Showing 39001 words to 42000 words out of 137891 words
Chapter 14 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
matsayi aduniya kuce zaku wulaƙanta wanda ke ƙasa da ku domin bakusan Wace rana zai yi muku ba, kuma Allah zai iya kar6e wannan matsayin da kuke taƙama dashi yaba shi wannan wanda kuka ƙasƙantar aranar ya zakuyi ? kowa zai iya kuskure a rayuwarsa amma aduk lokacin da wani yayi maka badai dai ba kazamzo mai hakuri da yafiya domin Allah ma yana gafarta mana in mukayi ba dai dai ba sai mu ƴan adam zamu gaza yin haka bazamuyi koyi da manzon Allah (SAW) ba ?
tuna wannan maganar yasa shi fita cikin sauri ya , cikin gaggawa yake saukowa down stair a lokacin har sehrish ta sume a ƙasan last step ɗin benen, shi kasan fawan baisan hakan ya faru ba saboda wayarsa yake ta faman daddanawa ,
Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda me aikin nasu yake sume a kwance ba numfashi ,
tsallake sa yayi ya wuce inda fawan ke saune sai faman murmushi yake yana daddana waya ,
Kamar daga sama yaji an fizge wayar daga hannunsa, cikin sauri ya ɗago yana kallonsa yace "Junaid wannan wane irin abune zaka sa hannu ka fisge waya daga hannuna kamar wani tsaranka,'
harara junaid ya wurga masa tare da cewa "bansani ba! saboda tsabagen mugunta irin taka kasa wancen mai aikin wahala wadda tasa shi sume wa amma sam baka damu ba ,"
tsoki fawan yasaki tare da sa hannu ya ƙarbe wayarsa ya wuce tagabansa yana faɗin "Matsalarsa ce,"
Binsa da kallo yayi har ya shige bedroom ɗinsa,
Ba yadda junaid ya iya dole ya koma inda tukur ke sume yasa hannu ya ɗaukesa, sam baima san ina ne inda ɗakin kwannansa yake ba ,
Amma yasan cewa bazai wuce kwanar da ɗakin azmi take ba, kama hanyar yayi , ko nauyi baya ji haka ya dauke ta kamar yar baby ,
cikin sa'a ya samu ɗakin,da kafarsa ya turo kopar ɗakin ya shiga da ita , a saman bed ya kwantar da ita
Ransa ne ya basa ya dauko ruwa a freezer yazo ya yayyafa masa , yana sa hannu zai buɗe kofar idonsa yakai a jini dake hannunsa, har sai da gabansa ya faɗi rass ! ya soma tunanin jinin menene wannan !!! 😳
Bin jinin da kallo yayi tunani yayi kodai kansa ne ya bugu ayayin da ya sume a gefen stair,
Don haka cikin sauri ya koma yahau saman gadon inda ya kwantar da shi, a hankali yasa hannunsa yana tattare hular dake kanta a ƙoƙarinsa na ya cire hular yaga ta inda jini ke zuba,
Can kuma ya fasa saboda ganin yadda fuskar tukur ɗin ta dame da jini da majina, handkchief ya zaro daga front pocket ɗin rigarsa, ya shiga goge mata fuskarta,
Kwatsam gashin bakin da take manna wa a fuskarta ya ya goce saboda ya jigata gashi dama gam gare sa ruwa ya taba sa sosai ,
Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin ya cirewa tukur gashin bakinsa duk sai yaji ba daɗi yakai hannu domin ya gyara sai yaga ya ballo gaba ɗaya, da ya ƙura ido yana kallon ƙasan hancin sai ya gane cewa dama babu gashin bakin fixing ɗinsa akayi,
Saboda babu hudojin gashi a wurin sai kansa ya ɗaure ya gaza gane menene dalilin liƙa gashin baki,
tabe bakinsa yayi alamar i don't care, ci gaba da gogewa yayi ana haka sai ya ga gashin girar ta da aka liƙa masa shima ya zame gefe guda, tashin hankali a fili ya ce meke faruwa ne wai
Hannunsa ya sa ya ciro gashin girar duka guda biyun nan take asalin jagirarta mai kyau ga tsari ta bayyana,
Natsuwa yayi ya ƙurawa face ɗinta ido sai yaga fuskar ta koma ta mace sak ! Kansa ya gama ɗaure wa sanya gashin girar dana bakin yayi cikin handkchief ɗinsa ya naɗe su ciki ya ajiye gefen bedside drawer ɗinta,
Ya jima yana kallon wannan kyakkyawar fuskar har lokacin bai kawo wa ransa cewa maca ba ce ba sai da yasa hannu ya tumbuƙe hular dake kanta, nan take gashin kanta ya tarwatse ya warwaro har saman shoulder ɗinta mai kyau ga laushin gaske,
Nan fa junaid yayi zuru yana ganin wannan ikon Allah ( wonders shall neva ends)
ganin ta soma motsi zata farka, yasa shi yin wuff ya dira daga saman bed ɗin ya boye abayan curtins ɗin dakin,
buɗe idonta tayi waɗanda suka cika tab da kwalla, sunyi jawur sun ƙanƙance, wani irin raɗaɗi taji a marar ta, gashi sam ba ƙwarin jiki atattare da ita, wata irin kasala ce ta dabaibaye ta a galabaice ta miƙe tana zubar da hawaye, yunƙurawa tayi tare ɗan matsawa gefe nan taga jini malale a saman bedsheets ɗinta ya baci sosai ,
Wani irin mugun bugu xuciyarta tayi mata saboda ita sam batasan jinin menene ba, saboda bata ta6a yinsa ba wannan ne karo na farko a wannan shekarun nata 17years,
lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka ganin jini 6aro 6aro na fitowa daga jikinta, cikin kuka take faɗin "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan na mutu wayyo Allah wannan wane irin ciwo ne naji haka, nasan mutuwa zanyi
tashi tayi a firgice tasa hannu ta cire zanin gadon ta nannaɗe sa ta ajiye sa anan,
gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta zabure kamar wata mahaukaciya tama rasa me zatayi , cikin toilet tashi ge tana kukan baƙin ciki ,
A jiyar zuciya junaid yasaki, har yanzu ya gaza gasgata abunda idonsa ke ganin masa, shin wanene wannan tukur mai aikin mu ko kowa ? kamar mace nake gani fa, oh my God mafarki nake ko gaske, kodai idanuna ne ke nuba min hakan taya tukur mai aikinmu zai kasance mace !! Ya jefa kansa wannan tambayar
Hannu yasa tare da murxa eyes ɗinsa don yayi comfirming abinda ke faruwa cewa gaskiya ne its not a dream,
yana nan tsaye la6e a bayan labulen yana jiran fitowarta, saboda ya gane wa kansa zahiran abunda ke faruwa ,
Sehrish kuwa tamkar ranta zai fita, saboda tsoran jinin da ta gani ga kuma ƙyanƙyami daya kamata,
cire wandon jikinta tayi sannan ta cire rigar ma, hannu tasa ta balle abunda take matse ƙirjinta dashi tayi wurgi dashi,
ta firgita da ganin yadda jinin yake gangarowa a tsakankanin cinyoyinta kai kace fanfo aka buɗe,
Cikin tsananin tsoro ta ƙarasa gaban fanfo tashiga dambe da jinin nan ita ala dole sai ta dakatar dashi daga fitowa 😟
Tana wanke wa yana sake kwaranyo wa kamar ana ingiza shi,
ganin yaƙi tsayawa yasa ta dakata, ta zuƙunna a wurin tana kuka tayi mai isarta, sannan ta yanke shawarar ta koma cikin bedroom ɗin ta samu wani abu ta cusa, sam ta manta cewa pant ɗinta ɗaya ne kuma ya bace shima, koda me zata sa ?
A haukace ta fito cikin sauri junaid ya rufe idonsa tare da jan labulen ya rufe face ɗinsa, bai jin daɗin tsayawa ba saboda yaga abunda yake haramin agare sa sam babu kaya ajikinta,
Jikinsa ne yasoma kerma nan take yadinga jin zuciyarshi na tashi ynx ya tabbatarwa kansa cewa tukur mai aikinsu zankaɗeɗiyar budurwa ce ba namiji ba, shigar maza kawai take yi saboda wani dalili nata,
buɗe wardrobe ɗin tayi saboda rashin natsuwa duk ta watso da kayan dake ci tashi ga laluben ɗan kyallen da zata sa, wani mayafi ta ɗauko sai da ta riƙe sa gam a hannunta sannan ta tuna cewa bata da pant ɗin da zatasa,
zuƙunne wa ƙasa tayi ta shiga rera wani sabon kukan, gwanin ban tausayi jin har yanzu wannan blood ɗin yana mata flooding a under ɗinta yasa ta koma cikin toilet tana kuka,
Shiga tayi taja kofar ta rufe ...
Ganin ta shige yasa junaid saurin fita daga ɗakin, tafiya yake amma tunanin yadda zai taimaka mata yake yi saboda ya gane cewa akwai abubuwan da take buƙata, amma tayaya? bayaso ta gane cewa ya ganta a matsayin mace, baisan wani hali zata shiga ba,
Maganar abbansu ya tuna a inda ya ke cewa
_aduk lokacin da kuka ga wani na buƙatar taimako, to kutaimaka masa indai kuna da halin yin hakan, a sanadiyar hakan kuma Allah zai agaza muku a lokacin da kuka shiga wani hali na rayuwa,"
Cikin sauri ya hanzarta nufar bedroom ɗinsa , key ɗin motarsa ya dauko tare da kuɗi , sannan cikin gaggawa ya kama hanya ya fita daga main palour ɗin ,
Babu kowa tsit kake ji amma ko'ina akwai haske kamar rana, saboda an ƙawata gidan gaba ɗaya da wasu irin electric bulbs,
Moto park ɗinsu ya nufa buɗe inda tarin motocinsu ke nan, motarsa yayi ya shiga nan take yayi mata key yaja ta,
Sam junaid ya manta cewa security guards ɗin gidan soldiers ne kuma bana wasa ba, kuma ba'a basu iznin subar wani ya fita a wannan lokacin ba kosu fawan dake satar hanya su fita night club su suka san ta boyayyiyar hanyar da suke fita,
Santal ya miƙi titin da zai sada ka da babban gate ɗin gidan, yana isa wasu gabza gabzan sojoji guda 4 suka tunkare sa kamar zakuna,
a dolensa ya dakata da tuƙin ya tsaida motar, jikinsa sai rawa yake yi ba don komai ba sai don uzirin dake gare sa, zuge glass ɗin motar yayi yana kallonsu a yatsine, .
"Where are you going in this darkness night,"? ɗaya daga cikinsu ya tambaya yana kallonsa, banza yayi baice musu komai ba don yasan koya ce ɗin ba barinsa zasu yi ya fita, rigima ce zata tashi ƙarshe suce zasu sanar da Abbansu a tada hargitsin duniya,
jin yayi shiru yasa ɗaya daga cikinsu daka masa tsawa tare da cewa "maza ja mota ka koma gida ƙaramin yaro dakai sai taurin kai,'
Ɗaya daga cikinsu ne ya kwatsa ma wanda yayi masa tsawa magana" stop shouting at him ! he's a young lallashinsa ya kamata kayi ya koma "
xukunno wa yayi cikin lallami ya ce masa "pls go back ba'a bamu izni mubar wanin ku ya fita ba daga gida a wannan time ɗin,'
girgiza kai junaid yayi tare da cewa "am sorry to say i won't go back just allow me to go, duk rigimar da za'ayi sai dai ayi amma ba inda zani i will stay here till u give me the permission to go,'
Ya ƙarasa maganar tare da jingina kansa jikin kujerar motar yana kallonsu fuska adaure"
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Page 33-34
Kallon juna suka shiga yi, ganin cewa ya toge yasa ɗaya da cikinsu sake yi masa magana cikin lallami " tell me why do u want to go out ? if u need something i can go and buy it for you ,"
Jin hakan yasa junaid jin sauƙi aransa, hannu yasa ya zaro kuɗi kusan dubu goma ya miƙa masa sannan ya cije ya daure ya ce "pads nake so na mata kwali guda sannan panties dozen ɗaya bansan size ɗin ba amma karya wuce na ƴar 17 years "
tsananin mamaki ne ya kamasu jin yace pad da panties, amma basu ce komai ba saboda baya a tsarin aikinsu fira ko tambaye tambaye da ɗan masu gida,
"Sojan yace shikenan, ka koma ciki nan da 15 minutes sakonka zai iso,
Amsa yayi da cewa "thank you i will be waiting,"
Sannan yaja motar a hankali yayi baya da ita ya karya kwana ya koma ciki,
A bangaren sehrish kuwa tagama galabaita, ta jigata sosai tarasa uwar ubanta , sai faman zarya take tsakanin toilet da bedroom , daga taji ya zubo sai taje ta wanke ta dawo ciki yana ƙara zubowa sai ta koma da gudu tana kuka 😖
Junaid sai faman zagaye zagaye yake yi acikin babban falon yana jiran dawowar sojan da ya aika, sai faman zullumi yake yi gudun kada yarinyar ta halakar da kanta da damuwa saboda ya lura ta tsorata sosai,
Knocking yaji da sauri ya ƙarasa bakin kofan shiga falon , sojan ne ya dawo hannunsa ɗauke da kwalin pads tare dozen na pant kamar yadda ya umarta , hannu junaid yasa ya karba yana zabga masa godiya,
Sergiant ɗin yace "ga sauran chanjin " ko dubu biyar bai kashe ba a siyayyar junaid yace " bana buƙata"
Yana faɗin hakan ya kama hanyar da ɗakin sehrish yake,
murmushi sojan yayi tare da cewa a cikin zuciyarsa "lallaine yaro! iyayenka sun tara ma kana daga zaune kana shan iskar A.C,'
yana faɗan hakan ya juya ya fi ce,
Cikin sanɗa yake tafiya time ɗin da ya isa kofan ɗakin tsawa yayi jikin door ɗin yana sauraren kukanta tana cewa " Ya Allah kadauki raina na huta, narasa me zanyi bansan menene ke faruwa da ni ba, jini ko ina ya ilahi
lumshe idonsa yayi tare da buɗe su lokaci guda, hannunsa na rungume da kwalin pads ɗin ga panties ɗin dake cikin leda asaman kwalin ya haɗa ya rungume a ƙirjinsa,
"Junaid ynx taya za'ae ka kai mata wannan ? Shin zata ji daɗi kuwa idan ta gane cewa ka gane cewa ita maca ce ba namiji ba? mezai faru idan tagane cewa ka ganta acikin wannan yanayin zata ji daɗi kuwa !?
Natsuwa yayi yana sauraran abunda zuciyarsa ke sanar dashi , rufe idonsa yayi tare da cizon red lips ɗinsa yana mai jin takaici gaza shiga yakai mata taimakon gaggawa, ga kukanta da yake ji ba ƙaramin hurting ɗinsa yake yi ba, tausayinta yake ji saboda bata da kowa anan da zai taimaka mata in bashi ba dayasan halin da yake ciki, Allah sarki daɗin uwa kenan da ƴan uwa da ace tana da ɗaya daga cikinsu a kusa da ita da abun yazo mata da sauƙi,
Jin alamar ta shiga cikin toilet yasa shi yin saurin kutsa kai a hankali ya shiga, ya ajiye mata kwalin pads ɗin a saman gadonta abunda bai sani ba sehrish bata da masaniya akan wannan abun daya ajiye mata,
Jin alamar tana ƙoƙarin fitowa yasa shi yin wuff ya fice, a kofar ɗakin ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya natsuwa yayi yana sauraran ta taciki,
Sai faman wiping tears take yi, tayi jaga jaga tafita out of sense ɗinsa, har wata ƴar rama tayi ga azabar menstruation ga tashin hankalin blood din dake bleeding a in between legs ɗinta,
dakyar tasamu ta ɗaura wannan mayafin fari mai sharara ajikinta, tsayawa tayi agaban mirror tana lalube lalaube ita kanta batasan me take nema ba kawai burinta tasamu abunda zata cusa a vagina ɗinta ko tasamu yadaina zuba tana cikin laluben nan ,
Karaf idonta ya hango mata kwalin nan da junaid ya ajiye mata a saman bed, ta cikin madubi ta hangosu,
A firgice ta juya tana kallonsu, cikin tsananin tsoro take takawa a hankali tana tunkararsa har ta isa gabansu,
Tsayawa tayi cak tana kallonsu , ledar sama tabi da kallo dayake ta kana iya hangen set na panties ɗin da ke ciki, tabbas tagane cewa pant ne amma tarasa gane wannan madai-daicin kwalin na menene 😥
Karanta jikinsa tayi tare da furta "Dry love" sunan pads ɗin da tagani ajikinsa kwalin kenan,
tunani take wanene ya ajiye mata wannan? anya ba al'janu bane ba? waiwaye ta shiga yi tana kallon gefe da gefenta taga ba kowa sai ita,
Kamar wata sullu6uyo haka ta koma, hannu takai cikin tsoro ta ɗauki ledar panties ɗin ta zaro su tana kallo,
Ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, amma bata jin zata iya anfani dasu saboda batasan waya ajiye mata ba,
Ajiyesu tayi sannan takai hannu tasha fa saman kwalin pads ɗin kafin ta janye hannun cikin wani irin yanayi furta " Ya allah ka tsare ni daga sharrin aljanu, ni dama nasan wannan blood ɗin da nake gani bana lafiya bane, ashe sune suka shafe ni,"
Nan tashiga jera wani kukan, duk a kunnan junaid ganin cewa zasu kwana ido a buɗe ga dare yayi sosai kusan ƙarfe 1:00 ynx ,
Cikin kuka ya sake jiyo ta tana cewa "Dan Allah koma wane aljani ne yake hukunta ni akan ƙaryar da nayi na shigar mace a matsayin namiji don Allah ayi haƙuri a haife mun wlh nima ba da son raina nayi ba.." kuka ne yaci ƙarfinta
Jin cewa yarinyar tayi amanna da cewa aljanune suka kawo mata kayan nan kuma sune suke horar da ita yasa junaid gyara muryarsa cikin wata irin amsa kuwa yace "Ke ! Yarinya ! mune nan ke hukunta ki bisa zunubin da kika aikata ! ," .
Zaro ido sehrish tayi jin wannan muryar mai ban tsoro tabbas wannan muryar aljanin ce ta faɗa a ranta, nan take zufa ta soma sintiri a fuskarta dukkan ilahirin jikinta kuma ya soma makekketa, ta ƙanƙame jikinta a tsorace tace "dan Allah kuyi hakuri bazan ƙara ba i promised u kuskure ne ku yafe mun wayyo Allah na nashiga ukuna,"
murmushi junaid ya saki dama yayi tunanin hakan yadda take a firgice tsaf muryarsa zata koma mata ta aljanu,
don haka ya ƙara gyara muryarsa ya ɗaga ta sosai ya ce "Munjiiiiiii ! Zamu iya yafe miki amma bisa wasu sharruɗɗa in kuma kika kuskure zamu raba sassan jikinki mu kaisu bayan duniya hhhhhhhhh,"
ya ƙare da wata irin dariya mai razanarwa, nan take fitsari ya kubce mata ta tsorata matuka kuma ta ƙara tabbatarwa kanta da cewa aljanun ne ke maganar saboda ita dai bata ga kowa ba acikin ɗakin,
cikin kuka tace "Na amince komai kuke so zanyi," .
lumshe ido junaid yayi shi kaɗai yasan yadda yake jin daɗin wannan yanayin,
Hannu yasa tare da gyara makoshinsa yace "Sharuɗi na farko ! Zaki runtse idanunki kada ki buɗe har sai munce ki buɗe in ba haka ba hhhhhhhhhhhhhhh zamu tsoma ki jikin rijiya gaba dubu,"
la66anta har rawa suke yi wurin faɗin "Na amince na amince zann ..zann