Showing 6001 words to 9000 words out of 137891 words

Chapter 3 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete

yarje mata sauran shirin yarda abun zai kasance ,
Mayar da idon ta kan larai tayi tace "To ynx ta ina zamu fara "? Larai tace "ae magana ta kare kawai mu da muke da Professional makeup artist a hannu ko kin manta da Mariiiya ? murmushi hajajju tasaki tare da cewa " ae Mareeya karshe ce ! Indai wurin canzawa mutun kamanni ne insha Allah gobe zan yi inviting din ta kuma a gobe za'a kammala komai don ya ce mun Jibi suke son mai aikin ta je ,"
Har larai ta bude baki zatayi magana ta jiyo muryar yaran nan dake cikin Kitchen wadanda take koyama aiki , suna kokoyi muryar d'aya daga cikinsu taji tana cewa "Aunty larai gatanan xata wanke gas cooker da ruwa ," da sauri ta mike ta nufi hanyar kitchen din tana cewa "Allah ya wadaran naka ya lalace har waning nayi muku kada ku taba komai amma saboda kan kifi gare ku baku gane komai salon kujama mutane ko !?
Hajajju tace "ke ma da laifinki akan me zaki baro min su a kitchen salon suyi mun barna ," mayar da idon ta tayi kan Sehrish "ki je ki huta time din sallah ma yayi nima bari na tashi ,"
Ta shi tayi ta shiga ciki , wanka tayi ta dauro alwala , ta fito ta shimfida prayer mat tayi sallah , kamar yarda ta sama kullum sai ta daga hannayenta tayi sama da 30mins tana rokon Allah cikin harshen larabci take jero addu'oin ta da bukatanta da damuwarta tana neman Allah ya yaye mata su ,
Bayan tagama ta tube hijabin ta ajiye , sannan ta hau saman bed ta kwanta dama jiya bata samu isasshen bacci ba , don haka lokaci guda bacci ya kwashe ta , tana cikin bacci y'an matan nan suka shigo , sai faman fadin wash Allah suke , koda sukayi arba da ita kwance ta baje gashi ta cire hijabin kan ba head tie, nan fa suka fara santin gashin kanta , ita dae bata son meke wakana ba tadai ji sama sama ana ja mata gashin kai ,
Zama sukayi kamar sun sami television sukai ta kallonta , ba karamin lalata sukayi ma kanta ba duk sun cukuikuye mata gashi yar kalaban nan sun warware mata ita , sun mai da karamar mahaukaciya ,
Nauyin bacci ne ya hana ta farka amma tabbas taji ana shafa mata kai kasa kasa ,
Sai da ana kiran sallan isha sannan ta farka , mika tayi tare da yin hamma , time din sun fita daga cikin bedroom zuciya sauko da legs dinta tayi kasan tiles din tana sauke ajiyar zuciya , kafin ta mike ta shiga toilet , tana cikin yin alwala tayi shafuwan kai ta shafo gashin kan ta mamaki ne ya kamata jin ba kitson dake kanta da sauri ta idasa alwalar ta je gaban mirror ita kanta sai da ta firgita da ganin yadda suka susuce mata gashinta , amma ba wannan bace damuwarta , zullumin kada husanna ta mutu da kuma aikin da zata fara ,
Zama taci gaba da yi a bedroom din , tana tunene tunane , ga yunwa tana ji amma takasa fita ta nema ,
Turo kofan sukayi suka shigo hannunsu dauke da tray abincin aka zuba musu shinkafa da miya ne sun cinye sun rage mata d'an kadan, ajiye mata sukayi suna dariya suka fice , abunda basu sani ba ita kallon Shashashu take masu ,
Bin a bincin tayi da kallon ba don tana jin yunwa ba da bazata ci Ba don sun jagula shi, haka ta zauna ta dinga turawa a baki kamar zatayi kuka , har dare yayi tana zullum abu daya kuma dashi ta kwana,
.......................................ABBAN SOJOJI
.......................Story by MrsBature
..................Part 1

In the morning
Around 10:30am makeup artist dinan ta iso gidan a time din duk sun hallara a falon hajjaju , bayan sun gama gaisawa , ma'reea ta bukaci ganin Sehrish , kwala mata kira hajajju tayi fitow tayi da sauri ta iso inda suke , bin ta da kallo mareeya tayi frm head to toe , sannan tace "Wannan ae mai sauki ne , naga tana da tsayi jiki ne dai babu sosai , abunda za'ae kayan maza za'a samo riga da wando oversize saboda su kara mata girma , sannan wadannan abubuwan , tayi magana tana nuna kirjinta da hannunta " dole a matse su don naga suna da girma ssae tubarkalla , " cikin jin kunya rishi ta dukar da kanta kasa , murmushi larai da hajajju sukayi , su kuwa y'an matan nan dake baje a kasan carpet dama basu da burki washe baki suka shiga yi wato anzo dai dai inda suke so ,
Hajajju tace "ynx me za'a sa a yi tighting dinsu "? Ma'reeya tace "mai sauki ne akwai wani abu da muke amfani dashi na matse tumbi shima zai iya yi ," hankalin rishi ba karamin tashi yayi ba har bata son lokacin da tayi subul da baka ba tace "in suka bace fa ya zanyi ,"? gaba dayansu suka kwashe da dariya mareeya tace "wato kada su bace a rasa nayiwa miji gayu ko ," cikin jin kunya ta dukar da kai , larai tace " dagaskiyar ta fa nono ae yana daya dagacin abunda ke kayatarda maza in suka bace ae ba magana ," ta karasa magana tana dariya , duk kunya ta gama kamata,
Ma'reeya ta ci gaba da magana "Sannan naga kamar tana da tsayin gashi ko,"? hajajju tace "Sehrish cire hijabin mana tagani , hannu tasa ta cire hijabin ta rungume a kirjinta ,
Hada baki sukayi wurin cewa "Tubarkalla masha Allah ," ma'reeya tace " yarinyar kamar balarabiya wurin tsawan gashi, gsky ni kishi nake da wannan gashin naki don haka dama dole indai zakiyi acting a matsayin namiji sai an datse miki shi ya koma guntu kamar nawa dai", nan fa hankalin ta ya tashi saboda tana bala'en son gashin nan nata , kamar zatayi kuka tace "don Allah hajajju karki bari ayimun aski ni inason gashi na ," takarasa maganar tana kallon hajjaju ,
Murmushi hajajju tayi tace " Sehrish ba Aski zata miki ba rage miki shi za'ae , ke da zaki neman kudi wake ta wani gashi , "
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta , larai tace "Gsky yarinyar nan da ace a matsayin mace zata je aikin nan tsaf zata auren mai gidan," hannu hajiya tasa abaki tace "ke ! tab y'ay'an sa kuwa da sun yi farfesu da namanta sojoji fa akace hmmm !! " dariya sukayi su duka , mareeya ta cigaba da bada bayani "Sannan dole a canza mata suna daga SEHRISH zuwa TUKUR ," a tare suka hada baki wirin cewa "Tukur kuma !"? murmushi ma'reeya tayi tare da jaddada masu maganarta ta " kawai kuwa ! sannan zan sa mata gashin baki irin na maza wanda ake fixing dinsa tare da eyebrows na kanti.

*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~


Page 7-8


Hajajju ta ce "Gashin baki dai. wannan dana nasani ? amma me amfanin hakan "? ma'reeya tace "Wannan wani salo ne kuma ina tabbatar miki da zaiyi aiki , duk da sehrish yarinya ce har a fuskarta amma indai nasa mata gashin baki dana jagira , zata kara suffanta da namiji zata koma kamar d'an daudu kuma dama in kin lura yanayin jikin y'an daudu basa da kiba sai tsayi ,"

Gaba daya sun amince da maganar ma'reeya , shiri na musamman akayi ma Sehrish a washe garin ranar cikin riga ta maza milk colour mai maballai a gaban rigar , sai wani burgujejan wando falazu da aka sama ta kamar kafar agwagwa haka yake pink colour , sun matse mata kirjinta , shafe ta koma kamar babu su , an datse dogon gashin kanta an barmata guntu irin nawa sai suka samu kallabi irin launin trouser din suka nannade mata shi akai kamar rawani , kallabin nada tsayi sai da yar jela ta zubo ta gefe , sai ta koma kamar d'an chali chali , ga gashin bakin da suka sanya mata , ya hau radau ya zauna , haka jagirar da suka samata , ta zauna cuf , duk wani abu na ado na jikin y'a mace babu shi a tattare da ita yanzu ,

Shin koya wannan wasan kwaikwayon zai kasance ? mezai faru ranar da suka gane cewa sehrish macace ba namiji ba ? Kowa yasan ya sojoji suke 👊.
Tunda a sussuba suka kama hanyar zuwa abuja , ita da hajjaju , zuciyarta sai dar dar take yi mata , a natse hajjaju ke driving dinsu , yayin da sehrish ke gefenta , idonta nakan glass din motar , tana kallon yadda suke wuce wurare daban daban , zahiri tana kallon bishiyoyin da suke giftawa na cikin dajijjikan da ke a side road kamar suna gudu da kafafuwansune , a hankali zuciyarta ta sauya mata akalar tunaninta izuwa rayuwarsu ta baya , nan take taji wasu zafafan hawaye na sintiri a idonta , zuciyarta ce ta soma yi mata magana "Sehrish kowane d'an adam yana da irin tasa kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa ne domin ya gwada imaninsu , kiyi kokari ki cinye wannan jarabawar , ki rungumi kaddara a duk yadda tazo miki dama can rutacce ne daga Allah dukkan tsanani yana tare da sauki ! Allah yana sane daku kuma shine gatanku ,"

Hannu tasa tana clearing face dinta saboda bata so hajjaju tagani , tunanin y'an uwanta shine yafi komai tayar mata da hankali , bata san wani gidan mahaukata bane zasu juri daukar nauyin haukan ta ba idan akace yau husanna tarasa ranta , haka abubuwa suka dinga zuwa mata aranta har suka isa garin abuja, wuraren karfe 2:30 na rana ,

Wannan ne karo na farko da ta fara yin tafiya mai nisa irin wannan ,

tunda suka shiga take kallon manya manyen gine gine , har suka iso gidan da zasu wato gidan Abban sojoji , sehrish ta razana da ganin katafaren ginin mai matukar girman gaske da daukar hankali , irin gidan da ta saba gani a cikin mafarki,

Lokaci da idonta suka sauka kan Narka narkan sojojin dake tsare da babban gate din gidan sai da taji gabanta ya fadi rass , bakake ne wulik dasu sanye cikin uniform dinsu , ga bindigu rike a hannunsu , ga wasu guns din soke a west dinsu ,

Wani irin miyau ta hadiye ganin an tsaida motarsu , nan take taji zufa na gangaro mata ta cikin sumar kanta , guda biyu ne suka karaso inda motar tasu take , d'aya ne yasa hannu yayi knocking , hajjaju ta zuge glass din , ita kanta a tsorace take cikin en ena tace "barka dai sannu ku da aiki ," amsa yayi da "yawwa muna bukatar sanin daga ina kke kuma wurin wa kka zo "?

Da sauri hajjau ta dauko wayarta cikin yar purse dinta ta shiga neman number abban, yatsun hannunta sai kakarwa suke , kira d'aya tayi masa ya daga , bayan sun gaisa ta sanar masa da abunda ke faruwa, ya umarce ta da ta basu wayar , mika musu tayi daya daga cikinsu yasa hannu ya karba tare da karawa a kunnansa , juyawa hajjaju tayi tana kallon sehrish wadda tuni ta ta gama tsuma , ta nannade wuri d'aya ta matse jikinta , idon nan sunyi furi furi kamar wadda tayima sarki karya , muryar sojan taji yana cewa "take your phone , u got permission to go in , but firstly we must check the car ," kallon sehrish tayi tare da cewa " mu fita zasu bincika motar ," bude mota sehrish tayi ta fita , itama hajjajun ta fito , suka tsaya suna jiran su gama binciken nasu ,

Matsawa Sehrish tayi kusa da hajiyar tayi kasa kasa da murya tace "hajiya amma nan barrack din sojoji ne ko "? cikin rashin natsuwa hajjaju tace " A'a gida ne na sojoji dae not a barrack ni bana cikin kwanciyar hankalin wadannan sojojin sun firgitani , sai kace wasu masu safarar miyagun kwayoyi za'a tsare mu ! that's why ban cika son zuwa gidannan ba ! ," takarasa maganar tana yatsina fuska ,

Jikin sehrish ya gama yin sanyi , bin jikinta tayi da kallo tasha kayan maza , ga uban burgujejan wandon da tasa kamar zata tashi sama, kara kankame jakar dake hannunta tayi wacce ke kumshe da y'an kayan da hajjaju ta bata kyauta ,

Hatta purse din hajjaju sai da suka bincika , zuciyar sehrish sai bugawa takeyi tunanin ta masu gadi sun kasance haka da ban tsoro ina ga y'ay'an gidan da taji ance they're all soldiers 😒

Muryar sojancce ta ratsa kunnanta "lemme see your bag "! cikin sauri ta mika mar jakan , zazzago kayan ciki yayi kasa yana duddubawa , trousers ne da riguna na maza , da hijabai da ta kudundunesu saboda sallah , bayan ya gama checking dinsu ya dago ya zuba mata ido yana kallonta , nan take taji fitsari ya cika mata mararta , sunnar da kanta tayi kasa , jikinta na rawa , Ji tayi yasa hannunsa ya dankwashi kanta yana cewa "mara kunya kana namiji baka iyasa Cap akan ka , kai ga d'an daudu ko ? sai dai kasa abu na mata ka nannade kai kamar wani limamin masallaci ",
Karasa maganar yyi tare da wurga mata jakar , sannan ya juya ya tafi , hannu tasa ta dafe wurin don taji zafin rankwashinta da yayi mata wannan gabjejan hannun nasa , dole ita ta zukunna ta kwashe kayanta daya zubar a kasa ,

A karshe dai Sun sami shiga ciki , a jiyar zuciya Sehrish tasaki , time dinda motar tasu ta wuce babban gate din ta shantalelen titin da zai kai ka can cikin gidan ,

A hankali take bin ko ina da kallo ta cikin glass din motan , tana kara jaddada haduwar ginin , taga wurare daban daban masu ban sha'awa , sai ta dinga tunanin cewa kodai tabar nigeria ne domin daga inda kasa kafarka cikin gidan kamar ka fita daga 9ja ne 😔

ihu da sowar da taji ne yasa takai idonta wurin , y'an matasan samari ne kyawawan gaske suke wasan football , acikin playing field n gdn , gwanin burgewa tabisu da kallo har sai da suka wuce su ,

A wurin da aka ware na parking space , hajjaju ta tsaida motarsu , wurin cike yake da motocinsu Na gayu ga kuma jibjibgan motocin irin na sojojin man

Waigawa hajjau tayi ta kalle ta tace "sehrish ki natsu dan Allah in mun shiga kada ki jamun , kuma kada ki manta sunan ki tukur daga ynx ," cike da gamsuwa ta masa mata da "Toh"

Fitowa sukayi daga motan suka miki hanyar data zata sada ka da babban falon gidan , tuni sehrish ta raina kanta , tamkar karta taka kasan tiles din take ji saboda wani irin design ne mai daukar ido , duk yadda ka taka saiya bada sauti kwas kwas ,

Komai na cikin living room din mai tsadar gske ne , kana gani kasan bana nan bane , an kawata shi da expensive furnitures , wasu hamshan royal sofa ne aciki , set shida ne a jere , ko da ido ka kallesu kasan zasuyi laushi da dadin zama , duk yawansu basu cike falon ba saboda girmansa ya isa a gina madai madaici gida acikinsa,

Komai da ake bukata acikin falo akwaisa sai da ba tarkacen nan na hauka komai a natse ,

Bin ceiling din tayi da kallo ba irin rufin da tasaba gani bane , wannan na glass , acikinsa akwai light bulbs masu haske wurin ,

Hankalin hajjaju ba karamin kwanciya yayi ba ganin falon tsit ba kowai sai sanyin a.c dake ratsa sassan jikin mutun, dama zullumin ta ace wadannan sojojin na nan ,

Ruko hannun sehrish tayi wadda hankalinta ke kan twin stairs din da tagani wato tagwayen bene guda biyu wadanda zasu kai ka upstairs, tsantsararrun gaske ,

Sehrish tace "hajiya naji tsit ko ba kowa ne ? hajjaju tace "ina ga duk suna wurin aiki , mu samu wuri mu zauna mu jira wata'kil mai aikinsu na nan ,"

Suna kokarin zama suka ji takon takalmi daga left dinsu , karfaffar maca ce irin giantess dinnan , tana da hasken fata , jikinta na sanye da doguwar riga ta atampa har kasa ta kashe daurin d'an kwalinta , tana ganin hajjaju ce ta saki fara'a tana fadin "me nake gani kamar hajjaju makkatin "? murmushi hajjaju tasaki tare da cewa "kwarai kuwa nice AZUMI ashe kina ciki , nayi tunanin ba kowa ciki ne ,"

Karaso wa tayi inda hajjaju take tayi hugging dinta tana cewa " I really missed u alot hajjaju kin boye mana nayi expecting din bakya kasar ne ," sakin juna sukayi hajjaju tana dariya tace "Ina nan mana ina zani an gaya miki ynx barin kasar nan sauki ne yadda komai ke kara farashi , yar dubai dinnan danake zuwa kamar hauka ynx nadaina saboda rashin kudi ,"

Murmushi azmi tasaki , tare da nuna masu wurin zama tace "bismillah ku zauna bari na shiga na kawo muku abin sha , firar zata fi dadi idan kuka jika makoshinku ,
tana gama fadan hakan tajuya ta nufi hanyar da zata kai ka kitchen dinsu , zama sukayi a tare saman 3 seater , har lokacin sehrish na makale da yar jakarta a kirjinta , sai karewa falon kallo takeyi tana jinjina kyansa , wai itace zata rayu a cikin katafaren gidannan , wayyo dadi boye farin cikinta kawai take yi , ta wani bangaren kuwa hankalinta a tashe yake , saboda batasan ya rayuwarta zata kasance ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login