Showing 93001 words to 96000 words out of 183527 words

Chapter 32 - Zafin Kai Book One Complete Hausa Novel

Mamugee   

26 Oct 2025

358

sauke ajiyan zuciya a boye kafin ta wuce tayo alwalan sallar laasar data wuceta ta fito tayi.

Tana idarwa ta fito sbd takasa samun nutsuwan jikin Amnah.

Ko da ta fito likita yazo yana duba Amnah din.

Gefen Umme ta silalo ta zauna a hankali tana sauraran Abinda likita ke fadawa DD.

"Sanyi ne kawai yake son Dan shigarta sai a kiyaye barinta wasa da ruwa gaskia"

Juyawa yayi ya Kalli Bena dake bayan Umme likitan yace

"Madam ai last time na fada Miki Hakan please a sake lura sosai a kiyaye."

Ajiyan zuciya ta sauke tana gyada masa Kai ahankali.

Magani yace zai Aikowa Amnah din yayi musu sallama ya wuce.

Bayan fitansa bacci ne ya dauke Amnah din har lokacin tana jikinsa.

Shima zazzabin yakejin Yana Neman kamasa sbd zafin jikinta da tin dazu yake shiga jikinsa Kuma shi fatansa batada Wani karfi da wuri wasu abubun ke saurin shigesa.

Abincin dole Bena ta miqe taje dining taci tana gamawa tayi dakin Zeenah Datake ta fama da nata aikin kwana biyu sbd itama zatai joining kamfanin Amma Kuma tana buqatan attending wasu online classes na sati uku ga service dasuke Shirin zuwa wannan Karan inshallah itada Bena din.

A dakin suka zauna itace ta ringa fahimtar da Zeenah din wasu abubuwan na course nata datai attending Wanda ya banbanta dana online da Zeenah keyi Kuma gashi Wanda Bena tayi dama ce da sai Dace ake samunta yanzu bazaa sake course din ha sai after like 3 years.

Har kusan 9:40 tana dakin kafin ta fito Takoma dakinta tana mamakin Ina Amnah ko tana dakin Umme.

Bedroom dinta ta Bude ta shiga Kai tsaye..
Ac din Dayake kashe ya saka mahaukacin qamshinsa yiwa dakin Wani irin gaurayar data sakata kallan gado Kai tsaye.

Zaune yake bakin gadon har lokacin Amnah na maqale dashi taqi yarda ya tafi yabarta.

Idanuwansa Wani laushi sukai da suka sakata rikicewa tana rudewa da kallansu tafara kokarin juyawa a hankali cikin Wani lazy sauti yace

"Kinsan meye time kuwa?"like kinsan ana duba time kuwa??

Dakatawa tayi tareda kasa fita tana daidaita numfashinta dake Dan fita da qarfi ta juyo ahankali batareda ta kallesa ba ta Kalli Amnah wadda da alama tana Jin zazzabin sosai har lokacin sai taji jikinta ya mutu ahankali ta Dan dago tanasan kallansa Amma ta kasa iya sake kallan idanuwansa ta Bude baki ahankali ta furta "sorry na bari kayi having time naka da ita ne"

Bai iya cewa komai ba sai kallan da yayi mata na minti Daya kafin ya Dan sauke numfashi Mai dumi da zazzabin dake cinsa Shima yakai hannu zai Zame Amnah ta sake qanqamesa cikin bacci da radadin ciwo tareda ambatan sunansa cikin bacci da qaraman muryanta me taushi.

Shiru sukai dukkaninsu suna kallanta shi Kuma zuwa lokacin zazzabin yakeji sosai Yana buqatan zuwa gida sosai.

Lumshe idanuwansa dasuka sake saka Bena Neman rudewa ga ciwon Amnah da riqesan da Amnah tayi ga idanuwansa da duk ya motsa su saita ji tana Neman rudewa.

Ahankali ya dago ya Kalli Bena din jinta shiru takasa qarasowa ta karbi Amnah din daga jikinsa.

Ganin kallan da yayi mata ya sakata takowa ahankali ta iso gurin hannuwanta na Dan rawa ta ranqwafo takai hannuwanta cikin sanyi ta Dora akan na Amnah dake qanqame da jikinsa.

Dumin numfashinsa Mai zafi ne ya sauka wuyanta zuwa cikin rigarta ahankali take rawar hannunta ya qaru ahankali ta Dan rintse idanuwanta tana Kai hannunta Daya zata Ciro Amnah numfashin nasa Mai dumi ya sake saukar mata a fatan wuya ta Bude idanuwanta dake rintse ta kallesa daidai Shima ita din ya kalla ganin hannuwanta na rawa ahankali.

Kallansa tamkar wata fitina ce ga duk Wanda yayiwa irin wannan kallan na cikin tsakiyan Ido Dan haka haduwan idanuwansu ya sakata miqewa ahankali daga raqwafan da tai tana cika masa hanci da qamshinta Daya sake tsananta zazzabinsa.

Hannunsa Daya taji akan nata daidai lokacinda taso matsawa baya zata bar gurin sbd saukan dumin numfashinsa fatan jikinta zazzabin itama zai saukan mata.

Tinda take rayuwanta yau ne ranar farko da namiji yayi mata irin wannan rikon Dan haka Saida bugun zuciyarta ya tsaya cak ta rufe idanuwanta ahankali kafin tayi Wani motsi ya Dora hannunta kan Amnah ya Zame a hankali ya miqe ya fice daga dakin yabar dakin da fitinanniyar qamshinsa.

Kasa motsawa tayi tsawon seconds tukuna ta iya motsawa ta silale ta zauna bakin gadon inda ya tashi har lokacin tana sake Jin saukan dumin numfashinsa akan fatarta.

Gyarawa Amnah kwanciya tayi kafin ta miqe ta shiga toilet Bata Wani jima ba ta fito ta saka pyjamas masu tsantsi ta hau gadon ta kwanta tareda hade kanta dana Amnah pillow Daya tana Jin qamshinsa na shiga hancinta a duk numfashin da zata ja.


Qarfe 3 na dare jikin Amnah din ya sake tsananta zafi ko Kuka da rigima Bata iyawa Wanda ya saka hankalin Bena mummunan tashi ta fara hawaye tana shafa Amnah din.

Magani ta sauko ta sake Bata ko gamawa batai ba Amnah ta amayo sa jikinta na sakewa Dan haka hankali tashe ta janyo wayarta ta kira Nafisat daga bangaren masu aiki saiga Nafisat din tana wartsakewa daga bacci.

Motsin shigowan Nafisat sashen ya saka zeenah fitowa itama sbd Bata jima da kwantawa ba itama karatu ta kwana Yi.

Ganin halinda Amnah ke ciki ya saka Zeenah dauko wayarta ta kira DD sbd Umme na sashen dad.

Bena kuwa toilet ta shiga tayo Wani wanka sbd Amai dake jikinta ta fito daure da towel purple,lokacin Nafisat ta sake sauya zanin gado ta gyara dakin duk da tsakiyan dare ne Amma dole tayi aikinta.

Amnah ma tini aka goge mata jikinta aka saka mata wasu kayan baccin jikinta na Dan fisga sbd zafin zazzabi da qarfinsa.

Zeenah data sake Kiran DD Dan tanada tabbacin Kila Yana kaantes zai kwana sbd jikin Amnah bazai barshi ya tafi ba.

Koda kiran Zeenah keta shigowa wayansa Yana bacci ne sbd zazzabin Daya kamasa Shima Dan haka Bai ganiba sai asubata Daya farka Yayi sallah yaga misscalls nata.

Time datai kiran yafara kalla a natse yaga 3:36am.

Kai tsaye yasan jikin Amnah ne kawai dole zaisa tayi masa kira wannan time din Dan haka ya fito da Kansa yaja mota zuwa kaantes.

Koda ya Isa securities sunyi mamakin ganinsa lokacin suka Bude masa gate ya shige Kai tsaye sashen Umme ya nufa Koda ya Isa Zeenah ce ta Bude masa kofa sbd akwai sauran duhun Asuba Kuma lokacin masu aiki Basu isa shigowa ba.


Tana Bude masa tayi dakinta sbd baccin dake cike da idanuwanta daqyar sukai sallar Asuba kowannensu bacci yakeji musamman Bena data kasa rintsawa tin farkon dare har qarshensa.

Kai tsaye bedroom dinta ya nufa ya Bude ya shigo babu haske a dakin sosai sbd rage wutan datai sosai.

Kwance take daga ita sai silk kayan baccinta datafi sakawa sun maqale jikinta musamman da AC yake kashe Basuyi rufa ba Amnah na kan jikinta bacci sike cikin galabaituwa daga rashin baccin da Basu samuba da dare.

Qarasowa yayi Bai damu da tsayawa kare mata Kallo ba Amnah kawai yakai hannunsa ya taba fuskanta yaji zafin jikinta ya sauka Dan haka ya juya juya zuwa window ya Ciro wayarsa ya kira likita ya sake masa bayanin ko zai sake dawowa duba Amnah din.

Yana kashe wayarsa Amnah ta Bude idanuwanta Jin muryansa ahankali ta Bude baki ta kira sunansa cikin sanyi.

Juyowa yayi Yana kallanta cikeda kauna da kewanta ya Tako zuwa inda take Yana dauke idanuwansa daga kallan Bena Datake bacci cikin wata irin nutsuwa kaman baby itama ga idanuwanta datasha kukan ciwon Amnah din sun Dan kumbura kadan.

Tashi zaune Amnah tayi tareda miqa masa hannuwanta tana cewa ya dauko da ita gadon.

Cirota yayi ya fito dakin Kai tsaye sbd baida nutsuwan jira cikin dakin Daman.

Suna fitowa Palo Nafisat ta koma da ita tayo mata brush da yan wasu abubuwan ta sake canja mata kaya kafin ta dawo gurin daddynta lokacin Umme ta shigo ganinsa ya sakata mamaki.

Gaisawa kawai yayi da Umme ya fice da Amnah suka tafiyarsu gidansa.

Bena Bata farka ba sai 10 lokacin itama kaman zatai zazzabin takeji Amma Dayake tasamu baccin kirki ta Dan sake.

Umme ce ta fada mata yazo ya fita da Amnah dan haka breakfast sukai itada Zeenah suka tafi gurin dd babba ta jima tana magana dashi kafin suka fita sbd dole a satin zasu wuce Camp.

Amnah Bata dawo ba sai yamma sosai itada daddynta ya ajeta ya wuce sbd Shima yanada tafiya a satin zuwa Lagos Wanda suma acan zasuyi service Amma baimasani ba Saida dd babba ya sanar dashi a gidansa zasu zauna dake can Dan haka ya shirya zama dasu kafin ya gama nasa aikin ya dawo ya barosu.
burin dd babba a yanzu na ganin ya saka Bena cikin business dinsu ne sosai sbd ta tsaya cak anata future din Dayake san ta samu Dan yanta kanta da mahaifiyarta har abada daga mahaifinta Dan haka yafara sakata cikin ayyukan office kafin service nata da sai yanzu zasuyi itada Zeenah wadda itama takesan shiga family business dinta.
##MAMUH#

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
53
Amnah ta samu sauki sosai ta warware Dan haka yanzu Bena ta samu nutsuwa da kwanciyar hankalin aikin office Datake Dan leqawa hakama tana samun time sosai yanzu na zaunawa da dd babbanta suna maganganu na businesses sbd kusan matsayin da Bilal ya rasu ya bari ne yake son Maidata Akai sbd Shima Bilal din yanada Saar iya gudanar da kowane irin business ya qulla sai an samu Abinda akeso 100 percent.

Umme Sam batason suje Lagos service nasu Amma Kuma kaman raayi da buqatan dd babba ne suje can din Dan haka dole ta hakura gashi anan zaa bar mata Amnah sai Mummynta ta gama ta dawo Kuma.

Lokacinda tafiyansu ya qarato Amnah harda ciwon kewan mummynta da zatayi ta kwanta daqyar Bena ta iya danne zuciyarta ta tafi tabarta Allah ma ya saka daddynta Yana Nan shi Dan haka kewan da zai ringa debe mata daban ne musamman wasu lokutan gurinsa take kwana sun Saba.


****Sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da hutawa suka fara a Lagos sbd Sam ba Wani wahala ko gwagwarmayar dasuke fama da ita sbd tini suka gama komai suka fara bautan qasansu a natse.

Wani 2 bedroom duplex ne dake Ikeja suke ciki na DD Wanda babu Abinda gidan ya rasa na Jin dadi da tsadan rayuwa,

Komai na gidan bisa ga tsari da yanda yake buqata yake hakama komai na a tsare yake kaman gidansa na Zurich da can gida.

Bedroom Daya suke amfani dashi sbd dayan bedroom din nasa ne basuma San Ina key dinsa yake ba bare Yaya yake.

Zeenah datai missing rayuwarta na turai suna zuwa Lagos din ta koma baturiyarta suka goge abinsu suna zuba life daidai yanda tayi musu.

Dayake service din nasu na yayan manya ne akwai ranakun da bama sa zuwa Dan a sati baifi suje so biyu ba gabaki Daya Zeenah ta zarar da Bena wadda itama Daman rayuwarta ta zurfafa sosai a rayuwan hutu da wayewa kawai tanada kawaici ne dakuma kalan rashin sakewanta da mutane sosai Daya zama kaman Wani Jan ajinta ne,

Amma a rayuwar da suka samu Kansu ta garin taji Dadin garin sosai fiye da wasu qasashen turawan Dataje Dan haka ta sake tana rayuwanta hankali kwance.

Kullum tana waya da video call da Amnah matiqar tana gida saidai ranakun Datake gurin daddynta to wannan shine Bata samun ganinta a waya sai ranar data dawo.

Ahakan suka dauki lokaci Dan har suna maganan wata biyu a garin Basu koma gida sbd dd babba yace su zauna su kammala gabaki Daya tukuna tinda a gida suke.

***Yau Zeenah ce kawai ta fita ita kadaice a gida
Itama Bata fita bane sbd yau Bata buqatan fita koina hutawa takesan Yi sbd jiya har dare sosai Basu dawo gida ba.

Baccin Rana tayi sai yamma ta tashi tayi wanka ta fito ta nufi kitchen,
Ruwa tafara Bude fridge ta dauko roba ta Bude Tasha kafin ta nufi kitchen island ta janyo kayan tea dake Kai ta hada warm tea Tasha sbd batasan Abu me zafi sosai ita.

Tana gamawa ta fito tana duba sakonnin wayarta har Dana Zeenah dake sanar da ita zata jima Bata dawoba.

Palo ta zauna tareda janyo laptop ta Bude zata fara Wani Aiki taji ana taba kofan shigowa palonsu.

Juyawa tayi ta Kalli kofar Rabin hankalinta na kan laptop din sbd ta kunna.

Password din kofansu taji ana sakawa Dan haka ta dawo da kanta kan Abinda takeyi sbd tasan bayan ita da Zeenah babu Wanda yasan password nasu so definitely Zeenah ce.

Maida hankalinta kan Abinda takeyi tayi tana Dan Dan girgiza qafanta ahankali.

Harta fara Abinda takeyi taki shiru ba hayaniyan shigowan Zeenah din batareda ta juyoba da muryanta me shegen nutsuwa da Wani aji irin class irin na 'yayan hutu da wayewa tace

"Zee, kikace you're not coming back early¿ Ko Zak....... Cak ta tsaya da maganarta tana kasa qarasawa tareda dakawata daga Abinda takeyi bugun zuciyarta ya Dan tsananta sakamakon qamshin Daya shiga hancinta da sauri ta juyo daidai qarasowansa cikin palon sallamansa a makoshi.

Kallansa takeyi batareda tasan tana Hakan ba sbd mamaki da rudewa.

Kallanta dayaji akansa ya sakasa dakatawa ya zuba mata nasa idanuwan dasuka sanyata sake shiga Wani yanayi na bugawan zuciya da sauri.

Kaman daga sama taji muryarsa me wuyan ji

"Kin San ana amsa sallama right?"

Dauke kallanta tayi daga Kansa tareda Bude baki ta amsa sallamansa tana Dan tahowa gurinsa tace

"Barka da zuwa"

Tana tinkarosa ya Dan dauke Kansa daga gefen Yana wucewa zuwa hanyar bedroom dinsa sbd kayan dake jikinta da itama ta manta short free size Balenciaga sweet shirt ne kawai jikinta.

A Palo yabar luggage dinsa wadda Naseer ya ajiye masa bakin kofa ya juya batareda ya shigo ba.

Wucewa yayi yabarta palon tana Dan sauke numfashi kadan tanajin kanta na sarawa ma sbd bazata iya zaman palon bama Kuma.

Laptop dinta ta dauka zata tafi daki sai Kuma ta Tina cajan laptop din Yana palon Kuma Sam Bata taba ciresa bama tinda ta saka sa gurin Dan haka tayi zamanta gashi yariga ya shige tasan ba lallai ya fito yanzu ba Shima.

Zaunawa tayi taci gaba da Abinda takeyi hankalinta kwance cikin nutsuwa.

Wayarta ce tayi ringing a Dan kasalance sbd tafara gajiya ta duba taga Umme ce Kuma vidcall take taji zuciyarta tayi sanyi sbd sanin Amnah ce Dan haka ta dauka tana Sakin kyakyawan murmushin farin ciki tana cewa

"Oh my, ya Akai my baby tasan mummynta is Missing her like crazy da yamman nan?"

Dariyan farin ciki Amnah ta saki har tana kwantawa kan gadon Umme data Bata wayar ta fice duba baqin dake jiranta Palo.

Amnah na tsananin son iyayenta su ringa fada mata yanda suke tsananin sonta shiyasa dukkaninsu dasuka San halinta suke yawan fada mata ire iren Hakan sbd tana nuna Jin dadinta sosai.

Murmushi Bena ta sake saki tana sake cewa

"Baby na tayi missing mummy nata kuwa?
Naga kinyi Wani kumatu bayan mummy duk ta rame sbd kewanki,
Daddynki Yana baki more chocolates right??

Dariya Amnah ta sake Yi tana cewa

"Mummy Nima fa sosai nake missing naki and my daddy ma yayi tafiya yau yace he's coming to you and.....

Fitowan Daddyn nata ne ya saka Zeenah Dan kallan gefe batareda ta juya ba shikuma luggage dinsa ya fito dauka harya tube daga shi sai black towel daya dauro qugunsa kaman yanda yake daura towelsa kaman zasu Fadi Amma yau din ya daure da kyau sbd sanin akwai Wani gidan bayansa,
Da ire iren wainnan sabon nasa yasaka baya iya hada muhalli da kowa sbd shi mutum ne me tsananin son yin komai nasa yanda yakeso ba takura ko wane kame kame.

Amnah ce idanuwanta suka hango mata shi da qarfi tana tsalle tace

"Daddy,daddy.."

Dakatawa yayi ya Kalli wayar hannun Bena yaga fuskar babynsa tana tsallen murnan ganin iyayenta tare tace

"Zo daddy kaima inata son ganinka Ina kewanka."

Ta bayan Bena yazo ya tsaya ahankali tareda ranqwafowa Yana kallan Amnah ya saki Wani fitanannen murmushin Daya saka ruwan jikinsa na wanka da Bai goge ba sbd Yana buqatan sabbin towels dazai iya goge jikinsa da bedroom din sun jima aje bazai iya sakawa jikinsa ba.

Ahankali ruwan ya digo kan wuyan Bena ya gangara cikin rigarta
Numfashinta ya kusa tsayawa kafin ta iya janyosa ahankali kirjinta na Dan yin sama Wanda yasashi Dan motsawa sakamakon motsin ruwan ya sake digar mata a wuya wannan Karan rintse idanuwanta tayi ahankali
Amnah data Gani tace

"Daddy ka digawa mummy na ruwan wanka fa Kuma ya mata sanyi tace Kuma ruwa ajikin mutum idan ba wanka zaiyiba ko alwala Yana saka mutum yayi rashin lafiya ka goge mata banason mummyna tayi rashin lafiya.

Maganar Amnah ya saka Bena kallan wayar shikuma ahankali ya juyo idanuwanta kan wuyanta da daidai lokacin wasu suka sake digar mata suka gangarowa ahankali zasuyi cikin rigarta ba tsammani Bena taji saukan tattausan tafin hannunsa kan wuyanta,Saura kadan Numfashinta yabar jikinta ba zato ta Dora hannunta Daya akan nasa ta tsayar hannunsa ta hanasa goge inda ruwan suka bi.

Yanda ta Dafe hannunsa da nata ya sakasa karkato da fuskansa kadan ya zuba mata idanuwansa da suka sake tsananta bugawan kirjinta dake sama yana qasa.

Duk kirjinta yayi sama saiya shafi hannunsa dake kusa da gurin
Ya sake zuba mata lazy eyes nasa zaiyi magana Amnah datake kan waya har lokacin ta kira sunansu da qarfi tana cewa

"Daddy kanata sake zubawa mummy ruwa fa nidai daddy ka goge mata Dan Allah." Kuka take Neman Yi masa Dan haka a hankali yakai hannunsa Daya ya kife wayan ahankali tareda birkito Bena data kasa motsi yana kallan fatan wuyanta da santsinta ya saka ruwan Yana diga yake gangarawa ya sauko.

Kasa Bude idanuwa Bena tayi tana qanqame hannuwanta sbd kusancin dasuka samu yayi kusa sosai gashi jikinsa babu Riga qamshin shower gel dinsa Mai shegiyar qamshi da tsada sai shiga hancinta yakeyi direct.

Saukan hannunsa kan wuyanta a Karo na biyu ya sakasata sake riqe hannunsa a Karo na biyu itama saidai kafin tayi Wani motsi ya bi ruwan zai goge ba shiri ta qanqame hannunsa tareda Bude idanuwanta ahankali ta dago ta kallesa Shima ita ya zubawa idanuwansa.

Baki takeson budewa tayi magana Amma ta kasa sbd dumin da jikinta ke dauka na shigar zazzabi a take.

Shikuma ahankali ya janye hannunsa data riqe ya gangara da idanuwansa zuwa wuyanta a Karo na biyu ahankali ya Bude baki sbd cikin qaramin sauti me kashe jikin Wanda yake sauraro yace

"Bantaba kasa yiwa Angel Dina Abinda takeso ba."

Juyawa yayi kaman ba shine yayi maganar ba yaja kayan Daya fito dauka ya koma bedroom dinsa ya shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login