Showing 3001 words to 6000 words out of 137891 words

Chapter 2 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete

ranta ba face y'an uwanta, in ta tuna irin wannan yanayin sai taji komai ya fita ranta.

Bayan sun kammala ci , hajjaju ta kai isu zuwa bedroom din da ta ware domin irinsu in ta dauko su anan suke kwana sannan ta yi masu sallama ta fice, tana fita y'an matan kauyen nan suka haye saman bed din dake ciki kuma shi kadai ne, bin su da kallo tayi ganin yadda suka wawware kafafunsu saboda kar tasamu wuri tace zata hau.

Murmushi tasaki, "Allah sarki rayuwa ni ina ne bazan iya kwana ba, bed is ur problem, Sisters dina sune damuwata,
Cire hijab din dake jikinta tayi, wardrobe din dake manne a bango, ta bude babu wasu kayan kirki a ciki, zannuwan atamfa ne kawai, saka hijab din tayi ciki ta rufe,
toilet din dake ciki ta shiga, komai na ciki a tsaftace yake, fari kal! Gaban mirror ta karasa tana kallon fine face dinta, fanfo ta kunna ta tarba hannuwanta tana wanke fuskanta, bayan ta gama tasa hannu ta cire head din dake kanta, ta yi holding dinsa a hannunta tana kallon doguwar kitson kalabar da akayi mata guda biyu ta zubo tun daga head dinta har zuwa west dinta, tana da Yalwatacciyar sumar kai dark brown colour very smooth ga kwantaccen saken gefen fuska.

Fitowa ta yi daga toilet din, samunsu tayi sai minshari suke ja tamkar raguna, wardrobe din ta sake bude wa daya daga cikin zannuwan da ta gani ciki ta dauko, ta shimfida a kasa, ta kwanta
Washe gari tunda sassafe suka fita, hajajju ce ke driving yayin da yarinyar take a gefenta , sai kalle kallen hanya take ta glass din motor, hajajju ta ce "Har yanzu baki fadamun sunanki ba ! da age dinki yakamata nasani ko"? tayi maganar ne a lokacin da take kokarin juya sitiyarin motar wurin canza hanya tabi titin da zai kai ka har izuwa asibitin.

Murmushi yarinyar tasaki tare da cewa "Sunana SEHRISH amma Oumman mu tana ce mun RISHI , shekarata 17 cif ," jinjina kai hajajju tayi tace "Wow nice name and it really deserves , " cike da jin dadi Sehrish tace "thanks" har suka isa asibitin basu kara magana ,
Sehrish tayi ma hajjaju jagora har izuwa ICU intensive care unit , inda aka kwantar da sisters din nata, lokacin da suka shiga ciki, da gugu wata kyakkyawar yar matashiya ta taso ta rungume sehrish, tsananin mamaki yasa hajajju sakin baki, sai ta dinga ganin tamkar mafarki take yi, tun da Allah ya halicce ta bata taba ganin yara masu shegen kama irin wadannan ba basu da wani banbanci ko miskala zarratin komai nasu iri daya sak , lokaci guda ta rikice takasa gane wacece ma suka zo da ita, wacece sehrish din don ta saje da dayar, hajjaju bata gama mamaki ba sai da taga dayar wadda take kwance saman gadon marasa lafiya ansa mata Oxygen dakyar take jan numfashi gwanin ban tausayi , nan takara rikicewa saboda itama wacce take kwancen Sak kamaninsu ba banbanci hakan na nufi su y'an uku ne kenan.

Kankame ta tayi tana kuka , itama sehrish din kukan takeyi hannunta tasa tana d'an bubbuga bayanta tace "Jahad ki daina kuka hankalina yana kara tashi komai zai tafi dai dai insha Allah, janye jikinta tayi daga nata tace "ina kuka ne ba don kai na ba sai don Husanna dr yace in ba mu fara biyan kudi an mata aiki ba , mutuwa zatayi kuma ynx haka kudin gado ya kare sallamar mu zasuyi ko kudin magani babu ," hankalin Sehrish ba karamin tashi yayi ba,
Hajajju dake tsaye tana kallonsu, jikinta yayi mugun sanyi saboda tsananin tausayi, ita kanta wadda sehrish takira da Jahad akwai wound a goshinta, anyi mata dressing da bandage duk jini a jikin sa , hannunta ma akwai kanula alamun anyi mata karin wani abu jini ko ruwa , a kagare hajajju take da taji labarin wadannan y'an ukun lallai bakaramar wahalar rayuwa suka sha ba.

Muryar Sehrish ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga "Jahad ga hajajju ku gaisa kuma kiyi mata godiya sbd itace zata sama mun aikin da zan fara yi nasamu kudi nabiya ayi maku aiki," matsawa tayi gaban hajjaju tana share hawayenta cikin girmamawa tace" ina kwana hajiya ," murmushi hajajju tasaki tare da dafa kadarta tace "lafiya lou ya jikin naku "? Jahad tace "Alhamdllh ni da sauki husanna ce abun sai kara gaba yake yi don dr yace koda an mata aikin ba lallai ta dawo yadda ake so ba...."

Kuka ne yaci karfinta har takasa karasa maganar , rungumo ta hajjaju tayi a jikinta tana lallashinta " am sorry my daughter stop crying insha Allah everything will be ok , cikin kuka ta amsa da "zandaina mungde ssai ," karasawa Sehrish tayi wurin husanna dake kwance rai hannun Allah , gefen gadon ta zauna tana kallonta idonta cike tab da kwalla tace "Allah ya baki lafiya yar uwata ina jin duk wani irin radadi da kike ji a zuciyarki wanda yayi sanadiyar shigarmu cikin wannan halin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba Allah ya isa tsakanin mu dashi mugu azzalumi macuci ..." a karshe ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a saman jikinta , har cikin ranta take kukan.

Tsohuwar dake kula dasu ce ta shigo cikin sauri hannunta rike da magunguna da takarbo masu , a nan tasamu hajjaju tsaye ita da jahad tana lallashin ta , jin alamar shigowarta yasa suka jiyo suna kallon , cikin sakin fuska tace "Sannun da zuwa hajjaju ke ce da kanki ," murmushi hajjaju tasaki dama sun son juna da alama , " kwarai kuwa nice gwaggo dama ke ce ke rike da yarannan amma ni ban taba ganinsu ba gsky ," murmushi gwaggo tayi tace "bakya leko mune shiyasa amma sun jima wuri na ni nake kula dasu ," jinjina kai hajjaju tayi tace "hakane amma gwaggo jikokinki ne su"? Goggo ta girgiza kai tare da cewa "a'a Allah ne ya hadani dasu nima labari ne mai tsawo , amma ynx bani da kwanciyar hankalin da zan zauna na baki shi , ki bari saina samu natsu," tana gama fadan hakan ta mika ma Jahad magungunan "karbi nan naki ne dakyar nasamu kudi na siyo su," godiya tayi mata ta karba , a tare suka taka izuwa inda sehrish ke kwance jikin Husanna , cike da nuna tsantsar tausayi hajjaju tace "Allah ya bata lafiya Allah sarki mutum baya sanin halin da duniya take ciki wani sa'in sai ziyarci asibiti nan zai ga marasa lafiya iri iri gwanin bantausayi hakika na tausayawa wannan yarinyar tana cikin hali Allah ya kawo musu sauki da duk marasa lafiyan dake fama da ciwo ," amsawa sukayi da amin , har time din sehrish bata dago da kanta ba , ita kadai tasan yadda take ji aranta.

Hajjaju ta mayar da idonta kan Gwaggo tace "idan ba damuwa muje ki raka ni wurin likitan zanyi magana dashi ,"
fita sukayi a tare , wuri Jahad tasamu ta zauna a chair din dake facing din gadon mara lafiyar, kallonsu takeyi su biyun tana kara jin kaunar y'an uwan nata , taji dadin zuwan rishi har cikin ranta , jajircewarta akan ganin sun samu rayuwar mai kyau yana kara mata ninkin son yar uwarta ta, tazama tamkar uwa agare su , alhalin ita age dinsu daya duk da tare suka zo duniya amma sun tsere wa rishi da mintina a wurin haihuwa , tunani iri iri ke zo mata a ranta runtse idonta tayi hawaye na kwaranyo wa daga idonta

Gabad'ayansu sun shiga cikin yanayi , duk sunyi zurfin tunani , numfashinta suka soma ji da karfi da karfi wani irin sauti mai matukar razanarwa , a firgice sehrish ta dago da kanta cikin rudu ta furta "Subhanallah! jahad husanna ta cire oxygen da aka samata," a rude jahad ta matso kusa da su hannu tasa ta tana kokarin mayar mata roban oxygen din , buge mata hannu tayi tana wani irin gurnani ga zufa sai ke to mata take yi ga wani irin tari da take yi cikin kuka take ambaton "Seh..seh..sehrish ,"

Dakyar sound din ke fita , hakan ya tambatar masu da cewa so take tayi ma Sehrish magana amma takasa , matsawa sehrish tayi kusa da ita tare da sa hannu tana shafa mata gefen fuskarta cikin kuka tace "pls husanna kiyi hkr kinji Allah zai baki lafiya , nasan mai kike ji a zuciyarki, zanyi kokari koda zan rasa raina ne wurin ganin kin samu lfy , wlh sai inda karfina ya kare , ina sonki sosai my sister," gaba dayansu kuka sukeyi , mayar mata da roban oxygen din Husanna tayi , bin ta su kayi da kallo ganin tana kokari kakaro murmushi a fuskarta , wani sabon kukan suka sake fashe wa dashi.

"Yar'uwata kada ki tafi kibarni ni nafiso na mutu a gabanku dan Allah kada ki tafi ," lokacin da sehrish ta tuna da wannan kalami na Husanna sai jikinta ya kara mutuwa lukus , kamar ba kasusuwa a jikinta, zamewa tayi ta zauna kasan tiles din tare da jingina kanta gefen gadon , wasu abubuwa ta dinga tunawa arayuwarsu wanda in har taci gaba da tuna su to tabbas zuciyata zata buga ne! komai ya dawo masu sabo fal , komawa Jahad tayi ta zauna tana shesshekar kuka hada majina a hancinta ,
Hannun husanna taji cikin nata , dayake ta aza hannun nata a saman bed din, ta rike shi gam cikin nata , dagowa sehrish tayi da fuskanta wadda tayi jawur , ga idonta sun kada , fuskarta tayi kwaba kwaba cikin kasalalliyar murya tace "Husanna ki daina zubar da hwayenki nasani abun da ciwo , zafinsa yakai kunar wuta amma ki daure pls , ba irin whalar da bansha ba wurin ganin nasamu kudi an miki aikin nan ke da jahad especially ke , kai karshe ma an kokarin bada kaina nayi amma dana tuna abunda mama ta fada saina gaza , duk da haka ban hkr ba na soma kokarin samun wanda zai siye ni yabani kudi kawai na kawo muku ni natafi amma saina tuna cewa in na tafi wazai kula daku ? duk da nasan akwai Allah shine gatan kowane bawansa ...' muryarta ce tashaqe ta gaza idasa maganartata saboda kululun bakin ciki daya tokare mata makoshinta .

Jahad da ke sauraron maganar yar uwarta su sai taji wani sabon kukan ya balle mata, domin duk wannan gwagwarmayar da Sehrish tayi sam basu sani ba a boye tayi kayanta.

Sun sha kuka kamar ba gobe nima na tayasu kukan duk da bansan takaimaiman tarihin rayuwarsu ba da kuma dalilin kukan nasu.

A haka goggo da hajjaju suka same su gwanin ban tausayi , wayar hajjaju dake cikin yar purse dinta sai ringing take yi don haka tace ma serish ta taso su tafi , cikin kuka ta tashi a hankali take tafiya tana waiwayansu , goggo tace " kada ki damu rishi hajjaju ta biya mana kudin gadon kuma tace zata samu koda bashi ne a fara biyan kudin aikin inyaso daga baya kin fara aikin kin samu sai ki biya,"
Ba karamin dadi sehrish taji ba , haka jahad ma godiya suka shiga yi mata , a karshe tayi masu sallama suka tafi ,
Har a cikin motan kuka takeyi dakyar hajjaju ta lallashe ta tayi shiru....

Time din da suka dawo , larai na kitchen ita da y'an matan kauyen nan tana koya masu wasu abubuwan daya kamata su sani.

A falon suka zauna gaba daya jikinsu a sanyaye, sehrish na zaune kasan carpet jingine da 2 seater , tana sauraron abunda hajjaju zata ce ,
magana ta soma mata "Sehrish ni yanzu bansan ya zanyi dake ba, game da aikin nan m, gashi ni already ina da y'ar aiki kuma gsky ko da ace ban da ita, ba zan iya daukarki sbd kina bukatar kudi masu yawa ni kuma iya salary din da nake biyan larai 10k ne."
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 5-6


Jin wannan bayanin daga bakin hajajju yasa jikin Sehrish yin sanyi , bata ce mata komai ba sai ma ta ci gaba da wasa da yatsun hannunta. Ci gaba da magana hajajju tayi "abunda za'ae tunda dai naga sisters din naki kuma munyi magana da gwaggo da take kula daku , ynx ki koma ki ci gaba da kula dasu saboda suna bukatarki kafin Allah yasa asamu aikin ,"
Kamar an dasa ta haka tazauna idonta suka ciko da kwalla, kiris take jira ta fashe da kuka , dama bata jima da gama wancan kukan ba
Wayar dake hannun hajajju ce ta soma ringing , picking tayi tare da karawa a kunnan ta tana fadin " Manyan manyan gari ! Abban sojoji ashe kana nan ba'a neman mu , koda yake dama ku hamshakan masu kudinnan ganin ku sai an cike file."

Natsuwa sehrish tayi tana sauraranta , ta lura da yadda hajjaju ke washe baki da alama koma wanene take wayan dashi Babban mutum ne ,
tuna damuwar da take ciki yasa ta daina sauraron wayar tasu ta shiga tunani kala kala a cikin zuciyarta , har hajjajun ta kammala wayar bata sani ba sai da taji tace "Ga samu ga rashi !!" dagowa tayi da idonta tayi tana kallon , hannu hajjaju tasa ta dafe kanta alamar takaici.

Sehrish tace "Hajiya meya faru?" Hajajju tace "Aiki ya samu mai tsoka , jin hka yasa sehrish ta soma murmushi "amma sai dai kash Namiji suke so mai aiki ba mace ce ba !" lokacin da hajajju ta idasa maganar tuni sehrish ta gumtse fuska hankalinta ya tashi.

Hajjaju ta ci gaba da cewa "ina tayaki bakin ciki gsky, sbd kinga mutumin nan daya kira ni ba karamin mai arziki bane , cos they can pay u 50k as your salary after that zasu dauki dukkan responsibilities din ! Ci da shan ki wurin kwana lafiyayye sannan har school zasu iya saka ki ga sutura ya kike gani "?
Takaici ya hana tace komai ga samu ga rashi , ji take kamar ta cire takalmanta ta watsa da gudu saman titi kota rage radadin da take ji a zuciyanta ,
"Sehrish kinyi shiru baki ce komai ba "? ta jima ba tare da ta ce wani abu ba sai da tayi zurfin tunani kafin tace "ZanJe ! Zan yi aikin a matsayin NAMIJIN akan y'an uwana babu abunda bazan iya yi ba don nayi basaja a matsayin namiji wannan abune mai sauki a wurina ,"
In serious matter take mgnan ba tare da jin wani dar a zciyarta ba dagaske take dai , murmushi hajjaju tasaki don ba karamin burgeta tayi ba saboda tana da confidence akan komai da take so , " hmmm sehrish kenan how can u change ur creator frm a girl to a boy i dont think u can act like a male zasu gane ki ne , "
Matsawa tayi kusa da hajiyar tare da rike kafarta tace "Don Allah hajiya ki taimake ni wlh zan iya , indai za'a samu makeup artist din da zai tsara ni ya mayar dani kamar namiji this is a simple thing , kawai amincewarki nake bukata,"
hannu hajjaju tasa ta cirewa Sehrish hannunta data rike mata leg dinta dashi sannan tace "Babbar magana ! tun da nake bantaba yin wannan kasadar ba , natura house maid mace a matsayin namiji , sannan wannan mutumin da kika ji ina magana akan sa wato Abban Sojoji , y'ay'ansa maza goma sha takwas kuma dukkansu sojoji ne masu rike da manyan mukamai , dalilin dayasa yace namiji suke so a matsayin d'an aiki saboda ba yadda za'ai mace ta iya , bai ma dace ba , balle ma yaransa da kwata kwata basa da sauki , zafin rai ga ji da isa , "
Kamar zata yi kuka ji take in har hajajju bata amince mata ba zata iya rasa ranta , cikin kasalalliyar murya tace "Hajiya ki amince mun kawai ae ni nace zan iya wlh idan baki amince ba shinkafar bera zanci kawai na mutu kowa ya huta don bazansu naga mutuwar y'an uwana ba , " zaro ido hajajju tayi jin ta anbaci zata je taci shinkafr bera , kuma dagaske take ba alamar wasa a mgnrta ,
ruko hannunta tayi saboda harta mike zumbur zata figi hanya , "Meya yi zafi haka dawo ki zauna kinji , ni bazanso nayi sanadiyar mutuwar wannan innocent face din ba ," komawa tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya ,
Shiru suka yi na wani lokaci daga ita har hajajju , jin shirun yayi yawa yasa tace "Hajiya baki ce komai ba am so eargerly to hear frm u ," ta karasa maganan tana kallon ta ,
Wan nan shirun da hajajju tayi sake sake takeyi a cikin zuciyarta "taya zan kai yarinyar nan gidan soldiers a matsayin namiji ! duk ranar da asiri mun ya tonu daga ni har ita kashin mu ya bushe , maganar da sehrish tayi ce ta dawo da ita , " Sehrish i dont know what to do am just comfused ina tsoron hakan fa ,"
"Nima ina goyon bayan yarinyar nan" larai ce tayi maganar shigowarta kenan taji suna tattauna wa , bin ta su kayi da kallo , wuri ta samu ta zauna kafin taci gaba da magana "Wurin samun biyan bukata rai ba abakin komai ya ke ba , tun da har tace zata iya kawai ki amince mata ! saboda ni na taba kallon wani korean film irin haka actress din ciki ta yi shigar namiji ba tare da wani ya gane ta ba kuma tacimma nasara ," jinjina kai hajajju tayi tare da watsa hannayen ta tace "Shikenan Finally i agree tunda har larai ta Jefa miki kuri'a kun rinjaye ni ," dariya sukayi su duka ba karamin dadi sehrish taji ba , ynx hajajju ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login