Showing 27001 words to 30000 words out of 74786 words
dai2ta, har ankawo kuďi dan anaso ayi bikin tareda na Nawaf, yasmeen tayi farinciki sosai da faruwar haka, bare ameena amarya, ai tafi kowa farinci, dan tana son mas'ud sosai.
Yau kuma aka kawo lefensu su duka akwatuna bakwai2, komai iri ďaya, wanan aikin papa ne, dan shida momcy suka haďo lefen.
Wannan shi ake Kiran lefen 'yan gata, mutanen anguwa da dangi duk sun yaba.
Filin jirgin na kano cike yake da matasa domin tarbar NAWAF!!.
🛬jirgi yafara shawagi neman muhallin sauka, bayan tsayawarsa fasinjoji suka fara fitowa, Nawaf shine na 6, ahankali yake sakkowa kamar bayaso, jikinsa sanye da 'kananun kaya, ya ďora 'katuwar rigar sanyi fara, ya saki hular a baya, sai tashin 'kamshi yakeyi, yagoyo jar jakka abayansa wadda aka rubuta (Adidas)na ce, "kai gay ďinnan handsome ne gsky.
Da gudu anwar yaje ya rungumesa, shima cikin farinciki ya rungume shi, yana faďin i missing u autan momcy.
Missing u too yayana.
Gaba ďaya 'yan uwa da abokan arzi'ki suka taso gareshi, 'yan jarida kuwa sai 'kutsa kai sukeyi domin samo bayanai.
Da'kyar suka barshi yashiga mota mas'ud yaja suka nufi gida, anata ďaga masa hannu shima yana ďagawa.
Abdallah ya ce, "yaya dabamu samu mun gudoba dasai yamma zamu baro filin jirginnan.
Nawaf ya ce, "gsky ne brother shiyyasa naso na sauka da daddare.
Mas'ud yay dariya ai koda daddaren ne sai mutane sun jiraka tunda anuna a labarai zaka sauka kano yau, aii ko randa kazo daga Spain mutane basu taru hakaba??.
Abdallah ya ce, "to ba sunga ya cimusu kwalloba yau, suka tuntsure da dariya su duka.
Anwar ya ce, "nifa wani tsareni yayi saina bashi number yaya, na ce, "masa banida waya kuma ban ri'ke number ba.
Mas'ud ya ce, "hummm autan momcy sarkin wayo.
A babban tsakar gidan sukai Parking, Nawaf yasha mamaki dan ganin dangi cike da gida, 'yan katsina da saudia, duk sunzo, dangi sai rungumeshi ake ana murna, musamman 'yan saudia dansu dama al'adarsuce.
Family falo suka nifa inda sauran dangi suke harda kakarsu Nawaf ta wajen uwa tanan darai hajja humaira kenan.
Hajja humaira ta ringume Nawaf tana farin cikin ganinsa, ta ce Masha ALLAH mai gida ka 'kara 'kyau da girma, kodai an canja mini kaine??, Nawaf yay dariya A'a hajjana ba a canja miki niba ninedai maigidanki na 'karfen!!!.
Gaba ďaya akasaka dariya, ta ce, "kamanta damu ko Nawaf!!?, da sauri ya 'kara rungume hajja ya ce, "ni na isa na manta daku, uwargida sarautar mata, hajja nayi missing ďinki sosai.
Hajja ta ce, "ďan nema kai dai bazaki hausarba bare larabcin?, turawa sun 6ata mana ka!!.
Nawaf yay murmushi yabi dukkan iyaye da kakannin yana gaishesu, har 'yan katsina.
Ya ce, "ni banga sauran sisters ďina ba??, kobasu zoba??.
Tab wazai 'kizuwa bikin ka (Abi)yaya kenan, kowa yazo, sauran suna gidan amaryarka, muma yanzu za'a kaimu, wai a al'adar hausawa yaune ('kunshi)to zamuje mu ganine!!.
Nawaf yay murmushi, lallai kam idan kun gani saiku koya koh??, dariya ameera tayi ta ce, "to Abi!!.
Duk da larabci suke maganar, ina fassara mukune yanda zaku gane😜lol.
D'akin kusada papa ya shiga inda ya maida kayansa kafin yatafi, yay wanka, yaci abinci, kwanciya yayi domin yaďan huta.
Sai wayarsa ta hau wringing, mas'ud ne yake kiransa, ya ce, "ďan uwa ya akayine??, ya ce, "tambayata ma kakeyi?? To kafito muje wajen kamu.
Nawaf ya yatsine fuska, miye kuma kamu??, dariya mas'ud yayi ya ce, "idan munje zaka gani, kai malam nidai hajja haka ta ce, "mini sai gobe.
Dariya mas'ud yayi ya ce, "nima wasa nake maka, bari nabarka kayi barci ka huta, sai mun haďu anjima.
Okey bye🖐🏻Nawaf yafaďa yana ďaga masa hannu kamar yana ganinsa.
____________________________
A 6angaren yasmeen kuwa suna gidan su ameena anan ake zaman 'kunshi, gidan cike yake da 'kawayensu da dangin Nawaf larabawa da 'yan katsina, muta nen saudia dai basa jin hausa saidai turanci, dan haka gurin yazama dandalin turanci, tunda duk sunaji.
Wata mai 'kunshi aka ďakko tanama amare yasmeen da Ameena ta iya sosai, saikuma wasu su biyu sunayima 'kawayen amre suma kam gwanayene, yasmeen bata cikin walwala, amma bataso dangin Nawaf su gane dan haka ta saki jiki anata hira, Ameena ce kawai take gane damuwarta.
suma sai jida ita sukeyi, wata budurwace dai yasmeen takula batada walwala, tunda sukazoma tanemi guri ďaya ta zauna ita kaďai, (ummu habeeba ce) tana mutuwar son Nawaf, ita ce Nawaf ya ce, "ta cika 'kyau, kuma gsky ya faďa dan tafi sauran 'yammatan 'kyau gsky.
Sai dare aka maidasu gidansu Nawaf,, Nawaf yana zaune a harabar gidan tareda sauran samarin 'yan uwansa na katsina dana saudia, anata hira da raha.
Moto ci suka fara sauke 'yammatan, wajansu suka nufo suna mai farin cikin ganin Nawaf, gaisuwa aka shiga yi irinta al'adar larabawa, ummu habeeba kam saita tokare agefe ta'ki zuwa, Nawaf yana ganinta ya shareta, saida ga baya kuma ya mi'ke ya nufeta.
Tana sanye cikin ba'kar jallabiya ta naďe kanta da ďankwalin kamar yanda larabawa keyi.
Ya tsaya yana kallonta, ta harareshi nagode abi tafaďa tana turo baki gaba.
Yay ďan murmushi minayi miki kike yimini godiya??, tai far da idanu, ta ce, "kaima kasani.
Yay murmushi har fararen ha'koransa suka bayyana, yasan inda ta dosa amma saiya basar, ya ce, "kinga koma mikike ganin nayi miki to ki share ki tayani murnar aurena kamar yanda kikayi niyya tun farko, wananne zuwanki 9ja na farko ko??.
Bataso aka daina waccan maganarba amma yazatayi tunda ya nuna bayaso, ta ce, "eh shine na farko, ahaka dai sukaita hirarsu, cikin harshen larabci.
_______________________KAMU.
Yau takama kamu, kamu kuwa za'ayi irin na saudia ne, a harabar gidansu ameena za'ayi saboda yafi girma, an 'kawata gurin da kwalliya mai tsari, an baza 'katuwar darduma inda amarya da ango zasu zauna, agefe kuma an jere fararen kujeru inda sauran mutane zasu zauna.
Hajja ce tazo da kanta ta ro'ki su umma akan abarasu suma suyi al'adarsu ta larabawa a wajen kamu, su umma sukace babu damuwa suma sunada iko akan komai aii.
Wajen 'karfe 4:00pm na yamma aka gama shirya amarya cikin ba'kar doguwar riga ba'ka mai ďan karen 'kyau, gashinta yasha gyara an ďaureshi abaya wanda bai saniba saiya ďauka itama balarabiyar ce, dan NAFISAR KADUNA ce ta tsara mata kwalliya wadda amaren zamani suke yayi.
Kowa ya hallara sai amarya datake falo tana jiran isowar ango, dan tare akeso su fito.
Bayan kamar minti10 ango ya iso da tawagar abokansa, kowa ya zauna inda ya dace, aka raka ango inda zai ďakko amaryarsa.
Kai kawai ya tura cikin falon batarda yayi sallamaba, tana zaune akujera hankalinta yana kan waya tana game.
Ai gogan naku yana tsaye ya daskare dan ganin tsarin hallita irinta ubangiji, gsky koba komai yayi dacen mata 'kya'ky'kyawa rashin kunyartane kawai matsalarsa.
Jitai kamar alamar mutum yana kallonta, ta ďago da sauri, Nawaf tagani tsaye kamar gunki yayi masifar 'kyau cikin kayan larabawa wando da riga farare, anyi musu kwalliya da golden ďin zare, sumarsa tasha gyara daka gansa kaga cikakken balarabe.
Saida ta murguďa masa baki😏ta ce, "malam lafiya??, katasani gaba kana kallo, mi naci naka??.
Hararar ta yayi ya ce, "ki ajiye makaman rashin kunyarki har zuwa nanda kwana uku, domin yanzu ina kan bin umarnin iyayenane, bazanyi abinda zai 6ata musu rai ba agaban ďumbin jama'ar dasuka tara.
Yay wani murmushin mugunta, yaďora da faďin amma nanda kwana uku, ko ance ki kalleni kimin rashin kunya wlhy baza kiyiba, dan zanyi maganinki 'karamar mara kunya kawai.
Ta buďe baki domin mayar masa da amsa sai aka turo 'kofar.....wata 'kanwar momcy ce Fateema, ta ce, "Abbuna ku ajiye wannan soyayyar taku sai nan da kwana uku dan yanzu mutane suna jiranku.
Nawaf yaďan sosa gefen wuyansa ya ce, "sorry Abla(aunty kenan) muna zuwa.
Ya juyo ya harari yasmeen sanan ya 'karasa wajenta, hannunta yakama, jikin yasmeen yay wani yarrrrrrr, shimadai gogan naku saida sassan jikinsa suka amsa, Abla fateema ta gyarawa yasmeen ďankwalinta tabaya, sannan ta rufe mata fuska da wani jan gyale.
Nawaf ya ce, "Abla ai bata gani, idan ta faďi fa??.
Abla tayi dariya kai ka bari tafaďi bayan kaine ďan jagora.
Ya ce, "hakane idanma kin amince na ďauketa gaba ďaya naje na dire awajan.
Abla fateema ta tuntsure da dariya ta ce, "babu ruwana.
Yasmeen ta ce, "azuciyarta mugu saika nemi wadda zaka ďauka amma baniba.
Catake a zuciya take magana bata san afili takeyiba dan Nawaf yana jinta, amma Abla bataji tunda da hausa take maganar kuma ahankali.
Bayan sun fito gurin ya ďauki tafi, wajen kujerar da'aka tanadar musu mai ďan faďi sukaje suka zauna, saidai sun matsu juna sosai, yasmeen sai takurewa takeyi.
Agaban kujera aka shimmfiďa dardumar daza ayi kamu.
Ba6ata lokaci akayi addu'a ga ma'aurata, har yanzu fuskar yasmeen a rufe take.
Nawaf tya ce, "malama nifa kin matseni.
Dariya bin yabama yasmeen dan haka tayi murmushi, ta ce, "kanka akeji wai mahaukaci ya faďa ruwa.
Nawaf yay murmushi mai sauti, kema za'aji kankine yarinya, dan ďazu ina jinki.
Idan kagansu saika ďauka hirar arzi'ki sukeyi.
Bayan angama addua aka fara shirin kamu, ango da amarya suka sakko 'kasa kan dardumar, suna fuskantar juna fuskar yasmeen arufe.
Wani haďaďďen kwando aka ajiye agefensu wanda yake cike da turarurruka kala2 masu tsada da 'kamshi, abla ta su'ko tanama Nawaf magana acikin kunne da larabci, wanan yasa yasmeen bataji abinda suke faďaba, yay murmushi tareda jan kwandon gabansu.
Saida akasaka wa'ka wadda akayima ngo da amarya amna da larabci, sannan aka bama ango umarni yashiga cikin gyalen da'aka rufe fuskar yasmeen dashi.
Ya yaye ahankali ya rufa akansa, yazama su biyune aciki.
Kan yasmeen na 'kasa Nawaf ya ce, "ina fata dai al'adarmu ta 'kayatar dake, taďan ďago ta kalleshi ganin ya kafeta da idanu yasa ta maida kanta 'kasa da sauri.
Turare ďaya aka mi'ko masa yashiga fesama yasmeen, harda mugunta saida ya 'karar da turaren duka ajikinta, saboda 'karamar kwalba ce, fitinannen 'kamshin ya gauraye wajen.
Ya yaye mayafin daga fuskokinsu, gaba ďaya gurin aka saka tafi, daganan kowa yataso saiya ďauka a kwandon yazo yaďan fesa musu, saida kowa ya fesa sanan aka rufe taro da addu'a kowa ya kama gabansa.
____________________________
Yau aka ďaura auren mas'ud da Ameena, ALLAH yasanya alakairi mas'ud.
Da yamma aka tafi bababan filin kwallo na kano anan za'a buga wasan biki, wanda (KANO PILLAS SUKA SHIRYA DOMIN KARRAMA ANGO) an tsara wasanne 6angaren ango da amarya, abokansa 'yan kwallo dasukazo daga 'kasashe daban2 da 'yan kano filas, 'kuria aka yi idan ka ďauki 6angaren ango kona amarya to suzaka bugawa.
Wasankuwa ya 'kayatar dan har a labari aka nuna, antashi 8 da 5, ango 5 &amarya 8.
------------------------------------------
Da daddare aka shirya kai amare ďakinsu anan naga kuka, yasmeen kuka take kamar ranta zai fita, sai nasiha da lallashinta akeyi, hakama ameena.
Da 'kyar aka 6an6are yasmeen daga jikin umma, tanata kuka dafaďin bazatajeba itafa tafasa aueren, amma ina, tuni aka dannata amota, sai gidan ango.
An mi'ka Amin gidansu mas'ud yasmeen kuma gidan su Nawaf, a ďakin momcy.
Bayan kamar minti30 aka shiryasu zuwa wajen gagarumar dina da abokan Nawaf suka shirya, amma sun haďe harda mas'ud, ammafa wajen ya 'kayatu sosai.
Amare sunsha shiri cikin rigunan aure, yasmeen sai masifa takeyi, wai rigar arna, Nawaf yana jinta yay mata banza.
Komai ya 'kayar agurin, amma wajen bada cake Nawaf saida ya ciji hannun yasmeen, tai wata 'yar 'kara, wadda tasa muta nen gurin ihun dariya a zatonsu duk cikin soyayyane😜lol.
Sai shabiyu aka tashi, idanun yasmeen cike da barci, suka fiffito tana tangaďi, ga wani dogon takalmi data saka, tako goce zata faďi da sauri Nawaf ya tarbota ta faďo jikinsa, sai kawai ta lumshe idanu dan barci takeji.
Girgizata yayi da 'karfi, ke dallah malam tashi karki karya mini hannu, inko ba hakaba zan sakeki ki faďi 'kasa ALLAH.
yasmeen batasan yana yibama, Kausar ta ce abi! ka ďauketa kawai wlhy barci takeyi tagaji dayawa ne.
Bayaso danginsa su gane komai gameda auren, dan haka ya sa6eta kawai sai ďakin momcy, ALLAH ya taimakesa ma 'yammatan ne a 6an garen momcy, kuma babu wadda yake jin kunya acikinsu.
Ruwa ya ďauka a saman madubi da wata tasha tarage, yazuba ahannusa ya shafa afuskar yasmeen, tako kawo numfashi.
Ahankali ta buďe idanu tana kallonsa, ya ce, "ke kitashi kicire wanan rigar, sanan ki kwanta yana gama faďa yafice, da'kyar ya iya tashi tacire, ta koma ta kwanta................✍🏻
Na ce, "asuba tagari yasmeen.
©2016
💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆
NA BILKISA IBRAHIM💞
Page👉🏻27 & 28
......Washe gari akayi walima, dakuma wa'azi wanda manyan malamai suka gabatar.
Masha ALLAH wanda akayi dansu sun 'karu sosai, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a.
Kowaya kama gabansa, musamman ma abokan Nawaf dasukazo daga 'kasashe daban2, karfe 2:30pm na rana jirginsu ya ďaga, cikin 'yan katsinama wasu sun tafi mazansu da matansu, sai 'yan kaďan aka bari.
'Yan saudia ne dai sai gobe wasu zasu tafi.
8:30pm
Da daddare aka shirya yasmeen tsaf, dan za'a maida ita 6angaren Nawaf, wata 'kanwar papa tashigo tana faďin amarya tashi akaiki ďakin ki ko??.
Yasmeen ta marairaice fuska kamar zatayi kuka, ta ce, "inna dan ALLAH abarni anan, yafi daďi ga abokan hira.
Murmushi tayi, ta ce, " 'yanan idan anbarki anan ďakinki kumafa, da angoki, mukuma dakike gani nanda jibi bazakiga kowaba fa?, dan haka tashi muje kinji 'yar albarka.
Badan yasmeen tasoba ta tashi suka rakata, wooow!! Lallai an gyara 6angaren Nawaf sosai an sake masa fenti, sannan komai na 6angaren an sake, tundaga kujeru labulaye tv kayan gado, komai ansake, dama papa cayayi karsu abba suyi komai, amma duk dahaka saida umma tasayi kayan kichin masu yawa, aka kawo, gakuma wanda momcy tasaya, kichin ďin kam aii ya 'kayatu da 'kyau.
Tana kuka suka tafi suka barta bayan an kaita bedroom ďin Nawaf, wanda shi kaďaine a6angaren nasu.
Falo ne babba sai bedroom, kichin da sito, dakuma wani 'karamin ďaki agefe wanda Nawaf yacika da kayan motsa jiki, sai kuma wani ďan fili awaje wanda aka 'kawata da kujeru masu 'kyau domin hutawa, komai yayi awajen kuma komai naciki 6angare lemon green ne.
Yasmeen tana zaune a tsakkiyar gado inda su inna suka barta, kuka taketa yi, na ce, "dama aike gwanace wajen iya kuka.
Har 'karfe goma Nawaf bai shigoba ta mi'ke ta cire kayanta ta canja da marasa nauyi, gadon ta haye batareda wani tunaniba ta kwanta abinta, dan danan barci yay awon gaba da ita.
Nawaf kam yana ďakin daya koma harma ya kwanta, momcy tazo kawoma papa lifton sai taga wuta a kunne, ta ce, "oh ni modebbo akunne yabar wutar ďakinnan, tura 'kofar tayi tashiga da nufin kashe wutar, turus tayi dan ganin Nawaf bisa gado yayi ďai2 yana barci.
Kai ta girgiza ta 'karasa gaban gado tafara kiran modebbo! Modebbo!!.
Nawaf ya buďe idanu ahankali yana kallon momcy.
Ta ce, "mikakeyi anan???.
Ya ce, "momcy kamar ya??.
Hararar sa tayi, ta ce, "shine kabaro matarka ita kaďai kazo nan ka kwanta, maza katashi kafin raina ya 6aci kawuce ďakin matarka.
Baki ya buďe zaiyi magana........da sauri momcy ta ďaga masa hannu🖐🏻kaga bana son jin komai, katashi kawai ka tafi.
Bayanda zaiyi dole ya mi'ke wayoyinsa kawai ya ďauka, dan tunda rana momcy tasa Anwar yamaida masa kayansa 6angarensa, yafice yana turo baki gaba.
Momcy ta bishi da kallo tana girgiza kai.
Nawaf yashigo ya rufe ko'ina mai makon yatafi ďaki saiya kwanta saman kujera doguwa.
Can dare Nawaf yakasa barci dan bai saba kwanciya ahakaba, sai tsaki yakeyi yana juyi, ga kujerar ledace.
Ya sakko 'kasa saman kafet ya kwanta aii saiyaji tamkar ana tsira masa allurai, yatashi zaune ya rabga uban tagumi kamar wanda uwarsa ta mutu, ga barci yana cin idanunsa.
Tashi yay yanufi ďakin, ahankali ya tura 'kofar, amamakinsa saiya jita abuďe, baiyi zaton hakaba.
Yasmeen tana kwance ďai2 dan barci ya saceta, ga gajiyar biki, yanda ta kwanta saida ya ta6a zuciyar Nawaf.
Ya kauda kai daga kallonta tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, asanyaye ya zauna saman kujerar dake ďaki, yakai minti biyar ahaka, sannan ya tashi yanufi bayi, shawa🚿 yasakarma kansa, na ce, "ai dama ka saba.
Yadaďe ruwa yana ji'kashi, wanda 'karar ruwan tasa yasmeen farkawa atsorace, tana nan zaune yafito jikinsa ďaure da farin tawul, hannunsa ri'ke da 'karami yana tsane sumar kansa.
Kallo ďaya tai masa ta kauda kai, shima haka,