Showing 72001 words to 75000 words out of 137891 words

Chapter 25 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete

kerma,

Allah yaso bata ɗago ta kalli cikin mirror ɗin ba, da tabbas sai tayi fitsari a wando, in tayi arba da kwayar idonsa me rikitarwa,

gaba ɗaya komai ya tsaya cak, jiki ba ƙwari sehrish ta duƙa a hankali tana tattare abunda ta zubar, cikin gaggawa take tsince bananar da ta zubar da tufan da lemun 6awo sai tsintarsu take tana jerawa a tray ɗin, zufa na ɗiga a face ɗinta sunan Allah kawai take ambato,

Abunda bata sani ba, jira yake kawai ta ƙaraso zata ɗauki apples ɗin dake wurin ƙafarsa yayi mata Kyakkyawan riƙo, itama ba hauka take ba a hankali take bin tufan dake wurin ƙafarsa da kallo so take takai hannu ta ɗauka, amma zuciyarta nace mata "Karki kuskura"

hawaye har sun soma wanko mata a fuska, cije wa tayi ta daure zata ɗauka har takai hannu, Junaid ya turo door ɗin yana faɗin "Am back babban yayanmu,"

Jinsa yasa tasaki ajiyar zuciya, shima ganin sehrish ga kuma halin da take ciki yasa shi ƙarasawa da sauri yana faɗin "Let me help"
.shiya sa hannu ya tattaro mata apples ɗin, yasa mata a tray ɗin yana kallonta duk ta firgice,
Cikin rawar murya tace "Nasa ne aunty azmee tace na kawo masa,"
Ƙarba junaid ya yi tare da cewa "ok ki je kawai,"

tana miƙa masa ko waiwaye batayi ba, ta fice jiki na rawa wato tagama rikice wa, wai a hakan ma bata ga fuskarsa da kyau ba,

Kamar wata zararriya haka ta koma kitchen din, duk tabi ta ruɗe she was amazed by his beauty,
Kallo guda azmee tayi mata tagane cewa ba lafiya, cikin mamaki tace "Sehrish lafiyarki kuwa"? da budar bakinta sai cewa tayi "Babban yaya aunty azmee,' wuce wa tayi gaban kitchen sink ɗin in da tabar vegetables din da take wanke wa,

Bin ta da kallo azmee tayi tana sakin murmushi aranta tace "kaɗan kenan,"
"Sehrish ni zan je nafara jere breakfast din a dining pls ki kular mun da farfesun dana ɗaura,sannan na manta bansanya salt ba ki zuba mun,"

A cikin wasu haɗaɗɗun food warmers ta shirya su, ta jerasu a saman faffaɗan tray ta fice don tafara jerawa,

sehrish sam bata farimtar komai still she's out of sense , ita dai taji kamar tace ta zuba gishiri,

Cikin rashin sani tasanya Hannu ta ɗauki Ledar detergent, bil'haƙki da gaske taje ta bude murfin sauce pot (tukunyar miya) dake a saman gas, ta zazzage sa duka kaf Aciki , ta kuma ɗauki turner tana motsawa, gaba ɗaya hankalinta nakan surar babban yaya da ta gani, ta mutukar jan hankalinta,
bakomai idonta ke hasko mata ba fa ce wannan doguwar sumar kan tasa mai dan bala'in kyau, 😳😳😳

Shigowa azmee tayi tana fadin "kinsa mun gishirin aciki "? jin muryar azmee yasa ta dawo daga tunanin da take yi, sai lkcn ta ankara da ledar detergent ɗin da ta zazzage acikin farfesun wadda ke a ƙasa, a razane ta dafa ƙirji tana fadin "Nashiga ukuna, wayyo Allah wlh omo na zuba maimakon gishirin !!!?
Sakin baki azmee tayi tana kallonta, jinjina kai kawai take yi, tana jinjina wa lamarin, sehrish kuwa ido yayi luhu luhu duk ta kame kanta,

"Sannu kin ji ? Azmee ta fadi tana kallonta, sunnar da kai ƙasa tayi tana fadin "am so sorry aunty azmee sharrin shaidan ne ba yin kaina bane,'

Azmee tace "sharrin shaiɗan kuma ko dai sharrin babban yaya wanne ciki? cije le6enta kawai take yi itama tarasa meke damunta,
"U did a good job sehrish, u need to ave some rest, aikin ki ya ƙare, sai da anjima in kin dawo hayyacin ki,' cikin sanyin murya tace "dan Allah aunty azmee kiyi hkr, nasan fushi ki kayi dani, I made a big mistake am so sorry, bazan kara ba"

Murmushi azmee tayi tace "sam ni baki 6atamin rai naba, hasalima tausayin ki nake ji, Je ki huta,'

Kama hanya sehrish tayi ta fice daga kitchen ɗin tana mamakin haukanta na yau akan big bro, (nace ba saura na anjima ko na gobe) 😂

Sehrish bata dawo cikin hayyacinta ba sai da tayo wanka, tasamu natsuwa sosai, a gefen gadonta tazauna tana ta faman zabga murmushi, farat ɗaya taji wani irin yanayi atare da ita, har takai ga ko runtse ido tayi shi take gani sanye cikin bathrobe, a tunaninta jinsa yafi ganinsa ashe ganinsa yafi jinsa nesa ba kusa ba, hannu tasanya ta janyo fillow ta kwantar da jikinta a saman gadon, idonta na kallon ceilling,

*tabbas shiɗin burin kowace ƴa mace ne 💋
_Alƙalamin_ *HAFSAT BATURE MOHD*



~BossLasy~ 🔥💋



*Page 65*


*Baki washe an samu dinner 😂*

....................*...........................

~Husanna & Jahad~


Ƙanƙame suke da junansu A cikin Cell ɗin, cikin mawuyacin hali, sun rame sunyi baƙi, haƙiƙa sun ga rayuwa, yanzu an kammala shirya komai na shigar dasu kotu domin gudanar da shari'a A next week,

ƙarar bude cell ɗin suka ji, da sauri suka ɗago, wata jami'a ce sanye cikin kakin ƴan sanda, mai riƙe da muƙamin inspector,

su biyu ne ita da wani jami'i amma ita kaɗai ta shigo ciki, zuƙunnawa tayi gabansu tana binsu da kallo fukarta cike da tausayinsu,

a tsorace suke kallonta, baka ce babu annuri a fuskarta sai manyan tsaguna a fuskarta na rumawa,
"Idan zaku bani haɗin kai zan taimake ku, ku fita daga haɗarin da kuke ciki," ta faɗi tana kallonsu

Cikin sanyin murya Jahad tace "komai kike so zamuyi dan Allah ki taimake mu mubar wurin nan, mun gaji, bamu ji daɗin zama anan, kuma bamu so akwai mu kotu a yanke mana hukuncin kisa," ta kare maganar idonta cike tab da kwallo,
Murmushi inspector eesha tayi kafin tace "tabbas zaku fita, amma bisa sharaɗin in muje kotu zaku amsa cewa kune ku kayi kisan batare da jayayya ba !!!?
Zaro ido jahad tayi tana fadin "sabod me ? taya zamu ansa hakan bayan bamu ne muka kashe ta ba "?
shiru inspector ɗin tayi tana kallonta, da alama yarinyar zatayi taurin kai,
Husanna dake kanƙame gefen jahad tace "Ni na amince zan ce ni nasanya mata shinkafar 6era taci ta mutu, indai zaki fidda mu dan Allah,"
"Husanna !!! kada ki kuskura ki amince wlh ni banyarda ba wlh,"
Jahad ce tayi maganar tana kallon fuskar jami'ar, wadda tabisu da ido,
"Wlh ni na amince dan Allah aunty ki fidda mu, zance ni nayi kisan indai zaki cika alƙawari,
hannu jahad tasa ta rufe mata baki daƙarfi tana cewa "amma sai yau na tabbatar baki da hankali husanna wlh bazan bari hakan ta faru ba sbd we're not guilty, '

ganin sun soma ƙoƙarin ɗaga murya yasa ta dakatar dasu da cewa "You have to trust me, ni turo ni akayi na taimake ku kuma dole sai ta wannan hanyar,
Cikin mamaki Jahad tace "wa"?
Murmushi tayi kafin tace "daga wurin ƴar uwarku SEHRISH,"
Jin ta ambaci sunan sehrish yasa su gyara zama suna masu tsananin mamaki, wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu,
"Dan Allah dagaske ne sehrish zata taimake mu ? dama tasan halin da muke ciki ne, Allah ne ya amshi addu'ar mu zamu fita daga wannan uƙubar,"
Jahad ce tayi maganar da tsantsar farin ciki aranta, husanna kam sam tagaza rufe bakinta murya na rawa tace "Dama nasani Sehrish bazata bari a cutar damu ba, nasan tana son mu sosai, dan Allah a fiddamu daga nan akaimu wurin ƴar uwarmu,"
Kallansu kawai inspector ɗin take yi, wani irin kallo na shu'umanci ganin sun miƙa wuya yasa tace "kun amince zaku amsa cewa kune ku kayi kisan!!"?
Atare suka haɗa baki wurin cewa ehh mun amince,'

ƴar dariya tayi kafin ta fita daga cell ɗin, a harabar police station ɗin ta tsaya jikin motarta, hannu tasa a aljihun wandonta ta ɗauko wayarta ƴar nokia, daddanawa tayi kafin ta kara a kunnanta tare da cewa "Yaran fa sun amince, zasu amsa cewa sune su kayi kisan, yaushe zanji alert na cikon kuɗi na ?
Natsuwa tayi tana sauraron mutumin da ta kira a waya, wanda ba'a bamu damar jin me yake cewa ba,
Dariya inspector ɗin tayi kafin tace "nima fa shu'uma ce kamar kai, muddin banji alert ba na cikon kuɗi na, ina mai tabbatar maka da cewa, zansa su fasa amsa laifin,'
Ta jima tana wayar kafin ta kashe wayar tana tikar dariya (to fa)

A can cikin cell ɗin kuwa, wani tunani ne yazo ma Jahad ita mai hankalin taya akai ƴar sandar nan tasan sunan sehrish !!!!? Kuma taya akai Sehrsh tasan halin da suke ciki ? Tabbas akwai makirci acikin lamarin,

Miƙewa tsaye tayi tana zagaye, can dai tace "husanna so ake mu amsa laifin kisan nan don akashe mu, ba don ataimake mu ba !!
jiki a mace husanna tace "jahad ni nagaji da rayuwarnan, so nake na mutu kuma yanzun nan,!!

hankali atashe jahad tayi hanzarin komawa kusa da ita tazauna tare da dafa shoulder ɗinta tace "Husanna bakya jin daɗi ne,"

"Eh mutuwa zanyi yanzun nan,"
ta bata amsa, bin ta da kallo jahad tayi a tsorace ganin , jini ya soma biyowa ta hancinta, daga magana sai abu ya tabbata, kafin ta ankare husanna ta zube ƙasa, ba numfashi,
Wata irin razananniyar ƙara Jahad tasaki tare da faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'una !!! Nashiga uku !!Wayyo Allah na Husanna ta mutu...........
da gudu police ɗin dake waje suka shigo ciki, sun gigita da ganin halin da yarinyar take ciki tamkar ba numfashi, kuma sun son tabbas ta mutu a hannunsu sai anji dalili,
hakan yasa aka kira women police guda biyu suka ɗauki husanna, hada jahad aka tafi da su cikin mota domin kaita asibiti,
Sai faman kuka Jahad take kamar ranta zai fita saboda tana ji aranta cewa Husanna fa wannan karon dakyar zata rayu,

Ganinsu da ƴan sanda yasa, reception nurses saurin karbarsu, aka shiga da husanna ciki a (A&E) accident and emergency ward aka kwantar da ita,
nan da nan likitoci suka shiga duba ta, Jahad na zaune a saman waiting seats dake daga waje Ward din, tasha kuka ido sunyi jawur,
Ga ƴan sanda zagaye da su,kamar wasu 6arayi, addu'o'i kawai take karantowa abakinta , tana roƙon Allah yasa Husanna karta rasa ranta, tsananin ƙunci ne a ranta, kuma tasawa ranta cewa muddun *Husanna* ta mutu itama sai ta kashe kanta ❗‼⁉, 😭😭😭

...................SEHRISH..............................

Oya drop your comment after u finished reading i wll be waiting for u 😎

*🌹HAFSAT BATURE MOHD BOSS LADY🌹*



*page 65 to 67*

_Sannan daga numbers na pages ɗin littafin nan sun kai 80 zasu canza zuwa Episode one1_



.........Sehrish..................

gaba ɗayansu sun hallara, kowannan su ya sami gurbi a dining chairs ɗin, azmee ce ke ta faman ɗawainiya yin saving ɗinsu, saboda sehrish na can cikin yanayi

_kowannan su ya hallara a saman dining chairs ɗin, kwansu da kwarkwatarsu,

Yau suna gida ba fita aiki, a bisa umarnin Babban yayansu,

_Duk sunyi dress cikin Jallabiya, dama yana ɗaya daga cikin favourite dress ɗin su, basu cika son kaya masu nauyi ba_

_azmee ce ke saving ɗinsu, kowa tana zuba masa abunda yake so_

_duk sun natsu suna ci, hannu ayan yasa acikin aljihun jallabiyarsa ya zaro wayarsa dialing ɗinta ya shiga yi Jahan ya tura wa saƙo kamar haka_

_"ya maganar hotel room ɗin? Kayi mana booking?_

Jin ƙara shigowar message a wayarsa dake ajiye gefen plate ɗin abincinsa yasa shi duba ya karanta, ɗan murmushi yayi kafin ya bashi amsa da cewa _"Eh yaushe zamu fara zuwa don a matse nake wlh_

duba wa Ayaan yayi ya basa reply shima,

_"ko yau ka ce am ready to do it, am so horny dear kamar nayi hauka_😖

duba wa jahan yayi wit smile on his face ya tura masa reply shima, _" u must be horny dear, 2 days ba testing ɗin *Ak47* dole Mu shiga yana yi_

Before Ayaan ya bashi amsa muryar fawan ta katse su da cewa

*Ga Babban yaya nan kowa ya shiga taitayinsa*


Cikin sauri kowannan su ya mayar da wayarsa cikin aljihunsa, don ya hana ana cin abinci ana danna waya,
Atare da junaid suke saukowa ɗga stairs ɗin, farar shirt ce ajkinsa ta ɗame sa, mai dogon hannu , daga ƙasa kuwa shorts ne launin ash, gaba ɗya surar jikinsa a bayyane take sboda duk yadda Sgr zai sa sutura sai halittun jikinsa sun fito muraran,ba abunda ke 6oyewa nadaga kyakkyawar surarsu, hakan ba ƙaramin tayar musu da hankali yake ba especially abbansu yayi fama dashi saboda bakin mutane tun da dai abu tubarkalla, Bai jin kunyar shiga ko wata iri ce da zata nuna tsiricinsa, bai sa suturar kirki sai in takama yafi son yasa sexy underwears sune best dres nasa, hada ƙarin hakan yasa ake kai masa farmaki,

tun da azmee ta ɗago so ɗaya batasake ɗagowa ta kalle sa, sbd tshn hankali, wannan kallonsa ma a wurin mace zai iya zama haramun,

Kujera ya ja ya zauna yana facing kowannansu, shima junaid ya zauna yana ta faman zabga murmushi,

cikin sauri azmee takai hannu zata zari plate ta zuba masa abun sawa abaki , amma abun mamaki sai fawan ya riga ta kai hannu ya ɗau plate ɗin jiki na rawa, ya buɗe warmer ɗin dake ɗauke da farfesun naman shanu, yasa saving spoon ya shake masa plate ya ajiye masa a gabansa, sanna ya haɗa masa da kakkauran tea a gefe,

Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya, wannan fadancin na fawan ya bata mamaki,
Bin su ya ke da kallo ɗaya bayan ɗaya, bayan sun gaishe shi, kowannansu ya shiga taitayinsa, don sun sani sarai bayason hayani ko kɗan, hakan yasa suka rage ƙarar spoon ɗin da hannunsa daga wannan sautin kwas kwas da ya ke yi,

Hannun sa ya miƙa acinkin wani empty bowl, azmee tasanya masa ruwa ya wanke, kafin ya tsoma hanun acikin naman, tsoka ya ɗauke ya jefa a bakinsa, a hankali yake taunarta, yana ci yana binsu da kallo One by one,

Ƙasa ƙsa da murya irfan yayi shi dake kusa da jabir yce "wannan kallon da babban yaya yake yi, bana lpy bane, duk ƴan ciki na sun kaɗa , jabir ya ɗauki cup of tea ɗin dake front ɗinsa ya kare fuskarsa dashi kamr zaisha, sannan yace "kai kenan ma, wlh jiki na kamar na mai zazza6i don fargabansa,'
Khadeel dake sauraronsu ya ce"jikin wasu na ƙaiƙayi da alama,'

Sun gane me ya kenufi cikin sauri suka ja baki su kayi shiru,
Kowa tsit kamar mutuwa ta gifta, sautin ƙarar cokulan da hannunsu twins yake yi ne (kwas kwas) ya cika masa kunne, ɗagowa yyi ya aza eye balls ɗinsa akansu, zo ka ga tashin hankali, bakomai ya haddasa hakan ba, face kermar da jikinsu ke yi,
mirya na rawa ayaan ya ce "mun shiga uku, idon babban yaya akan mu jahan,'

"menene" ya tambaya a ɗan firgice suka ɗago suna Kallansa, ya sake cewa "are u not feeling well ? ganin yadda jikinsu ya ke rawa,

Ido luhu luhu Jahan yace" Ba mu jin daɗi ne, ni da ayaan, "

ɗgowa yusif yyi yana kallansu, jin zasu ja masa bala'e, tun Kan big bro yace wani abu, yusif yayi hnzarin cewa "but why u didnt tel me about ur sick ? ya tambya yana kallansu,
cikin sauri ayan yace "dama tun jiya da dare ne,
"Atlease u should inform me abt ursick, ko ƙarfe nawa ne zan duba ku ae,? shiru su kayi shi dae Rafayet binsu da kallo kawai ya ke yi kafin ya dakatarsu da cewa "its ok, after we finish the breakfast, yusif makes sure that u check them well,'
".Insha Allah babban ya ya" zuru su kayi jin za'a duba su, Bayan sun san cewa lfyarsu lou,

Mayar da idonsa yayi kan Junaid wanda ke ta faman murmushi, kamar zautacce, ada sun yi tuanin cewa yaron ta6in hankali gare sa, amma da aka bincika sa sai aka tabbatar da cewa haka Allah ya haliccesa wit smiling face,

ɗagowa junaid yayi suka haɗa ido da babban yayan, cikin sauri ya sunnar dakai yana ci gaba da murmushi, Shifa kallon dollar $ ya ke ma yayan nasu, shiyasa murnarsa ta ƙaru in ya kallesa $ kawai ya ke gani a fuskarsa, ya riga da ya kammala lissafin nawa zai amsa da nawa zai kashe wa sehrish ɗinsa 😥

.................SEHRISH........................

A 6angaren sehrish kuwa, zarce wa tayi da bacci, na ɗan mintina ta farka tana sauke ajiyar zuciya, sunan shi ne kawai zuciyarta ke ta faman ambato, idonta takai kan agogon bangon dake manne, ƙarfe 12:30am, ynx sun isa kammala breakfast ɗin,

tashi tayi ta kimtsa, ta fita taga me ke wakana, basa nan ciki duk sun fita, wayam kuma azmee ta gyara ko'ina yayi fess, a kitchen ta same ta, tana wanke dishes ɗin da su kayi amdani dashi,
"Aunty azmee sannu da aiki," da fara'a a face ɗinta tace "Yawwa Sehrish ina fata kin washe yanzu,"

Murmushi sehrish tayi tare da cewa "eh Alhamdulillah da wani aiki da zanyi yanzu?. ta tambaya tana kallonta,
Azmee tace "a'a yau fa hutu ki ke hajiya sehrish, na ma kammala komai sai zuwa anjima zamu shirya dinner atare amma pls karki maimaita shiriritar ɗazun,"

Ƴar dariya sehrish tayi kafin tace"Insha Allah" ta ɗan yi shiru tana so ta zuba abinci, taci amma ƙunya take ji saboda 6arnar da tayi na zubawa farfesu abun wanki,"

"Ke bakya jin yunwa ne wai? kullum sai na ce ki zuba abinci ki ci, ko saina fara sa miki bulala ne?

Azmee ce tayi maganar cikin zolaya, dariya sehrish tayi da cewa "dama ynx nake so na zuba ne,"
ƙara sawa tayi ta ɗauko tray,
Bin ta da kallo azmee tayi ganin ta jera pancakes, ga sandwich ta kuma haɗa da scrambled eggs, duk a ciki a haka bai ishe ta ba sai da ta hada da fried chicken, taje ta ajiye ta kuma dawo ta haɗa cornflakes a cup ta zazzaga uwar madara, ta tsula sugar,
Zama tayi asaman dining chairs ɗin na kitchen tana kallonsu, tunani take da me zata fara, muryar azmee ce ta katse ta da cewa "Sunyi miki haka? Ko zaki ƙara da wani abu ne? 😒
sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunya tace "sun isa haka," Wato su sehrish banza ta samu, dama talaka bai iya samun wuri ba, ni bama wannan ba, Soyayyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login