Showing 75001 words to 78000 words out of 137891 words
Chapter 26 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
babban yaya tasa ta manta da halin da su Hosana ke ciki, ada in zata sa abu mai daɗi a bakinta sai ta tuna dasu tayi kuka sosai, amma ynx ba wannan mgnr, *BABBAN YAYA* kawai 😥
Sandwich ɗin tafara ɗauka tana ci, tunanin ta nakan *RAFAYET* azmee na lura da ita duk wani motsi da sehrish zatayi murmushi take yi, hankalin azmee bai kwanta da irin wannan zauce war da Sehrish tayi ba akan Babban yaya, tabbas soyayyace mai ƙarfin gaske take masa, tunkan tasa shi ma a idonta, da jin sunansa kawai ta faɗa tarko, balle ynx da tasa shi a ido? hakika jikin azmee yayi mugun sanyi tunawa da Junaid, bawan Allah wanda kullum burinsa ya ga yarinyar cikin farin ciki,
Babu wanda yasan da zaryar da junaid ya ke yi izuwa ɗakin azmee, kullum roƙonta ya keyi akan dan Allah taba sehrish kulawa ta musamman, komai sehrish take buƙata, tagaya masa zaiyi mata,
Junaid ba ƙaramin so ya ke mata ba, 😿
(Tabbas akwai tashin hankali, ni babban damuwa ta, waɗannan zuciyoyin guda biyu ❗‼⁉
Wane hali zuciyar sehrish zata shiga ita da ta kwallafa rai akan mutun da ya kasance misoganist ! ya ƙi jinin mata, baya sha'awarsu basa gabansa, balle ma maganar aure, shin wane hali zuciyar junaid zata shiga ❓shi da bashi da ƙoshin lafiya, ga soyayyar wadda bashi ke gabanta ba, yayansa take so ❗ wane hali hosanna da Jahad zasu shiga in suka amince da bukatar Inspector Eesha!? shin za'a yanke musu hukuncin kisa ne, ko zasuyi zaman gidan yari ne ⁉ 😭😭😭
Me zai faru idan su Aunty Babba Suka ziyarci Bokan nan na dajin enugu wato baba Iblis wanda muddin yayi asiri sai ya ci mutun jazamun, in ba wani iko na ubangiji ba 😿 dole fa ku gyara zama domin yanzu cakwakiyar ta soma 🔥🔥🔥
"Idan kin kammala cin abinci, inaso mu zagaye gidan nan tare dake ki ƙara ganin haduwarsa sosai," murmushi sehrish tayi wadda tuni cikinta ya fara birkice mata dakyar ta iya cewa "tom aunty azmee, amma sai na fara shiga toilet shaf shaf,'
Azmew tace "dama nasan wannan jazamin ne ae, zuba miki ido kawai nayi Allah, ni zan shiga ciki, in kin kammala ki same ni a bedroom ɗina, kyau ma mu fara sallar azhar naga time yayi,"
Sehrish ta amsa da toh, cikin sauri ta kammala, sbd dama a ƙagare take ta zagaye gidan, ta gaji da zama wuri ɗaya, daga bedroom sai kitchen, shaf shaf ta wanke kayan da ta 6ata, sannan ta wuce ɗakinta toilet ta shiga, bayan ta fito da alwalarta tayi sallah, sai wurin addu'a ta tuno da su hosana, tayi musu addu'a sosai, kafin ta cire hijab ɗin ta tura a wardrobe, dama already dress ɗinta na maza ne ajikinta, gashin baki kawai ta aza, tagyara sumar kanta, ta naɗe ta cikin hularnan tashi da kwakwa, daga sama ta bi da mayafi ta yi kamar turban, ta saki jelar mayafin gefe,
A tare da azmee su ka zagaya, sehrish tasha mamaki, ganin haɗuwar katafaren gidan, ko'ina take bi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, muryar azmee ce ta katshe ta da cewa "kin ga nan, wurin motsa jiki ne wato gym, bi da kallo sehrish tayi an kawata abun wurin da komai na motsa jiki, kamar ta shiga ta jaraba itama haka taji, amma taci alwashin watarana sai ta shiga ciki tayi gym itama,
gaba su kayi suka sake zuwa wani room ɗin, "nan kuma ɗakin bincike kenan ," jinjina kai sehrish tayi ganin wasu matsiyatan Computers gava ɗaya na'urori ne a ɗakin ke sarrafa komai, wurare daban daban ta nuna mata Hada weapon's room ( ɗakin ajiye makamai) , hada haɗaɗɗen parlor wanda suka ware domin yin kallo acikinsa, an ƙawata shi da faskekiyar plasma tv, ga speakers na sauti, ga ƙawatattun kujeru aciki da sauransu,
daga nan suka fita can harabar wajen, sehrish tasha kallo sai taga kamar tabar 9ja ne, saboda cikin gidan duniya ne, bakomai ya ƙara burgeta ba face swimming pool ɗin da tagani, mai faɗin gaske ruwan ciki yayi blue sky, daga gefe a hada kujerun shakatawa da table, bata ga komai ba sai da su ka shiga garden Aljannar duniya, juyawa tayi ta kalli azmee tare da cewa "har yanzu muna cikin nigeria"? dariya azmee tasaki tare da cewa "of course," jin jina kai tayi wasu komai na cikinsa kore ne 🌲, sai aka ƙawata shi da Red & yellow flowers 🌹🌻, ga wani tsaftataccen ruwa dake guda na (waterfalls) yana gangarowa daga jikin dutsi zuwa ƙasa ya taru acikin pool yyi kamar lakes, Bakomai ya burge sehrish ba face agwagin dake ciki suna yawa farare,
"Aunty azmee gaskiya gidannan ina kokwanto anya ba hotel bane, girmansa da haɗuwarsa yayi yawa," tayi maganar tana kara bin ko'ina da kallo, azmee tace "haryanzu fa akwai sauran wuraren da baki gani ba, ynx dai na gaji mu zauna mana,
Wuri suka samu asamn garden chairs ɗin suka zauna auna facing juna, bin ta da kallo azmee tayi ganin tana ta faman murmushi, wato bakomai sehrish ke tunani ba fa ce ranar da zasu fara magana da baban yaya harsu shaku ssae su rinka zuwa garden ɗinnan atare suna kewaya wa, lumshe idonta tayi sbd wata iska da ta ratsa ta, aranta tana cewa "Ya Allah ka nunamin wannan ranar da raina da lafiya ta, ni da shi atare muna strolling Cikin farin ciki," 😥
"Me ki ke tunani ne"? Firgit sehrish ta yi jin maganar azmee a dodon kunnanta , cikin sauri tace "bakomai kawai ina mamakin haɗuwar gidan nan kamar a mafarki,"
Murmushi azmee tayi sbd sarai ranta ya bata cewa, tunanin ta na babban yaya ne,'
"Estate za'a mai dashi" cikin mamaki sehrish ta ce "dagaske aunty azmee? Amma zai fi kyau wlh girman yayi yawa,"
Azmee ta ce "eh naji da jima wa abbansu ya faɗi cewa za'a ƙara wasu part ɗin, yana so zai ware ma kowannansu nasa saboda baison in sunyi aure suyi nesa dashi, yace duk wanda yayi aure zai dawo ciki da matarsa, duk da sun mallaki gidajensu nakansu, amma shi yafi son hakan,"
Wani daɗi ne ya rufe sehrish, kamar anyi mata albishirin cewa itama zata kasance ɗaya daga cikin surukansa da zasu zauna agidan, 😒
Bayan sun ɗanyi shiru na wani lokaci azmee tace "i have something to discuss wit u,'
"Menene aunty azmee" sehrish ta tambaya da ɗan mamaki a fuskarta,
"Ko kinsan cewa a cikin sojojin gidan nan akwai wanda yasan cewa ke maca ce ba namiji ba !!"
A firgice sehrish ta mike hannu dafe da kirji tace "Who"? fuskarta da tsananin tsoro,
Dariya azmee tayi kafin tace " zan faɗa miki but firstly ina so ki mun alƙawarin cewa u will calm urself,"
Jiki a sanyaye ta koma ta zauna zuciyarta na bugu, tsoranta kar ace cikin jarababbun ne wato Fawan ko Twins,
"Aunty azmee wanene dan Allah.. .." tayi maganar tana haɗiye yawu,
Murmushi azmee tayi kafin tace "king of smile"
"Wanene haka azmee"? Ta tamvaya da mamaki,
"Oh baki gane ba tom nabaki satar amsa kije ki gano waya dace da sunan,'
duk iya tunanin sehrish bata gano wa azmee take nufi da *King of smile* ba, takasa samun natsuwa ta gano sa, sun jima suna fira bfr su koma ciki donyin sallar La'asar,
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
~🔥the father of soldierd🔥~?
💋💋💋💋💋💋💋💋
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💞💞💞💞💞
ﻗﺼﺔ ﻛﺘﺒﻬﺎ ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ🌹🌹
_Story & written by_
*Hafsat Bature Moh'd*
~BossLady~ 💋
*page 68*
..........SEHRISH...........................
bayan ta kammala sallar la'asar, kimtsawa tayi kafin ta fito ta wuce kitchen tayi mamakin jin shiru alamun duk sun fita ne, tunanin ta ko'ina Babban yaya ya ke, ta lura baya fita sai dai azo a same shi in da ya ke, tun kafin azmee ta iso, sehrish ta fara ɗauko abubuwan da zasu yi amfani dashi, doya ta fara ferewa tasan suna yawan amfani da ita, tana aiki tana ɗan murmushi, sa6anin da tana aiki cikin damuwa saboda tunanin halin dasu Hosana da Jahad su ke ciki, zuwan big bro ya canzawa sehrish rayuwa gaba ɗaya,
Sam bata ji shigowar azmee ba, sai dae muryarta taji "Sannu da ƙoƙari rishi hakan ya burgeni,"
murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Yawwa aunty azmee ina wurina,"
"Lafiya lou ta faɗi tare da shige wa ciki domin fara gudanar da aiki, cikin lokaci ƙankani kitchen ɗin ya fara kamshin abinci,
"Wani kalar abinci ki ka fi so"? Azmee ce ta jefa mata wannan tambayar yayin da ta ke zuba kayan ƙamshi acikin sauce ɗin da ɗaura, sehrish tace "farar shinkafa da jar miya ina son abincin nan sosai aduk lokacin da akayi mana shi a gida zumuɗi muke yi kamar hauka saboda muna jimawa bamu ci ba, shine abinci mafi daɗi a wurin mu," ta karasa maganar muryarta a sanyaye ba don komai ba sai don tuna wa da hosana, a lokacin da su ke tare da mahaifiyarsu duk in akayi musu tuwo tafi kowa mita ta rinƙa sababi tana cewa "oumma wai mu kullum tuwo kullum tuwo, da rana ayi tuwo, da daddare ma tuwo, in safe tayi ma ɗumamen tuwo, ni wlh nagaji zanje gidan makwabciya in ciyo shinkafa da jar miya hada ma wasilla zata samun, "
Hawaye ne suka soma koƙarin zubowa a fuskar sehrish tunawa da rayuwarsu ta baya,
"Ni kuma nafison Tuwo arayuwata miyar ku6ewa da busasshen kifi wayyo daɗi in inaji kunne na har motsi ya keyi, musamman in ya kasance ɗumame ne,"
Azmee sai zuba ta keyi sam bata lura da sehrish ba wadda, take matsalar kwalla, jin shesshekar kukanta yasa azmee saurin ƙarasowa inda take tana faɗin "subhanallahi sehrish meke faruwa ne ? Cikin sauri sehrish ta dai dai ta natsuwarta,
Murya na rawa tace "ba komai aunty azmee, zafin albasar da nake yankawa ne, ya shiga ido na,'
"Eyyah sannu barshi na ƙarasa kawai,"
"A'a aunty azmee aikin zaiyi miki yawa, zan idasa,'
"Sehrish akwai ayyuka dayawa ba dole sai wannan ba, kibarmun yankar albasar ki kula da miyar dana ɗaura,"
"Shikenan aunty azmee amma kafin nan, ayimun uziri zan shiga toilet,"
"Shikenan ba damuwa kije kawai,"
Cikin sauri sehrish ta fice, saboda tana so tasamu space ta matse hawayen dake son zubo mata, tana shiga bedroom ɗinta, ta fashe da matsanancin kuka, a gefen gado tazauna tana matse hawaye,
Cikin murya kuka tace "Ya' Allah ka karemun ƴan uwana, aduk inda su ke, ka sauƙaƙawa rayuwarsa, Hosana da jahad kowane yanayi zan shiga na rayuwa duk mun daɗinsa I will neva forget about you, i will keep praying for u till d rest of my life 😭
haka ta dinga addu'o'i akansu, sai daga baya ta tuna da azmee wadda ta baro a kitchen tana aiki, cikin sauri ta shiga toilet, agaban wash basin ta tsaya, ta kunna fanfo ta wanke face ɗinta sannan ta fito,
ƙarar shigowar motoci taji, a lkcn da take ƙoƙarin barin ɗakin, nata cikin sauri tadawo ta tsaya agaban window ɗin da tasaba leƙe, janyen labulen tayi ta zuge glass ɗin tana kallonsu,
Motocinsu ne a jere, bayan sunyi parking wani Soja black american gabjejan gaske, ya fito ta gaba tare da buɗe mashi mota, a hankali ya zuro kafarsa dake sanye cikin slippers ɗin *Gucci* sun hau ƙafarsa raɗau ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, idasa fitowa ya yi zuba mishi ido sehrish tayi sam batasan time ɗin daya fita ba, ashe baya gidan,
Sanye ya ke da V-neck shirt light green color, sai dogon wando Army trouser, surar nan fa tafito raɗau bai matuƙar jan hankali, sumar kansa mai tsayin nan tasha gyara na musamman ta zubo masa abaynsa ya ɗaureta,
Ba shi kaɗai bane tare da abbansu su ke, da Kanal yusif,
gaba ɗaya jikin Sehrish ya gama mutuwa, zuciyarta ta gama narkewa, tafiyarsa ma kawai abun kallo ce, ta majiya ƙarfi *Rafayet* tamkar Zaki ya ke, wanda ke mulkar namun dawa a ƙarƙashinsa,
Zuge glass ɗin window tayi, tare da cije le6enta, sam bata gajiya da kallonsa, cikin sauri ta fito ta wuce kitchen saboda tasamu damar ƙare masa kallo in sun shigo,'
"Sannu da dawowa ya idon nake"? Azmee ce tayi mata wannan tambayar,
"Alhamdulillah ae sun dawo dai dai aunty azmee," sai faman murmushi take tana ƴan kame-kame,
Shigowa su kayi atare suna ɗan ta6a fira, anan main palor ɗin suka samu wuri suka zauna, abbansu na facing ɗinsu yayin da shi da Kanal yusif suke zaune a 3 seater,
Murmushi abbansu ya ke ta faman saki ba don komai ba sai don jin daɗin zuwan Babban yayan, musamman yau da suka yawata atare, duk da kin sakin fuskarsa da kuma ƙarancin maganarsa, _muryarsa tsada gare ta, saboda daɗinta shiyasa wata'kil ya ke rowarta_ (nace ba, da zai faɗi farashinta dana ƙulkula nasiya😂)
Hannunsa na riƙe da wayarsa, yana daddanawa, bazan faɗi ƙirar wani company bace, sbd wata irin haɗaɗɗiyar waya ce, very expensive wadda takasance mallakinsa, kuma sunan sane ajikinta wato (SGR) ba mai iya controlling ɗinta sai shi duk bala'in mutun, saboda sometimes da Voice ɗinsa take amfani, daga ya faɗi abu zata nuno masa, 😔
gyaran murya abbansu ya yi tare da cewa "Ina magana," a hankali ya ɗago da sexy blue eyes ɗinsa ya aza akan abban nasu tare da cewa "Am all ears,"
Abba yace "Ina so kayi mun promise ɗin cewa har ka bar nigeria, bazaka ta6a kowa ba kayi shiru da bakin ka salin alin ka tafi cikin salama dan Allah,'
wani irin kallo babban yayan ya ke wa abban nasu jin abunda yace, hannu ya kai tare da ajiye phone ɗinsa saman table ɗin da ke front ɗinsa, ya jingina bayansa jikin royal sofa ɗin, tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya, duk abban nasu na kallonsa burin sa ya ji amsar da zai basa,
murmushi kawai kanal yusif ya ke yi wanda ke ta faman danna wayarsa, amma kunnansa nakan maganar da suke yi,
ɗan ta6e small lips ɗinsa ya yi kafin yace "*IMPOSSIBLE*" atakaice,
Sauke ajiyar zuciya abban yayi dama yasan amsar kenan,
Cikin takaici yace "Oh sai kayi kenan"?
"Eh" ya bashi amsa ba wasa,
Jinjina kansa yayi tare da cewa "ni narasa gane tsakanin kai da Momynka Alexandra waya fi wani taurin kai, kafiya da ji da izza,'
da buɗen bakin babban yaya sai cewa ya yi "Ita,"
Fashewa da dariya yusif yayi, tare da sa wayarsa a saitin mouth ɗinsa yana karewa, saboda gudun kar babban yayan yakai masa naushi,
"Yi mai Isarka," Babban yayan ya faɗi yana shafa damtsen hannunsa da right hand ɗinsa alamar zaiyi bugu,
yusif yace "Ai ni na wuce bugu ko Abba," ya faɗi yana kallon abban nasu wanda shima dariyar ya keyi,
Da ƙarfin gaske babban yaya ya yunƙura zai kaiwa Yusif punch a face ɗinsa, jiki na rawa abbansu ya taso yayi saurin rikosa, duk da yasan wasa ya ke ba bugun nasa zaiyi na, yusif ihu yayi yana faɗin "Abba dont let him punch me,"
Dole yusif ya tsorata, shifa Babban yaya a ƙa'ida ya naushi mutun a cheeks ɗinsa, sai haƙori ya fita 😳
In kuwa yakai ma zazzafan naushi a saitin zuciyarka, sai dae uwar mutun ta haifi wani, bugu ɗaya sai lahira 😳😳😳
Murmushi kawai sehrish ke saki domin komai ke faruwa a idonta, duk da akwai tazara sosai amma tana hangensu ta cikin kitchen ɗin, bakomai ya burgeta ba, fa ce yanayin yadda Sgr ya ƴunƙura ya dunkule hannu zai kaiwa yusif naushi, sumar kansa da ta yarfo ta gefen forehead ɗinsa ba kamin tafiya yayi da ita ba,
"Bari na shirya miki abunsha ki kai musu," muryar azmee ce ta katse ta daga kallon nasu,
ɗan zaro ido tayi jin ance zata kai masu abunsha, ga tsoran tunkararsa ga kwaɗayin son ganinsa da take yi,
A tray ta shirya mata cups masu ɗauke da coffee, ta miƙa mata jiki na kerma, sehrish tasa hannu ta kar6a, a hankali take tafiya zuciyarta cike da fargabarsa,
Da sallama ta isa inda su ke, duk suka amsa, miƙa wa abbansu tafara yi, da fara'a fuskarsa yasa hannu ya ɗauki cup ɗin tare da cewa "Yawwa madallah sannu da ƙoƙari," murmushi ɗanyi tare da juyawa wurinsu heart ɗinta na beating, tsoro yasa tafara miƙa wa yusif cikin sauri yusif yayi mata alama da hannunsa tafara miƙawa babban yayan, Saboda ba'ayi masa haka sam, wato afara mika wa nakasa dashi abu kafin a bashi, hakan laifi ne a wurinsa,
Ita kanta batasan tana da irin wannan natsuwar ba, sai da taje gabansa, ji ka ke tsit hatta zuciyarta sai da ta lafa da bugawa cikin sauri, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya gauraye hancinta, zuba mishi ido tayi tana kallonsa,
Idonsa nakan screen ɗin wayarsa, jin alamar mutun ƙiƙam akansa yasa shi ɗan dagowa, tray ɗin hannunta yaci karo dashi,
cire hannu yayi yasa a hankali ya ɗauki cup ɗin, bin hannusa tayi da kallo, wasu irin zira-ziran yatsun hannu, dogaye farare ƙal, ga fatar nan sai ɗaukar idon tsiya, mutun kamar ya lashe, agogon hannunsa tabi da kallo tazauna masa raɗau sai kyalli take,
Mayar da idonta tayi akan sumar kansa mai ɗan bala,in kyau sam sehrish tagaza matsawa daga tsayen da take akansa, batasan bayason Kallo ba, a hankali yake kur6arsa a mouth ɗinsa,
Abun ya daurewa abbansu da