Showing 78001 words to 81000 words out of 137891 words
Chapter 27 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
kanal yusif kai, ganin yadda mai aikin nasu Ya tsayawa Babban yayan akai kamar sai lashe sa, duk da sun cewa shi abun kallo ne, dole akallesa,
"Miƙo mun mana,' kanal yusif ne yayi maganar don yayi saurin dakatar da mai aikin nasu daga kallon ƙurullan dayake wa Babban yayan nasu, kafin ya fusata,
Lokacin da mgnr kanal yusif ta dira a ears ɗinta, jiki na rawa tadawo hayyacin ta, tare da matsawa ta miƙa masa shima ya ɗauka sannan jiki a matse ta koma kitchen, har ta shiga cikin ƙamshin turarensa ne ke ɗawainiya da ita,
Sam tarasa sukuni, sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke, kamar wadda tasha gudu,
Muryar azmee ce ta katseta da cewa "tun da mun kammala, mu bari sai after magrib ayi arranging ɗinsu a dining,"
Sehrish ta amsa da "Toh aunty azmee,"
tana ganin lokacin da suka kammala firar tasu, su ka kuma fita atare,
........*Junaid*.........................
Da tunanin sehrish ya yini, kasancewar ya fita gidan wani friend ɗinsa daya jima shima bai lpy, yaje duba sa, a can ya yini yana ta jansa da fira, hakan yasa ya jima, bashi ya dawo gida ba sai wuraren magrib ya shigo da motarsa, zuciyarsa cike da son ganin sehrish ɗinsa, da murmushi ya shiga ciki, bakowa duk sun je sallah da alama,
Bedroom ɗinsa ya wuce, cikin sauri ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito, shirt yasanya tare da dogon wando, kullum ya kalli kansa a mirror sai ya furta wannan kalmar wato "Mallakin sehrish,"
(Sai naji dama ni yakewa tanadin kansa da ban bari yasha wahala ba, dama ƙopa a buɗe take musamman ga irinsu Junaid masu kyawun hali) 😅
Jin takon takalminsa yasa sehrish ɗagowa, wadda ke tsaye tana ta faman jera abincin a dining, ita ta riga azmee fitowa bayan sun gudanar da sallar la'asar, zuba mishi ido tayi atlease tayi kewarsa sosai don tun safe rabon da tasa shi a idonta,
Shima farin ciki ne ya dabaibayesa ganin muradin ransa, ƙarasawa yayi yaja kujera ya zauna yana kallonta,
Cikin sauri tace "me zan zuba maka,"
"duk abunda yayi miki," kai tsaya ya faɗa,
Jim sehrish tayi shiru ta tsaya da jeran da take yi, maimaita maganar da yayi yanzu acikin zuciyarta tayi wato daya ce "duk abunda yayi miki amaimakon yace duk abunda yayi maka tunda amatsayin namiji take,"
ɗan ɗagowa tayi ta saci kallansa, har ynx idonsa na akanta fuskarnan ɗauke da murmushi,
Jiki a sanyaye ta zaro plate haɗaɗɗiyar jallop din taliya ta zuba masa, tare da haɗa masa da Cokali aciki ta miƙa masa,
"Thanks" ya furta tare da soma cin abincin, ganin yana ɗiba da zafinta yasa tace "ka bi a hankali kana ka ƙone,"
ɗagowa yayi ya kalle ta da buɗen bakinsa sai cewa yayi "kada ki damu zan kula"
daram taji gabanta ya ƙara faɗuwa, yau junaid yasaki layi sai kiranta ya ke da sunan macen ta,
Jin ƙarar dirar motoci ya tabbatar mata da cewa sun dawo, nan da nan taji zuciyarta ta bada wani sound, saboda tasan hada mutumin ta aciki,
Shigowa su kayi atare suna ta faman fira, kamar ba'a tare suke ba,
fawan da khaleed ne suka fara shigo wa tare da su Irfan da jabeer banda su twins,
tayi tunanin shima zai shigo ne amma babu shi, haka abbansu ma, da kanal yusif,
kai tsaye suma suka wuce izuwa dining ɗin suka ja kujera kowa ya zauna,
"Sannun ku da dawowa" acewar junaid,
Su ka amsa su duka, cikin sauri sehrish ta shiga yin saving ɗinsu,
"Ina yaya Ayaan da Jahan su ke, banganku atare ba? Su basu dawo ba ne?
Junaid ne yayi wannan tambayar,
Fawan ne ya basu amsa da cewa "taya muma zamu sani? mun jima da rabuwa dasu, su sukansan inda suka je"
Jabeer yace "ko tsoro basa ji, babban yaya ya neme su, su basusan su kame kansu ba, kamar yadda mukayi,"
"Ka rabu da shaggun jiki magayi," acewar irfan,
~Hafsat bature~ ✍️
Keep sharing 😘*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
~🔥the father of soldiers🔥~
_💞Romantic Love story between Hosana& Marshal Omar💞_
*💋HAFSAT BATURE BOSS LADY💋*
*page 69&70* 💋
"Ka rabu da shaggun jiki magayi," acewar irfan,
haka su kayi ta fira suna zuba abinci acikinsu,
Bayan sun kammala sehrish ta kakkwashe dishes ɗin da sauransu duka tayi kitchen dasu, har time ɗin azmee bata fito ba har sai da ta kammala wanke komai da su kayi amfani dashi sannan tashigo agajiye tana faɗin"kin ji shiru ko wlh bacci ne yayi awon gaba dani shiyasa ban fito ba,
"Babu komai aunty azmee kwarama da kika huta sbd kina aikatuwa ssae,"
Azmee tace" hmmmm nasaba ne, bana gajiya da aiki,
shiru su ka ɗayin kafin rishi ta kuma cewa "Su babban yaya basu shigo ba, shi a part ɗinsa za'a kai masa abincinsa ko anan down ?
murmushi azmee tayi tace " a can ake kai masa amma in yakasance dinner ne, wani time ɗin kuwa anan su ke haɗuwa suci gaba ɗaya, ke zaki kaimasa ?
"Eh zan kai masa,' cikin zumuɗi sehrish ta bata amsa,
"Shikenan amma akwai wani abu da zan faɗa miki u ave to know it,"
Sehrish ta ɗan yi jim kafin tace "menene shi"?.
"Babban yaya fa, baya son kallo sai fa kin kiyaye, because in ana kallonsa yana ji ajikinsa, sannan in ya tambayi abu ko menene kawai ki ce akwai, karki kuskura ya ce yana buƙatar wani abu akawo masa ki ce bamu dashi, ya tsani wannan ki kiyaye ! Sannan baisan kwaratsi ko kaɗan, sannan shi mutun ne mai tsaftar gaske, ko da gigin wasa kada ki kuskura ki bar abun ƙazanta a part ɗinsa ko min ƙanƙantarsa ko da ajikin ki ne, ke ma ki ƙara tsaftarki abisa wadda ki ke yi don daga yanzu ke ce zaki rinƙa kula da part ɗinsa,"
Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, jin cewa itace zata rinƙa kula da part ɗinsa, koba komai zasu samu kusanci da juna, 😇
Azmee ta ci gaba cewa "and then he doesnt repeat words in yayi magana, dole yayi magana aji farat ɗaya, sannan in yana bacci ba'a tashin shi, don naushi ya ke kaiwa bana wasa ba......'
Katse ta sehrish tayi da cewa "In time ɗin sallah ne fa? Shima ba'a tashin sa? ta tambaya tana kallon azmeen wadda ke daga tsaye,
Azmee tace "Abun ajinin sa ya ke ! muddin lokacin sallah yayi dakansa ya ke farkawa, sometimes kuma alarm ke tashinsa,
Jinjina kai sehrish tayi aranta tace"akwai matsala, Anya kuwa zan iya ? ta tambayi kanta,
Muryar azmee ce ta dawo da ita "zaki iya mana, matukar ki kasa natsuwa,"
Wata tambayar sehrish ta ƙara jefa mata,
"Aunty azmee wai babban yaya ɗan wrestling ne?
"Meyasa ki ka tambaya"?
sehrish tace "naga yanayin kirar jikinsa ne, wlh irin ta tasu ce,"
Hmmm azmee tace "shi da ya ke soja, sojan ma bana wasa ba, wanda ya amsa sunansa ae fiye da wresting ma yana yi,"
Murmushi sehrish tasaki Aranta tace "a shirye nake dana zama tamkar baiwarsa wurin yi masa biyayya sau da ƙafa, zan yi komai zan yi iya ƙware wata don naga yasan da zamana acikin gidan nan,
tayi maganar atime ɗin da take jera dishes din da takammala wanke wa, a cikin shelves ,
Atare da azmee suka idasa gyara kitchen ɗin su kai mopping da komai," daga bisa azmee ta wuce ɗakinta bayan ta sanarwa sehrish cewa idan sun dawo ta tabbatar da ta kai musu dinner ɗinsu,
Kasa bacci tayi burin ta, taji shigowar Babban yaya, domin takai masa dinner ɗinsa,
Murmushi kawai ya ke saki ynx ya yanke shawarar zai sanar wa sehrish da cewa yasan ita mace ce ba namiji, rungume ya ke da pillow a ƙirjinsa, night dress ne ajikinsa riga ce ta wuce guiwa, ya baje a saman gadon abban nasu yana jiran dawowarsa,
Ƴunkurawa yayi ya ɗan tashi zaune, yana tunanin taya zai sanar mata batare da ta tsorata ba, gyara murya yayi kamar yana agabanta ya ce "Sehrish na riga da nagane cewa ke maca ce, don haka ki kwantar da hankalinki, ni mai sauƙin kai ne bazan bari kowa yasani ba, i promise u, ni burina ki ɗauke ni tamkar ɗan uwanki na jininki, nima zan ɗauke ki amatsayin sister ɗita........'
dariya ya saki bayan yagama tsara wannan maganar, ajiyar zuciya ya saki tare da cewa haka yafi dacewa na tunkare ta, na sanar mata, Allah yasa kada ta razana, ko taƙi accepting ɗinsa as her brother,
Koma yayi tare da kwantawa idonsa na facing ceiling, fuskarnan da murmushi, har cikin ransa yarinyar ta kwanta masa luf~~~~~~~
Har bacci ya soma ɗaukarta, taji dirar motocinsi, cikin hanzari ta buɗe idonta, murmushin farin ciki tasaki, tashi tayi zaune tana jira su kammala shigowa kafin takai masu dinner ɗinsu, zuru tayi tana jiran shigowarsu, tana jiyo muryar abbansu da kanal yusif suna magana, amma bata jiyo tasa ba, tamasan baza taji tashi ba, saboda wata irin Voice ce dashi bata da sauti sosae, wata'ƙil sai ransa ya 6aci sannan Za'aji tsiwarsa,
Sai da ba da kusan 30 mins, sannan ta tashi cikin sauri ta gyara kanta, kafin ta wuce kitchen, sai da tafara kaiwa kanal yusif nashi a room ɗinsa, sannan ta wuce kaiwa Abbansu nashi shima,
Da sallama tashiga,atare da junaid suka amsa mata, cikin natsuwa ta shiga da tray ɗin mai ɗauke da food warmer tare da plates da spoon, sai jug da cup,
Kwance suke atare shigowarta yasa su tasowa zaune, cikin girmamawa tagaishe da abbansu, da sakin fuska ya amsa mata,
umarni ya bata da ta ajiye mashi anan ƙasa, ajiyewa tayi a hankali kafin ta tashi, suka haɗa ido da junaid ya kashe mata ido,
gabanta ne taji ya faɗi, sai ta ga abun kamar a dream, tafiya take zata bar room ɗin nasu, tasake juyawa tare da kallonsa, again ya sake kashe mata idon,
Cikin sauri ta fice tana mamakin wannan abun, amma tariga tasawa ranta cewa "Junaid yana da ta6in hankali," wasu ɗabi'un nasa yayi mata kama da na masu psychiatric disorder 😂
A ɗan kayataccen tray ta shirya mashi nasa, gabanta na faɗuwa ta tunkari upstairs apartment ɗinsa,
A buɗe tasamu kopan parlor ɗinsa, haske everywhere, bata gajiya da kallon hadaɗɗen parlor dinsa, sallama tayi taji shiru idasa shiga ciki tayi, asaman table ta ajiye masa shi, tsayawa tayi tana tunanin ya za'ae yasan ta an Kawo masa dinner ɗinsa, ran ta ne ya bata cewa ta shiga cikin bedroom ɗin nasa tayi informing nasa,
zuciyarta na ɗar ɗar ta tunkari cikin bedroom ɗin nasa, a hankali ta ɗanyi knocking door ɗinta, gabanta na faɗuwa,
shiru tayi tana jira abata umarning shiga, sexy Voice ɗinsa ce ta ratsa kunnanta da cewa "Come In"
Ajiyar zuciya sehrish tayi, tare da lumshe idonta, wani irin sanyi ne ni'imataccen gaske tare da ƙamshi su ka ziyarci hancin ta, a hankali ta idasa shiga ciki tana wurwur ga eyes ɗinsa can ta hangosa, daram taji wani irin bugu azuciyarta,
daga shi sai ɗan pant na maza ajikinta, yana tsaye at the front of the mirror Allah yaso ya juya mata baya, ba ita ya ke fuskanta ba, da taga tashin hankali,
Zuba wa surar jikin shi ido tayi cikin tsananin tsoro, dogo ne bana wasa ba, ga wannan ƙirar karfin tasa, idonta ta saukar akan zanen tattoo ɗinsa mai tsananin kyan gaske A farar fatarsa, bata ta6a lura dashi ba sai yau,
sam tarasa buɗe baki ta faɗi abunda ya kawota sbd kallon Kyakkyawar surar Babban yayanmu, 💞
hannayensa na cikin sumar kansa, yana shasshafa mata mai, sai salƙi take kafin ya ɗaure ta yasa ke ta izuwa bayansa, mayar da hannunsa yayi acikin jerin tsadaddun turarukansa dake agaban mirror ya ɗauko kwalbar turaren (Imperial Majesty) haɗaɗɗen turare mai wani irin fragrance mai ratsa sassan jiki, sai wane da wane ke mallakar irinsa,
Feshe jikinsa ya yi dashi ta ko'ina kafin ya mayar ya ajiye,
Ya jima yana mamakin wanene ya shigo masa bedroom ɗinsa haka, ya ba da permission ɗin a shigo amma shiru ba aƙara magana ba,
gyaran murya yayi alamar son jin bayani daga wurin wanda ya shigo masa ɗaki,
gyaran muryar da yayi ne ya dawo da ita cikin hayyacin ta, cikin sauri murya na rawa tace "am...dama...dinner....ne ....na kawo......yana a parlor,
"Its okay, wait 4 me there, am coming now," ya faɗi yana kai hannunsa saman bedmatress ɗinsa inda ya ajiye sleeping dress ɗinsa da zai sanya,
Jiki a mace sehrish ta fice, tana cizon lips ɗinta, haƙiƙa tagama narkuwa cikin tsananin ƙaunarsa 💘
A parlor dinsa ta tsaya tana jiransa kamar yadda ya umarta, hannunta na a chest ɗinta dafe da saitin Zuciyarta, surarsa kawai idonta ke tariyo mata, Murmushi kawai take saki *Big bro* ya gama tafiya da ita, 😍
Sam bata ji fitowarsa ba, sai da ya ƙaraso ya zagayo inda royal sofa ɗin suke sannan ta ankara,
Wani sabon kallon tabi shi dashi, sleeping dress ɗinsa sunyi matuƙar yi masa kyau, koda ya ke shine yayi musu kyau, irinsu Babban yaya sune suke wa kaya kyau, wato masu sa kyau tayo kyau ko bata da kyau 😇
Riga da wando ne ƴan ƙasar indonesia masu laushin gaske, irin wanda ko mutun baijin bacci yasa su dole yaji shi, maroon colour masu zanen flowers milk colour ajikinsu, daga sama rigar bata rufe ƙirjinsa ba, dama shi bai cika sa kaya waɗanda ke covering chest ɗinsa ba, bai sanya links na rigar ba,
Cikin natsuwa ya zauna saman 3 seater, sam sehrish tagaza janye idonta akansa balle tafara saving ɗinsa har sai da taji voice ɗinsa a ears ɗinta yace "Ni zanyi saving kaina ne!? ya tambaya fuska a ɗaure,
Cikin sauri sehrish ta ɗauke ɗan bowl tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da Chicken pepper soup, tasanya saving spoon ta Shaƙe masa shi, wani irin aroma ne ke tashi daddaɗan gaske, ajiye masa tayi sannan ta zuba masa white rice acikin plate, bayan nan ta haɗa masa da drink mai sanyi,
Natsuwa tayi bayan ta kammala zuba mashi duk abinda ya dace, ta ɗan ja baya zata juya ta fice sbd tuna mgnr azmee na cewa Bayason kallo, muryarsa tasake ji ya ce "In na kammala wazai kai kayan kitchen!"? tsananin mamaki sehrish kawae take yi, ashe yana magana har haka, acewarta, muryarsa ba ƙaramin daɗi take mata ba, tayi mamakin yadda yake furta yaren hausa duk da kana ji kasan bai saba da ita ba, in ka gansa bazaka ta6a tunanin cewa zai iya magana da hausa ba, saboda yanayinsa,
Cikin hanzari tace "Ni" jinjina kansa yayi, ya ci gaba da cin kazar dake gabansa, murmushi ta ɗan saki tasamu wuri ta tsaya, da tazara tsakaninsu, amma komai yakai hannu zai ɗauko cikin sauri sehrish ke ɗauka ta zuba masa in na zubawa ne, in kuma nasha ne ta tsaiyaya masa, har ya kammala sam babban yaya baya wasa da cikinsa, yana basa haƙƙinsa yadda ya dace,
Sehrish ta tsaiyaya masa ruwa ya wanke hannunsa acikin wani bowl, sannan ta ciri tissue ta miƙa masa ya goge mouth ɗinsa dashi,
Haka tabi shi da ido harya tashi ya wuce cikin bedroom ɗinsa, ta lura bacci yake ji yadda taga yana lumshe idonsa,
Sai daga bisani ta tattare kayan ta fice tana mai jin kewarsa atare da ita, kafin zuwa gobe ta kuma sashi a idonta, cikin kitchen tamayar da kayan sai da ta wawwanke dishes ɗin acikin daren sannan ta wuce nata room ɗin tana mai cike da shauƙinsa,
Ta jima ba tayi bacci ba, su twins basu dawo cikin gidan nan ba sai around shabiyu na dare, Time ɗin ma kowa yayi bacci, cikin sanɗa su ka wuce room ɗinsu,
a cikin ƴan kwanakin nan rayuwar sehrish ta canza sosai, wani irin azababben so take mashi, wanda har ya kai ga ko sallah take yi da tunaninsa aranta, daker take samu ta dai daita natsuwarta wani sa'in,
Junaid kuwa sam ya gaza gaya mata abunda ya shirya zai sanar mata, ƙarshe azmee tace yabarta ita da kanta zata sanarwa sehrish ɗin, a yayin da sehrish ke wannan haukan sam Rafayet har yau bai ta6a ɗagowa da idonsa ba, yasa cikin nata, bae masan wanene ba ko wacece ba ke famar ɗawainiyar kai masa abinci da gyara masa part ɗinsa ba, abunda yasani shine yana samu kyakkyawar kula agurin kowanene ma 💋
*Hafsat Bature*..................................................................
.............._Katsina state_................
Zaune take ta haƙimce a saman 3 seater, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, hannun ta na riƙe da remote, ta ƙura ido tana kallon faskekiyar plasman dake manne jikin bango tana facing ɗinta,
Ko kyaftawa batasan yi, dayake shirin ta ake yi, wato shirin daɗin kowa na Arewa 24, maimaici ne take kallo, sai faman washe baki take yi tana fadin "Oh koya za'a kaya tsakanin mlm na tala'a da hajiya fatima akwai bada ƙala a wurin nan,' ta faɗi tana jinjina kai, ita kadai abunta, acikin matsakaicin parlor ya hadu iya haduwarsa ba hayaniya, ga komai cike da tsafta kwal,
Tsohuwa ce amma ba tukuf ɗin nan ba, tana da hasken fata, jikinta na sanye da riga da zani na atampa, ta coge ɗaurin dankwali, daga ganin ta kasan taji hutu ga kuma kwanciyar hankali da natsuwa,
"Saude ! Saudee !! saudatu wai ina ki ka