na zuwa gaisuwa da janaiza.


*****A lokacinda labarin rasuwar ya shiga kunnan Ababa a lokaci Daya shi da benazir wannan Karan suka Yanke jiki suka fadi sbd sani da tabbacin Data Basu na cewan Bilal ne ya dauke sumayyah.

Anne da zuciyarta ta qyame kyam a tsakanin Daren jiya zuwa safiyar itace ta zubawa benazir ruwa ta farfado itama tata zuciyar na qamewa tana tashi daga tsoka.

Ababa kuwa Yana farfadowa ya sake yanke jiki ya Fadi sbd ta tabbata sumayyah da Bilal sun mutu sun bar duniya.
38👇👇👇👇👇👇
##MAMUH#
#BENAZIR
#ABABA
#AMNAH
#DD KAANTE
#MARRIAGE/LOVE/ROMANCE


*_Arewabooks@Mamuhgee_*
38
Benazir data kasa yadda da sumayyah ta tafi barsu rawa dukkanin jikinta rawa yakeyi ahankali tana kasa Jin hawaye ko Daya cikin idanuwanta,
Bakinta da makoshinta Wani irin bushewa sukai tana kasa samun yawu ko kadan cikin bakin da moqoshinta.

Babyn dake jikinta ce ta motsa ahankali
Hannuwanta dake rawa ahankali tasaka ta sake rungume 'yar tana sake Jin zuciyarsa, idanuwanta da bakinta na bushewa sbd su 'yar uwarsu,Rabin jikinsu suka rasa ita Kuma babyn uwa da ubanta ta rasa a lokaci Daya.

Ababa Da ake kokarin kwasa zuwa Asibiti Anne ta kalla da idanuwanta dasukai jajir Amma babu Wanda ya samu Kuka a cikinsu sbd basuda sauran Abinda suke ji a zuciyoyinsu dasuka sanqare,

Hande Kuka takeyi tana qarawa akan kada ta rasa 'danta,
Mutane ta samo aka shigo aka dauki Ababan zuwa Asibiti cikin tashin hankalin kada a rasa shi.

A wannan lokacin ne Wani irin kukan da Bata San dashiba ya zuwar mata dukkanin jikinta na rawa da jijjjiga ganin ita tata 'yar kusan mutuwa tayi cikin tsananin wahala baa damu da akaisu asibiti ba har aka rasata gashi yanzu gawar ma sun rasa a lokacinda suke sakaran Bata mutu ba Kuma labarin hadarin ta da mutuwarta da Bilal yasake tsinka fatansu,

To su kuwa a yanzu meye suke da Wani buqata ko fata bayan mutuwar Suma su huta,
Ga sabuwar Alhaki Allah ya sake jefo musu a cikin wannan lokacin da Suka gama sarewa gabaki Daya da duniyar da rayuwarma.


Benazir na Jin kukan Anne na shiga zuciyarta yana yankan Amma Bata iya matsawa saima sake rungume babynsu datayi tana Jin a yanzu da babu shigowa wannan babyn rayuwarsu da babu Abinda zai hanasu samun bugawar zuciya a ayau din su mutu su huta Amma duk motsin da babyn keyi jikinta Jin sumayyahnta takeyi a jikinta da zuciyarta Dan haka take sake qanqame babyn.


Kukan da Anne tayi Mai tsananin gaske Bai rage mata komai na nauyin da takejin zuciyarta tayi mata ba Dan haka ta share hawayenta ta miqe tsaye ta kama benazir din itama ta tayar da ita suka koma dakinsu.

Suna shiga Annen ta hau tattara dakin ta kwashe kayan da sumayyah ta haihu Akai ta fito dasu ta debo ruwa tahau aikin wankewa batareda ta furta kalma ko Daya ba.

Tana gamawa ta dawo dakin ta gyaran musu shi tas
Har lokacin benazir na zaune rungume da 'yar Bata motsaba idanuwanta a bushe.

Anne ma da aikin fitan hayyaci takeyi tana gama gyara dakin ta fito ta share tsakar gidan ta gama ta Dora ruwan zafi suna tafasa ta juye tayo dakin dasu ta ajiye ta Kalli benazir tana miqa hannu zata karbi babyn tace

"Kawota a sake mata wanka"

Sai alokacin benazir ta dago da busashin idanuwanta ta Kalli Annen tsawon mintina
Take a lokacin siraran hawayen tausayin mahaifiyarta suka gangaro mata sbd tasan baa cikakken hayyacinta take ba.

Hannu Daya ta saka ta share hawayen tareda daurewa ta dawo hayyacinta ta Kalli Annen ta girgiza mata Kai ahankali tana Ciro babyn daga jikinta ahankali tace

"Zan Yi mata Anne ki zauna ki huta"

Hakan data fada ya saka jikin Annen sanyi sbd tasan tsoron Bata yar takeyi sbd tinanin Bata hayyacinta kada ta jefata cikin ruwan zafi.

Dan haka Bata Musa ba ta juya ahankali ta koma gefe ta zauna tana kallan benazir zubawa benazir da babyn Ido.

Hannuwa na rawa da tsoron rashin iyawa Benazir tayi qarfin halin yiwa babyn wanka hannuwanta na tsananta rawa.

Bayan ta gama mata duk ta jiqa jikinta da gurin.

Ta miqawa Anne babyn Dan ta samu miqewa ta kwashe kayan wankan
Anne ta girgiza mata Kai tareda cewa ta riqeta kawai bari ita ta kwashe kayan.

Kayan ta kwasa ta fitar ta dawo ta goge gurin tana gamawa ta karbi yar benazir ta sauya kayanta sbd kada sanyinsu ya damu babyn dake jikin nata
Tana gama saka kayan ta fice tayo alwala sbd lokacin sallar azahar da yayi tini.

Tareda Anne sukai sallah babyn na tsakiyarsu shimfide.

Suna idar da sallah suka fara jerowa sumayyah addua zuciyoyin kowannensu na dakewa da qarfafa tawakkalinsu,
Gawarta ma Basu saka ran Gani ba sbd zuwa lokacin sun sani an hadata da Bilal anrufe tinda danginsa sun San ita zai aura,
Basuda masaniyar komai sai Ababa ya dawo yajiyo idan gawar zaa Basu kokuma an rufeta tini.


Babyn suka zubawa Ido dukkaninsu suna qarewa fuskarta Kallo zuciyar benazir na karban duk Wani feeling akan babyn.

Sai alokacin takejin 'yar cikin ranta sbd dama da sumayyahn na Raye da Bata Nan 'yar sumayyah 'yarta ce,
Cikin ne kawai Bata dauka ba da haihuwarsa Amma kusan duk Wani wahala,Reno,farin cikinsa da baqin cikinsa Dede sukaisa da sumayyahn a yanzu Kuma ta tafi tabar mata 'yar bayan tazo duniya.


Anne kuwa miqewa tayi ta fito ta Dora musu abinci duk da tasan ba cinsa zasu iya ba Amma dole zasu rayu suci gaba da rayuwa sbd 'yar sumayyah data barmusu Dan haka komai a yanzu ba Dan kansu zasuyi ba sbd babyn zasuyi.

Tana gamawa ta tilasta benazir suka zauna suna cusa abincin a dole
Suna gamawa sukai sallar laasar
Lokacin babyn tafara Kuka sosai tana Neman Nono.

Kukanta ya saka radadinsu dasuke dannewa Neman tsinkewa Amma Anne ta daure ta shiga dakin Ababa cikin kayan haihuwar Daya Tara ta samo ruwan zamzam suka taho suna cikin bawa yarinyar Aka dawo da Ababa a jeme ya zabge cikin wuni Daya.

Hande ma har lokacin kukan takeyi Akai Akai.

Gidan tsit ya dauka kowa na jimamin mutuwa da rashin da sukai gashi kaman yan kankan Kai baa ma San anyi mutuwa ba gidan bare a shigo musu gaisuwa tinda baa ga ana janaiza ba bare karban gaisuwa.

Ababa Dayake fama da Kansa Jin kukan babyn yayi yawa yasa jamilu yaronsa siyo madarar jarirai gwangwani uku da ruwan roba Katan Daya.

Ana kawowa aka bawa benazir batareda an sanar da ita yanda ake bayarwar ba.

Dayake babyn tafara galabaita Bata tsaya Bata lokaci ba itada Anne suka dafa ruwan zafi suka hada mata a fidar dake cikin kayan haihuwar da hande ta watso musu daki bayan dawowar tasu.

Ana sakawa jaririyar fidar farko kasa kamawa tayi dai daga baya Anne ta karba ta ringa diga mata madarar cikin baki tukuna ta Dan fara motsa bakinta madaran na shigewa.

Hawaye masu zafi ne suka gangarowa benazir lokacin da babyn ke Shan madaran tana motsawa ahankali batareda tasan Tayaya zasuyi rayuwa da babyn a haka ba.

A haka suka kwana zaune gidan babu Wanda ya iya kwantawa bare ya iya rintsawa sai hande kawai Amma Ababan ma a zaune ya kwana cikin ciwon zuciya Dayake Neman Kaisa lahira a kwana daya da wuni biyu.

Har safe zuciyarsa cikin mummunan hali take ciki Yana saka da warwara Dan kuwa yasan ya tabbatarda sumayyah akwai Abinda dai yake qasan bacewarta bat,
Gawar da aka samu cikin motar Bilal kaante guda Daya ce bayan biyu ya kamata a gani idan Kuma drivernsa ne ya tuqosa gawa uku yakamata a gani Amma Daya aka samu wadda Suma jamian tsaron kaman wainda aka Basu San aikinsu ba baida tabbacin anduba gawar an tabbatarda ya waye.

Zafin da Kansa ya dauka ya sakasa kasa tantance komai bayan tabbatarda koma meyake qasan wannan lamarin Bai lalata komai nasa ba ya janyo masa lukutar masifar dazata Kaisa qasa.

Dan haka da safe bayana ya sake samun saukin dawowa hayyacinsa Ya Yanke Wani mummunan kudirinsa akan Abinda yayi Niya Dan haka Yana fitowa Abinda yafara shine sanar da benazir da Anne dake jiransa akan maganar sumayyahn cewa anriga anyi janaizarta tareda Bilal tin jiyan addua da fatan samun rahamar ubangiji kawai zaa ringa mata harma da Bilal din.

Daga Anne har benazir ga mamakinsa babu Wanda ya some masa kaman yanda ya tsammata,. Abinda Bai saniba sun riqa sun Riga zuciyoyinsu sun bushe sun saddakar sun karbi kaddarar mutuwar sumayyahn tin jiyan dan haka suna samun tabbacin daga bakinsa suka sake daukan taurin zuciya suka sawa kansu.

Ababa kuwa Daman Hakan yakeso Dan haka shiryawa yayi ya nufi KAANTES gurin gaisuwa da sanar dasu an haihu lafiya kalau.


*******A Kaantes

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login