Showing 33001 words to 36000 words out of 137891 words

Chapter 12 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete

tasa hannu ta 6an6are abunda take matse ƙirjinta dashi, tana ciresa taji wata irin iska na shigarta, gaba ɗaya boobs ɗinta a mugun taƙure suke, ba abunda ya same su, amma ƙan nipples ɗinta ba ƙaramin hurting ɗinta ya ke ba,
Ita kanta tausayin kanta taje ji, yadda ƙiri~ƙiri ta canza kanta daga mace zuwa namiji, duk tabi ta takure halittarta, hannu tasa ta cire ɗan gashin bakin da take mannawa, ɗago dashi tayi tana kallonsa tana matuƙar son ainihin halittarta ta mace,
gaban dressing mirror taje ta ajiye shi, toilet ta shiga tasakarwa ƙanta shower, ta haɗa hada hairs ɗinta ta wanke saboda ya fara tashi, gashi tana buƙatar tayi shaving, batasan ya zata yi, sauƙin bata da gashin armpit amma can under ɗinta kuwa akwai sosai,
ta gama yanke shawarar zata ɗebo shaving cream ɗin junaid taga hada set na shaver gare sa, dama shine marainin wayan ta,
ganin cewa babu kowa gidan daga ita sai azmi wadda ke can kwance tana sharar bacci, hakan yasa ta yanke shawarar cewa yau zata sakata ta wala, don haka ta shirya tsaf cikin riga t-shirt white colour da black trouser, sai da ta tabbatar ta matse ƙirjinta kamar yadda ta saba, sannan ta aza gashin bakin da take sawa, lalubawa tayi cikin jakar kayanta dayake ba duka kayan ta zuba cikin wardrobe ɗinba, anan tasamu hular da hajjaju ta siya mata, irin wannan hular da ake kira da tashi da kwakwa,
sai da ta tabbatar ta naɗe gashinta cikin ta cunkushe ta matse shi sannan ta kifa hular a saman kanta, sai gashi ta fito fes kamar ɗan saurayi,
Ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, fitowa tayi ƙafarta sanye da takalmi roba na maza,
Kama hanyar ɗakin junaid tayi, cikin sauri take tattaka matattakalar stair ɗin, a gajiye ta iso ɗakin tura sa tayi ta buɗe ta shige,
Komai tsaf a tsanake dama ita ce tayi gyaransa, cikin jin daɗi ta wuce cikin toilet ɗinsa, agaban bathroom cabinet ta tsaya, anan taga jerin tsaddun mayukansa, duk wani abu na gyaran jiki akwashi kai kace na macene ba na namiji ba,
Tsawa tayi tana tunanin me yakamata ta ɗauka, tunani ta shiga yi " kodai kawai na tsaya anan nayi shaving ɗin inyaso in na gama in tsaftace masa wurin yadda bazai gane ba sai in samu in lalla6a in fi ce, saboda in na ɗaukar masa zai iya gane wa, ƙarshe ya kamani a matsayin 6arauniya, ya zanyi ni," ta fada tana ƙarewa wurin kallo
hannu tasa ta ɗauko roban shaving cream ɗin ganin yana da kusan guda uku yasa ta yanke shawarar ta ɗauki ɗaya bazai gane ba, sai ta haɗa da shaver guda biyu, tun da taga yana dasu dayawa a cikin ledarsu,
ruƙo su tayi a hannun ta saboda haɗama irin tamu ta bil'adama zuciyarta ta raya mata cewa mai zai hana ki haɗa da shampoo saboda wanke kai ga kuma sabulai masu ƙamshi sannan kina buƙatar turare na fesawa a jiki,
Murmushi tasaki jin wannan zancen na zuciyarta,
A fili tace "abun sai na samo wurin da zan zuba su baxan iya ɗauka ba a hannu na,
Fitowa daga bathroom ɗin tayi ta shiga neman wurin da zata sa kayan, a nan tasamu wata shopping bag, ƴar jakar nan ta siyayya, komai cikin sauƙi take ganin sa,
Komawa cikin toilet ɗin tayi ta shiga jidar kaya tana zurawa aciki, Sam bata tunanin cewa sata take yi ita ina gani take kamar ta zama ƴar gida in ta ɗauka halal ne.

A gajiye ya shigo cikin gidan jikinsa sanye da kayan kwallo riga da gajeran wando, yellow colour ba ƙaramin kyau sukayi masa ba, hannunsa riƙe da kwallo yana ɗan bugata a hannunsa, kafin ya rungumo ta a ƙirjinsa, cikin sauri ya haye upstair yana isa kofan ɗakinsa, yasa ƙafarsa ya harba door ɗin ta buɗe,
Saboda tsananin firgice sai da tasaki kayan dake rungume a ƙirjinta, zo kaga tashin hankali, daga cikin toilet ɗin take jin shigowarsa, tuni ido ido ya raina fata musamman da taji tabbas shine ɗin dai ya shigo, ana dara ga dare yayi 🙉

"Nashiga ukuna junaid ya dawo tafaru ta ƙare " ta faɗa ido luhu-luhu, tuni jikinta ya fara rawa, matsawa tayi jikin kofan tana leƙansa,
samun shi tayi yana cire takalmansa, ganin he's trying to takeoff his clothes,
Hakan yasa ta fargaba, koma wa tayi ciki tasa tafin hannunta tana bugun goshin ta, tuni ƴan matan hawaye sun bayyana, sintiri hawayen suka soma yi suna sauka a kumatunta, tashin hankalinta kada junaid ya ce zai cire kayansa saboda shi baisan da human being aciki ba,
Kuma tana da tabbacin cewa yadda ya dawo a gajiyen nan, wanka zai buƙaci ya fara yi, cikin tsananin tsoro ta furta "ae shikenan waman ƙadarallahu hakka ƙadrihi,"
wayyo Allah na there's no way out, ya Allah ka kawo min mafita, ni nasan alhakin satar dana zo yi masa ne Allah ya kamani, hannu ta ɗaga sama tana addu'a tana cewa Ya Allah bazan ƙara ba ya Allah kafi kowa sanin cewa ni ba 6arauniya bace wlh sharrin shaɗain ne da kuma zuciya 😥
Ashhhh ! a wani irin yanayi yayi wannan sautin yayin da yake cire rigarsa da alama something is hurting him may be he gets wound,
Wurgi yayi da rigar saman bedmatress ɗinsa, hannu yasa yana shafa gefen cikinsa wurin yayi jawur abunka da kalar madara, ciwo ne wurin amma is not much,
A gefen gadon ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,
Leƙo shi sehrish ta ƙarayi ganin sa zaune yasa taji sanyi aranta, zuba mishi na mazurin ta tayi tana kallonsa
A wani irin yanayi yake lumshe kyawawan idanuwnsa, teeth ɗinsa ya ɗansa yayi biting red lips ɗinsa, kai ka ce wanda ke cikin shauƙi ne,
hakan ba ƙaramin feelings ya sa sehrish ba, ita da ke leƙensa ta cikin toilet,
Mayar da kanta ciki tayi tana tunanin dabarar da zata yi masa ta samu ta fice, ranta ne ya bata cewa kawai ta fauze tayi kamar wanke toilet ɗin take yi tunda ita house maid ce tana da damar shiga ko'ina,
Murmushi tasaki tuna wannan dabarar, acikin zuciyarta ta ce ashe hakanan nake wahalar da kaina gaskiya kan kifi ne dani, bana gane komai cikin sauƙi
wurga idonta rayi kan kayan da ta zubar, ji tayi bazata iya barin shaving cream ɗin nan ba, koda zata mayar masa da sauran, matsawa tayi wurinsu da ta zubar da kayan, ta zuƙunna ta kwashi robar shaving cream ɗin da shaver guda ɗaya,
Cikin aljihunan wandon jikinta ta sanya su, amma robar tayi ɗan zumbuɗi tayi tayi amma taƙi idasa shiga haka tabarta,
Sauran ta tattara su ta mayar masa a cikin bathroom cabinet ɗin,
cikin sanɗa ta tura kofan ta fara zuwa kai tana leƙansa, ganin idonsa rufe ya tabbatar mata da cewa junaid fa bacci yayi awon gaba dashi don haka ta soma tafiya cikin sanɗa maimakon ta wuce ta fice cikin salama,
Amma hango jerin turarurrukansa da tayi agaban mirror yasa ta tsayawa, koma wa tayi a hankali ta cafko kwalbar turare ɗaya, ƙiris ya rage kwalbar ta faɗi kasa saboda ta kusa ta zame daga hannunta,
Wani irin bugun zuciya taji amma ganin ta same ta raɗau a hannunta ysa ta sauke ajiyar zuciya,
"na tsira" ta faɗa alokacin da ta samu ta fice cikin sa'a ,
Sam sehrish batayi tunanin cewa yaya Qarfin ƙamshin turaren yake ajikin mutun ba ! Kunsan turaren maza da ƙamshi,
cikin jin daɗi ta wuce bedroom ɗinta, jera su tayi agaban mirror ɗinsa, ran ta fal da farin ciki ganin itama yau ta fara jera abu a gaban mirror,
junaid
Bacci yayi na ɗan wani lokacin sai wuraren asr prayer ya farka, ƙarar shigowar message a wayarsa ne ya tayar da shi, a ɗan firgice ya tashi hannu yasa tare da shafa face ɗinsa yana sauke ajiyr zuciya,
Idonsa yakai kan well clock ɗin dake manne, hadaddiyar gaske ƙarfe 3:59 dai dai time haryaso ya goce masa,
Cikin kasala ya tashi kamar wanda ke shirin yin kuka, faɗawa cikin toilet yayi ya jagwalgwala wanka ya fito,
Closet ɗinsa ya bude riga da wando ya dauko, t-shirt ɗin ja wandon black colour,
Hannu ya kai ya dauki wayarsa dake gefen fillow ɗinsa, buɗe wayar ya yi tare da karawa a fuskarsa nan take security ɗin wayar ya buɗe,
buɗewa yayi ya fito daga room nasa, a natse yake tafiya yana daddana wayarsa message ɗin ya buɗe ya soma karantawa kamar haka
"Sister kwana biyu naji baki kira kin tambayi ya ya jikin mu ba, anyi mana aiki cikin nasara, naji sauƙi sosai husanna ma taji sauƙi sai dai hanyarzu akwai sauran mentel illness akanta, sunanki kawai take kira sehrish sehrish dan Allah ki kira mu muji voice ɗinki,"
tsayawa ya yi cike da tsananin mamakin ganin wannan saƙon a wayarsa a fili yace wacece kuma sehrish da husanna ! A wayata kuma !! me hakan yake nufi, wani namin amfani da wayata ne shin wai ma wanene wannan sehrish ɗin !!!
Kansa ya gama ɗaure wa, a hankalin ya idasa saukowa daga saman stair ɗin, ransa ne ya basa cewa kawai wasu ne sukayi kuskuren hada numbarsa, don haka ya share lamarin da cewa in ya samu lokaci zai kira number ɗin ya sanar dasu cewa its a wrong number, tunda yaji maganar rashin lafiya ce tana da mahimmanci kwara su son cewa basu sa number dai dai ba. 😳

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~



Page 27-28




Fitowa ta yi tana leƙensa, lalla6awa tayi ta ƙaraso gabansa kamar wata munafuka tace "barka da fitowa yaya Junaid," ɗagowa yayi tare da kallonta ya ce "zan fita masallaci before na dawo pls a shirya min abinci bazan iya jurewa ba cos am starving," dariya ce ta kusa kubce mata hannu tasa a bakinta, harara ya jefa mata "dariyar uban me ka ke?
hannun ta cire daga bakinta tare da cewa "dama....ran nan ka ce min baka iya cin abinci saboda tare da brothers ɗinka kke ce kun sa6a dole sai kun haɗu sannan kke ci atare shine...." tsayawa ta ɗan yi tana kallonsa

sakin baki yayi yana kallon wannan ɗan rainin hankalin ɗan aikin nasu, rai abace ya ce "kai !! NI tsaran wasanka ne ? raini ya fara shiga tsakanin mu ko !" ya ƙarasa maganar yana kallon ta,
Hankalin ta ba ƙaramin tashi tayi ba, bakin ta ya ja mata,
Saboda bacin rai muryarsa har rawa yake yi wurin kwalawa azmi kira,
Nan fa ta aza kai a saman ka tana faɗin "wayyo Allah na Sorry sir,"
duk a tunanin ta korarta zai sa ayi, jiki na rawa azmi ta fito baiwar Allah kana ganin ta kaga wadda bacci bai isheta ba,

Ƙaraso wa tayi tana faɗin "meya faru junaid kke kwalamin kira,"
Mayar da idonsa ya yi akanta ya ce "wannan mai aikin so nake nabasa punishment, cos he distains me ,
Ya ƙarasa maganar tare da kallon sehrish ya ce " kasan yadda ake tsallen kwaɗi ko," cikin tsoro ta girgiza masa kai alamar bata sani ba,
Jinjina kansa yayi tare da cewa "amma kasan yadda ake up and down,"
Zuru tayi da ido don batasan me ake nufi da up and down ba, juya wa tayi ta kalli azmi,

da ido azmi tayi mata alamar tace masa batasani ba,
Amma rashin fahimtar hakan yasa ta ce masa "eh na iya,"
cike da bada umarni ya ce "azmi inaso ki samun ido akansa, har nadawo daga masallaci nasame sa yana yi if not kowa zai gane kuransa,"
Yana gama faɗar hakan yasa kai ya fice,
Kallonta azmi tayi tana murmushi tace "oya start ae ke kika ce masa kin iya, ke kinsan menene up and down kuwa? mugun punishment ne mai wahalar gaske,"
murya na rawa tace" i don't know how to do it ,"
Dariya azmi tayi , tare da gyara tsayuwarta, ta some yin ƙasa da sama tana nuna mata yadda zata yi,
"Toh kin ga yadda zaki yi, maza ki fara kafin ya dawo sbd kowani lokaci zai iya faɗowa, ni zan koma ciki saboda haryanzu kaina ciwo ya ke min,"
tana gama faɗan haka ta shige ciki, zugudum sehrish tayi ganin ba kowa yasa ta lalla6a tasamu wuri saman 2 seater tazauna, daga taji motsi sai ta ɗan firgita in taga bakowa sai ta natsu,
zaman zuru tayi ga fargabar karya zo yasame ta zaune batayi abinda yace ba, bacci ne ya ziyarce da kuma dama kowa yasan bacci 6arawo ne, nan ta soma gyangyaɗi a hankaki yayi Wuuuf da ita,

Tsayawa yayi cike da mamaki yana kallon ikon Allah, mutumin da aka ba punishment ya shi baiyi ba, kuma yasamu wuri dirshen kamar ɗan masu gidan ya kwanta,
Jinjina kai junaid yayi wanda shigowarsa kenan, zuwa yayi inda tanƙamemiyar freezer ɗinsu take yasa hannu ya buɗe, robar ruwa ya dauko mai sanyin gaske har ya fara kankara,
Yana zuwa inda sehrish take, ta saki baki baiwar Allah sai sharar bacci take yi ga gashin bakin nan da take manna wa yamayar da ita wata yar cartoon guda,
Buɗe murfin robar yayin, kai tsare ya zazzage mata shi ajikinta,
Wani irin firgit tayi ta farka lokaci guda ta tashi zaune jin yadda ruwa mai sanyin gaske yayi mata dirar mikiya,
dogon numfashi taja tana sa hannayenta tana yarfo da ruwan dake zuba a fuskanta, idonta jawur ta ɗago ta kallesa,
faɗa yasamo yi mata" saboda raini in saka ka aiki kazo kasami wuri ka zauna kana bacci ko kai ga riƙeƙƙen ɗan bariki ko,"?
Saboda tsananin baƙin ciki fashe mashi tayi da kuka kamar jinjira, tama rasa me zata yi, me zatace masa
Ganin yadda tukur ɗin ke shesshekar kuka yasa yaji kamar baiyi adalci ba, kasancewar junaid nada matukar tausayi wani sa'in,
juyawa yayi ya mayar da robar ruwa, sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, har lokacin kuka take kamar ranta ze fita,
Muryarsa ce ta ratsa sa" Am sorry" ɗagowa tayi cikin mamaki tana kallansa bata ta6a tunanin zai iya bata hakuri ba,
Ci gaba da magana ya yi " ka gane am very simple man kaine ka cika sa ido,komai kaji sai kaja bakin ka kayi shiru karka sake mun haka !,"
Tsagaitawa tayi da kukan tace" kayi hkr bazan ƙaraba bazan ƙara ba insha Allah,"
yanayin yadda tayi maganar sai ya ji kamar muryar mace amma aduk lokacin da yaji hakan sai kawai yasa wa ransa cewa namiji ne saboda akwai waɗan da halittarsu ce hakan,
"Its ok now i need something to it, go get it for me, am waiting ,"!
ya faɗi hakan cikin nuna buƙata, ta shi tayi ta nufi kitchen tana mai tunanin me zata sama masa ya ci, babban tashin hankalin ta azmi bata jin daɗi hakan na nufin cewa yau ita ce zata haɗa masu dinner kenan, gashi bata iya irin girkinsu ba na ƴan gayu,
da wannan tunanin ta shiga kitchen ɗin, babu wani dafafen abinci sun cinye komai da safen nan, dole sai dai tayi preparing wani, cikin gaggawa cos he needs it immediately,
cikin sauri ta za masa taliya saboda ita ce abu mai saurin dafuwa, kayan miya ta ɗebo ta gyara su ta markaɗesu , ta haɗa da kayan kamshi duka, ta jagwal gwala masa sai gashi ta fara ƙamshi, murmushi tasaki "Allah sarki har miyau na ya gwada bari in zuba masa sai in rage saura nima inci,"
a cikin plate ta zuba masa ta haɗa masa da spork a ciki, lokacin da ta isa samun shi tayi yana daddana wayarsa,
Cikin girmamawa tace "na kammala gashi,"
ajiye phone ɗin yayi side ɗinsa sannan yasa hannu ya karba, a hankaki ya furta "shukran laka,"
maimakon ta tafi sai ta tsaya tana kallon yadda yake sargafo taliyar a cokali mai yatsun yana turawa bakinsa, da alama tayi masa daɗi,
Sai wani ɗan murmushi take saki, ita dae a rayuwarta tana so tayi abu aci, hakan yana mata daɗi axuciyarta expecially da ya kasance junaid ne ke ci 😘
. Bata gajiya da kallonsa batasan meyasa ba amma tana da tabbacin cewa ba so bane na soyayya kawai burge ta yake yi,
ganin mai aikin tsaye akansa yasa shi tsagaita wa da tura abincin abakinsa ya ce "lafiya ka tsare ni da ido"?
da sauri ta girgiza kai tare da juyawa ta koma kitchen, zuba taliyar tayi itama ta samu wuri a ɗaya daga cikin chairs ɗin dake zagaye da dining table wanda ke a kitchen, ta soma ci farat ɗaya zuciyarta ta tunano mata da wani abu nan take ta fashe da kuka mai cin rai , tura abincin kawai take yi amma ita kaɗai tasan me take ji acikin ranta,
Aduk lokacin da takai abu mai daɗi zata sa abakin ta, sai ta tuna cewa wani hali ƴan uwanta suke ciki, me suka ci ? Shin suna samun abunda zasuwa cikinsu
😥
Babban tashin hankalin ta, shin ya aikin da akayi masu asibiti ke tafiya, husanna taji sauƙi ? shin ta rayu ko ta mutu saboda doctor yace ba tabbas ta rayu,
Cire hannunta tayi daga plate ɗin abincin ta turasa gefe, tashiga matse kwalla,
Bata jinkirta ba har saida taji alamar shigowar mutun, cikin sauri ta shiga goge hawayenta don batasan wani ya gani balle ya tambayi dalilin zubarsu,
"Sehrish me kike yi a zaune, i think zanzo na same ki kin fara aikace aikacen fara girki,"
tashi tsaye tayi cikin sanyayyiyar muryarta tace " ae mun afwa aunty azmi,"
Hmmm azmi ta tace , kafin ta wuce ciki domin fiddo kayan da zasu fara aiki da su,

Lafiyayyen abinci aka girka masu, fatan doya da wake, sakwara da miyar egusi taji kayan ƙamshi ga naman ganda a ciki, farfesun iri biyu na kifi dana naman shanu,
Saboda rashin lafiyar azmi yasa suka girka abinci kaɗan, saboda a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login