Showing 81001 words to 84000 words out of 137891 words
Chapter 28 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
shiga ne? kin shanya ni ina ta faman jiran ki, da alama watan barin ki agidannan ya tsaya," 😡
tsohuwarce ta fadi tana murguda baki kamar wata yarinya,
Cikin sauri wadda aka kira da sunan saude ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da plate wanda naman kaza ne acikinsa jar suya
Karasowa tayi tana faɗin "dan Allah goggo ayimun afwa, wlh bata ida soyu ba ne shiyasa,'
hararar ta tayi tana yamutsa fuska tasa hannu ta kar6i plate din tana cewa "Last warning, in ki ka kara, zaki tattara kayanki ki koma can ƙauyenku aci gaba kiwon shanu baki ba ra6ar A.c ,"
Shiru saudatu tayi tana tamke fuska, ta tsani taji ance za'a maida ta ƙauyansu, gashi kullum tsohuwar cikin yi mata mita take bata gajiya,
hannu tasa ta ɗauki tsokar naman ta tusa abaki, tana tauna tana yamutsa fuska,
"Anya kuwa saude kinsa farin magi aciki kuwa," ta tambaya tana kallonta yayin da take lasar naki,
A ƙule saude tace "bansanya ba, babban likita ya hana,!
dagowa tayi baki asake tana kallonta "saudatu ! Rashin kunya ko? Ki kalli tsabar idona ki ce babban likita ya hana ! shiya haife ni koni na haife sa dazai hanani jin daɗin rayuwa!?
Cikin ƙunkuni saudatu tace "Ke ki ka haifesa, amma ae don lafiyarki yayi hakan....'
tunkan ta idasa magana, goggon ta jefe ta da ƙashin ciyar kaza a fuska,'
Hannu saudatu tasa ta shafa wurin da ta jife ta, kafin ta kalle ta tana zumbura mata baki,
"Ke ki kiyaye ni Allah ! wato ya daure maki gindi kina iya shegen da kika ga dama ko ? Cikin sauri saude ta dafe kai cikin jin kunya tace "dan Allah goggo wannan maganar ba daɗin ji Allah, gatsar ba sakayawaa,
Baki asake goggo tace "ba shakka, yau yarinya zatayi fiffike ta koma gidan ubanta,'
Kafin Saudatu ta bata amsa, sukaji dirar motoci a cikin gidan da jiniya,
Kallon juna su kayi atare, saudatu tace "goggo meke faruwa ne, ko kinyi da wani zai zo ne ? ni naji kamar jiniyar motar ƴan sanda,"
Murmushi goggo tasaki tare da ajiye plate ɗin kazarta, kasa tana cewa
"Kin manta muna da rundunar sojoji a family ɗin mu 😇 Shiyasa nake gargaɗinki kibi ni a hankali, kiyi mun biyayya ko kin gama da duniya lafiya, cikin zolaya tayi maganar, dariya saudatu tayi,
adai~dai lokacin marshal omar ya shigo wanda dirarsa kenan,
sanye yake cikin jeans da farar t shirt mai dogon hannu tabi shape din jikinsa, surar kirjinsa ta bayyana muraran, fuskarsa na sanye da face mask, ba karamin kyau yayi ba, koda yake dama jinin kyau ne su,
tun da ya shigo baki asake saudatu ke kallonsa kamar ranar ta fara ganinsa,
Cike da wannan tafiyar tasa ta nigogi majiya karfi yake tafiya,
Tsananin farin ciki yasa goggon katsina harba plate ɗin kazarta ya watse ƙasan carpet ba tare da ta sani ba, kamar karamar yarinya haka ta watsa a guje ta rungumesa tana fadin "Wata sabon gani, mafarki nake ko gaske, Oh ni Omar,
Sakin shi tayi tana ta faman zabga murmushin jin daɗi, a hankali yasa hannu ya ɗan zame facemask ɗinsa yana kallonsa fuskarsa da fara'a ya ce "Goggo na har ynz dama baki daina wannan tsalle tsallen ba sai kin 6alla ƙafa ?
dariya tayi ta ruko hannusa tana fadin" wlh duk cikin farin ciki ne Omar, ji nake kamar in zuba ruwa a ƙasa in sha,
zama su kayi atare, sai lokacin saudatu ta samu damar gaishe shi " sannu da zuwa ƴa'ƴa Omar,'
"yawwa" ya bata amsa without looking at her, idonsa na akan goggonsa wadda ke ta faman binsa da kallo, hannu tasa ta shafa fuskarsa tana faɗin "Oh ni Omar haka ka zama, tukunna ma dai yaushe ku kazo daga U.s ɗin? kuma ya naganka kai kaɗai ina sauran suke ? tare da matarka ku ka zo ? ta haihu yanzu ko ?
Zuru yayi yana kallonta, aransa yace mai hali bai ta6a canzawa in banda zafin ɗumi irin na goggon katsina Yaushe yayi budurwar balle akaiga maganar aure da ƴa'ƴa?
ajiyar zuciya ya saki kafin yace "wacce amsa ki ke so na fara baki gaggona ?
Murmushi ta dan saki tare da cewa "ni ba wannan ba ma, Oh ni Omar wai kai ne ka zama haka ! kazama kamar dodo, Ka tara ƙirar karfi ba mata, kyau ace akwai inda za'a rinƙa sauke nauyin nan,...
Cikin jin kunya saudatu dake tsaye ta juya tayi cikin kitchen, domin kawo masa abun sha,
dafe kansa yayi tare da cewa "Omg !! goggo shiyasa ba kowa ke son zuwa wurinki ba, sbd in ki ka fara zuba kamar radio mai jini,' ya faɗi yana yamutsa fuska saboda baisan hayaniya arayuwarsa,
Hannu tasa tare da rufe bakinta tace "nayi shiru tom, ka da kace zaka daina zuwa wurina bari nayi shiru,
dawowa saudatu tayi hannunta rike da tray da ta zuba masa snacks da abunsha a cup, ajiyewa tayi agabansa,
hannu yakai ya dauki lemun domin ya kur6a, muryar goggon ce ta katse sa da cewa "dole nayi magana Omar, Oh ni Jibi yadda ka tara nonuwa a kirjinka sai kace dai za'a sa akwatin nono na mata a suturta......"
ae baisan lkcn da ya ajiye cup din ba ya miƙe tare da cewa "Ni zan tafi, kunyartar ta isa haka,"
saude dake a wurin tuni ta sulale ta gudu,sbd tayu matukar kunya ta, da sakin layin da goggon take masa,
Cikin lallami ta tashi itama tsayen tana cewa "haba ɗan shalelena, duk fa cikin murnar ganin ka ne,'
ta6e bakinsa yayi tare da cewa " no goggo tafiya zanyi, dama bani kadai nazo ba akwai yara na dake a waje suna jira na,"
Sam bataji daɗi ba, jin zai tafi tayi tunanin zai tsaya ya kwanar mata ne, itama tasan cewa surutunta ne ya ja mata, sarai tasan cewa bayason ɗumi haka,
Cikin sanyin murya goggo tace "toh baza ka tsaya ku gaisa da Babban likita ba ? kusan kullum sai yayi mgnr yaushe zaku zo daga America,
marshal Omar ya ce " yana ina ne ? Ko yana on duty ne ? goggo tace "Eh tun da safe ya tafi asibiti aiki,'
"Okey may be na leƙa masa bfr na wuce kaduna gobe da safe, '
"Yanzu omari tafiya zakayi daga zuwa,' ? tayi mgnr kamar zata yi kuka,
"Calm down your mind gaggo na, Captain adam da su mg Osman na nan zuwa, duk zagi gansu, nima zan dawo insha Allah, ynz akwai mahimmin aiki a gabana ne shiyasa,"
Jin sunan waɗanda zasu zo dayawa yasa ta washe daga ɗaure fuskar da tayi,
"Aiko da naji daɗi, in suka zo, zan masa a ayi musu fura, in suka zo suyi ta sha,"
Murmushi Omar yasaki ya fice yana faɗin "Zaki ga saƙona gaggo,"
Cikin jin daɗi tace "ina jira ɗan Albarka, ta ɗaga murya tana ci gaba da cewa "Allah ya haɗa ka da kaddarar ka acikin garin nan,'
sarai yaji ta fita yayi yana ɗan murmushi, yarasa dalilin dayasa, tsofaffin nan suke disturbing ɗinsu akan aure aure 😏
tunkan ya ƙarasa inda motocinsu su ke, da sauri wani sergeant ya buɗe masa mota ya shiga A jere motocinsu suka fita,
sai da ya tafi sannan saude ta fito tana cewa "wlh goggo sam bakya kyauta, shikenan daga tsufa ya fara kama mutun sai yaita ƴan sambatu yana sakin layi ynx abunda ki kayiwa ƴaƴa omar kin kyauta "?
ta tambaya tana kallon goggon wadda ke zaune saman kujera, baki asake take kallon sauden,
Jinjina kai tayi tare da cewa "ba shakka raini ya shiga tsakanin mu, gobe goben nan zaki koma ƙyauyenku ni nagaji dama liƙamin ke akayi aka manna bin ba don naso ba,' ta faɗi tana hararar ta,
Riƙe ƙugu saude tayi tare da cewa "to kisa ni ba inda zani je, koma tafiyar zanyi ƙafa ta ƙafar Babban likita ,'
"Saboda ke ki ka haife shi"? goggon ta tambaya,
Saude tace "bani na haifeshi ba, amma zaki ga yadda soyayya ke aiki......' bata idasa ba goggo tabi ta aguje itama ta tashige ciki da sauri, dama sun saba,
_Husannsa & Jahad_
A 6angaren husanna dake kwance rai hannun Allah magashiyan, ba'a son inda kanta ya ke ba,
Likito ci sun gaza gane, menene matslarta, iya abunda suka sani tana da mental ilness sai asthma, bayan nan binciken su bai nuna masu komai ba,
Rashin kwanciyar hankali ne ya hana, jahad ta yi masu bayanin cewa tana da Iska, sam ta manta da wannan sbd ba natsuwa kullum cikin kuka take asibitin,
Atare suka shigo inda aka kwantar da ita, suna tattauna wa akan ciwonta, su biyu ne professional doctor ne wanda su ke kira da Babban likita (big doctor) tare da wani jami'in ɗan sanda, dr ɗin na koƙarin yi masa bayani akan yarinyar,
Sam basu lura da husanna wadda ke kwance, magashiyan sai faman fisge fisge take tana nishi, hannu tasa ta cire roban oxygen ɗin da suka sa mata, tari wurgi da shi, tana wani irin huci kamar zakanya, idanunta sun juye sun canza launi,
A haukace ta ƴunkura da ƙwarin gaske takai hannu ta zare bingidar dake soke ƙugun police man ɗin da suke magana da big doctor ba tare da saninsa ba,
sai da ta zare sannan likitan ya lura cikin tashin hankali yace "Innalallahi wa'inna ilahirrraji'un !!"
A firgice ɗan sandan ya shafa waist ɗinsa yaji ba gun ɗinsa, gaba ɗaya hankalinsu ya tashi ganin tayi sai ta su da ita, kuma ta rike maɗalllin, nan fa ido ya raina fata, lallashin ta suka shiga yi don ta ajiye bindigar amma ina, sai ma ta fisgi hanya da gudun gaske tana harba bindigar a duk inda ta samu ji ka ke daram!! Daram !! , zo ka ga yanda mutane ke gudu ba likitocin ba, ba nurses ɗin ba hatta marasa lafiyan dake kwance magashiyan neman hanyar gudu wa su ke yi, a tunanin su, ƴan bindiga daɗi ne suka kawo masu ziyara ta musamman 😂🤣😂
Jama'a gawa na tsoran rami, 😂🤣
Husanna fa ta haukace, misbehaving take yi kamar ƴar mahaukaciya,
Gashi dama ba hijabi ajikinta sun cire mata, da za'a kwantar da ita,
Wannan mahaukacin gashin, nata mai yawan gaske da tsayi ya bazo mata ta ko'ina har gaban fuskanta, tana gudu yana kara rufe mata ido ko gabanta ma bata kallo,
"Jama'a kowa ya watse, kowa ya gudu yayi takansa an samu matsala, mahaukaci ta gudo daga psychiatric hannunta riƙe da bindiga kowa yayi takansa," 😆
Wani copral ne ke bada wannan annoucement ɗin, don asamu kowa ya kare kansa,
Bin ta police men ɗin suke da gudu suna rokon tabasu bindigar nan, amma ina Husanna tayi nisan da bata jin kira,
Jahad ta gama rikicewa ganin bala'in da husanna ke ƙoƙarin ja, musu a guje itama take binta tana faɗin "Husanna dan Allah ki daina, kada ki kashe wani kija mana bala'i, dan Allah ki basu bindigarsu, innalallahi wa'inna ilaihirraji'un
Asibiti fa ya harmutse, kowa gudu yake yi , gashi ita husannar sai yawo take musu da hankali sai zagaye cikin asibitin suke, duk inda tabi mutane sai su watse, sai ihu ake ana zabga salati kai ka ce zombies ne suka bayyana,
Ƴan sandar sun fusata sosai ransu yayi mugun 6aci, kiris ya rage su harbe ta gudun kada tasa ayi asarar rayu ka, sbd ko'ina tasamu harbi take yi,
Abunda basu sani ba wannan ihun da ake yi shi ke ƙara haukatar da ita, bata cika son ƙara ba,
Sannan ita kanta husannar a tsorace take sbd police ɗin dake bin ta,
Tana cikin gudun nan hankalin ta atashe , gudu take amma tana waiwayon su cike da tsoronsu, cikin rashin sani kwatsam taji ta faɗa ajikin mutun,
Gam ta faɗa a faffaɗan ƙirjinsa, ta ƙankamesa, ta rungumosa sosai, a tsananin tsorace,
Nan take komai ya dakata, ji ka ke tsit kamar mutuwa ta gifta, babu mai kwakkwaran motsi acikinsu,
Gaba ɗaya duk suna tsaitsaye likitocin da nurses ɗin da wasu daga cikin marasa lpy masu ƙwarin jiki da ƴan dubiya, ga ƴan sanda , kowa dai
Saukar ajiyar zuciya kowa yake saki, ita kam jahad ta tsorata, da ganin mutumin da Husanna ta faɗama wa, duk da yasa face mask a fuskanshi, amma ƙirar karfin nan tasa, dole tasa hankali tashi,
Tsoranta karya ce zai hukunta Husanna da ta faɗa masa bagatatan,
A tare zuciyoyinsu ke bugawa, bugu bana wasa ba, ta kwanta luf ajikinsa, wato wata irin ni'ima ce atattare dashi wadda tasanya husanna dawo wa cikin hayyacinta lokaci guda, sam tagaza tashi daga jikinsa, ƙamshin turarensa ya gama kashe mata dukkan wani ƙwari na jikinta, 😌
Sai faman ajiyar zuciya take saki, hannunta ta ƙarasawa ta zagaye waist ɗinsa so tightly,
Ganin hakan yasa Soja dake bayansa mai riƙe da mukamin major, yasa hannu ya zare gun ɗin dake hannunta , saboda ta zagayo da hannun nata a ƙugunsa ga bindigar a fili,
_NOT EDITED_
Keep sharing everywhere🫶 ❤️ Alhamdulillah ynx sai monday
*BossLady* 💋*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🌹🌹🌹Romantic Love story🌹🌹🌹*
Writer *HAFSAT BATURE* 💋
~Boss Lady~💋💋💋
*frm today, na dakata da rubutu har sai naji sauƙi insha Allah zan ci gaba, seriously bani lpy so i won't kill my self* 😔👍
~page 71 to 72~ ✨
✨✨✨✨✨✨✨✨
Not edited, 👏
At same time heart ɗinsu ke beating da karfi, ya jima yana mamakin wata zararriya ce wannan ta faɗo masa a ƙirjinsa haka, this is d first time da mace ta faɗa masa a jikinsa, wadda ba muharramarsa ba, babban abunda ya ɗaure masa kai yadda yarinyar ta ƙanƙamesa bama Alamar zata sake shi, yana jin duk wani moving ɗinta ajikinsa, hatta numfashi ta dake fita cikin sauri sauri, kamar jinjira haka ta kwanta masa luf tana sauke ajiyar zuciya,
Mutanen dake wurin kowa yayi zuru yana kallon ikon Allah, wasu kam sai godiya suke wa Allah daya kawo masu sauƙi, har aka amshe gun ɗin dake hands ɗinta,
Jahad kam wadda ke cikin matsanancin tashin hankali, ganin bala'en da hosana ke ƙoƙarin ja musu, cikin yanayi na firgici ta ƙarasa inda hosana ke jikin bawan Allahn nan ta ruƙo hannunta da ƙarfi ta fisge ta daga jikinsa tana cewa "Dan Allah kayi Haƙuri bawan Allah, ba da sanin ta tayi hakan ba, she did it unintentionally, tana da ta6in hankali ne.....' muryar na rawa Jahad ke kora masa bayani,
Har time ɗim bai cire face mask ɗinsa ba, kuma bai janye idonsa daga na Yarinyar ba,
"Ki rabu dani !!!!" honasa ta faɗi tare da cire hannunta daga na Jahad ta matsa wurin mutumin nan, da ta faɗa mawa ta sa hannunta cikin nasa ta riƙe kam tana kallonsa cikin muryar kuka tace "dan Allah ka rabamu da waɗannan masu baƙaƙen kayan wlh sun takurawa rayuwarmu, duk inda mu ke bin mu suke yi, wlh ba mu bane muka kashe ta ba, mun faɗa musu sunki yarda, ni dai kace su rabu ni in ba haka wlh zuciya ta bugawa zatayi na mutu kowa ya huta.....'
"Hosana !!! Ba ki da hankali ne !! Kinsan wanene shi ki !! meyasa ki ke tona mana asiri ne agaban mutane," jahad ce tayi maganar ranta a 6ace ta janyo hosanar da karfin gaske ta dawo gefenta,
Su dae mutanen dake tsaye tare da police ɗin sun zuba ido suna sauraron su,
Rai a 6ace hosana ta sake fisge hannunta daga na Jahad cikin ƙunar rai tace "ki rabu dani, ki ƙyale ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !! Laifin me muka aikata, babu mai ƙaunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,' tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan idanuwanta tace "Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waɗannan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses ɗin dake wurin) kuma bana son waɗannan masu bakaken kayan," ta faɗi tana nuna ƴan sandan dake tsaye baki asake suna kallonta,
kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan)
Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men ɗin dake tsaye a wurin yace "wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!"? Ya tambaya yana kallonsa,
Rai a6ace wani inspector yace "kaga malam ka iya bakinka, mu jami'an ƴan sanda ne munsan me muke..." tunkan ya ƙarasa major ɗin dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace "Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!"?
"maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke," wani inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana,
Itakam ƙara kanƙameshi take yi, gaba ɗaya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi,
"Laifin me suka aikata"? Ya tambaya yana kallon ƴan sandar,
Wannan copral ɗin ne yayi saurin cewa "ana suspecting ɗinsu da kisan wata tsohuwa wadda take riƙonsu,"
Shiru ya ɗanyi tare da jinjina kai, kafin yace "Cancel the case (akashe case ɗin)"
ɗagowa su kayi jami'an ƴan sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector ɗin yace "malam wai wanene kai !! dame kake taƙama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haɗa dakai mu tafi police station.....'
Jikin major ɗin dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa," Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka ƙaramin ƙwaro ko kuma nayi ƙasa ƙasa daku a wurin nan....' cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa "i did not allow u to talk again, last warn,'
Shuru major ɗin yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa ƴan sandar bindigarsu ƙasa,
Matsawa Inspector ɗin yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa "karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roƙe ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je,"
Mamaki ne ya rufe ƴan sandan,