Showing 54001 words to 57000 words out of 137891 words

Chapter 19 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete

in yaro ya wuce 18yrs yana da ƴanci ba wanda ya isa ya takamasa burki, har shari'a zai iya yi da iyayensa insun takura masa,

Hakan yasa suka ƙyale Alexandra ta auri Abba, ba tare da sanin family ɗinsa ba, shi kuma soyayya ta rufe masa ido baya ganin kowa in ba ita ba, dama fa su akwai iya tarairaya ga ɗaukar wanka da jan hankali,

A nan los angels california suke da zama a katafaren gidanta, nata na kanta dayake itama ta tara kuma ta fito daga babban gida, kuma ita ma soja ce tana riƙe da muƙamin major genaral,

Sunsha soyayya kamar romeo da juliet, acan kuwa 9ja sunyi mamakin jimawar abba, ganin sauran da aka tura Us tare dashi duk sun dawo sai shi kaɗai,

Ga maryam da ƙaramin ciki, kullum cikin zullumi take akan mijin nata,

time ɗin daya shirya dawowa 9ja yasha wahala kafin Alexandra ta amince cewa zata biyo shi na wucen gadi,

Aiko lokacin sun ga tashin hankali, ganin abba ya dawo da mata jinsin turawa, ran mahaifiyarmu baƙaramin 6aci yayi ba, saboda ta tsani jinsin turawa, sbd tasancewa basu da kunya fitsararru ne, an tada tarzoma a lokacin, gaba ɗaya danginmu sukayi masa caaa akan alexandra,

Amma abun mamaki mahaifinmu Salahudeen ya amince masa, kuma ya tsawatar da kowa akanta, ya hana kowa ya sa baki akan alexandra, haka yayan mahaifiyarmu modibbo ya tsawatar mata akan taja bakinta tayi shiru, haka kowa ya zubama sarautar Allah ido 👀

A katafaren gidansa dake abuja suke zaune ya ware mata part ɗinta daban, na maryam ma da ya'yanta daban, kowa baya shiga harkar kowa,

Sam maryam bata kishi da alexandra, tafison su samu zaman lafia a tsakaninsu,amma ita alexandra kishin maryam take ji, bakomai yaja hakan ba face sanin cewa su ba'ayi musu kishiya, basa zama da kishiya,

Cikin rashin sani sai ga ciki a jikin alexandra wanda ya tayar mata da hankali saboda tana shan maganin hana ɗaukar ciki don ita bata buƙatar ƴa'ƴa arayuwarta,

taita faman kiciniyar cire cikin hankalin abba ya tashi, faɗa sosai sukayi a lkcn, yasha wahalarta sbd sai da takai ga har zuƙunna mata yake akan guiwarsa yana roƙonta akan karta cire masa ciki yana so,

dakyar ta amince bisa sharaɗin inta haihu, ba ita zata shayar da yaron ba, kuma ba a nigeria zata haifesa ba, tafi so taje can ƙasarsu saboda tafi yarda da likitocinsu, kada a kashe ta tsoran mutuwa gare ta, 😂

haka ta maida Abba kamar ɗan aikinta da matsayinsa da komai haka zai zauna, yana mata aiki komai takeso shi zatayi, ita dai maryam bata cewa komai binsu kawai take da ido 👀

Hankalinta kwance saboda haryanzu Abba yana tsananin sonta bai wulaƙanta taba, bai kuma canza mata ba, sa6anin wasu mazan da zaka gani daga inda suka yi sabuwar amarya tofa ita waccen tazama expire product, 😥

wata rana yana zaune ɗakinsa saiga alexandra ta shigo da ƙaton cikinta, hannunta ɗauke da farar takarda da wani rubutu ajiki wanda aka rubuta da harshen spanish, ta miƙa masa takardar da biro tace yasa hannu,

_Gudun rigima yasa bai tambaye ta takardar mecece ba kawai ya raftaka signature ɗinsa, ajiki tare da miƙa mata , tayi murmushi ta kar6a, 😂_*💋ABBAN SOJOJi💋*

_mallakin_

_Hafsat Bature_ *Boss Lady*



_subhanallah_Walhamdulillah_Allahu akhbar_🙏


*page* *47* to *48*




_Dont worry your self guys, sergeon general is on the way soon insha Allah_😘

Ya Allah kaji ƙan waɗanda suka rasu, ka gafarta musu, muma in tamu tazo kasa mu cika da kyau da imani, 😔 Mutuwa ake kamar hauka, yakamata muji tsoran Allah muyiwa kanmu tanadin kyakkyawan ƙarshe tunkan tazo kanmu, mu kasance a cikin shiri domin akowane lokaci mutuwa zata iya zuwa😭 Ya Allah kasa mu cika da kyau da imani, Ya Allah ka haife mana zunubbanmu, Ya Allah ka kare mu daga aikata aikin dana sani😢 mu rage dogon buri a rayuwa, mu rage kwaɗayin abun duniya wanda daɗinsa ƙalilan ne, wannan rayuwar bata da tabbas wlh, amma wasu sun mai da ta wurin zama, suna aikata abunda suka ga dama, zalunci iri iri basa tunanin menene makomarsu 😭 Allah kasa mu dace 🙏 wlh sai mun gyara indai muna so muga dai-dai arayuwarmu 😔




Bismillah




a na nan lokacin haihuwarta yayi, abba dakansa yakai ta Airport kamar yadda yayi mata alƙawari,
kuma ya cika,

Cikin sa'a Alexandra ta haifi santalelan yaronta na farko, wanda ya gigita kowa, kyakkyawan gaske mai matuƙar ɗaukar ido, komai nasa na mahaifiyarsa ne ya ɗauko, hatta launin idonta blue eyes,

Ta jima a us kafin ta zo nigeria, domin ta gwada musu babynta, aikuwa nan fa dangi suka susuce akansa, amma ta hana kowa ya ta6a mata yaronta, iya kallo daga nesa, jinsa take tamkar gold koda yake darajarsa tafi darajar zinari,

Abba yayi mamakin ganinta tana shayar da yaron, bayan ita da kanta tace anemi mai raino don baxata shayar dashi nono ba inyazo duniya, da alama soyayyar yaronce ta kamata,

A lokacin itama maryam ta haifi nata yaron kyakkyawan gaske wanda duk cikin ya'yanta bamai kyansa, farinciki a wurin abba ba'a magana a lokacin yama rasa ina zai tsoma kansa, saboda ƙaunar yaran nasa da aka haifa masa,

Babban tashin hankalin shine, Alexandra ta tada 6alli akan cewa yaronta addininta zai biyo kuma tasanya masa suna Alex, nan fa hankalinmu ya tashi, kowa ya harzuƙa akan lamarin,

Ran abba ya 6aci sosai kamar yayi ihu, a ƙarshe daya takura mata akan cewa shifa yaronsa addininsa zai biyo, sai ta ɗauko masa wannan takardar daya sa hannu ajiki wadda akayi rubutu ajikinta da harshen spanish ta nuna masa,


Cikin rashin sanin ma'anar hakan yace "me wannan ke nufi"?
Dariya tayi masa tare da cewa " wannan takarda dace, ta yarjejeniya dake nuna cewa ka amince ƴa'ƴana su bi addini na! in har ka matsamin zamu shiga court ne ayi shari'a, kuma kada kayi tunanin zaka iya ɗauke takardarnan domin akwai copy ɗinta awurina ba ɗaya ba, signature ɗinka ne ajiki, 🙆

Hankalin abba fa ya tashi, bai ta6a dana sanin auren Alexandra ba sai alokacin domin takaisa ƙarshe, Ashe wayau tayi masa, tasan hakan zai faru shiyasa tayi rubutun da harshen spanish, shi kuma gudun rigima ya sa bai tambayi menene fassarar abunda aka rubuta ajiki ba kawai yasa hannu, 😥

yaso ya tada 6alli akan koma mai zai faru sai dai ya faru , amma maryam ta dakatar dashi takwantar mashi da hankali ta nuna masa cewa, inya bi komai asannu wata rana ita da kanta zata canza, canjin da har yau muke jira amma Alhamdllh an samu ci gaba,

Bakowa bane wannan yaron da ake tada jijiyoyin wuya akansa ba face Surgeon general Rafayet wato BABBAN YAYA,

tun yana jariri bai ta6a kuka da hawaye ba, kuma likitoci sun tabbatar da cewa lafiyarsa garas, amma momynsa har ƙasar waje ta fiddasa aka ƙara dubasa aka tabbatar mata da lafiyarsa, sannan ta yarda,

A lokacin da yana yaro yayi tashen ƙiwuya, ya tsani bakar fata indai launin fatarka ba fara bace irinta mahaifiyarsa tofa kun raba jaha,

Duk bala'inka baka ɗaukarsa, hatta mahaifinsa dake mutuwar son shi, bai yarda da shi duk da hasken fatar abban nasa, tsakaninsu sai dai kallo daga nesa , sai kuma in yana bacci uban ya lalla6a yaje ya zuba mishi ido yana kallonsa,

Shi kuma yaron da maryam ta haifa, ba kowa bane fa ce Marshal omer tazarar satittika ne a tsakaninsa da Rafayet,

Tun suna yara omar ke son wasa da rafayet, amma bai yarda dashi ba duk da kasancewar omar fari ne sosai kamar balarabe, yabiyo mahaifiyarsa Maryam bafullatana,

Gashi shima rafayet ɗin yana son Omar amma tsakaninsu sai dai daga nesa a rinka jefawa juna murmushi 😊

daya ƙara wayau hankali ya fara shigarsa, wata irin shaquwa ce ta shiga tsakaninsa da omar, duk da momyn shi bataso yana hulɗa dasu,
kai har takaiga idan dare yayi sai ya saci hanya daga bedroom ɗinsa izuwa nasu, ya haye saman gadonsu wurin omar ya kwanta kusa da shi,

Shima omar ɗin harya gane idan dare yayi, yazauna yaƙi bacci yayi ta zaman jiran rafayet, har sai yazo sannan su kwanta tare suyi bacci,

Maryam kaɗai ce ta lura da hakan, ita dai ba ruwanta, tana son rafayet tanajinsa kamar ɗan cikinta, haka zata je tayi musu addu'a tashafa musu kawunansu,

Ranar da alexandra ta gane hakan akan idonta, taga rafayet ya shiga ɗakinsu omar tsakar dare , aiko washe garin ranar tarinƙa zabga masifa har sai da kowa ya gaji,

Bayan wannan lokacin maryam taci gaba da haihuwa a inda ta sake haihuwar namiji again wanda yaci sunan shi najeeb, gaya nan kuna kallonsa, wato captain najeeb,
daga shi kuma sai Kanal yusif shima gashi nan zaune, daga yusif kuwa sai commender haroon, daga haroon sai Captain adams,

daga adams sai khaleed daga shi kuma sai jabeer da irfan, haka ta haifesu, daga nan ne ta dakata,

A bangaren Alexandra kuwa shiru sbd tace ta kammala nata, abba najin baƙin cikin musamman inyaga Ya'yansa zasu masallaci sun haɗu su duka amma babu rafayet acikinsu,

Ya so ya sake tada 6alli akan yaron, saboda yana da hanyar da zai kwaci kayansa daga faɗawa daga halaka, amma mahaifiyarsa tayi masa tatass akan cewa lokacin da ya aurota dawa yayi shawara, taja masa kunne akan cewa kada ya kuskura ya ƙara tankawa akan alexandra,

A dolensa yaja bakinsa yayi shiru bisa umarnin mahaifiyarsa,
A karshe ya koma yana nuna mata soyayya don yaja hankalinta, y rinƙa binta sau da ƙafa,

dalilin komawar Rafayet us da zama ba kowa bane face wan mahaifiyarsa mr donald, mugun son rafayet yake kamar hauka, duk weekends sai yazo nigeria don kawai ya gansa, kai daga baya ma sai ya kai sau 3 yake zuwa a week sam baya gajiya da zarya daga us zuwa 9ja, ran abba yayi matuƙar 6aci, har dai wata rana ya tambayi donald yace masa wai shi bai da ƴa'ƴa ne? da buɗen bakinsa sai cewa yayi, shiya riga da yayi plan ƴa'ƴa biyu yake so arayuwarsa, yanzu ya samu ya'yan kuma dukkansu mata ne, guda biyun ,

abba tamkar ya shaƙe shi haka yaji, wato tunda yasamu biyun duk mata, shiyasa ya dakata bayan yasan cewa yana son ɗa namiji,

Ba yadda abba ya iya haka ya zuba ma sarautar Allah ido 👀 haka donald zaizo yaita kashe ma rafayet kuɗi shida omar, kamar hauka bai gajiya,

bayan wannan kuma abba yaji yana son ya sake samun ƙaruwa da Alexadra, yaje cikin lalama yayi mata magana, sai yaga tana dariya abun ya ɗaure masa kai ,

gyara murya tayi tare da cewa " na amince zan sake haifa maka ƴa'ƴa har 3 amma bisa sharaɗin cewa zaka amince Alex ya koma wurin ɗan uwana Donald da zama gaba ɗaya, don na fi yarda da ya zauna can sbd zai fi samun tarbiya, zai wataya ya samu rayuwar ƴanci,
.(wai tarbiya a us 😂)


Kai tsaye Abba yace ya amince dalili kuwa shine ya gaji daganin rafayet ba sallah ba salati ba karatun ƙur'ani, kwara ma yayi nesa dashi zaifi samun salama,

Amma shima yace yana da sharaɗi guda ɗaya, tace tana sauraronshi,

Abba yace "yaran da zata haifa mashi dole su bi addininsa wannan karan,'

Batayi masa gardama ba tace ta amince, a wannan lkcn ALexandra ta ajiye aikinta gaba ɗaya, sbd ta mallaki komai takeso a ynx, tayi mai isarta ynx lokacin hutun rayuwarta ne acewarta,

A nan ne kuma cikin ikon Allah ta samu ciki, a inda ta haifi twins tagwaye wato Ayaan da jahan, kyawawan gaske Allah ya zuba musu kyau, abba yayi farin ciki sosai, da aka tashi sa masu suna akexandra tace Za6i na wurinta, sbd a yarjejeniyarsu bai ce zaisa ma yara suna ba, don haka tasanwa Ayaan (John) Jahan kuma (James) kowa ya zuba mata ido 👀

daga su kuma ta ƙara samun ciki inda ta haifi fawan shima tamkar sauran wurin kyau, kyakkyawan gaske Fari sol, a inda tasanya mishi suna (Michael) nan Ma kowa ya zuba mata ido 👀

Bayan shine ta dakata da haihuwar gaba ɗaya, nan fa abba yasa rigimar cewa haihuwa uku tace zata yi masa, ita kuma tace ae inya lissafa da twins da fawan ƴa'ƴa uku kenan, ba dole sai ta yi ciki uku ba, Allah ya kawo mata cikin sauƙi,

Rigima ta 6alle a tsakaninsu daga ƙarshe da Abba yaga ba riba sai ya koma yana lallashinta akan ta taimaka masa ta haifa masa last born, uhmmmmm

A lokacin maryam tana ɗauke da cikin autanta na ƙarshe wanda a wurin haihuwarsa ne ta rasa rayuwarta, bakowa bane fa ce Talal,

Aunty azeema ta faɗi tana nuna sa, jikinsa yayi mugun sanyi, tuni hawaye sun zubo masa, haka sauran ma duk jikinsu ya mutu,

Ita kuwa alexandra dakyar abba ya samu ta haifa masa last born ɗinsa,
Wanda ya tafi da zuciyar kowa, da irin kyawunsa, shi na musamman ne, kowa rububinsa yake tun yana yaro yake fama da athma, ko ban faɗa ba kunsan ko wanene, mahaifiyarsa tasa mashi suna ROMEO, a inda mukuma muke kiransa Junaid,

Ansha wahala sosai kafin alexandra ta kar6i musulunci, a inda sunanta ya canza daga Alexandra zuwa FATIMA, kowa yayi tunanin cewa tayi imani da Allah ne, ashe ita bada son rantaba takar6i addinin,
Takurawar abbace,

dalilin barin alexandra nigeria tsakaninta da mahaifiyarmu ne basu shiri, hajiyarmu ta tsane ta ba don komai ba sai don yadda take wahalar mata da ɗanta,

Duk in tazo abuja gidan abba sai sunyi cece ku ce, tun daga ranar da hajiyarmu ta buɗe baki tace ma Alexandra musuluncin ta ba kar6a66e bane, ta musulunta a banza domin kota mutu wuta zata shiga,

Ran Fatima ya 6aci sosai jin wannan maganar hakan yasa, ta koma addininta kai tsaye,
shiyasa ba a so in mutun ya shiryu arinƙa ƙyamatarsa ko kuma ana goranta masa, sbd gudun irin hakan ynx gashi ta koma yar gidan jiya, a ƙarshe da hajiyarmu ta Tsananta mata da baƙaƙen maganganu, ranta ya 6aci sosai

Wannan shine silar da fatima ta koma ƙasar Australlia da zama wurin danganin mahaifiyarta can sydney, babban tashin hankalin ma tabar masa jinjirin yaro batare da idasa shayar dashi ba,

Junaid yaga rayuwa, naso na ɗauke shi,amma azmee ta nuna cewa tana so ta shayar dashi, shiyasa nabarmata sbd nima ina shayar da talal da mahaifiyarsa ta bari,

Rafayet ya musulunta ne a sanadin omar, saboda duk ƙarshen wata donald yana kawosa su gaisa da mahaifinsa, a haka ahaka har suka ja ra'ayinsa duk da ansha wuya kafin asamu ya kar6a, abba yaji daɗi sosai a lokacin, shima kuma donald yayiwa abba alƙawarin cewa bazai ta6a takurawa rafayet akan addininsa ba, zai bashi ƙwarin guiwa duk da kasancewar shi mabiyin addinin catholic,

A lokacin abba ya haɗa rafayet da omar tare ya damƙawa donald ba don komai ba, sai don kukan da yake yi mashi akan yana son ya zauna kusa da ɗan uwansa, sun shaƙu sosai, duk in zasu rabu sai sunyi zazza6in rashin junansu,
Sannan kuma haɗa omar da rafayet ba ƙaramin ci gaba muka gani ba , domin shike juya rafayet, ya ja ra'ayinsa sosai akan musulunci yana ƙara nutsar dashi, yana tunasar dashi akan ibadarsa da kuma addininsa, da haka aka samu rafayet har ya sauke al'qur'ani mai girma, A shekarar daya musulunta kowa yayi mamakin hakan, duk da munsan cewa shi na musamman ne lu'u lu'u ne , mr donald yayi bajinta domin har yau muna ƙara jinjina masa kuma muna yi masa addu'ar Allah yasa ya musulunta dashi da yar uwarsa fatima,
Domin shi yayi ɗawainiyar su rafayet da marshal omar har suka kai wannan matsayin da suke a yanzu wanda duniya tasan dasu ,
Kuma shi da kansa yasama musu malamin addini wanda ke koyar dasu littattafan addini tun suna yaransu,

Tun wannan lokacin fatima bata ƙara taka nigeria ba, sai dai duk mai son ganinta yaje inda take,

Wannan shine takaitaccen labarin gidan Abban sojoji, Allah yasa an fahimta,
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa "Allah ya jiƙan surukata, ya haskaka ƙabarinta,yasa Aljanna ce makomarta, da dukkan waɗanda su ka rasu Allah ya gafarta musu, Alfarmar annabi muhammad (SAW) ❤
gaba ɗayansu suka amsa da amin ,sannan ta ƙara da cewa "sannan muna yi ma fatima addu'ar Allah ya shirye ta, yasa ta gane gaskiya ɗaya ce, ya bata ikon musulunta, da ita da ɗan uwa Donald,'
Jikinsu twins da fawan yayi mugun sanyi, ta shi su kayi cikin wani irin yana yi zasu shige ciki.....................😔*💋ABBAN SOJOJI💋*

_mallakin_ *HAFSAT BATURE*💓

*BossLady*🫶



_Subhanallah_ _Walhamdulillah_ _Allahu akhbar_ ☝️


*page* *49* to *50* 🤗


_💋Extraordinary Love💋_





general ishaq yace "kai ina zuwa? Maza ku dawo ku zauna, ku ka yana magani ne? ynx tsakanin ku da mahaifiyarku addu'ace kawai, that's the only solution, in Allah yasa fatima zata musulunta ae ba wanda ya isa ya hana hakan,'

Cikin shesshekar kuka fawan yace"idan ta mutu fa ba tare da ta karbi addinin musulunci ba, azabar Allah zata tabbata akanta ne, kuma wuta zata shiga, aduk lokacin dana tuna wannan ina jin ƙunci araina...'
Ayaan ma yace "abba bai kyauta mana ba, kullum cikin zullumin makomar mahaifiyarmu muke,'
Jahan yace "kuma bata son mu, ta kama hanya tayi tafiyarta, ko waiwayan mu bata yi, ita wata irin uwace? cikin rashin tausayi ta tafi ta6ar ƙaninmu shi da bai mallaki hankalinsa ba, da tun farko Abba ya za6a mana uwa tagari munyi rayuwarmu cikin salama, da ynx labarin ba haka zai kasance ba,
"Kada na sake jin wani daga cikinku yayi magana, ku koma ku zauna, koba komai ae kuna da mu, wani irin gatane bamu nuna muku ba, mu fa jini ɗaya ne, babu wani banbanci a tsakanin mu ! ku kun kasance jinin dake yawo ajikinmu, kasancewarku farar fata ba hakan yana nufin kun fita daban acikin mu ba, kuma don mahaifiyarku ta tafi ta barku ba hakan yana nufin kun rasa wani sashe na jin daɗin rayuwarku ba,
Da ran mu da lafiyarmu bazamu ta6a bari hawayen ɗaya daga cikin ku ya zuba ba, Allah ya riga ya haɗa kuma ba wanda ya isa ya raba, nasan cewa abunda Ammy take yi muku bakwa jin daɗinsa, shine abunda yasa ku ke jin kan ku daban, to inaso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login