Showing 21001 words to 24000 words out of 137891 words
Chapter 8 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
tsayin ta har bayan wuyansa baka wulik,
Kyawawan lips ɗinsa tabi da kallo dark pink kamar ya shafa janbaki, ga wani dogon hanci tubarkalla masha Allah,
Tayi nisa cikin ƙurewa hoton kallon, sam ta manta da abunda take kokarin yi sai da wayar hannunta tayi ƙarar shigowar sako sannan ta dawo hayyacin ta,
Da sauri ta shiga wurin contacts, numbar goggo ta rubuta ta danna mata ƙira, ba tayi tunanin ko akwai recharge card a phone din nasa ba, amma ranta ya bata cewa ba zama a rasa ba, su da kullum cikin kuɗi suke,
A jiyar zuciya ta saki jin numbern ya fara ringing, sai Allah Allah take suyi sauri su ɗaga before he get up,
Jin muryar goggo yasa sehrish sakin murmushin jin dadi
"Assalamu alaikum goggo sehrish ce! Ina jahad don Allah inason magana da ita cikin sauri," ta karasa maganar tana waige waige kar wani ya ganta,
On the other hand goggo ta miƙa wa jahaad wayar, cikin dauƙi ta ƙarba tare da fadin"yar uwa ! dagaske ke ce ! Wayyo Allah na farin ciki,"
Dariya sehrish tasaki jin abunda jahadar ta ce, kamar zatayi kuka itama ta ce"I really missed you my sisters, so much, dana ji voice ɗinki i just felt like to cry," ta karasa maganar idonta cike taf da hawaye,
"sister dama akwai abunda nake na fada miki amma narasa taya zanyi magana dake,"
Sehrish ta ce "yanzu ina jinki pls kiyi sauri ba wayata ba ce ta yaron gidan ce baisan ma na dauka ba,"
Cikin fargaba take sauraron jahaad ɗin"sister doctor ya ce ƙarshen month ɗin nan indai ba ayiwa husanna aiki ba, to ciwon nata zai habbaka sai dai a fidda ita ƙasar waje in ba haka ba mutuwa zata yi, sun sa mana ranar aiki 5 ga watan da zamu shiga...." kuka ne ya ci ƙarfin ta, itama sehrish ɗin kukan take yi haka suka dinga kuka ta wayar, babu mai lallashin wani,
"Idan kin gama wayar ina jira!!!
A firgice ta juya idanuwanta azare jin muryar junaid, rufe idonta tayi tare da buɗe su ashe kunnanta ne suka jiyo mata hakan sam bashi bane ,
Ganin ya fara yi mata gizau yasa ta ce da jahad ta ajiye waya, zasuyi magana next time in ta samu chance irin wannan,
Cikin sauri ta goge numbar goggo da ta sanya, a wayarsa da duk wata shaida da zata tona cewa tayi amfani da wayarsa,
Cikin sanɗa ta lalla6a ta mayar masa da wayar, har time din bacci yake yi,
Haka ta koma ɗakin ta tana sharar kwalla, safa da marwa ta shiga yi tana zagaye ɗakin, tunanin ta yadda zatayi ta samun kuɗin nan,
"Yanzu yaya zanyi! kada husanna ta rasa rayuwarta! sam bata cancanci haka ba, tazo duniya a wahalce kuma ta koma! Ya ilahi i dont ave any other choice fa ce kai Ya Allah, nayi imani dakai, kai kaɗai ne gatan mu, Ya Allah ka kawo mana mafita Albarkacin manzon Allah (SAW) ❤
Dakyar ta samu ta shiga toilet don wanke jikinta, ganin cewa basu da wani aiki a kitchen saboda guys ɗin gidan in suka fita sai da marece suke dawo wa, hakan yasa basa making lunch da wuri,
Don haka tana kammala wankan ta, da alwalarta tafito domin time ɗin azhar ya yi, har ta kammala sallah bata tuna cewa tabar gashin bakinta a cikin toilet ba,
A saman sallayar ta kwanta tun tana shesshekar kuka tana rokon Allah har bacci ya ɗauke ta,
Sehrish ta manta bata rufe kofan ɗakinta ba kamar yadda ta saba, shin na tuna mata ko kuma na kyale ta? tuna wa da cewa ba'a so a tashi mutun in yana bacci indai ba abu mai mahimmanci bane kamar sallah yasa na ƙyale ta, me zai biyo ba?
"Babu amfanin zama da mutun fasiƙi irin ka ! Ka saida mun ƴaƴa ! Saboda son abun duniya da son siyasa kai mutunne ko dabba! hakan baiyi maka ba sai da kabi ƴaƴana ka lalata musu rayuwa wannan wace irin masifab ce?
"Wayyo Allah abba kadaina dukan oumman mu, jini ke zuba a jikinta, oumma ki daina kada ya kashe ki ! Oumma! Oummahhhh!
Da ƙarfi ta ambaci sunan a firgice lokaci ɗaya ta farka, kukan da take a mafarkin har a fili sharkaf haka tayi da zufa, zaune ta tashi a fujajen tana kuka bil haƙƙi,
Dafe kanta tayi saboda wani matsanancin ciwo da yake yi mata, cikin shesshekar kuka take ambaton "umman mu,' fuskarta duk ta jagule dama dama da hawaye, da alama wani mummunan abune daya taba faruwa a rayuwarta ta tuna,
Haka ta dinga maimaita "Innalallahi wa inna ilaihirraji'un,
Cike da jimami ta tashi daga saman sallayar, agogon dake manne jikin bango ta kalla ƙarfe 4:00 dai dai time ɗin la'asar yayi har yana kan wuce wa,
dole ne ta canza sabuwar alwala saboda tayi bacci mai nauyi,
Cire hijab ɗin dake jikinta tayi ta aza asaman gadon, ta jiƙe sharkaf da zufa, shiga toilet ɗin tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, hannun na dafe da chest ɗinta, cire kayan jikinta tayi , ta sakarwa kanta shower , yadda sassanyar ruwan ke sauka a jikinta haka zuciyarta ma ke sauka daga hawan da tayi, (ruwa rahama Ne!) duk yadda kake cikin kunar rai indai zaka shiga ka watsa ruwa a jikinka to tabbas zaka samu natsuwa,
Bayan ta kammala bath ɗin ta karasa gaban mirror ɗin dake cikin toilet ɗin, tana bin jikinta da kallo, tana da tsayi ba laifi , sam bata da ƙiba amma ƙirjinta cike suke da boobs, sannan daga kasa akwai hips sosai faffadan gaske, launin fatarta choculate colour ce, expensive skin colour, tana da sexy eyes masu lumshe wa sometimes kamar na mai jin bacci wani lokacin kuma sai kayi tunanin tana shaye shaye ne, kwayar idonta fara ce tass mai launi brown colour, hancin ta ba dogo bane ƙarami ba ƙaramin kyau yayi mata ba, a bangaren lips kuwa tamakar shape ɗin love ❤ red colour masu tafshin gaske (macen novel ke nan komai nata is 100% 😂
Hannu tasa tare da shafa gefen wuyanta inda ke akwai wani rubutu a jikin fatar wurin da bakin rubutu kamar na tattoo aka rubuta (Sb) murmushi ta ɗan saki tuna wanda yayi mata rubutun, mayar da hannunta tayi akan sumar kanta wadda tayi tsayi yanzu ta sauko mata har kafaɗar ta , asalin gashin kanta har ƙugunta ya dira, amma silar hajjaju da ma'reeya suka datse mata shi saboda gudanar da aikin ta a matsayin namiji,
Tunawa da sallah yasa tayi gaggawar mayar da kayanta, ta dauki gashin bakinta da ta bari a gaban mirror, ta fita
Cikin sauri tayi sallar , bayan ta gama ta nufi kitchen wurin azmi taga in akwai aiki, samun ta tayi tana a ciki tana shirye shiryen fara aiki,
"Barka da aiki aunty azmi " sehrish ta faɗi hakan tana kallonta, ɗagowa tayi da fara a fuskarta tace "ke ke da sannu saboda naganki kina ta sharar bacci,"
Ras! Sehrish taji gabanta ya faɗi hankali a tashe take kallon azumi, itama kallon ta take tana sakin wani bazawarin murmushi, lokaci guda sehrish tabi ta susuce murya na rawa tace "dagaske kin ganni ina bacci !" dariya azmi tasaki tare da cewa "kwarai malam tukur ɗan basaja naganka kona ce naganki, "
Kallon kallo suka shiga yiwa junansu sehrish na tunanin tabbas ƙaryarta ta ƙare saboda azmi ta kira ta da ke amaimakon kai sannan taganta tana bacci da hijabi kuma ba gashin bakin nan nata da take sawa ya ilahi,
Yayin da azmi ke mamakin wayau irin na wannan yarinyar, har tasan tayi shigar namiji tazo gidan sojoji aikatau ko tsoro bata ji, gskya ba ƙaramar ƙuruwa ba ce,
Sai faman wurga ido sehrish take yi,hannu tashiga tafawa tana faɗin "nashiga uku shikenan komai ya ƙare"
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Page 19-20
sai faman wurga ido sehrish take yi,hannu tashiga tafawa tana faɗin "nashiga uku shikenan komai ya ƙare"
Kana kallonta ka ga tsananin tsoro a fuskarta, lokaci guda tabi ta rikice ganin bata da wani mafita fa ce ta roƙi azmi ta rufa mata asiri, don haka jiki na rawa takarasa gaban azmi ta zube saman kneel ɗinta tana roƙonta "nasan nayi laifi amma bani da wata mafita ne don Allah ki rufamin asiri aunty azmi kamar yarda Allah ya rufa miki,"
Hmmm ja da baya azmi ayi tare da cewa"am sorry to say bazan iya rufa miki asiri ba ! laifin zai shafe mu mu biyu, wannan babbar qarya ce a girma na bai kamata na goyi bayan hakan ba, sannan bugu da ƙari sojojin gidan nan suka gane cewa ke maca ce ba namiji ba to tabbas ƙasusuwanki za'a fidda daga cikin gidan nan! kinsan matsalarki ? Cikin sauri ta ce "a'a "
"matsalarki shine kin aikata laifi biyu, na farko namiji suke so a matsayin ɗan aiki ba mace ba, ke kuma kinyi shigar mace kinzo, duk sunyi tsammanin ke namiji ce hakan yasa suka amince da ke rinka shiga har ɗakunansu kina gyara musu da sauransu, nabiyu laifin ƙarya! sun tsani maƙaryaci, kinyi karya baiwar Allah idan har suka son da wannan zancen ko ! Ba ma ke ba ni kaina ta shafa! don haka cikin salama ki tattara kayanki ki bar gidannan kafin su ankara"
Azmi na kaiwa nan ta juya mata baya ta ci gaba da abunda take yi,
Jiki a mace sehrish ta miƙe, hawaye na gangarowa daga idonta kamar an kunna fanfo, cikin sanyin murya ta ce "shikenan...bakomai naji daɗin hakan zan tafi insha Allah,"
Fi ce wa tayi a guje tana shessheƙar kuka, fadawa tayi ɗakinta ta datse kofar ta faɗa saman gadon ( kamar a indian film 😂)
Tasha kuka kamar ba gobe lokaci guda fuskarta ta kumbura tayi suntum, idonta suka yi jawur suka ƙankance kamar na ƴan chaina,
Haka ta taso daga saman bed ɗin tana bin bedroom ɗin da kallo "ko a mafarki ban taba tunanin haka zata kasance dani ba, yanzu zan tafi nabar wannan daular, ni bama wannan bane damuwata ba ya rayuwar su husanna zata kasance su da suke cikin wani hali a asibiti, gashi bansamu kuɗin ba, wayyo Allah na, bansan wane irin zunubi muka aikata ba da rayuwarmu bata tafiya adai dai ba, tun kafin mu mallaki hankalinmu mu ke fuskantar ƙaddara iri iri meyasa !?
Zube wa kasan tiles ɗin tayi tana kuka jikinta har jijjiga yake yi,
Sam bata ji shigowar azmi ba sai dai mutyarta taji ta dirar mata a kunne" Ya sunanki ? ta jefa mata tambaya ,
yunkurawa tayi ta tashi tsaye tana matse hanci ta ce "SEHRISH"
Jinjina kai azmi tayi tare da ƙarasawa inda take, tafin hannunta ta sa tana share mata hawaye, sam sehrish bata yi tunanin hakan ba,
sannan cikin natsuwa ta ce" nayi takaici dana sa wannan kyakkyawar fuskar zubda hawaye am so sad," cike da mamaki sehrish ke kallonta, azmi ta ci gaba da cewa "kiyi hakuri ko kusa bazanso na raba ki da aikin ba! duk da ina tsoran abunda zai biyo baya, amma zan iya jurewa don ganin na taimaka miki," jin wannan bayani yasa sehrish sauke nannauyiyar ajiyar zuciya,
mayar da hannunta tayi a saman shoulders ɗinta taci gaba da cewa" da farko ina so ki fadamun dalilin dayasa ki kayi basaja a matsayin namiji"?
Muryar na rawa ta soma magana cikin sheashekar kuka" ƴan uwana ne basu da lafiya rai hannun Allah an kwantar dasu asibiti, kuma doctor ya ce aiki za'a yi musu, shine nake kokari naga nasamu ƙudi na biya musu, ɗayar ma dr yace in har ya wuce 5 ga watan da zamu shiga sai dai a fidda ita Qasar waje ko tarasa ranta.....' kukan ne yaci ƙarfin ta,
Cikin lallashi azmi ta ce "daina kuka ya isa haka, na fuskanci matsalarki, duk da ina buƙatar bayani amma bani da enough time, riƙe wannan zamuyi magana an jima yanzu dai taimakon da zan miki shine, zaki ci gaba da aiki a matsayin Namiji kamar yadda kike yi, ko da gigin wasa karki bari su gane cewa ke maca ce ! sannan maganar kuɗi kuma nawa ne ake bukata ?
Azmi ta tambaya tana kallon ta, sehrish ta ce "dubu ɗari tara ne" a tunanin ta azmi zatayi shock in taji kuɗin amma sai taji tace"zan iya ansar miki albashinki na wata na shekara ɗaya da rabi ! a baki a ɗunkule amma inaso ki sani ! duk runtsi duk wuya duk kuma duk irin wahalar da zaki fuskarta da wulaƙanci a wurin masu gidan nan, dole kiyi haƙuri ki jure! kiyi musu biyayya sau da ƙafa, ba maganar barin aiki , in kuma har kika ce zaki bari toh sai fa kin biya sauran kuɗin da kika ƙarba kin amince!!? 😰
taji ma tana nazari kafin tace"Eh na amince !!! zuciyarta na wani irin bugawa ba kowa ya faɗo mata a rai ba face Ayaan da jahaan , ynx ana nufin ta ɗaura aure da kaddararta na zama cikin gidan nan! ya ilahi,
"Yanzu account number zaki bani na wanda za'a turawa kuɗin aikin nasu," azmi ta faɗa tana kallon cikin idonta, tsananin farin ciki ta gani a fuskar sehrish 😇
cikin jin daɗi tace "babu a wuri na amma zuwa anjima ko gobe zan samu na kawo miki," azmi ta amsa da toh sannan ta kama hanyar fita har takai bakin kofa xata buɗe ta juya ta kalli sehrish dake ta faman sakin murmushi tace "kada ki manta ynx kina ƙarƙashin Iko na! komai zakiyi saida umarnina, idan har kika saba hakan, hmmmm,
bata ida ba ta fi ce,
sam sehrish bata damu da hakan ba, ita dai indai akan sisters ɗinta ne toh ko fiye da hakan ma zata iya jurewa,
Jiki na rawa baiwar Allah ta shige toilet ta dauro alwala taci gaba da zabga nafilfilin miƙa godiya wa ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala,
Matsalar su husanna tazo ƙarshe, sauran damuwa ta kau, shin yaya kke tunanin rayuwar sehrish zata kasance a gidan ABBAN SOJOJI ? 😢
yinin ranar da fara'a a fuskarta hakoranta a washe kamar mai tallar maclean, cikin jin daɗi suka gudanar da aiki a kitchen tare da azmi don shirya dinner,
tunanin yadda zata sake ɗaukar wayar junaid takira husanna ta ce su turo mata account number, har zuciyarta take jin ƙaunar azmi saboda tayi mata rana ! Har abada kuwa ji take bazata taba sa6a mata ba! tayiwa kanta alkwarin zatayi mata biyayya bazata taba bijire mata ba ko taci amanarta ba,
A 6angaren junaid kuwa, bayan ya tashi daga bacci da jimawa ya wuce masallaci daya dawo ya tsaya a filin da suke buga ball na gidan tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan,
yunwa ce tasa shi shigo wa ciki after magrin prayer, muryasa suka dinga ji yana kiran "tukur ! ,
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish, cikin ɗauki ta ajiye wanke wanken da take yi agaban fanfo, na kayan da suka yi amfani dasu,
Karasawa tayi wurinsa yana zaune saman 3 seater, yana daddana wayarsa, cikin girmamawa tace"gani ya ya junaid" ta kirasa da hakanne saboda ya hana ta ce masa yalla6ai, girman jiki ne kawai dashi da kuma tsawo fuskarsa ce kawai zata nuna maka cewa yaro ne sharkaf,
ta6e baki yayi tare da ɗan jefa mata kallo ya ce" ƴunwa nake ji, " ya faɗa a shagwa6e, yana kallon ta
cikin zumuɗi ta ce " a shirya ma abinci a dining ko nan zan kawo maka,?
ta tambaya tana kallon wayar hannunsa kamar ta fisge ta saboda ita take bukata,
ɗan yatsina fuska yayi kafin ya ce" No a tsarin gidan nan bama iya cin abinci in ba tare da junan mu ba, duk yunwar da mutun ke ji dole sai an tattara an haɗu a table aci a tare, don haka kawo min coffee kawai, zan jira brothers ɗina su dawo sai mu ci dinner a tare,"
Wannan haɗin kan nasu ya burge sehrish sosai, suna son junansu, juya wa tayi, taje da tadawo hannunta dauke da cup din saman ɗan plate ɗin da ake aza sa, miƙa masa tayi tana kallon fine face ɗinta,
Ƙarba yayi tare da faɗin"thanks"
komawa dining room ɗin tayi, tana goggoge chairs ɗin dake kewaye dashi, daga inda take tana satar kallonsa shi da yake zaune a falo,
Bayan ta kammala ta koma kitchen ɗin, azmi ta samu tana a ciki tana ganin ta ta ce "yawwa mlm tukur ayi maza a fara jera abincin a dining ko," sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya, azmi tace "gsky hajjaju yar daru ce! da ita duk aka shirya wannan ƙaryar," murmushi kawai sehrish take yi tana wasa da yatsun ta,
Ba tare da bata lokaci ba, suka soma shirya abincin, tana kaiwa tana jera masu,
Ƙiris ya rage a fara kiran sallar magrib, bayan sun girma shiryawa azmi ta wuce ɗakin ta , sehrish kuwa falo ta wuce, anan ta samu Junaid yana sharar bacci, ya mimmiƙe kafafuwansa a saman doguwar kujerar, Alhamdulillah thanks to Allah ta fadi hakan, ƙyalle ido tayi ta ga inda ya ajiye wayarsa saman chest ɗinsa,
Cikin sanɗa ta soma tafiya a hankali a hankali take takawa, har ta idasa isa gabansa, leƙa fuskansa tayi kyakkyawa mai annuri, dimples ɗin nan nasa a lotse, kamar ba bacci yake yi ba,
Hannu takai a hankali ta ɗauki wayar tasa cikin rashin sa'a ta zame daga hannunta ta faɗi kasa ta daki haɗaɗɗen tiles ɗin dake kasa, har cikin zuciyarta taji faɗuwarnan, tsadaddiyar waya irin wannan, dafe ƙirjin ta tayi tana kallon wayon, ƙarar faɗuwar wayar tasa junaid yunkurin buɗe idonsa daga baccin da yake, cikin sauri ta boye bayan hannun kujerar tana sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarsa yayi ya ci gaba da bacci, jin sakin ajiyar zuciyarsa yasa ta gane ce ya koma baccin nasa, hannu ta zura ta janyo wayar tana kallon screen ɗinta, Alhamdulillah ta fada ganin ba abunda ya same shi,
Yunƙurawa