Showing 30001 words to 33000 words out of 137891 words
Chapter 11 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
fitsari ya zo mata, komai ya tsaya mata cak, bugun zuciyarsa kawai take saurara,
Sun ɗau 30 mins a haka, ta ƙura masa ido yayin da shi baisan meke wakana ba,
Wayarsa ce ta soma ringing da ƙarar gaske, wannan sautin ne ya dirar masa a tsakiyar kunnansa, nan ya soma nuƙu nuƙu buɗe ido,
tsananin tsoro ne suka bayya na a fuskar sehrish, yana ƙoƙarin buɗe idonsa, cikin sauri ta janye hannayensa daga jikin ta, ita kanta batasan ta iya wannan ƙarfin halin ba sai yau, juyi tayi da ƙarfi ta sulale a ƙasan bed ɗin ta durkushe a ƙasan, hankali a tashe
kamar mafarki haka junaid ke kallon lamarin, tabbas ya ga gifcin mutun daga jikinsa, amma sai ransa ya basa cewa duk cikin bacci ne abunda ya gani,
hannunsa ya kai tare da ɗaukar wayar tasa dake ta faman buga ringing, tare da karawa a kunnan sa cikin shagwa6a ya ce "Assalamu alaikum babban yaya na, am angry wit u cos i ave been waiting for your call since yesterday night, " ya yi maganar tamkar yana a gabansa,
Sehrish da ke zuƙunne kasa cikin tashin hankali, tabaza kunne tana sauraron wayar da junaid ya ke yi, jin ya ambaci sunan babban yaya yasa ƴan cikin ta ƙadawa, sam tarasa dalilin daya sa in aka ambaci sunan nan take jin faɗuwar gaba,
ganin yayi nisa a wayar tasa ne yasa tayi tunanin ta rarrrafe ta fi ce daga ɗakin, don haka ta soma tafiya a ɗurkeshe a ɗurkushe, cikin sanɗa take rarrafa wa,
Ko waiwayen bayanta bata yi burin ta ta fice daga ɗakin before ya ankara, junaid kuwa dake maƙale da waya yana zabga wa yayan nasa shagwaba sam bai lura sai da yayi wani kwakkwarn juyi yana faɗin "just come back home i wanna see you serious..." bai ida maganar ba karaf idonsa suka sauka akan ɗan aikin nasu wanda ke tafiya cikin sanɗa yana rarrafawa zai fi ce,
Ƙura ido 👀 junaid yayi yana kallon ikon Allah, acikin ransa yana cewa" lallaima wannan ɗan rainin hankalin wato raini ya fara shiga tsakanin mu, bari in tsara in ga ƙarshen game ɗin,
sam batasan ya ganta ba,lokacin da ta isa ƙofan ɗakin ta saki wata irin ajiyar zuciya, maimakon ta fice ba tare da ta waiwaya ta kallesa ba, amma ina ranta ne ya bata ɗan juya mana ta kalle sa tun da ta tsira, juyawa tayi a hankali tana sauke ajiyar zuciya, karaf idonsu ya shiga na juna, ganin dagaske ita yake kallo ido cikin ido ya ganta asiri ya tonu, hannu ta shiga tafawa da yake ta kware wurin iya fauzewa sai kawai ta 6a66ake da dariya hhhhhhhh kamar mahaukaciya,
Tsananin mamaki ne yasa junaid yin kasaƙai yana kallon ikon Allah,
bata dakata da dariyarba cikin salon wayau da dabara ta fice tana tikar dariya, hada janyo masa kopa da rufe wa,
tana ganin ta fito ta tsagaita da dariyar tare da aza hannunta a saitin zuciyarta tace"wai Allah na tsira" da gudu ta sauka kasa ta wuce kitchen,
har ynx junaid bai dawo daga duniyar mamakin da ya tafi ba, tunda ya ke a rayuwarsa ba'a ta6a raina masa wayau irin na yau ba, ya ma rasa mai zaiyiwa ɗan aikin nan nasu, wane hukunci zaiyi masa,
"Zamu haɗu" ya fada a fili, kafin ya tashi ya shiga cikin toilet,
gaban wash basin ya tsaya, yakai hannu ya ɗauko toothbrush ɗinsa, ya matsa maclean a jikinsa, ya shiga goge hakoransa,a hankali yake komai saboda tunanin mai aikin nan nasu daya tsaya masa aransa,
Bayan ya kammala ya kunna mixer tap ɗin ruwa ya soma zubo wa wanke mouth ɗinsa yayi sannan shima brush ɗin ya wanke sa ya mayar dashi cikin holder dinsa,
wanka yayi shaf shaf ya dauro towel a west ɗinsa, ya fito yana matse sauran ruwan dake ɗiɗɗiga a sumar kansa da hand towel,
a gabn mirror ya tsaya yana kallon zunzurutun kyansa, a nan ne idonsa yakai saman fatar wuyansa, wani dogon gashi ya gani siriri mai tsayin gaske, tsananin mamaki ne ya kamasa, a cikin ransa ya ke faɗin "ynx duk wankan danayi amma wannan gashin bai bar jikina ba kodai har yanzu ban iya wanka bane haba junaid be a big man mana kana abu sai ka ce na ƴara,"
hannunsa yasa a hankali ya tsafko gashin, ya ɗago sa izuwa saitin eyes ɗinsa yana kallo, sai lokacin ya lura cewa tabbas wannan gashin mai tsayi bana sa bane to na wanene !!!! 😱
Sannu da zuwa mlm tukr, acewar azmi wadda ke magana tana kallon sehrish dake shigowa cikin kitchen, ɗan murmushi tayi tare da cewa ........................
Page 23-24
Kin riga da kin gane cewa ni maca ce," ta faɗi hakan da ƴar shagwaba
Azmi ta ce "Oh kin shirya asirinki ya tonu ko? muddin nakira ki da sunanki na ƴan gayunnan to zasu gane cewa mai aikinsa fa maca ce ba namiji ba, daganan zasu ɗauke shi izuwa barrack ɗinsu na sojoji a acanza masa halitta,"
azmi tayi maganar ne da zolaya, yayin da tsoro ya bayyana a fuskar sehrish hannu tasa tare da rufe baki alamar ta shiga uku,
dariya azmi tayi tare da cewa" idasa shigowa mana, ina so zaki yanka mun wasu fruits nan zan hada fruit salad ne, ki duba cikin fridge ki dauko kayan marmarin kizo ki fara,"
karasa wa tayi inda refrigerator ɗin ya ke sai da ta fara daukar bowl ɗin da zata zuba su ciki sannan ta buɗe sa, kaya ne iri iri shaƙe acikinsa, dangin kayan marmari dasu vegitables, ga ɗanyen nama iri iri na dabbobi daban daban,
Zubo su tayi da yawa ta fara wanko su sannan ta dawo ta aza saman table, ta dauko knife ta shiga gyarasu, yayin da azmi ke ta faman ƴan soye soye,
Jin shirun yayi yawa yasa sehrish cewa" aunty azmi wai inaso in san wanene wannan babban yayan dasu junaid suke yawan faɗansa, wai shine babba a gidan nan ne,"?
da ta ambaci sunan shi sai da azmi ta ɗan girgiza, tajima bata yi mata magana ba, sai da tasamu natsuwa ta kana face " idan na fara baki labarinsa to tabbas zamu kwana muna yi, bashi bane babba ba amma shakkarsa da suke ji yasa yazama babba, wani irin mutun ne mai zazzzafan zuciya, bai da sauki in dai akan aikinsa ne, baya ragawa kowa, baya sauraron kowa, yana da matukar karfi tun daga kan surar jikinsa zai tabbatar maki da cewa mugun karfi gare sa, idan yaga Mara gaskiya kuwa idonsa makancewa yake yi, in fara hukuntasa har sai ya ɗanɗani kuɗarsa, ko ni agabana kwanakin baya daya zo sai da ya kashe mutun 4 acikin gidan nan, ko kai ɗan ubanwaye kayi laifi, haka zaisa a kawo masa kai har cikin gidan nan ya yanke ma hukunci kuma ba uban da ya isa ya tanka, to wama ya isa? Jikan soja,ɗan shugaban sojoji mahaifiyarsa soja, yayyensa sojoji ƙannensa sojoji, shima kuma soja a bangaren kyau kuwa sai dai mu ce Tabarakallahu ahsanul khaliqin, wlh tunda nake a duniya ban taba ganin mutun mai zazzafan kyau irin nasa ba! irin kyan da sai Allah kawai ke tsare mutun saboda bakin mutane da masu kawo masa hari, wani irin miskilin mutun ne ke zan iya ce miki akwai lokacin daya jera kwana uku baiwa kowa magana ba hatta abbansu sai dai kawai yayi nuni da hannunsa ayi masa abu kaza, Isarsa da jin kansa ga izza dayake takama da abun sai addu'a,
Jinjin kai sehrish tayi kafin ta ce "amma meyasa shi bazai dawo gida bane ya zauna cikin ƴan uwansa,"
Azmi tace "ya za'ae ya dawo nan bayan a can us ya taso tun yana yaro a can kuma yake aikinsa a matsayin surgeon general," maimata sunan sehrish tayi "Surgeon general meke nan," murmushi azmi tayi saboda ta lura sehrish so take su ƙare firar tasu akan babban yaya ,
"Matsayinsa ne na aiki na faɗa miki bari nayi miki a ware yadda zaki fahimta, he's a professional surgeon doctor kuma general ne na sojoji,"
Sakin baki sehrish tayi don mamaki wannan matsayi har haka ! surgeon general, tabɗijan can ta ambata tana jinjinawa lamarin ashe mutun inya karanci military surgery zai iya kuma zama general ɗin sojoji lallai iko sai ubangiji matsayi biyu,
murmushi tasaki Cikin zumuɗi ta ce "zanso naganshi ga kyau ga class ga matsayi biyu gsky ba ƙaramin jarumi bane," a tunanin ta acikin zuciya tayi maganar sai ji tayi azmi tace"Insha Allah muna sa ran zuwansa nan kusa, amma kafin yazo ina tunanin Abbansu zai riga sa dawo wa domin shi ma yayi tafiya zuwa Qasar chaina, wani muhimmin taro ne yakaisu nasu na sojoji,"
wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, saboda ta ƙosa tagansa, acikin zuciyarta tace "naso naga ranar da zanyi tozali dashi nagadai wanene wannan babban yayan wayyo daɗi....
Muryar azmi ce ta tsaida ta daga tunanin "meyasa baki tambaye ni sauran matansa da baki taba ganinsu ba sai babban yaya,"? tayi tambayar tare da juyowa tana kallonta,
Sukuyar da kai sehrish tayi tace "saboda tun ranar da hajjaju ta kawo ni gidan nan da sunan sa na fara cin karo,shiyasa na kosa nasan wanene shi,"
Hmmmm azmi tace " akwai sauran zafafan ma irin su Captain duk wani matsayi da kika sani na soja agidan nan akwaishi, mutum goma ne sauran matasan da baki sani ba, ynx bamu da lokaci amma duk lokacin dana samu natsuwa sosai, zamu shiga garden ko muje swimming pool area akwai kujeru na shan iska awurin saina zauna na baki labarin gidan Abban sojoji,"
Cikin jin daɗi sehrish ta ce "zanji daɗin hakan sosai kinga saina san ta yadda zan zauna da kowa,"
Shiru su ka ɗanyi na wani lokaci kowa naci gaba da aikinsa, can da jimawa sehrish ta sake cewa "last question about babban yaya aunty azmi," dariya azmi tayi tace "ina sauraron ki," sehrish ta ce "wai bayan babban yaya menene sunansa ne na gaskiya,"?
"Zan faɗa maki amma da sharaɗi daga wannan tambayar mun rufe babin babban yaya," acewar azmi a yayin da take sauke kasko daga saman gas,
"Na yarda toh," sehrish ta ce tana ƴar dariya, azmi tace "Sunan shi......" shiru tayi ba ta ida ba,
Sehrish data ƙosa ta ƙagara taji sunan cikin zumuɗi tace "pls aunty azmi ki ƙarasa mana,"
murmushi azmi tayi dama ita take jira don ta ga yadda take son taji sunan,
gyaran murya azmi tayi sannan tace "Sunan shi RAFAYET!," 💋
kamar yadda sunan ya diro mata a kunnanta haka zuciyarta ma ta bata wani sauti na musamman, cikin sanyi murya ta maimaita sunan "RAFAYET suna mai daɗin gaske,"
daga nan firar tasu nasamata aya.
suka shiga shirya breakfast ɗin sehrish ce ke kaiwa kamar kullum tana jerawa a dining, har lokacin maimaita sunan take acikin zuciyarta "rafayet,rafayet, tarasa dalilin hakan (dama in mutun ya kasance ƙaddarar ka hakan ce take faruwa) 😉
Sun kammala shirya komai tsaf, one by one suka soma fitowa, duk sun shirya tsaf cikin kakinsu, banda junaid wanda jallabiya ce milk colour a jikinsa, abun ba'a magana,
Ynx sehrish ta daina bin ɗakinsu, tana tashe su, saboda sunce basa buƙatan hakan, taji dadin wannan saukin da ta samu, mutun ɗaya ne wani sa'in dole sai taje, wato junaid don nauyin bacci gare sa, bai cika tashi dakansa ba sai an tashe shi, gyaran ɗakunan su kawai ke kaita, sai kuma wani abun inya taso,
Kowa yasamu wuri ya zauna ana jefa wa juna kallo, kafin su soma gaishe da junansu cikin so da ƙauna,
Kowanne sai ya faɗi abunda yake so ya ci sannan saita zaro plate ta zuba masa, haka abun ke tafiya,
cikin natsuwa suke cin abincin nasu, fawan ne yayi gyaran murya tare da cewa "Uhm AK47 yau ba magana,"?
tuntsire wa suka yi da dariya su duka hatta shi kansa sai da ya yi murmushi, Ayaan yace "she's eating food thats why," nan ma wata dariyar ta tashi, ɗagowa jahan yayi ya saci kallon Ayaan tare da kashe mishi ido, dama suna facing ɗin juna, murmushi ayaan ya yi,
Jabeer daya lura da su ya ce "toh ƴan iska kashe kashen idon me naga ana yi ne," dariya su kayi su biyun, khaleed yace "there's something behind they're trying to hide it,"
ganin za'ayi babu shi yasa shi tsoma baki "abun sirri ne atsakaninsu," acewar Irfan wanda ke ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunsa saman plate ɗin gabansa,
junaid ya ce "what ever it is, idan kero na yawo zabo na yawo wataran za'a haɗu," cikin sauri Ayaan yace "ubanka mai bakin ja6a insha Allah baza'a taba haɗuwa ba,"
wannan maganar tasa su fashewa da dariya, ita kanta sehrish dake tsaye akansu daurewa kawai take yi amma bakinta na ƙumshe da dariya ,
kanal yusif dai baice komai ba yau baya jin ƴ'an maganar sai dai in sunyi shiriritar tasu ya ɗan murmusa 😊
kallonsa khaleed yayi ganin yau yaƙi cewa komai don haka ya ɗanyi gyaran murya cikin zolaya ya ce "su yaya yusif ciki yana ta ɗauka ko magana babu,"
ɗagowa yayi tare da ɗan jefamar harara cikin sanyayyiyar muryarnan tasa yace"bana son shashanci fa, kar na sake jin wani yayi magana acikin ku"
Shiru su kayi tsit kowa ya natsu yana zubawa cikinsa,
Karar faɗuwar cokalin junaid ne yasa su dagowa suka kallesa, cikin sauri sehrish ta duka domin ta ɗauko masa,
Zuƙunna wa tayi kasan table ɗin takai hannu zata ɗauko cokalin kenan !
Idonunta suka hango mata abunda su Twins ke yi, dayake suna facing ɗin juna shida jahaan, ƙafafunsu na maƙale dana juna sun harɗe su ,
girgiza kai tayi aranta tace"jaraba" ɗagowa tayi ta miƙa masa cokalin hararar ta yayi tare da cewa"change another spoon for me i can't use this one,"
mamaki ne ya kamata ganin inda cokalin ya faɗa a tsaftace yake, don ita ji take ko abinci za'a zuba mata a ƙasan wurin to tabbas zata sa harshe taci don ta shaida tsaftar wurin,
giɗa kai kawai tayi, ta ɗauko wani a inda suke jere ta miƙa masa, yasa hannu ya karba,
Sam ta gaza tsaida idanunta a kan wanda zata kalla cikinsu, kowa ta kalla kyau, shi dai kanal yusif wani irin sanyin kyau ne dashi ba fari bane tass wankan tarwaɗa ne, shi kuma khaleed tamkar ɗan kasar Ethiopia, launin fatarsa yayi irin choculate ɗin nan, da jabeer da irfan duk kalar fatarsu daya da yusif,
Amma in akazo wurin junaid, Ayaan da jahan da fawan farare ne tass kamar ka ta6a jini ya fito, natural white ne a tattare da junaid su twins kuma sunyi jawur, fawan kuma bai kaisu haske ba nasa mai yellow ne, dukkansu masha Allah suna da dogon hanci, ga kyawawan idanu ga kuma launin lips ɗinsu ga dimples ga kwantacciyar suma, duka dai 😇
Idonta yafi tsayawa akan junaid kallonsa take amma zahiri tunanin wayarsa take yi, har ranta bata ji daɗi daya canza security code ɗinsa ba, yanzu yaya zatayi ta kira su tsohuwa ?
ɗaya bayan ɗaya suka fara tashi kowa ya fi ce, wato wata irin motace jibgegiya ta sojoji idan suka hau ta, kowa sai yasan cewa ƴan gidan Abban sojoji ne suka fito Saboda da wata irin jiniya suke janta,
Sehrish
gyara wurin ta shiga yi, ta tattara komai da sukayi amfani dashi ta wuce dasu kitchen, sai da ta wawwanke komai tsaf ta mayar dasu cikin kitchen shelves,
Sannan ta koma tana gyaggara dining table area ɗin, ta tsaftace wurin sosai,
komawa tayi tana gyara babban falourn, ƴan goge-goge ƴan kakkabe kakkabe, da sauransu nan take wurin yayi tsaf, bakomai yake ƙara burgeta ba face komai nasu zaka ga launin sojoji ne (army colour) hatta teburin cin abincin da chairs ɗin dake zagaye dashi duk kafafunsu launin army ne, daga saman teble ɗin ne kawai glass,
Hatta 2 sets na royal sofa ɗin dake a katafaren palourn suma army colour ne, haka sofa tables ɗin duk launi ɗaya, da sauran abubuwan, lallai wannan yaci ka gidan Abban sojoji.
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Page 25-26
Ita kaɗai take ta faman wannan aika ce aikacen saboda azmi bata jin daɗi headache ke damunta dama ta sanar da ita, zata sha magani ta ɗan kwanta,
tunanin ta ynx yadda za ta goge waɗannan long stairs ɗin kullum wahalar su take ji, bin wurin tayi da kallo, wasu irin tagwayen bene ne masu double starcase ɗin nan, a zagaye suke, left & right , in kabi na hannun haggun zaka iya zagayo wa ka sauko ta hannun daman ka, a tsakanin su akwai space, a space ɗin nan zaka iya shiga ta tsakankanin benayen ka miƙi hanya anan zai kai ka bedrooms ɗin su Ayaan waɗan da ke a down kenan,
In kuma ka hau saman ɗaya daga cikin stairs ɗin zai kai ka , upstair in da ke akwai hanyoyin da zasu sada ka da jerin ɗakunansu junaid, a kalla bedrooms ɗin dake a gidan totally da wanda ke akwai mutane da wanda babu zasu kai 30,
Falo kuwa akwai manyan manya sunkai 9, kuma kowanne an ƙawata shi da attractive & expensive furnitures,
Amma babban cikinsu shine wanda kana shigowa ciki zaka fara cin karo dashi, main palour ɗinsu kenan
Ni nasan duk yadda zan kwatanta haɗuwar gidan nan ba kowa bane zai gane ba saini dana shirya kuma na gabatar
don hka just imagine it like the one u used to see in your dream, 🙅
tasha wahala sosai wurin gyara gyatan ɗakunansu don ma ba ɗauda kawai iya bedsheet ne zaka samu an yamutsa, sai kaya in an cire kaga anyi wurgi dasu ƙasa, wani ma don iyayi kayan nasa a saman mirror ta same su,
Bayan ta kammala dukan aiyukan, gajiya ta saukar mata bagatatan, ɗaki ta koma cike da jin ƙyanƙyamin jikinta,
Maballin rigar ta ciccire ta zame ta duka ta ajiye ƙasa, cire wandon tayi shima, sannan tasa hannu ta cire naɗin mayafin kanta, kafin