Showing 114001 words to 117000 words out of 137891 words
Chapter 39 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
ya hango babban yayan nasu yabar musu filin kwallon ya fito a guje kamar ƙaramin yaro bai tsaya ko'ina ba sai a bayan babban yayan nasu ya rungumeshi ƙam,
tsayawa da tafiya sgr yayi jin yadda junaid ya rumgumoshi ta baya,
"oh junaid ni baka ganni bane wato babban yayan naku kawai ka sani ko"? adams ya faɗi yana kallon shi,
Janye jikin shi yayi daga na Sgr, cikin jin kunya yace "a'a yaya adams ba haka bane," ya faɗi tare da matsawa yayi hugging ɗinsa "ko kaifa yanzu naji bayani, nayi tunanin wariyar launin fata za'a nuna mini," dariya su kayi atare jin abunda yace, shi kanshi sgr sai da ya ɗan so yayi murmushi,
"Yaya adams wane ni na isama, kafi ƙarfin wannan Allah, tukunna ma meyasa baka zuwa kawomun ziyara, ko dan Babban yaya baya ƙasar ne? Dama kullum ba'a ganin ka sai in Babban yayan mu yazo sannan kke zuwa ko? Ya tambaya yana kallon shi irin kallon na kama mai laifi ɗinnan,
Adams yace "junaid ba haka bane aiyuka ne sun min yawa, nima ae bana ƙasar ban jima da dawo daga Norway ba,"
Junaid yace "tom shikenan ina tsarabata "?
yayi maganar hada riqe ƙugunshi, hakan ba ƙaramin dariya ya ba Adams ba, hatta shi babban yayan nasu dake kallonsu abun ba ƙaramin nishaɗartar dashi yayi ba, especially yadda junaid ke magana, komai nasa burgeshi yake yi, junaid young bro ɗinshi ne kuma crush ɗinsa ne,
"In dae kana son tsaraba to kazo gidana ka amsa da anjima,"
ɗan zaro ido junaid yayi tare da cewa "tab !!" sannan Ya kalli babban yayan nasu tare da cewa "zaka barni inje ?"
Fashewa da dariya adams yayi yana kallon ikon Allah, wato sgr shine ke sarrafa shi,
Sgr yace "Why not but not today zuwa tomorrow ko jibi zan sa akawo maka shi har gida,"
Ya ƙare maganar tare da cewa "am tired of standing, Lets go in,"
Atare suka jera junaid na tsakiyarsu ya ruƙo hannun kowannansu fuskar nan ɗauke da murmushi a haka suka shiga ciki,
Wuce wa upstairs su kayi, a part ɗinsa adams ya zauna saman 3 seater, shi kuma sgr ya wuce bedroom ɗinsa don ya rage kayan jikinsa,
"Bari nazo yaya adams," junaid ne ya faɗi tare da tashi ya fice cikin sauri don yaje ya shirya masu abunda zasu sha,
Fitowa yayi sanye da shorts a jikinsa sai ƴar singlet fara, hannunsa ɗauke da phone ɗinsa ya ƙaraso ya zauna On royal sofa ɗin da Adams ke zaune amma akwai tazara a tsakaninsu saboda mai zaman mutun ukuce,"
Kallonshi adam yayi tare da cewa "Surgeon ka fa tara abubuwa da dama, ina so na tattauna wani abu dakai mana,"
Sgr yace "ina sauraron ka,"
Adams ya gyara zama tare da cewa "yanzu fisabilillahi kalli kanka da kyau,"
Cikin mamaki sgr yabi jikinshi da kallo kamar yadda Adams yace sannan ya ɗago ya kallesa yace "what u mean"?
Murmushi adams yayi kafin yace "Haba sgr ka mallaki kowane abu da ake buƙata ajikin ɗa Namiji harma ka wuce, kalli fa in kyau ne da anzo gunka anzo ƙarshe kai kankat ne, in arziki ne da anzo gunka anzo ƙarshe, in Ilmi ne na addini dana zamani da anzo gun ka anzo ƙarshe, baiwa iri iri Allah ya baka to maiya rage maka a yanzu "?
Tun da Adams yaso ma bayanin Sgr ya ke bin shi da wani irin kallo saboda ya gano inda ya dosa,
Duk cikin friends ɗinshi babu mai mishi katsalandan irin adams, saboda kusan halinsu ɗaya, adams ne kawai ya ware daban acikinsu,
Ci gaba da magana adams yayi " da ace ni na mallaki waɗannan abubuwan daka tara, wlh da yanzu na ajiye mata har 4 Cuf, yadda kke da farin jinin nan ta ko'ina binka ake don asamu shiga, Amma sam ka haramta ma kanka mace duk wannan Hadaɗɗiyar Surar taka sai dae suyi ta kallo suna haɗiye yawu'
Shiru sgr yayi yana kallon fuskan adams daya daddage yana kora masa bayani,
Jinjina kai adams yayi tare da cewa "ae dama nasani, u wll not say anything kabarni ina ta zuba kamar radion da bata da saiti,"
Lumshe ido sgr yayi tare da cewe "me kke so nace"?
ta6e baki adams yayi tare da cewa "abunda ka iya kenan, nasha wahalar koro maka bayani amma u ar asking me me nakeso kace," yayi maganar hada ɗaure fuska yana kallonshi,
hakan yasa sgr saki wani ɗan kayataccen murmushi batare da lips ɗinshi sun motsa ba, dimples ɗinsa ne kawai suka bayyana alamar murmushi yyi,'
adams yace " ka ga wannan murmushin naka, wanda ko namiji ya kalla sai gabansa ya faɗi, duk in kayi shi nasan da wata manufa,"
sai lokacin sgr yace "ka kammala bayanin naka"?
Adams yace "a'a ban idasa b
a, i just start it now," yayi maganar yana tsuke fuska
"Ok Go ahead in ka kammala zan baka amsa a dunƙule," sgr ya faɗi tare da ci gaba da dannar wayarsa kunnansa na akan Adams,"
Adams yace "haba jama'a kaga ƙato har ƙato amma ba zancen mace a ransa, zuciyarsa kaman ta dutse,'
Aransa kuma yace "kwarama da ba macen aransa, tab yadda yake da ƙirar nan da kyawun nan da ace ɗan iskane shi da Allah kaɗai yasan matan da zaiyi disvirgin ɗinsu, mata fa zasu sallawanta sosai yadda suke haukanshi suna kawo mashi kansu, tun ranar da matata tayi arba dashi shegiyar har yau kullum sai tace mun ina friend ɗin nan naka mai blue eyes shi bazai kawo mana ziyara ba,
Sam ya tafi tunani har sai da muryar sgr ta katse shi da cewa "are u gossiping me in your heart"?
Dariya adams yayi tare da cewa "ya akai kasan ina gulmarka bayan acikin zuciyata nake magana,"
"Naji araina" ya faɗi yana ɗan harararsa,
murmushi kawai adams yayi masa tare da cewa "nima bari na danni wayata, da na zauna naita zuba nikaɗae,' yana maganar yana sa hannunsa cikin aljihunsa ya zaro wayarsa yaci gaba da danna shima, falon yazama shiru,
___________________________________
Time ɗin da junaid yaje ƙopan kitchen ɗin domin ya shirya musu abunda zasu sha, Sehrish yasamu aciki ta kammala jera Fancy cups masu ɗauke da Coffee aciki sai plate mai ɗauke da snacks acikin tray, sam bata lura da junaid ba, shima tun da yazo ya tsaya yana ta faman kallonta fuskarnan ɗauke da murmushi har kullum ƙara burge shi tayi,
Gyaran murya yayi, hakan yasanya Reesh ɗagowa a ɗan firgice a tunaninta Haroon ne ashe junaid ne, tana ganin sa ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "junaid sannunka,"
"Yawwa sehrish na jima a tsaye ina kallon ki, wa kika shiryama wannan ne,' yayi maganar tare da idasa shiga ciki yana nuna tray ɗin dake saman table,
Sehrish tace "babban yaya nagama hada abokinsa suka zo"
Junaid yace "yawwa Good girl kin hutasshe ni, dama nima zuwa nayi na shirya musu sai naganki,"
Murmushi tasaki tana faman sunnar dakai,
"Bari naje ciki inaso na yi wanka, sannan pls in kina da free time mu haɗu a garden mana"? ya tambaya yana kallonta,
Cike da zumuɗi sehrish tace "Shikenan wurin ƙarfe nawa"?
"After magrib prayer yyi maki"?
"Eh" ta amsa mashi kafin yasa kai ya fice daga kitchen ɗin Izuwa br ɗinsa, dama a ƙagare yake daya cire kayan ball ɗinsa,
bakomai yasa ta ɗoki ba fa ce tana tsananin son garden ɗin gidan ya haɗu sosai dama ita ma'abociyar son kayataccen wuri ce mai shufke shufken flowers da ruwa mai gudana,
A hannu ta ɗauki tray ɗin ta fuce dashi izuwa upstairs part ɗin babban yaya, sai da ta ɗan jinkirta da ta iso ƙopan shiga, tasama ma kanta Calmness, Sannan tayi sallama a natse "Assalamu Alaikum,"
Ta jira aka amsa mata sannan ta shiga A hankali take tafiya kamar wadda ta ɗauko Kwai a hannunta,
Kowannansu wayace a hands ɗinshi, sai da taje gabansu tace "ina wunin ku," sannan adams ya ɗago yana kallonta yace "yawwa fine boy, drinks ne aka kawo mana," yayi maganar tare da sa hannu ya ɗauki one cup, matsawa tayi ta miƙawa sgr tana kallon shi sam bai ɗago ba har sai da tace "ga shi," sannan yasa hannu ya ɗauka, ta ajiye musu tray ɗin a saman table,
kamar karta fuce haka take ji, wani irin sanyi take ji in tana kallonsa, yayi wani fresh abunsa cikin singlet da shorts,
"Ji mana," adams ne yayi mata magana cikin sauri ta juya ta kallesa tare da cewa "Na'am"
"Amma kai sabon mai aiki ne ko? Ina aunty azmee ne?
ya tambaya yana neman jin ƙarin bayani
Sehrish tace "Eh sabone, aunty azmee tana nan,"
Jinjina kansa yayi kafin ya kuma cewa "Suna fa"?
Rishi tace"Tukur,"
Abun mamaki sai taga yana mata dariya gashi kuma yana bin ƙafafunta da kallo abun ya ɗan bata tsoro,
Tsagaitawa da dariyar yayi tare da cewa "Wow good wasan kwaikwayon fa yayi kyau sosai," sam Bata gane me yake nufi ba duk ta dabarbace, duk wannan maganganun nasu a kunnan sgr,
"u can go mr Tukur," adams ya umarce ta yana mai ci gaba da ɗan murmusawa,
Jiki asanyaye sehrish ta fuce tana mai mamakin wannan abokin na Sgr, komai yake nufi da dariyarsa Oho, ta faɗi tana yarfa hannayenta,
Kurbar coffee ɗin yayi yana cewa "Sgr ina kuka samu ɗan aiki ne?
"Don't know," ya bashi amsa,
Adams yace "Wannan fa maca ce tayi shigar maza wlh, amma fa ta iya shiririta,"
ɗan kallonsa sgr yayi tare da cewa "Wa kenan?
"House boy ɗin nan mana, daya kawo mana drinks yanzun nan,"
Sgr yace "Are u serious ?
Adams yace "Of course baka ta6a lura bane?
Sgr yace "taya zan lura, bayan ko face ɗin mai aikin bansani ba,'
Adams yace "No wonder that's y baka lura da hakan ba, amma fa maca ce wannan hada sa gashin baki, ' ya ƙare maganar yana dariya don kam ba ƙaramin nishaɗi abun ya bashi ba, shigar yarinyar amatsayin namiji kamar ɗan chali chali,
"Amma ko meyasa tayi hakan"? Adams ya tambaya yana kallonshi,"
Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa "Zan bincika, koma wa ya turo ta, zan sani ne, zasuyi bayani," Acewar sgr,
"Gsky kam, u ave to investigate about it, kasan mugun mutun bakasan da wata siga zai shigo rayuwarka ba, especially yadda kke da suna haka ba'a rasa enemies masu son kawo muku hari ta bayan fage, ya kamata ka miƙe tsaye akan lamarin wannan mai aikin tukur, kasan da wata manufa yazo domin kuwa wlh maca ce ba namiji ba,"
Adams ne yake kora masa bayani yana ƙara jaddada masa akan mai aikin Don ayi saurin dakatar da shi daga abunda yake ƙoƙarin aikatawa, 😳
Sehrish fa batasan wainar da ake toyawa ba, Ashe watan cin uban wata yayi acikin gidan nan 😂
bedroom ɗinta ta koma tana safa da marwa, cike da tunanin dariyar da taga abokin sgr nayi mata aranta tace wata'ƙil shigar mazan da nayice ta bashi dariya Allah saki,
__________________________________
A hankali motocin marshal Omar suke shiga cikin katafaren gidan General Ishaq wanda ke a Unguwar rimi,
Hamshaƙin gidan wanda sojoji ke tsare dashi ta ko'ina, jahad sai faman bin gidan take da kallo ganin haɗuwarsa ta cikin glass ɗin motar, jinjina kanta tayi aranta tace "Aljannar duniya,"
Juyawa tayi ta kalli hosana wadda ta kwantar da kanta a kafaɗar Jahad ɗin sai faman bacci take shararawa murmushi jahad tasaki tare da cewa "Nasan hosana in taga wannan haɗaɗɗen gidan dole ta susuce,'
Mayar da idonta tayi kan glass ɗin tana ƙarewa gidan kallo aranta tace "Allah yasa kamar yadda gidan nan yake da kyau mutanen gidan ma zuciyarsu ta kasance mai kyau ce kamar haka, Ya Allah kasa kasancewar mu acikin gidan nan yasa ƙarshen wahalar mu kenan, Allah yasa mutanen gidan suyi marhaban da zuwan mu kuma su tarbemu hannu bibbiyu kamar yadda goggon katsina tayi mana," ta ƙare maganar tana mai jin wani sabon yanayi atattare da ita,
A jere motocin suka tsaya, sajan ɗin dake driving ɗinsu ya fito ya buɗe musu mota,
fitow jahad tayi tana faɗin "Hosana ki tashi mun iso fa,"
daker hosana ta buɗe idonta da sukayi luhu luhu tana bin jahad dake mata magana da ido, daker ta iya sa ƙafa ta futo daga motar tana murje idanunta don taƙara tabbatarwa kanta cewa dagaske ne hamshaƙin gidan da take ganinsu aciki ba mafarki ba, aiko ta shaida hakan,
Fitowa Marshal Omar yayi daga tashi motar, yana sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalli su hosana yace " ku biyo ni,"
Bin bayansa su kayi atare suka shiga hadaɗɗen jigunannan babban falon Aunty babba, wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa ta cikinsa abunka ga ƴan maiduguri dama an shaidasu akan hakan,
Wasu irin haɗaɗɗun Sofas ne masu Numfashi sets guda, launinsu Maroon colour, ga sofa tables ɗinsu launinsu,
Falon yasha ado da decorative object ga vase ajiye (tukunyar flower) ga wata irin faskekiyar plasma manne a wall ɗin kai komai fa yaji ya haɗu,
Babu kowa a falon sai sanyin A.c dake ratsa sassan jikin mutun,
"Have a seat," umar ya umarce su sai faman bin ko'ina suke da kallo , a tare suka zauna saman 2 seater suka takure junansu tsoransu dawa zasu fara cin karo,
Shima yasamu wuri saman 3 seater ya zauna yana facing ɗinsu idon shi nakan hosana wadda ke ta faman lumshe ido saboda baccin da takeji ga yunwa,
Phone ɗinsa ya zaro daga trouser pocket ɗinshi ya danna numbar aunty Babba ya buga mata Calling,
Da ƙarfi wayarta ƙirar Iphone 13 pro max ta soma ringing tana ajiye saman bedside drawer gefen lamp,
Hajiyar na hakimce tana sharar bacci Saman haɗadɗen gadon nata, jikinta na sanye da riga da wando masu kyan gaske ga laushi kamar sleeping dress haka suke,
takurar da ringing ɗin yayi mata ne yasa ta buga uban tsoki a ƙule cikin bacci take cewa "Mtsww Wai wanene ne yake son takuramin ina tsaka da jin daɗin baccina," ta ƙarasa maganar tana buga Uban tsoki rai a bace ta tashi zaune fuskarnan kamar Alkubus a kumbure take don ma Allah yasa akwai kyau da haske ssae da ba ƙaramin muni zatayi ba,
Hannu tasa ta fisgi wayar ta duba ta ga wanene, sunan (Marshal Omar ) ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, ae tuni ta wartsake daga baccin da take yi, jiki na rawa ta ɗaga tare da karawa a kunnanta tace "salamun Alaikum," bai amsa mata ba sai cewa yayi "Muna a palor muna jira,"
Cikin sauri tace "oh to gani nan zuwa,"
Ta ajiye wayar tare da miƙewa tasa hannu ta ɗauki mayafin kayan jikinta dake ajiye saman gadon, ɗaure shi tayi akanta maimakon tayafa shi a jikinta, sumar kannan nata tasha ƙananun kitson kalaba,
A hankali take tattaka steps ɗin benen tana saukowa down, tun da suka ji takon takalmi suka ɗago suna kallonta haƙiƙa sun tsorata da kyawun matar ga yanayinta na marasa son mutane da hayaniya haka,
Jinjina kai su kayi tare da kallon juna lokaci guda suka mayar dakansu ƙasa,
A second to the last steps na stairs ɗin ta tsaya Curus ! tana kallon tagwayen matan da tagani zaune saman kujerunta sai taga abun kamar a mafarki gadai marshal omar zaune to su waɗannan isassun da suka zauna matan saman kujerunta su wanene ta tambayi kanta, har hannu take sawa tana murza idanunta don ta tabbatar cewa ba mafarki take yi ba,
Idasa saukowa tayi har time ɗin bata sauke idonta ba daga nasu Hosana wani irin kallo take binsu dashi kallon neman ƙarin bayani,
Muryar Omar ce ta katse ta da cewa "barka da fitowa aunty, fatan na same ku lafiya,"
Lokaci guda ta saki fuskarta ta ƙarasa ta zauna saman 1 seater tana cewa " Yawwa Omar saukar yaushe? wlh bacci ne ya kwashe ni nasan dae ka ce mun zaka zo nan bfr ka wuce abuja,"
Omar yace "Eh hakane, ina yaya ishaq ne?
"Ae bayan kabar nan, shima yayi tafiya,"
Ta faɗi tana kallonsu hosana da jahad, wadanda suka sha jinin jikinsu tuntuni musamman da suka gaisheta sai tayi kamar batagansu ba,
Miƙewa tayi tare da cewa "bari na kawo muku abun ta6awa,"
tayi mgnr tare da wuce wa kitchen, tana shiga ta tsaya riƙe da