Showing 123001 words to 126000 words out of 137891 words
Chapter 42 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
tsinin gaske,
Kai tsaye ta wuce bedroom ɗinta, hannu tasa ta turo kopan tana faɗin "am so tired ina buƙatar watsa ruwa naci abinci nayi wan........'
Bata idasa ba saboda abunda tagani kamar a mafarki Yan mata saman gadonta suna bacci,
Hannunta tasa ta murza idonta donta tabbatarwa kanta abunda take gani aikuwa ta sheda hakan
A fili tace "Bura'ubancan !!! Yau akeyin ta wlh,"
Wurga purse ɗinta tayi saman gadon sannan ta fuce waje a tsiyace take kwalawa Aunty Babba kira
"Mom!! Mom!! Mommyyyyyy !!
A razane aunty babba ta fito daga bedroom ɗinta ta sauko down tana faɗin "Hafsat meya faru haka kke kwalamun kira haka ? yaushe kika shigo ne?
ta tambaya tana kallonta,
Uban tsoki taja tare da cewa "Mom duk ba wannan ba! Suwanene waɗancan yaran isassu dana gani kwance asaman bed ɗina? a faɗace tayi maganar tana riƙe qugu,
Aunty babba ta yatsina fuska tare da cewa "ni wlh sam nama manta dasu, wlh Omar ne ya kawomana tsintattun yara tagwaye wai su zauna tare damu acikin gidan nan na wani lokaci..........'
Zaro ido hafsat tayi tare da cewa "Jakar uban can kayyasa !! sai kika amince ke kuma !?
Babu respect hafsat take magana da mahaifiyarta koda yake dama ance magaji mafiyi,
Yarfa hannu aunty babba tayi tare da cewa "To ya kike so nayi !? Omar fa ne ! Na isa na hana shi yin iko da gidan yayansa ?
Jinjina kai hafsat tayi tare da cewa "aiko zasu ci ubansu wlh ! they'll regret being here in this home !
"Ae bama sai kin faɗa ba, ynx dai am sorry my daughter nakai miki su bedroom ɗinki, nayi hakan saboda Omar yana nan ne shiyasa nayi musu amma ynx wancan Tsohon Store ɗin zan maidasu da zama ciki,"
Jinjina kai hafsat tayi tare dace "Can yafi dacewa dasu yanzu dae muje a fitar mun dasu daga bedroom ɗina, ni saina ma Canza bedsheet Allah, sannan ina jin yunwa hope kin shiryamin abinci na Mommy," tayi maganar tana shafa ciki
Aunty babba tace "dolena ne wannan, yanzu muje ɗakin mu fitar dasu, kisamu kiyi wanka na shirya miki abinci kici,
Atare da aunty babba suka shiga cikin ɗakin, su hosana bayin Allah na kwance suna sharar bacci
hafsat tace "Eyyehh !! Banza tasamu an haye mun gadona ana sharar bacci, wlh nasan maganinsu,'
Tana faɗin hakan ta juya ta fita daga ɗakin izuwa parlor in da freezer take,
Murmushi aunty babba tayi don tasan me hafsat zata ɗauko,
Aikuwa sai gata hannunta ɗauke da Cool water har yasoma ice acikinsa cikin ƙatuwar bottle,
Dariya aunty babba ta fashe da ita, tana faɗin "Good my daughter hakan yayimun wlh,"
Cire murfin robar tayi batare da tausayi ba ta zazzaga musu ruwan mai matuƙar sanyi a jikinsu,
A firce jahad da hosana suka farka jin dirar ruwa mai sanyi ajikinsu, jahad na faɗin "innalallahi wa'inna ilahirrajin'un, muryarta tamkar zatayi kuka ita kuwa hosana fashe wa tayi da matsanancin kuka saboda bata son sanyi balle ita mai asthma, jikinta har wani irin kerma yake yi,
Ido luhu luhu yayi jawur daker suke kallon Aunty Babba da hafsat dake tsaye suna kallonsu,.
Hafsat tayi mamakin kamannin su iri ɗaya sak aranta tace "Ashe har ynx ana yin twins masu kama da juna haka, ba laifi suna da kyau,"
A fili kuma ta daka musu tsawa har sai da suka firgita Hosana ta ƙanƙame jahad don batason sauti mai ƙarfi,
"GET UP !!!! Maza a tasarmun daga gado na, ku sauko Mun haka nan ankawo mana mutane tsintattu cikin gida,' tayi maganar tana yi musu alama da hannu na su sauko,
Jiki na rawa suka miƙe tare da saukowa daga saman gadon jikinsu na rawar ɗari saboda sanyin A.c ne ya haɗu da sanyin ruwan da Hafsat ta watsa musu,
Tsayawa su kayi a tsananin tsorace suna faman shessheƙar kuka,
Tsoki aunty babba tayi tare da cewa "ku biyo ni,"
Bin bayanta su kayi ta fuce dasu daga ɗakin, sunyi mamakin ganin suna ta faman tafiya acikin wata Corner na gidan,
Adai dai ƙopan wani Room ta tsayar dasu, hannu tasa ta riƙe handle ɗin kopar tare da buɗewa tace "To ƴan matan mama ga fa makwancin ku daga yau,'
Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba domin kuwa, wani tsohon store ne na ajiyar kayan abinci, tarkace ne kamar hauka, jarkoki da galon aciki na manja dana mai da akai amfani dasu awargaje, Sun tsufa sunyi ƙura, ga buhun hunan Shinkafa dana gero dana fulawa duk gasunan, ƙasa kuwa sunkin doyoyoyi ne ajere da dankalin hausa dana turawa, da gunduwa gunduwar Albasa, babban tashin hankalin ɗakin ko fanka babu duk ƙura ga yanar girgizo har jikin bango, ga ƙwari kuma a ƙasan suna shawagi, Ga manyan drawers waɗan da ke a datse jikin bango da alama na ajiyar tarkace ne,'
"Uban me kuka tsaya kuna kallo kushi ga mana! Ko saina shigar daku ne !?
Basu yi mata musu ba jahad ta ruƙe hannun hosana suka shiga cikin store ɗin sannan aunty babba ta ƙara da cewa "daga yanzu nan ne wurin kwanan ku Kuma wurin zamanku, saboda baku da gurbi acikin gidan nan,"
ta faɗi hakan tare da turo kopan kuma tasanya Key ɗin dake ajiki tayi Locking ɗinta, ba damar fita kenan, ko taya mutun zai iya kwakkwaran Numfashi a ɗakin nan !? 😰
____________________________________________*ABBAN SOJOJI*
*Story by Hafsat Bature*
*BossLady*💞💞💞
Around 12 Abban su ya dawo cikin gidan time ɗin duk sunyi bacci, bai wuce ɗakinsa ba sai da ya fara zuwa part ɗin Marshal Omar domin yaga ɗansa kafin ya wuce nasa ɗakin, lokacin daya tura kopan part ɗinsa shima nashi sak irin na Sgr ne, akwai hamshaƙin ƙayataccen palor aciki sai bedroom aciki,
Wuce wa bedroom ɗinsa yayi ya shiga Ciki samun shi yayi saman shimfiɗeɗen gadonsa ya lullu6e da lallausan blanket ɗinsa,
Murmushi Abbansu yayi tare da cewa "Yawwa haka nakeso my son asha bacci lafiya," juyawa yayi zai fita Muryar Omar ta ratsa shi da cewa "Abbana idona biyu fa, i ave told u that i wll be waiting to ave ur hug, that's why i stayed awake,'
Omar ne yayi maganar a yayin da yasanya hannunsa yana janye Bargonsa ya miƙe zaune da murmushi a face ɗinsa,"
Ƙarasawa Abban yayi Omar ya tashi tsaye suka rungume juna ssae,
"Nayi missing ɗin Tiger ɗina ssae, " ya faɗi yana bubbuga bayansa, Omar yace "Abbana nima haka, ina fata nasame ka lpy,"
"Lpy lou Alhamdulillah Omar," ya yi maganar tare da janye jikinsa daga na Omar yana cewa "Ka koma ka kwanta Omar nima zan wuce ɗaki ynx,"
"Shikenan Abba, Mu tashi lpy,"
Sallama su kayi abban ya fice, kwanciya Omar yayi amma yana jin there's something missing a heart ɗinsa tabbas akwai wanda baisa a idonsa ba, tun da ya dawo cikin gidan ba kowa bane face "Junaid," ya bari ne kawai sae gobe ya neme shi su gaisa cos yyi missing ɗinshi,"
Sehrish fa sam ta gaza runtse eyes ɗinta tayi bacci, duk ta takure kanta ta tsani jikin ta, ta6awar da haroon yayi mata ji take tamkar raping ɗinta yayi, tana saman gadon daga kwance ta tashi zaune tsakiyar gadon, ta matse kanta baiwar Allah,
___________________________/___/
Time ɗin da Abban su ya shiga ɗakinsa, yayi tunanin zai ga junaid a kwance yana sharar bacci, amma sai yaga wayam daga blanket sai pillow asaman gadon, abun ya ɗaure masa kansa, aransa ya ce "meyasa Junaid bai zo ya kwanta bane wai, ko dae yana a bedroom ɗinsa bara dae na canza kaya naje na duba sa,"
Shaf shaf ya cire kakin dake jikinsa, ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya zura jallabiya fara, sannan ya fice daga room ɗinsa izuwa na junaid dake a upstairs,
Yana isa ya tura kopan ɗakinsa abun mamaki babu junaid babu alamarsa, har toilet ɗinsa ya duba babu Shi saboda tsabar ruɗu har cikin Laundry basket ɗinsa ya duba da cikin Wardrobe ɗinsa don yaga ko ya 6uya aciki 😂
Amma babu shi, aikuwa hankali atashe abban su ya fito ya wuce part ɗin sgr, ya shiga har ɗakinsa ya bubbuga masa jikin ƙoparsa,
Sgr dake kwance natse saman gadonsa yaji knocing ɗin da abban ke masa,
Janye bargon jikinsa yayi, sannan ya tashi zaune yana kallon Abban nasu daker yake buɗe Eyes ɗinsa saboda bacci,
A sanyaye yace "Abba me ya faru ne? Kai ne da kanka?
"Ina fa lafiya babu junaid fa acikin gidan nan"! Jin hakan yasa sgr yin saurin haurowa ya sauko daga saman gadon, jikinsa na sanye da night dress riga ce dai dai guiwarsa ta tsaya babu dogon wando sai dai shorts acan ciki,
Cikin ruɗu yace "Abba kamarya? How za'ace junaid baya cikin gidan nan!!!? ya tmby yana kallon abban nasu dake a tsaye,
"Nima bansani ba, dawowa ta kenan, gsky akwai matsala,'
Fito wa su kayi atare shida abban suka bi sauran bedrooms ɗin sauran saboda su duba su gani ko ya kwana a ɗakin sauran saboda yana yin haka in rigimarshi ta tashi sai ya za6i inda yake so ya kwana ko ɗakin waye kuma dole abarsa ya kwanta,
Duk wanda akayi wa knocing ya buɗe daga yaji cewa Junaid ake nema sai kaga ya wartsake daga baccin da yake yi, hankalin kowa ya tashi matuƙa,
Gaba ɗayansu duk suka hallara a babban falon in ka cire Marshal saboda basu tashe shi ba tunda shi ranar ya dawo baisan wainar da ake toyawa ba Sai haroon,
Duk sukayi tsaye cirko cirko sai faman hammar bacci suke yi,
"A cikin ku wayasan inda Junaid yaje !!? Abban su ne ya tambaye su,
Kowa sai faman murxa ido yake yana hammar bacci,
Haɗa baki su kayi wurin cewa "Abban bamu San inda yake ba wlh,"
Tsawa sgr ya daka musu har sai da suka ɗan firgita yace "wannan wane irin shashanci ne ace junaid yabar gidan nan batare da kun sani ba har yakai wannan time ɗin a waje baku lura ba,!"?
Murya na rawa Su twins suka haɗa baki wurin cewa "Junaid fa baya zuwa ko'ina kowa yasani yana cikin gida kullum sai dae wani abun daban,"
"Nima a iya sani na kenan gsky akwai matsala* acewar fawan
Jabeer da Irfan suka ce "mun fa lura baya cikin gidan nan, amma gaba ɗayanmu munyi tunanin yana ɗakin Abba yana bacci shiyasa mukayi shiru,"
Bin su da kallo kawai sgr yake yi suma kallon shi suke yi suna kora bayani,
"Yakamata ajaraba kiran layinsa mana aji inda yake" acewar Khaleed, cikin sauri kanal yusif ya zaro wayarsa dake cikin aljihun wandon baccinsa,
Contact ya shiga ya dubo numbar junaid wadda yayi saving da *Last Born* Ya danna masa kira ta soma ringing,
Gaba ɗaya koya ya saurara yana jiran amsa kira daga junaid, 3 times tana ringing junaid bai ɗaga ba,
Hakan yasa kanal yusif yin amfani da wayarsa wurin duba location ɗin Inda wayar take,
Gaba ɗaya kowa na jiran tsammani, kanal yusif yace "kai ! Location ɗin fa ya nuna cewa wayar tana acikin gidan nan that means junaid yana acikin gidan kenan ko yabar wayar tashi a bedroom ɗinsa ne,
cikin hanzari su fawan suka haye upstars shi da su twins domin su duba ɗakin junaid koyana nan,
A tsiyace suka tura ƙopan ɗakin suka shiga cike da tsammanin ganinsa amma sai suka ga wayam, sae wayarsa dake ajiye saman Pillow bisa gadonsa, hakan na nufin gida yabarta,
Duk basu ji daɗin hakan ba, jiki amace suka sauko down ɗin har haɗa baki suke keyi wurin tambayar Su ina junaid ɗin ? Suka amsa musu da cewa basu ganshi ba sai dae wayar shi kawai,
"I know u will not see him cos i ave checked his bedroom already ya Ilahi," acewar Abbansu ya faɗi cikin tsananin damuwa,
Hankalin kowa fa ya tashi, bazaman lpy ba Romeo ba junaid ba last born, ba shagwa6a boy Ba dole kowa ya rasa natsuwa,
"nasan inda yake ni,"
Atare suka ɗago don suga wanene haroon ne wanda fitowarsa kenan daga shi sai gajeran wando ajikinsa,
Har haɗa baki suke yi wurin cewa "Yana Ina!?
"Abada cin hanci a ɗauko muku shi," kai kana ganinsa kasan yasha ya bugu idon nan sunyi jawur kamar na mujiya sai tangyaɗi yake yi,
Tsoki suka ja atare,
Abbansu ya daka mishi tsawa "Haroon kadaina mun wannan wasan kasan inda yake ne ko baka Sani ba _"!!!
Haroon yace "Billahil Azeemu na tsarance da rabbus sama'wati wal'ard nasan inda junaid yake, in ku kayi haƙuri kuka sa salama azuciyarku yanzun nan zan ɗauko muku shi,"
gaba ɗaya mamaki ne ya kamasu su kace shikenan "Muna jira,"
Juyawa haroon yayi ya nufi hanyar ɗakinsa yana faɗin "saboda wannan ɗan shilan duk kun bi kun tashe mutane Fil laili..........
Shigewa bedroom ɗinsa yayi yana ƙunƙuni,
Su kuwa zama su kayi suna ta faman jiran haroon ya fito musu da junaid,"
Jimmm kaɗan sai gashi ya fito hannun shi ruƙe da Pillow yana tangal tangal,
Zuba ido su kayi suna kallon ikon Allah, haroon na ƙarasowa ya shiga ƙoƙarin tu6e rigar pillown yana cewa "Yawwwa ynx zaku ga shegen ya faɗo daga cikin pillown ae nan cikin ya 6uya ja'irin,'
Rai a6ace har haɗa hannu suka yi Babban yaya da Abbansu suka sharara mashi zafafan maruka , daga shi har filon kowa yayi ƙasa baje,
Ihu haroon yasaki tare da cewa "Eeeeeeee !!!huuu!!!huuuu !!! waman ƙadarallahu haƙƙa ƙadrihi yanzu abba daga abun arxiki zan nuna muku inda junaid ya 6oye sai kawai naji saukar maruka? Yaron nan fa akan idona ya shige cikin rigar filon nan ya 6uya amma shikenan bakomai,'
Abun haushi abun takaici, banza kowa yayi dashi suka shiga tattauna yarda za'a yi a nemo junaid,
Kanal yusif yace "ina ga bari naje na sanarwa Azmee wata'ƙil tasan inda yake,
"A'a bana tunanin hakan, kwarama wannan mai aikin tukur raina yana bani cewa suna shiri sosai da junaid wata'ƙil shi yasan inda yake tunda kusan shine tsaransa," acewar Abban su
yace hakan ne saboda abunda yagani wato da Junaid yyai ma sehrish magana ƙasa ƙasa lokacin da suna Cin abinci dama abbansu shine ya lura da hakan,
Cikin sauri Fawan yace "Bari naje na tambayesa,'
Yakama hanya da sauri ya nufi wurin ɗakin azmee don yana da tabbacin ɗakin tukur yana kusa dana Azmeee
Sehrish na zaune idanu duk sun kumbura, taji bugun ƙopa da ƙarfi jiki na rawa tace "Wanene," a tsorace ta tambaya,
Muryar fawan taji yana faɗin "Fawan ne, Fito maza ina son magana da kai,"
Cikin sauri sehrish ta kimtsa ta mayar da gashin bakinta, ta gyara ɗaurin kanta,
Sannan ta taso ta buɗe ƙopan cike da mamakin ganin fawan tabbas kam akwai matsala,
"Gani," ta faɗi a raunane,
Fawan yace "Kana da masaniyar inda JUNAID ! Yaje !?
Zaro ido tayi gabanta na faɗuwa aranta tace "Ina junaid yaje har daren ne bai dawo ba ake nemansa,'
Cikin sauri tace "a'a gsky ban da masaniya akan hakan,"
"Ka tabbata'?
"Eh wlh," ta bashi amsa
jiki a mace fawan ya wuce izuwa falon,
Shigewa cikin ɗakin tayi gabanta na faɗuwa sai lokacin ta tuno da cewa ɗazu junaid ya sanar mata da cewa su haɗu a garden After magrib,
. "to kodai yana can ? May be ya jira ni ne yaji shiru banzo ba bacci ya kwashe shi Acan, kai anya kuwa !? taya ma zai zauna tun bayan magrib zaman jira na har yanzu kusan ƙarfe 1:00 na dare bai shigo ba, gsky bana tunanin hakan,
Haka sehrish ta rinƙa tunane tunane aranta, har ta samu wuri gefen gadon ta tazauna zuciyarta ta saƙa mata cewa "Junaid fa rigimamme ne zai iya yiyuwa yana can ya dage akan in banzo ba ba zai bar garden ɗin ba, kai gsky fa haka nake tunani hankali na bazae kwanta ba har sai naje na duba garden ɗin can, tana faɗin hakan ta miƙe .................................................
Wannan kenan 🙌
Keep sharing it everywhere pls 🙏
Boss Lady 💝
Masu son yi mun Comment ba hali ga Phone no ɗina Only message kuma mata kaɗai (08103884440)*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
*Na*
*Hafsat Bature Moh'd*
~BossLady~
🔔🔔🔔
_nataƙaita littafin Abban sojoji yanzu yakoma part one and part two only duk mun yawansa zai ƙare a part 2, namai dashi yanzu muna a part 1 sai ya kai 100 pages cuf, sannan part 2 zai shiga, sannan kuma yanzu free pages ne_💔👌
Page 94-95
a hankali ta buɗe kopan ta fito cikin sanɗa, gabanta ne ya faɗi da ta hango su gaba ɗaya sun hallara a babban palorn cikin tashin hankalin rashin junaid, har sun fara yanke sha'warar fara kiran friends ɗinsa da sauran ƴan uwa aji koya je can,
Dafe zuciya sehrish tayi tabbas kuwa in tabi ta entry ɗin main palor zasu tambaye ta jin ba'asin ina xataje, don haka tayi deciding ta canza hanya cos there's many doors acikin gidan da