Showing 129001 words to 132000 words out of 137891 words
Chapter 44 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
ajiye cup of tea ɗin dake hannunta ta kalli hafsat cikin natsuwa tace "daughter me kike tunani game da twins ɗin can da Omar ya kawo mana su zauna tare damu"?
ɗagowa hafsat tayi ta kalle ta da murmushi a fuskarta tace "Mommy ke baki fahimci komai ba kenan"?
Aunty babba tace "Eh gaskiya a tunani na,
Hafsat ta jinjina kai tare da cewa "Lallai kam Mommy ashe brain ɗita tafi taki ja? to bari na faɗa miki ma'anar waɗancan Twins ɗin,
tayi maganar tare da ajiye spoon ɗin dake hannunta cikin plate sannan tace "Mommy Omar ya kawo waɗancan Twins ɗinne domin su samu kyakkyawan kulawa a wurinki suyi kyau su fito ɗas, daga nan kuma kinsan me zai faru"?
ta tambaya tana kallon Aunty babba wadda tayi zugum tana kallonta tace "Har sai kin faɗa"
Hafsat tace "waɗancan twins ɗin babban matsala ne agareki Mommy, domin kuwa sune Nakiyar da zata tarwatsa miki target ɗinki akan Sgr da Marshal,"
dafe ƙirji aunty babba tayi tare da faɗin "Kamarya kenan hafsat? Kaina fa ya shiga duhu i didnt understand u,
dariya hafsat tayi kafin daga bisani taci gaba da cewa "Mommy kin shiga Uku domin kuwa a fahimtata Omar bakowa yake wa tanadin waɗancan kyawawan tagwayen ba face Shi Kansa Da BABBAN YAYA........' dakatawa da magana hafsat tayi ganin yadda aunty babba ta zabura tsaye tana zazzare ido tana cewa "Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani! Nashiga uku Ni LAILA !!
Dariya hafsat tayi tana cewa "Mommy Calm dowm ur mind,zauna mana,"
Hankali tashe aunty babba tace "taya zan kwantar da hankali na? Ni ina nan sake da baki sam ban lura da hakan ba, Eeeye!! Ni za'ae wa Iya shege,
tayi maganar tana komawa mazauninta, sam fa ta razana da maganar Hafsat,
Hafsat taci gaba da cewa "Mommy yanzu fa wuƙa da nama suna hannunki sai yadda kika so zakiyi,"
Cikin sanyin murya ta wanda ya ruɗe Aunty babba tace "Yanzu menene shawara hafsat? Don na lura kinfi ni kai,"
dariya hafsat tayi tana kallon mommynta ta, sannan taci gaba da cewa "Mafita ɗaya ce !! Koda gigin wasa mommy karki bari yaya Omar ya bar gidan nan da Twins ɗincan ! muddin hakan ta faru duk wani planing ɗinki akan Babban yaya da Marshal ya tarwatse,
Jiki na rawa aunty babba tace "taya ma zanbar hakan ta faru? Ae in kinga sunbar gidan nan gawarsu aka fidda Allah, yanzu sune enemies ɗina tabbas zasu ci Ubansu Allah,amma hafsat yaya zamuyi ? ta tambaya tana kallonta
"Abunyi shine kisa a 6atar dasu ! A jefar dasu nesa da gari can bayan gari,' hafsat ta faɗi tana murmushin mugunta,
Aunty babba tace "to idan Omar yazo ya tuhume mu fa? What will be the solution of it?
ɗan tsoki Hafsat taja tare da cewa "Kibarmin aikin kawai mommy, ni zan fitar dasu a moto ɗina da nufin zamuje wurin saloon, daga nan kawai sai in zubar miki dasu a nema arasa,"
Fashewa da dariya aunty babba tayi tare da cewa "Good Job, that's why am proud of having u as my daughter,yanzu abunda za'ai Dama Omar yace baya buƙatar kowa ya kashe kosisin shi akan yaran, komai suke buƙata ayi mashi list ya biya, don haka yanzu zan zuƙa mishi uban kuɗi ya biya, dama ina so nayi tanadin na ziyartar wurin bokana,
"Hakan yayi Mommy, text kawai zaki tura mishi kice zan fita dasu Shopping za'a siya masu suturar sawa, sannan za'a kai su gyaran jiki da sauran abubuwa da mace ke buƙata, kawai mom kice mashi ya bada miliyan ɗaya da rabi, ina mai tabbatar maki da cewa sai ma ya ƙara wani abu akai,"
Murmushi kawai aunty babba ke saki tana kallon hafsat, tabbas kuwa takawo mata shawara mai kyau domin kuwa ba ƙaramin kuɗi zata samu ba,
Miƙewa aunty babba tayi tare da cewa "Bari na ɗauko wayar na baro ta saman pillow,
Wuce wa bedroom ɗinta tayi cike da zumuɗi tana tafiya jikin na rawa dama akwai ƙiba don dae tana da tsayi,
Wayar ta ɗauko a hannunta tafito da ita tana faɗin "ashe Hajjaju ma tayimun missed calls ban gani ba,ƴar duniyar ae ina nan inajiranta,
Komawa tayi ta zauna saman dining chairs ɗin tana facing Hafsat wadda taci gaba da cin breakfast ɗinta,
"mommy bani wayar ki gani, ni zan masa text ɗin,"
Miƙa mata wayar aunty babba tayi, bayan hafsat ta kar6a ta shiga Messages ta zauna ta tsara komai na kuɗin da Omar zai turo hada account number, sannan ta tura masa,
"Yana ganin message ɗin zakiji Alert,"
Aunty babba tace "Allah ko"?
Hafsat tace "ae yadda kikasan Central bank haka suke shi da Babban yaya, basa jin wuyar fidda kuɗi a hannunsu,"
"Shiyasa nake so Hayaam da abrah su sami gurbi a zuciyoyinsu ta ƙarfi ta tsiya kin ga daganan zasu rinƙa tatso mana muma mu raya dangin namu koya kikace"?
Dariya hafsat tayi tare da cewa "ki dai raya danginki mommy, domin kune talakawa donni Dangin Abban sojoji ce gaba da baya,"
"To iya magana, gori zakimin sauƙin ma ae daga cikina kika fito,"
Dariya suka yi gaba ɗayansu,
Allah sarki su hosana kuwa tun da asussuba suke faman zagaye zagaye a cikin store ɗin, wata irin baƙar yunwa ke addabarsu gashi ko sallah basuyi ba tunda aunty babba ta garƙamesu acikin ɗakin, idanun jahad sun kumbura jawur saboda rashin bacci, ga wani irin matsanancin ciwon kai da take fama dashi mai raɗaɗin gaske,ita kuwa hosana babban tashin hankalinta shine Yunwa saboda bata da jumurin yunwa ko misƙala zarratin, tuni ta soma kuka tamkar ranta zai fita,
Sarai su Aunty babba da hafsat suna sane dasu, don suna jiyo kukan Hosana amma ko ajikinsu,
______________________________________
A 6angaren sehrish kuwa tunda asuba data farka tayi wanka tayi salla, bata koma bacci ba, zama tayi zugudum saman gadon tana tunanin abubuwa da dama, har time ɗin shiga kitchen yayi sannan ta miƙe dama a kimtse take, fice wa kawai tayi ta shige kitchen, gyara kitchen ɗin tashiga yi tsaf, daga bisani azmee ta shigo itama suka fara girkin nasu, a nan ne sehrish ke bama Azmee labarin abunda yafaru jiya tsakaninta da Junaid, tasha dariya kamar kamar me,
"Bawan Allah ya bani tausayi gsky, amma aunty azmee Junaid wasa yake yi ko? Ba asiri zai tonamin ba,"
Fuska ɗauke da murmushi azmee tace "Baya cikin hayyacinsa ne shiyasanya yayi maki haka,"
Ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da cewa "Amma fa gsky junaid ya tsoratar dani daren jiyan nan,"
"Naso ace nima ina nan abun ya faru dana kalli Comedy," acewar azmee,
Suna aiki suna firarsu cikin jin daɗi,
Junaid
A hankali yasanya hannu tare da janye bargon daya lullu6a dashi yana kallon inda babban yayan nasu yake kwance, babu shi a wurin, ransa ne ya bashi cewa tabbas ya shiga cikin toilet, don haka cikin hanzari yayi wurgi da bargon ya diro daga saman gadon ya lalla6a cikin sanɗa ya fuce, bai wuce ko ina ba sai kitchen dama da wata baƙar yunwa ya kwana jiya,
"Ga fa mutuminki nan", acewar azmee cikin sauri sehrish ta juya don taga wanene karaf suka haɗa ido da Junaid wanda shigowarsa kenan,
Batasan lokacin da ta fashe da dariya ba, cikin mamaki Junaid ke kallonta, mayar da idonsa yayi kan azmee yace "Aunty azmee meya faru ne naga duk fuskarku ɗauke da dariya "?
"Kana nufin ka manta abunda ya faru daren Jira kai da sehrish"? ta tambaya tana kallonsa,
Shiru yayi yana son tuna abunda ya faru jiyan, can yasaki murmushi cikin jin kunya yana sunnar dakai ƙasa,
Daker ya iya cewa "Sorry sehrish ni ba'a hayyacina nayi wannan ba, kinyi hurting ɗina ne, so abun ya tsaya mun araina shiyasanya nayi maki hakan,"
Murmushi sehrish tayi tare da cewa "babu komai ae ya wuce, amma fa ka tsoratar dani Allah,"
Dariya yayi tare da shigewa cikin kitchen ɗin yasamu wuri ya zauna saman dining chair ɗin dake a kitchen ɗin yana faɗin "Ataimaka mun da breakfast ɗina yunwa nake ji, in ma ba'a kammala ba ko fruits ne ina buƙata," yayi maganar da hamma a bakinsa,
"Sehrish ki haɗama mutuminki mana," murmushi sehrish tasaki jin abunda azmee tace,
A cikin tray ta shirya mishi lafiyayyen breakfast takai masa, sai faman satar kallon juna suke yi cikin jin kunyar abunda ya faru jiya,
"Ki haɗamun Cornflakes,Asa madara dayawa, a zuba sugar sosai" ya faɗi yana yakai hannu cikin plate ɗin dake ɗauke da Yam & eggs soup yana ci,"
Cikin hanzari sehrish ta ɗebo ruwan dispenser mai zafi ta haɗa masa cornflakes ɗin, ta zuƙa mishi madara da sugar aciki sannan takai mishi
"Thank u, amma ki sani wata rana saina tona miki asiri like i said,"
Fashewa da dariya sehrish tayi, shima dariyar yake yi,
Wuce wa tayi suka ci gaba da kula da girkin da suke yi,
bayan junaid ya kammala ya wuce wurin abbansu, a tunaninsa zaiyi masa faɗa akan nemansa da sukayi jiya amma sai yaga akasin hakan, kyakkyawar tarba yayi masa sai faman jan shi yake da fira saboda yayi kewar surutunsa jiya, hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa junaid ba don baisan kowa ya tambaye shi about yesterday night,"
Fitowarshi kenan daga bathroom jikin shi nasanye da short ba riga, da alama wanka yayi, shaf shaf ya kimtsa cikin jeans da white shirt, agaban rigar an rubuta*TIGER* Jikinsa sai ƙamshi ke fita komai nashi anatse yake, wani irin sanyin kyau ne dashi,
Yana tsaye agaban mirror yana gyara sumar kanshi, sam Omar bai tara gashi mai tsayi akansa, saboda wani irin haɗaɗɗen gyaran gashi yake ma sumarsa irin na nigogin nan, irin wanda gefe da gefe ake saisaye sumar kaɗan daga tsakiya kuma abar gashi ba ƙaramin kyau yayi masa ba saboda kyawun sumar shi gata kwantacciya itama,
Ƙarar shigowar message yaji, matsawa yayi tare da ɗaukar wayarsa dake ajiye saman bed ɗinsa ya duba, tun da yaga sunan Aunty babba yasaki fara'a saboda yasan maganar su Hosana da jahad ce,
Wuri yasamu ya zauna gefen gadon yana duba saƙon kamar haka
*Omar barka da safiya fatan kun tashi lafiya, dama maganar twins ɗin nan ce,na shirya zan fita dasu Shopping shine nace bari namaka magana tunda dama kace ko nawa ake buƙata asanar maka, to mun lissafa komai aƙalla zasu buƙaci 1.5 million da za'ayi musu purching duk da babu tabbacin ko zasu isa,bissalam,"
Murmushi Marshal Omar yasaki, aransa yace "in dai akansu ne fiye da haka ma zan bayar burina su samu kyakkyawar kulawa,"
Cikin sauri nan take yayi masu transfer ɗin 2million sannan ya rubuta cewa in basu isa ba a sanar mishi 😮
Lokacin da alert ɗin yaje masu wani irin ihu Aunty babba tasaki tare da cewa "Wlh sun shigo hafsat maganarki ta tabbata,2 million kamar a mafarki"
A lokacin suna zaune a palor suna kallo a faskekiyar plasman dake manne a bango,
hafsat tace "Lallaikam Yaran nan sun gama shanye kurwar yaya Omar,yanzu ya zamuyi da kuɗin toh?
Aunty babba tace "dabara zamuyi, mu sayi kaya na sanya wa, dai dai size ɗinsu mu siya musu komai har takalma da sauransu, amma fa basu zasuyi amfani dashi ba, kece zakiyi amfani dasu, iya kaci in Omar yazo mu ɗauko mu nuna masa saboda tsaro, sauran kuɗin kuma zan killace su awurina,"
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "good, Mommyna hakan yayi kuwa,wannan ba ƙaramar dabara bace, kin ga tanan zamu rinƙa tatsar wani abu muma dama salary ɗina na raina shi yayimun kaɗan," Hafsat tafaɗo tana yatsina fuska,
"Don't worry My daughter, ae banza tasamu yanzu, ta wani 6angaren zamu ƙaru da twins ɗincan fa,' ta faɗi tana ƴar dariya,
_________________________________________
Ajiyar zuciya Omar yasaki bayan ya musu transfer na kuɗin, shi dae burin shi in ya tashi zuwa yagansu sun canza sunyi kyau, tashi yayi ya fice daga ɗakin izuwa na abbansu donya miƙa mashi gaisuwa, acan ya tarar da junaid shida abbansu suna fira kamar wasu abokai a saman gado,
Junaid naganin marshal jiki na rawa ya tashi da hanzari ya rungumesa yana faɗin "Yaya Omar ashe ka dawo, nayi missing ɗinka sosai ,"
Omar yace "Nima nayi kewarka junaid My shagwa6a boy," yayi maganar ayayin da suka raba jikinsu,
"Nafa daina shagwa6a fa yaya Omar," yayi maganar yana ɗan zumbura baki
Omar yayi murmushi tare da cewa "Ae ga alama nan nagani, ka daina shagwa6a,"
Dariya junaid yayi shima Abban nasu dariyar yake yi, wuce wa Omar yayi wurinsa Cikin girmamawa suka shiga gaisawa,
Bayan sun kammala girke-girken nasu na breakfast, azmee ta shiryama sehrsih tana kaiwa dining tana jerasu just like always,.
Bayan sun gama ne ta shirya mata breakfast ɗin sgr a ƙayataccen tray,
Ita kuma ta wuce dining ɗin donta yi saving ɗin sauran,
A hankali sehrish take tattaka steps na stairs ɗin hakanan take jin fargaba a zuciyarta, har ta isa part ɗinsa a ɗan tsorace take,a hankali tayi sallama babu kowa a palor ɗinsa sai uban ƙamshi dake bugowa mai ratsa hancin mutun kai tsaye,
Ajiyar zuciya tasaki tare da ƙarasawa ta ajiye masa asaman table ɗinsa, sannan ta tsaya tana jiran fitowarsa,
tana jikin tsayuwar ta hango phone ɗinsa daya bari saman sofa ɗin, cikin sanɗa ta matsa daga tsaye tana kallon wayar, hannu tasanya ta danna power ɗinta, sai ta kawo haske abun mamaki hotansa tare da junaid su dukansu sanye da kakin sojoji a tsaye sunyi saluting
Cikin mamaki sehrish tace "Shin dama Junaid shima soja ne? kodai kawai kakin ne yasanya? tab aiko saina tambayesa Allah, amma fa sunyi kyau sosai,gaba ɗaya sehrish bata ji alamar mutun tsaye a bayanta ba,ya jima yana tunanin ta yarda zai damƙi mai aikin nan da akace masa namiji ne ba maca ba,laifi biyu gashi kuma yana leƙan wayansa, Anya wannan bai da ta6in hankali?
Jikinsa na sanye da fararen kaya na likitoci domin yau ya shirya tsaf yana son ziyartar katafaren asibitin shi mallakin shi wato SGR HOSPITAL wasu kuma suna kiranshi da Asibitin Doctor Rafayet, dogon wandone fari sai lab coat fara, daga ciki kuwa farar vest ce, takalman kafarsa ma farare ne, masha Allah white in white dress kyau Iya kyau, idonsa na manne da farin glass ƙayatacce yafito ɗass abinshi,hannun nan nashi na sanye da diamond wrist watch sumar nan tasha gyara ya ɗaure abunsa ta baya, sai ƙamshin turaren nan nasa na Imperial majesty ke tashi,
Ya jima a tsaye yana kallon ikon Allah, sehrish kuwa tamkar zatasa hannu ta ɗauki wayar haka take ji, tayi uban ruku'i tana leƙar masa wayarsa,
Murmushi tasaki tare da cewa "wai Allah na bari dae na koma kan aikina kada ya fito ya yaganni ina leƙar masa wayar,"
tayi maganar ne tare da yin wani irin kwakkwaran juyi karaf idonta suka sauka akan nashi,
Zaro ido tayi cikin tsananin mamaki da Al'ajabi a tsananin tsorace take kallonsa abun kamar a mafarki,Kuma shima bai janye idonsa ba akanta
Sai ma hannu dayasa ya cire glass ɗin dake a fuskarshi don yasamu damar kallonta da kyau,ya tabbatarwa kansa da abunda Adams ya sanar dashi na cewa maca ce ba namiji ba,
Ganin irin launin kwayar idon sgr tayi matuƙar firgita sehrish domin eye balls ɗin nashi har wani shining suke blue shar dasu,
tunkan ya buɗe baki yayi magana sehrish ta aza hannu akai tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un....' tana ƙarasa maganar zuciyarta tayi wani irin bugu ta sulale ƙasa a sume.....................................❤
Abun ya ɗaure masa kai, tun kafin yace wani abu mai aikin ya sume tabbas bashi da gaskiya maganar adams ta tabbata kenan,
tsallake ta yayi yasamu wuri ya zauna saman Sofa ɗin, dakan shi yashiga saving ɗin abincinsa, yana ci yana korawa da Cool milk, lokaci zuwa lokaci yana kai idonsa kan mai aikin dake sume ƙasa a baje,
Bayan ya kammala ya wanke hannunsa ya cire tissue ya goge bakinsa,
Sannan ya miƙe bayan ya ɗauki wayarsa dake ringing, picking yayi tare da ƙarawa yana faɗim "Alhamdulillah,Am coming down now,
Gogan naka fa sam ya manta da mai aikin daya sume masa a palor,tun da ya ɗauki wayarnan tasa yasa a kunnansa ya fice daga palor ɗin,
Down stairs ya sauka anan sukan haɗe da Omar suka fice atare,
Abu kamar wasa har ƙarfe biyu na rana yayi ba sehrish ba alamarta, Azmee sai faman nemanta takeyi saboda ta bata new phone ɗin da aka bata, Data shiga bedroom ɗinta taga wayau sai ta ajiye mata wayar cikin kwalinta ƙirar Tecno Camon 18,
Room ɗinta ta koma cike da mamakin ina Reesh taje ne, sam tagaza zama ganin har ƙarfe uku na rana tayi, ta duba ko'ina har bedrooms ɗin sauran amma bata nan, suma duk sun fita bayan sun kammala breakfast ɗinsu hatta junaid bayanan,
Sam ba tayi tunanin ta duba part ɗin Sgr ba, ƙarshe har garden azmee taje da sauran sassa na gidan ta duba amma reeshi bata nan,
da tagaji da neman nata sai ta koma ɗaki cike da zullumin ina Sehrish taje, addu'arta shine Allah yasa kada wani abu ya same ta,
______________________________________
Har wannan lokacin su hosana da jahad na'a store an garƙamesu kamar dabbobi ba sallah ba abinci, yunwa tamkar zata kashe su, hosana duk ta firgice tuni idonta sun juye ta zube ƙasa tana birgima, hakan yasa jahad fashewa da kuka hankali tashe taje bakin ƙopan store ɗin tana faɗin "Dan Allah ku buɗe mana ƙofa !! idan so kuke ku kashe mu kawai ku kashe mu !! laifin me muka aikata ne ? ku fidda mu daga gidan mana wannan wane irin zalunci ne ? Cikin kuka take maganar duk tafita hayyacinta saboda ganin halin da hosana ke ciki,
Amma shiru ba alaman za'a buɗe masu kopa ko motsin mutun babu, domin kuwa aunty babba sun fice da Hafsat izuwa kasuwa don suyi siyayya da kuɗin da Omar ya turo Masu hosana,
Rai a6ace jahad ke dakar ƙopar tana kuka tsoronta kar hosana ta mutu saboda tana kwance ƙasa tana juyi,
tana cikin wannan bugun taji kopar ta buɗe, key ɗin yasaki ,.
ɗagowa jahad tayi da kanta daga jikin ƙopan tana kallonta cikin mamakin ganin ta buɗe,
Cikin hanzarin ta