Showing 15001 words to 18000 words out of 137891 words

Chapter 6 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete

cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid'a kafet, ta soma yin sallar,

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad'in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce "barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,"

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce " karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan"

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu," azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba'a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa "who's trying to disturb me? d'aga murya tayi tare da cewa "tukur ne sabon mai aiki,"

"Shigo ciki" ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y'an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,

"Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka," muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan

Cikin en ina sehrish ta ce "am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku."
ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce "Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta ,

Cikin sauri tace "cikin ka ne" ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa ,
Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa " tab aiki y ganni ni sehrish daga abun arziki, wannan shi ake kira da samun wuri tusar asuba, Allah sarki mukam ya'yan talakawa don uban mutun kar Allah yasa ya nemi abinci har rana ta fadi ya ga in za'a a damu dashi kasha iya barcinka yunwa ta taso ka, ka lallaba ka je neman kason ka wani sa'in ma an manta dakai, su kam wadandannan genius din bibiyarsu akeyi suzo suci suna make wa,"

Ta karasa tunanin nata a dai dai lokacin da tazo kofar dakin the next person , knocking tyi bugu d'aya taji ance "Come in"
turo kofan tayi ta bude Samun shi tayi zaune saman sallaya jikinsa sanye da jallabiya ga kur'ani yana karantawa gwanin burge w, da alama wannan zaiyi saukin kai a cewarta

"Barka da safiya yallabai an tashi lafiya" sai da ya kai aya sannan ya juyo ya kalle ta ya ce "da ban tashi lpy ba zaka ganni ina karatun Qur'ani ne? to fah ta ambata acikin zuciyarta , shin mai ya kawo ka ma tukunna ? ya tambaya yana kallon ta a matsayin namiji,
Muryarta na rawa tace "dama an kammala breakfast ne shine ....." Interrupting dinta yayi tare da cewa "shine me ? kai shashashan ina ne da zaka fadowa mutun haka kawai tunda sanyin safiya,kama hanya ka fi ce tunkan nayi football dakai" (Jahan).

Jiki na rawa Sehrish ta fi ce zuciyarta na bugawa saboda tsananin tsoro, dafe kirjinta tayi domin ta samu natsuwar karasawa ga daki na gaba,zullumin ta kar asamu wanda zai kai mata duka don ta lura cewa fusatattu ne, ba mai sauki a cikinsu farawa da iyawa ta fara fuskantar haka nan gaba batasan mezai biyu baya ba.

Next room kwankwasa tayi tana jira taji an bata iznin shiga amma shiru , sake buga kofan tayi da d'an karfi da alama kowanane mamallakin dakin nan ya datse kofar ne,
Jin alamar ana tunkaro kofar yasa ta natsuwa, bude kofar yayi fuskar nan a daure kamar Alkubus "lafiya"? ya ambata rai a bace.
Har ta bud'e baki zata yi magana tajiyo muryar wani daga can cikin ɗakin yana cewa "Wai wane ne"?

"Wannan shashashan sabon mai aikin ne," wanda ke tsaye a gabanta ne ya basa amsa, sai lokacin ta gane cewa dakin twins ne wato kamar yadda suke y'an biyu haka ma wurin kwanansu d'aya ,"

Tuni taji zufa ta ke to mata ganin wancan dake daga ciki ya taso , dukkan su sleeping dress ne riga da wando ajikinsu kala daya milk colour masu kyan gaske,

Jerawa suka yi tsaye a gabanta kowanne na kallonta alamar sun ma rasa wane hukunci zasu yi mata saboda ta katse masu baccinsu,

Gudun kar ta ja ma kanta bugu yasa ta ce "Am...Da ma breakfast ne an kammala shine aunty azmi tace a zo a sanar daku,"

Kallon juna su kayi tare da cizon labba atare, Ayaan ne yasa hannunsa ya kamo kunnanta ya idasa shigo wa da ita ciki , ba karamin zafi sehrish taji ba har sai da tad'an saki y'ar kara "ko da gigin wasa next time ka kara attempting zuwa tashe mu bacci na rantse saika yabawa aya zaki sususu kawai," ya karasa maganar tare da sakin kunnan nata cikin sauri sehrish ta fice tana sharar kwalla don ba karamin zafi taji ba,

Sai da ta samu wuri ta tsugunna ta gama matse yar kwallarta sannan ta tunkari sauran dakunan kowane daki taje da abunda zata tarar na wulakanci, yanzu dai gashi ta tunkari saman bene last room da ya rage ta shiga,

Sai da ta tabbatar ta share dukkan ruwan hawayen da ya zubo mata sannan ta kwankwasa , kusan 3 times tana knocking a na karshen ne taji wata sanyayyiyar murya tace" shigo ciki."


Comment and share

*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~


Page 13-14

Da sallama tashi ga wani irin daddadan kamshi ne ya ratsa hancin ta, har sai da tasa hannu ta d'an matse hancin saboda scent din ya kai mata karo,

Samun shi tayi a kwance tsakiyar gado wani irin sabon salon kwanciya da bata taba gani ba, up yake fuskanta ya rungume fillow a kirjinsa ga wani filon a tsakankanin laps dinsa ya makalkalesa, fuskar nan dauke da murmushi just like always, Junaid kenan sarkin smiling,

Karasawa tayi gaban bed din yadda zaiji ta dakyau ta ce "barka da safiya' Zuciyarta na mata dar dar gudun karya yi mata abunda sauran su kayi mata,

A hankali ya bude idonunsa ya sauke su akanta "menene"? ya ambata cikin kasalalliyar murya,

"Breakfast ne ya kammala" ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa da jajayen lips dinsa,

Cikin shagwaba ya ce"wlh naji dadin zuwanka tukur dama tundazu nakeso na tashi kasala ta hanani pls taimaka min na mik'e" ya idasa maganar tare da mika mata hannunsa ,

Waro ido waje tayi domin wannan yafi sauran iyayi, fuskarta tamkar zata yi kuka gaba daya ta rasa me zata yi tun nan sehrish tagane kuskuren da ta tafka na zuwa amatsayin namiji bata da wani zabi fa ce tayi abunda ya ce if not her secrets will expose,

Mika masa hannunta tayi ya ruko cikin nasa, nan take taji wani irin yanayi a tattare da ita mara misaltuwa, lallausar fatan hannunsa ba karamin gigita ta tayi ba saboda softness dinta, a cikin ranta tace "wannan wani irin hannu ne mai laushin gaske da dadin tabawa, daga jin wannan hannun bai taba wanki ba,"

Gam ya ruke hannun nata a yunkurin ya taso ya janyo ta gaba d'aya ta rikito ta fada masa, dalili kuwa karfinsa ya rinjayi nata nesa ba kusa ba,

Wani irin bugu zuciyarta ta shiga harbawa duk tabi ta susuce ta rasa inda zata tsoma kanta, tashi ga yanayi mara misaltuwa, tsigar jikinta duk ta tashi tsaye hai kam, karo na farko da ta fada jikin namijin da ba muharramin ta ba, gashi ko riga babu jikinsa d'an short ne dai-dai guiwarsa,

Kamar anyi mutuwa haka sukayi tsit, junaid kam yarasa meyasa yaji tamkar maca ce ta fada masa a jikinsa shaukin daya ji ya basa mamaki, ita kam sehrish ji take kamar an manna mata magnet a jikinsa sam tagaza yunkurin tashi

Kasala ce ta rufe mata jiki sai da ta tattaro dukkan sauran karfin daya rage mata a jikinta ta yunkura ta mik'e cikin sauri ta zame jikinta daga nashi ta fi ce da gudun gaske kamar walkiya haja yake kallon lamarin,

Tunaninsa me yasa d'an aikin ya shiga feelings haka kodai d'an daudu ne mai bin maza ba shakka kuwa haka ne, ya fada aransa

A bangaren sehrish kuwa da ta fita a guje dakinta ta koma, tana tura kofar tashiga ta maidata ta datse sannan ta jingina da kofan tana shesshekar kuka,

ta riga da ta san ta yi kuskure tun farko cikin raunanninyar muryarta ta furta " Omg! i ave made a mistake Ya Allah makes it easy for me,

A cikin 2 weeks sehrish ta gama fita hayyacin ta, a tunanin zata huta a wannan katafaren gidan amma ashe ba haka bane, aikinsu Junaid kamar zai kashe ta, ga wani karen tsana da twins dinnan Jahan da Ayaan suka sa mata, yini take tana aiki tun safe har dare basa so suga tana hutawa sunfi so suga tana aiki kamar ansa mata battery, kullum sai azmi ta turata taso su suzo suci kalacin su na safe, haka Zata bi dakin kowannansu daya bayan d'aya, kowa taje tadawa da irin wulakancin da zata kwasa saboda jan kunnanta da suke yi har fatar kunnan tayi jawur, ga gyaran dakunansu, wanke toilet dinsu, gugar kayansu duk ita ke yi, wani lokacin ma idan suka ga babu aiki tana hutu sai su tattaro kayansu dake cikin laundry basket su bata ta wankesu tas, in azmi tace musu ba da injin wanki suke amfani ba dak sai suce ae wankin hannu yafi fidda kaya suyi kyau,

Baiwar Allah lokaci guda ta zama wata zararriya wani sa'in ko bacci take yi sai ta dinga jin muryoyinsu nayi mata gizau a kunnanta suna cewa "tukur tukur tukur kur "

Girki kad'ai azumi ke yi saboda sunce sauran aiyukan bana ta bane na d'an uwansu namiji ne wato tukur mai aikinsu,

Akwai lokacin da suka shigo atare suka same ta, ta kammala goge goge tayi aiki ta gaji, ta samu wuri saman 3 seater ta kwanta tana hutawa asalima batasan bacci ya dauke ta ba,

Kayan wanki suka shiga suka dauko kowa dana sa, bata yi aune ba sai dai taji ana zazzage mata jibgin kaya a jikinta, haka take faman hakuri dasu,

Yau ba ta makara wurin shiga kitchen ba, azumi ta taras tana gyara naman kaji, ba qaramin mamaki azmi ke bata ba sam ba ta gajiya da aiki kamar engine, gashi ta kware a wurin iya sarrafa abinci ta iya girki

"Barka da safiya aunty azmi" ta fada tana kallon ta , da murmushi a fuskarta tace "yawwa mlm tukur ya gajiyar jiya? Sehrish ta ce "Alhamdllh"

"Yau ba a makara ba kenan" azmi ta tambaya, sehrish ta ce "eh"

Zame hannun tayi daga gyaran naman da take yi, can cikin kitchen din tashi ga kofar da store yake ta bude, wasu manyan doyoyi ne ta dauko guda 3 lafiyayyu, tazo ta ajiye a saman table din da suke yanke yanke a saman sa da sauransu, " gasu nan a fere su da kyau in ka gama ka shiga store za ka ga crack din kwai ka debo 20 a cikin roba a farfasa su,"

Amsa wa kawai take da toh, wuka ta dauko ta fara daddatsa doyar , a natse take ferewa , junaid ne ya fado mata a ranta tunaninsa ta soma yi "har yanzu nagaza gane masa ni bansan meyasa ya ke da shagwaba ba kamar karamin yaro gashi da shiga rai uwa uba ga kyau kai dukkansu ma kyawawa ne idan har akace mun na zabi daya cikinsu to tabbas zanyi ruwan ido, amma fa gaskiya junaid na daban ne inason namiji mai shagwaba mai kyakkyawan murmushi domin murmushi alama ce dake nuna cewa mutun nada saukin kai, matsala da shi son jikin tsiya shi a tunaninsa ni namiji ce baijin komai ya rika ruko mun hannu baisan yana sani cikin yanayi ba.

Muryar azmi ce ta katse mata tunanin nata "sai kayi sauri fa tukur naga alamar yau shiririta kake ji,"

Mayar da hankalin ta tayi ta ci gaba da ferar doyar, bayan tagama tayi mata shape, gaban tap taje ta zuba ruwa ta wanke ta tas, ta dawo kan eggs din da cokali ta farfasasu ta dauko Whisk abun ƙaɗawa ta k'ada shi ya haɗe jikinsa, kayan kamshi azmi ta miƙa mata ta karba ta zuzzuba a ciki, bayan tagama ta shiga soya wa da doyar.

A kalla suna yin abinci kusan kala 8 na breakfast hada kayan snacks irinsu bugger, donuts, pancake, soyayyiyar ayaba (plaintain) chips doya da kwai, chicken pper soup, pasta wit stew , coffee , slide bread, gasasshen kifi, fried meat tarkace iri iri ,

Mafi rinjayen aiki azmi ke yi hakan ba karamin taimakon sehrish ta yi ba saboda bakomai ta iya ba,

"Ka je ka fara tado su lokaci karya kure tunda mun kammala da wuri" A cewar azmi da take shisshirya kayan abincin wanda zata je ta jera a dining,

fita sehrish tayi da sauri gaban ta na ɗar ɗar gudun abunda zata taras wurinsu,

Dakin kanal yusif ta fara zuwa, bayan ya bata iznin tashigo, ganin shi daga shi sai short towel a west dinsa ya sa ta yin ƴan kame Kame da alama daga wanka ya fito duba da yadda ruwa ke ɗigɗiga daga jikinsa,

Sam ta gaza control ɗin kanta har sai da ya juyo ya kalle ta dayake a gaban dressing mirror yake, ganin yadda mai aikin ya zuba masa ido yasa shi jan dogon tsaki tare da cewa "Stupid ! Why are you Looking at me? Ina namiji kana namiji amma kake kallo na anya kai ba ɗan iska ba ne?

Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa, "An gama shirya...' Bai bari takarasa ba ya ce "Na ji but this is the last warning da zan yi maka as from today bana bukatar sai an zo an sanar da ni in sauko in ci abinci,"

Cikin girmamawa ta amsa masa da ta toh insha Allah hakan bazai sake faruwa ba, fi ce wa tayi ta wuce dakin khaleed har cikin zuciyarta taji dadin abunda yusif ya ce mata saboda ita hutu ne a gare ta,

Shima khaleed kusan hakance ta faru ya ce baya bukatar ana zuwan masa ɗaki da safe haka indai ba shi ya bukata ba,

Wuce wa tayi dakin twins kwankwasa tayi taji shiru ba a bata izinin shiga ba amma kofar a bud'e take, a matsayin ta na me ragaggen hankali sai ta kutsa kai tashi ga kwata kwata babu su a saman gadonsu sai dai wani abu daya tayar mata da hankali, gurnani da wani irin nishi tadinga ji daga cikin toilet dinsu alamun akwai mutun ciki kona ce mutane ciki, tamkar ana sukuwa saman doki yanayin sautin.

Hakan ba karamin firgitar da ita yayi ba sai ranta ya riƙa bata cewa kodai wani ne bai lafiya a cikin toilet ɗin da bukatar tayi sauri taje ta sanarwa azmi abunda ke faruwa, juya wa tayi da sauri zata fita sai taji ana koƙarin buɗe kofan, tsayawa tayi tana kallon kofan toilet ɗin taga ikon Allah, a tare suka fito daga toilet din Ayaan ne ya fara fito wa sai jahan biye a bayansa dukkansu sanye da gajeran towel a ƙugunansu,

Gaba ɗaya tabi ta firgita sam basu lura da ita ba don haka ta lallaba ta fice cikin saurin,
Jikin ta a mace take tafiya abubuwa iri iri ne suke zo mata a ranta " dama mutum biyu na shiga toilet a lokaci ɗaya, menene dalilinsu nayin hakan? Shin nishin da naji da gurnanin nan na menene ? Allah wa alamu ta tambayi kanta sam ba ta kawo wa ranta wani abu ba amma hakanan take jin tabbas da akwai matsala a tattare da twins din nan.

Bedroom din fawan ta wuce tun kan tashi ga take jin sa yana waya, tsayawa tayi bakin kofan tana saurarinsa "baby nifa bana so a samu matsala bakisan halin yayyen mu ba muddin suka gane cewa ina mu'amala da mata to tabbas sai sun kusa kashe ni,"
Rass taji gabanta ya faɗi " mu amala da mata kuma wata irin mu'amala kenan?
Ta jefa wa kanta tambaya zuciyar ce ta bata amsa "duk wata mu'amala da mutun ke gudun a san yanayin ta to tabbas ba mai kyau bace,"

Wani irin miyau ta haɗiye lokacin da ta samu amsar tambayarta , sai da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login