Showing 18001 words to 21000 words out of 137891 words
Chapter 7 - Abban Sojoji Book 1 Hausa Novel Complete
samu natsuwa sannan ta kwaɗ'a sallama, jin muryar mai aikin nasu yasa fawan saurin yin rejecting kiran ya yi throwing phone ɗin nasa saman gefensa, rai abace yace " wai wanene "
Ko izinin shiga ba ta samu ba, murya na rawa ta ce "tukur ne dama an kammala shirya breakfast ne"
Wani irin dogon tsoki ya ja tare da cewa" Naji sai me"?
Jiki a sanyaye sehrish tabar kofan ɗakin nasa ta wuce na irfan, ita kanta ta shaida cewa yau babu sa'a ynx fargabanta me zata taras ɗakin sauran.
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Page 15-16
Kwankwasa kofar ɗakin nasa tayi , da wata irin kakkausar murya taji ya amsa mata da cewa"Uban wanene" kai kanaji kasan yasha ya bugu har takai masa aka.
Saboda tsoro bata basa amsa ba ta yi gaba da sauri, tun a lokacin ta gane cewa tabbas akwai matsala kuma sam bai kamata tana bin kowannan su ɗaki don tayar dasu ba, ta gama yanke shawarar sanarwa azmi cewa baza ta ƙara zuwa ba, tun da cikinsu ne in suna jin yunwa dakansu zasu fito su nema.
Gaba ɗaya a firce take da lamarin kan ta ya gama ɗaure wa, ɗakin Jabeer ta wuce tana sa hannu ta kwankwasa kofa , tana jiyo har mutsinsa ta ciki sallar karya ya kabbara , shiga ciki tayi abun saiya daure mata kai, Sallah karfe 9 na safe.
Har zata juya idon ta ya hango mata kwayoyi na shaye~shaye ga kwalabe kuma a gabansa.
Shi duk a tunaninsa yayansu ne kanal yusif amma jin shiru yasa shi katse sallar ya ɗago ya kalle mai aikin, wani mugun kallo ya wurga mata tare da nuna mata hanyar fita ya ce " karka kuskura ka ƙara zuwan min ɗakina in ba haka ba saina canzama kamanni shashasha,"
Abun da bai sani ba ita sam ba ta san kwayoyin menene a gabansa ba, a tunaninta bai da lafiya ne shine ya ajiye magunguna zai sha.
Ficewa ta yi a ranta tana cewa" Allah ya ba ka hakuri,"
Saura ɗakin shagwababben sarkin murmushi, har tsoran zuwa ta ke yi saboda manne mata da yake yi,
Tunkan ta shiga take jin muryasa yana faɗin "Coffee i need coffee pls " cikin magagin bacci ya ke wannan sambatun na neman coffee,
knocking tayi masa kusan sau uku kafin taji muryarsa yana cewa "wanene shigo ciki mana,"
Gyarawa tayi ta shiga ciki samun shi tayi kamar yadda ta saba samun shi irin kwanciyar nan tasa daya saba, kamar wani karamin yaro haka yake,
Karasawa tayi gabansa tare da cewa"barka da safiya junaid , tukur ne," ta idasa maganar tana kallon cikin idonsa daya buɗe,
A duk lokacin da ta kalle sa wani irin natsuwa da kwanciyar hankali ne ke shigarta, murmushi taga yana sakar mata dimple din nan nasa masu lotsawa guda biyu suka bayyana,
"Ohh tukur ne am really happy to see u, dama yau inaso ka taimakamin tun jiya nakeson wanke sumar kaina na kasa amma yau kam tare zamu shiga toilet ka taimakamin," a wani shagwab'e ya ke maganar.
Sehrish kuwa waro ido waje tayi jin abun da ya ce wannan da alama wata rana cewa zaya yi tayi masa wanka,
Cikin sanyin murya ta ce "ka yi hakuri dan Allah ba yadda za'ai na bi ka toilet sam a tsarin aiki na a gidan nan ba'a ba mai aiki izinin yin hakan ba,
Wani irin kallo ya wurga mata kafin ya ce" wa ye wanda ya tsara wannan dokar? bayan ni ne silar da aka kawo ka aiki a gidannan, tukunna ma kai ba jinsina bane? to kodai maca ce tayi shigar maza bansani ba,"
Jin wannan maganar tasa yasa sehrish jin faɗuwar gaba tuni ƴan hanjin cikin ta suka ƙaɗa har ta soma tunanin anya Junaid bai gane cewa ita MACACE ba NAMIJI ba !? duk tabi ta rikita kanta
Muryarsa ce ta sake katse ta "Am asking you ! answer me," dakyar voice ɗinta ke fita "ba haka bane, kawai a ganina bai da ce ba ina matsayin mai aiki nayi hakan,"
"I command you to do that! ae mu ne masu gidan kuma umarnin mu ake bi,"
Cike da isa junaid yayi maganar,ba yadda sehrish ta iya a dolen ta, tabi umarninsa, haka ya tashi yana yauƙi yana cika yana batse wa kamar bashi bane mai murmushin kashe zuciyarnan ba,
Miƙewa ya yi daga saman bed din ya sauko daga shi sai shorts a jikinsa, bin jikin shi tayi da kallo fari sol ba tarin gashin jiki a skin dinsa , ga kirarsa dai dai wa dai dai, kusan hasken fatarsa dana twins jahan da Ayaan ɗaya ne akan na sauran don haskensu ba irin na nan bane zai iyiyuwa cikin iyayensu akwai farar fata, mahaifiyarsu ko mahaifinsu,
"Idan ka gama kallon zamu iya shiga ciki ko" ya ambata yana kallon ta, gaba yayi cikin toilet din tabi bayansa zuciyarta na ɗar ɗar tsoranta kar ya ce zai cire shorts ɗinsa a agaban idonta batasan ya zata yi ba,
Da farga jikin ta na rawa ta dauko ɗaya daga cikin jerin shampoo dinsa na wanke kai, juya tayi da nufin ta nuna masa in da wanda ta dauko yake amfani kar asamu matsala, samun shi tayi yana kokarin cire shorts ɗin jikinsa, aiko a firgice ta saki roban shampoo ɗin ƙasa, ta karasa da gudu ta cafke hannayensa dake a saman mararsa gam ta ruke su, kallon juna suka shiga yi na wani lokaci, shi mamakinsa wai namiji ne ke gudun ɗan uwansa namiji a ganinsa is not a bad thing don ka cire kayanka gaban jinsin ka, ita kuwa miyau kawai take haɗiya gabanta na faduwa sai faman huci take kamar wadda ta yi ƴar tseral, Tuni hancin ta ya soma tsattsafo da zufa, tsoranta wane hukunci zai yi mata a sakamakon abunda tayi, ita dai tayi hakan ne don da abunda zata gani na tsiraicinsa kwara koma meye yayi mata tasan ba laifinsa bane, laifin ta ne da tayi shigar namiji,
Zame hands ɗinta tayi daga rikon da tayi masa, hannayenta ta aza a saman kanta tare da faɗin "nashiga ukuna am so sorry sir am just out of sense," duk a riki ce tayi maganar,
'Stop calling me sir! Cos may be am just your age mate, call me wit my name Junaid,
Ya karsa maganar tare da ƙara gyara gyara shorts ɗinsa yace " get out of my sign,"
Cikin sauri ta nufi hanyar fita har ta 6uɗe kofan tajiyo muryarsa yana cewa" Am watching you!" juya kanta tayi ta kallesa da yatsunsa yayi mata nuni da idonsa alamar zai sa ido akanta,
Cikin sauri ta fi ce tana faɗin " Insha Allah junaid bazaka gano komai ɗangane dani ba zan ta addu'a ina rokon Allah yaci gaba da rufamin asiri har nasamu na hada kudin aikin Husanna nabar maku gidanku,
ta fada acikin zuciyarta (abunda sehrish ba ta sani ba wannan gidan is part of her destiney)
Azumi ta kammala shirya musu abincin sai da kowannansu ya mula yasha iska sannan suka firfito, one by one duk sun shirya cikin kakin sojojinsu, banda mutun ɗaya junaid wanda ke sanye da jeans a jikinsa tare da farar tshirt mai dogon hannu ta ɗanyi tighting ɗinsa,
Kowannan su ya samu wuri ya zauna, sehrish ce ta fito frm the kitchen don ta fara saving ɗinsu, azmi kuma ta wuce bedroom ɗinta don dama already ta sanar da ita cewa zata shiga ciki tayi wanka don tasha aiki,
Hannu ta har kekkerwa yake yi saboda tsananin tsoran guyabarsu, junaid ta fara kallo tare da cewa"me zan zuba maka'? Kafin ya buɗe baki ya yi magana fawan ya kar6e da cewa"saboda shine babba acikin mu !"
Ayaan ya ce "thats what i was trying to say! Wannan house boy din ba karamin ɗan iska bane shi junaid ɗin special salary ya ware maka ne ɗayasa kke kokarin fara zuba masa abincin? ya tambaya fuska a ɗaure yana kallon ta,
nan fa hankalinta ya tashi ita batayi don wani abu ba ashe abun yana damunsu,
Muryar Jahan ce ta katse ta "Nima na lura da haka in banda iskanci ka rasa wanda zaka fifita sai karamin kanin mu wanda ko aiki baya zuwa sai dai yazauna kamar mace a gida,' ya ƙarasa maganar yana wurga masa harara.
Ran Junaid ba ƙaramin baci yayi ba, abun duk saiya bashi haushi musamman da Jahan yace masa kamar mace, wani irin ƙululu bakin ciki ne ya tsaya masa a maƙogwaronsa,
duk wannan abun da suke kanal yusif na jinsu bai ce komai ba haka zalika sauran y'an uwan nasa su irfan, sauraronsu kawai suke yi dama basu cika shiga faɗansu ba.
"Nima abunda nagani kenan Jahan kullum zaman kashe wando ya iya bai da wurin zuwa daga buga ball sai atake masa abinci a plate yaci yayi haikam ƙarshen wata nayi Babban yaya ya turo masa da dollars a account shiyasa gayanan duk yafi mu kyan gani,' fawan ne yayi maganar yana kallonsa daya ke suna facing ɗin juna a table ɗin,
ganin yadda suke ta faman yada masa magana a gaban ɗan aikinsu tukur yasa shi cewa "Ya Isa haka ! Ku ce koma me zaku ce! in da na gode ma Allah ma ba da son raina nima nake zaune gidan ba! Ciwo ne kuma zai iya samun kowa acikin ku!,' ya karasa maganar idonsa sun cicciko da kwalla,
Ran sehrish dake tsaye ba ƙaramin baci yayi ba ganin yadda manyan suka kasa dakatar dasu daga gaya masa magana musamman kanal yusif da yake babbansu a yanzu,
Dariya fawan yayi tare da cewa " aikin kenan! daga magana ƙaɗan sai ka nemi zubarwa mutane da hayawa kamar kafi kowa ruwan hawaye a ...' bai idasa maganar ba yaji saukar ruwan tea mai zafi a fuskarsa Allah yaso ba tafasasshe bane, ihu ya saki tare da faɗin "innalallahi junaid baka da hankali ne! ni ka watsa wa ruwan tea! wlh bazan yarda ba saina rama,
Hannunsa ya zura ya dauki kular da farfesu ƴan ciki mai zafin gaske ke aciki ya yunkura zai watsa wa junaid, da gudu junaid ya tashi , shima fawan ɗin yabisa kamar tom& jerry haka suka rinƙa zagaye wurin,
Hankalin sehrish ba karamin tashi yayi ba bata ta6a sanin haka suke ba wannan ai sai suyi kisan kai.
Ga haushin ƴan uwan nasa da take ji hankalinsu kwance sai ma umarni da suka bata ta zuba masu abincin nasu su ci, saving ɗinsu take yi amma hankalin ta nakansu Junaid da fawan dake ta faman ƴan guje guje , tsoran ta kada fawan ya zuba masa farfesun nan a farar fatar nan tasa mai laushin gaske don tasan tuni zaiyi mummunar ƙuna.
Har ta kammala saving ɗinsu ta koma ɗaki cikin rashin kwanciyar hankali, a bangaren su fawan kuwa dake faman faɗa tunda junaid ya samu ya shige room ɗinsa ya datse kofar, a dole fawan ya haƙura a zuwan Zasu haɗu ne ae ba kwana zaiyi a rufe ba,
Gaba ɗayansu sun fita tana jin tashin motocinsu, cikin sauri ta fita domin da ma ta ƙagara su fita taje ta sanarwa junaid ko ya samu yazo ya ci kalacinsa,
A falo ta gamu da azmi tana goge goge, cikin girmamawa tace"sannu da aiki aunty azmi me zai hana ki bani na idasa aikin tun da dama ni nake yi kinyi aiki sosai nasan kin gaji,"
fuskarta a sake ta ce" kada ka damu tukur ai an jima na nan, yanzu dai abinda zaka yi kabi bedrooms ɗinsu ka gyaggyara tsaf don Allah,'
Sehrish ta amsa mata da toh wuce wa upstair tayi ɗakin junaid babbuga kofan tayi, muryarsa taji yana cewa"wanene"?
Gyara muryarta ta yi tare da cewa"tukur ne mai aiki dama naga baka ci breakfast ɗinka bane,'
Ɗan guntun tsoki yaja tare da cewa"Naji a kawomin a ɗaki na zanci,'
Amsa sehrish tayi da toh sannan ta juya time ɗin da ta sauko azmi har ta kamma gyara falon yayi fes gwanin burge wa sai ƙamshi dake tashi, kai matar taji daɗi ga iya girki ga iya gyaran wuri ya koma kamar sabo uwa uba ga kyan hali, sehrish ta faɗa a ranta tana dan murmushi,
Kitchen ta wuce nan ma ta samu azmi ta gyarasa komai tsaf, shirya masa abincin tayi a tray, ta koma ɗakinsa nasa sai da ta jira ya 6uɗe mata sannan ta shiga.
Page 17-18
A wani madaidaicin table dake a bedroom ɗin nasa ta aza tray ɗin ta matsar dashi gabansa, yana zaune a gefen gadon yana daddana wayarsa,
satar kallon wayarsa tayi ba kowa ya faɗo mata a rai ba fa ce husanna da jahad tabbas tana bukatar tayi waya da su, amma babu hali cos bata da waya, kuma ba yadda za'ai ta ce zata ari wayar sa, hauka ma take yi ashe?
Muryarsa taji a kunnanta "Thank you zuwa nan da 30 mins ka dawo ka dauki tray ɗin,''
Ta amsa masa sannan ta fi ce, acikin ranta tana faɗin' tabbas ya kamata nakira naji wani hali husanna da jahad suke ciki wayyo Allah na gashi na lura kamar aunty azmi bata da waya a hannunta,
A ɗakinsu twins ta tsaya domin gyarawa masu shi, a hargitse ta samu ɗakin sun tarwatsa komai, haka ta kama aikin gyara masu shi, bed ɗin ta soma gyarawa bed sheet din takai hannu zata cire, tsayawa tayi tana kallon wani abu a jikinsa, wani irin ruwa ne mai kitib kitib kamar kokko mai yawan gaske a jikin zanin gadon, tunani ta soma yi' shin wannan menene ajikin zanin gadon a iya sani na gidan nan basa shan kokko to kodai madara ce ta zube a wurin gsky i na tunanin haka,
kasancewar zanin gadon maroon colour ne hakan yasa abun ya fito sosai raɗau, cike da jin kyankyami ta tattare bedsheet ɗin ta zuba a laundry basket ɗinsu,
Kammala gyaran gadon tayi sannan tayi mopping ɗin dakin tsaf ta gyara komai, gaban dressing mirror ɗinsu taje, mayuka tagani tsadaddun gaske iri iri, karaf idonta suka sauka akan wani kwalban magani, hoton dake a jikin kwalbar kawai take kwallo namiji da namiji ne zir babu kaya a jikinsu ɗaya yayi holding penis ɗin ɗayan,
Gabanta ne taji yayi mugun bugawa duk da batasan ma'anar hakan ba sai ranta ya bata cewa kawai magani ne na wani ciwon nasu na maza,
Kammala gyarawa tayi afterwards ta koma bathroom ɗinsu, anan ne fa kwalwarta ta ƙara rikice wa ganin wannan farin abun da tagani a bedsheets ɗinsu, gashi nan a har jikin bathtube ɗin ko'ina sun hargitsa shi, haka ta daure ta wawwanke ko'ina tass,
Bayan ta fito sai da ta sake duba kwalbar maganin nan a jiki taga an rubuta (Homosexual) shi kaɗai ta iya ganewa amma ita kanta bata san ma'anar kalmar ba don ba komai ta sani ba.
Sam ta manta da sakon junaid na ta koma after 30mins ta kwashi tray din abincin sa takai masa.
Sai da ta kammala gyarawa ɗakunan kowannansu ba ƙaramin gajiya ta kwasa ba, sauƙin ma ɗakunan sauran ba hargitsi ba kamar nasu Jahan da Ayaan ba,
Har yanzu sehrish ta gaza mantawa da wannan abun da tagani ɗakin su twins, akwai wani abu da ya tsaya mata a rai wanda take tuna shi da jima wa daya faru dasu tana kokwanton cewa kodai wannan abun ne, bakomai bane fa ce Sperm !!!
Tafiya take yi jikin ta a kasalance wata irin kasala ce ta dabaibaye ta, labari mara daɗin ji, abunda take kokarin yi musu shine (Kyakkyawan Zato)
Dakyar take taka matattalar benen, idonta a cike taf da hawaye 'Ya Allah kada kasa abunda nake zargi ya tabbata Ya Allah kasa nayi aiki na ba tare da na fuskanci wata matsala ba cikin salama na tafi nabar masu gidansu, ni kuɗi kawai nazo nema domin na taimaki ƴan uwana dake kwance asibiti bayan wannna bana bukatar wani abu,
Tura kofan room ɗin junaid ta yi, samun shi tayi ya gama cin breakfast bacci ya kwashe sa, sai sharar baccinsa yake cikin kwanciyar hankali da natsuwa,
ɗan murmushi ta saki tare da cewa" Ya Allah ka tsare wannan bawan naka bansan halinsa ba amma ina yi masa kyakkyawan zato"
Hannu takai zata ɗauki tray din karaf idonta suka sauka akan wayarsa dake ajiye saman nightstand, ba komai ya fado mata a rai ba fa ce ta saci wayarsa ta kira goggonsu taji ya lafiyarsu Jahad, murmushi tasaki a hankali ta soma tafiya cikin sanɗa, saɗaf saɗaf ta tafi,
Sai da tasha wahalar daukar wayar tasa sannan taga ashe thumbpring gare ta, dole sai da yatsansa sannan za ta 6uɗe, ɗafe kanta tayi tare da faɗin "wayyo Allah na" dama sarar ta ce,
Juyawa tayi tana kallonsa yadda ya ke kwance yana baccinsa a natse, sama ya ke fuskanta ya wawware hannayensa, murmushi tasaki tare da fadin 'abun zai zo mun da sauƙi,'
Hawa saman bed ɗin ta yi a hankali cikin sanɗa kamar mage, rarrafe a hankali tayi ta isa inda hannun damansa yake, yatsun hannunsa a buɗe suke gasu nan tsirara masu kyan gaske, bayan wayar ta juya inda thumbprint din ya ke, kwafa wa tayi a yatsansa na tsakiya, yasa mata wrong, matsar da wayar tayi ana gabansa cikin sa'a wayar ta bude, tsananin farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, cikin sauri ta sauka ta lalla6a tafita ta tsaya a bakin kofan room din nasa, jikinta har kerma yake yi karta ya farka, tuni zufa ta soma tsastsafo mata a hancinta,
Time ɗin da ta aza idonta akan wayar, Hoton da tagani a wellpepper ɗinsa ne yasa jin zuciyarta wani irin bugu,
Zuba ma hoton ido tayi wato ainihin wani haɗaɗɗen matashin saurayi ne, ko a mafarki bata ta6a ganin mutun mai irin kyansa ba, kwayar idonsa ce tafi ɗaukar hankalinta, blue eyes ne da shi, wannan wani irin zazzafan kyau ne! irin wannan kyan shine mutane ke neman tsari da shi, jikinsa na sanye da kakin sojoji ba ƙaramin daukarsa su kayi ba, yayi hoton ne kamar a shirin film a saman mota yayi irin wannan zukunnawar da suke yi in zasu yi harbi da bindiga, hannunsa riƙe da bindigar yayi hoton, doguwar sumar kansa wanda ya ɗaure ta