Showing 39001 words to 42000 words out of 74786 words

Chapter 14 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

361

yaďan murmusa, 'yar rainin hankali mikika maidani??, yarinya ni tausayinki naji dan wlhy kafin mu dawo kin galabaita, kuma sonake muje ko ina yau, dan gobe zamu koma safana, dan haka idan kinga zaki hau ki hau.
Jiki a sanyaye ta kama mashin zata hau saida ta rirri'keshi sanan ta iya hawa, ya tada mashin suka tafi.
Aikuwa da gskyar Nawaf, tabbas da a'kafa sukazo dataji jiki, ammafa atsorace take bisa mashin ďin, bata san lokacin datasaka hannunta biyu tai masa zobeba, ta kwantar da kanta abayansa.
Ahaka suka isa wani 'kauye, Nawaf yatsaya awani 'kofar gida na jar 'kasa,, ya ce, "to ba'kauya sauka, kinbi kin wani 'kan'kameni, kinsa sai kallonmu akeyi.
Ta sakeshi ta sakko tana faďin, wlhy suyita kallo, ai babu wanda yasanni, da asara gara gidadanci.
Yakafe mashin ďin yana dariya, to ke idan kin faďi wayayi asarar.
Ta ce, mutane dayawa kuma harda kai aciki wlhy.
Kai haba ALLAH yakiyaye, ni aii narabu da 'kayama".
Tsaki yasmeen tayi, ta ce, "aikai kafi 'kayarma.
Gaba yayi yana faďin idan mun koma gida zaki maimaita.
Suka shiga gidan da sallama, wata dattijuwa ta ďago tana amsawa da fara'arta, ta ce, "wanake gani kamar Nawaf, Nawaf yay 'yar dariya nine kuwa inna, kai lale daku, sannu dazuwa kinji ďiyata.
Yasmeen ta amsa da 'yauwa, inna ta kwala kiran dijengala!!, wadda aka kira dijangala ta amsa tana le'kowa.
Inna ta ce, "kawo tabarma maza.
To tafaďa tana komawa cikin ďakin, sabuwar tabarma dijangala tazo ta shinfiďa, tana faďin yaya na birni sannu da zuwa.
Nawaf ya ce, "yauwa dijengala ya garin??, ta ce, "gashinan 'kalau, ta ce, "sannu amaryar yaya, yasmeen ma ta amsa tana murmushi, bayan tagama suka zauna, aka shiga gaishe2, da tambayar juna bayan rabuwa.
Dijangala ta kawo musu ruwa, itadai yaameen sai kallonsu takeyi, dan ganin yanda suketa zabga sururutu, misamman ma dijangala, dan ita adole son Nawaf takeyi, shiyyasama ta'ki aure, tun abin yana burge yasmeen haryakoma bata haushi.
Babu kunya dijangala ta ce, "yaya na birni nimafa nagaji da zaman nan gsky, Nawaf ya ce, "tokiyi aure mana, baga su sa'a nan ba harsun haihu, kuma kin girmesu.
Tai far da idanu, to ai kasan kainake jira ko??, wata bazawarar dariya Nawaf yayi, ya ce, "yarinya kin ďakko dala babu gammo, bakiga matata tafiki 'kyauba, kuma ni mijin ta cene.
Dijangala ta rage fara'a, dan tadaďe tana nunama Nawaf tana sonsa, amma saiya maida abin wasa, dayake abokan wasa suke.
Nawaf ya katse mata tunani dafaďin inna kinji wani ďigimi wajen dijangala, ko inani ina auren baiwata?.
Inna habi ta ce, "aii komai na ALLAH ne, (WAYASAN GOBE??,) Nawaf ya ďan ta6e baki dan yasan itama innar duk jirgi ďaya ya kwasosu da 'yar tata, ya ce, "sai ALLAH, amma yakama ku aurar da dijangala kafin tarasa miji a 'kauyenana wlhy.
Dijangala ta ďaure fuska tamau kamar zatayi kuka, agaban matarsa yake gaya mata haka saboda wula'kanci.
Itama ran inna habi ya 6aci, jitake kamar ta doke Nawaf, dan itama tana fata dijangala ta auri Nawaf kodansu 'kara hutawa.
Nawaf ya kalli yasmeen data cika tayi fam kamar zata fashe saboda kishi, shi dariyama ta bashi, amma saiya gimtse ya ce, " 'yammata tashi muje munada sauran gurin zuwa.
Yasmeen tami'ke tana zuzzun6ura baki, sukayi musu sallama suka fito, bayan Nawaf ya ajiye musu kuďi da tsaraba.
Amma ko godiya basu yimasaba, shima bai damuba, dan hakan yafi sau'ki, inashi ina wannan kucakar yarinyar mai kamada 'yar bori.
Koda suka fito yasmeen sai wani shan 'kamshi takeyi, Nawaf ya ce, "yammata tunkan nayi auren har kin fara nuna kishi??.
Yasmeen ta murguďa baki😏tana harararsa🙄ta ce, "ALLAH ya kiyaye, miye abin kishi awurinka, ai abinda kakeso kakeyima kishi.
Dariya Nawaf yayi yana faďin aii kuma kin makaro yarinya, fuskarki ta nuna sirrin zuciyarki, dan haka babu abinda zaki faďa na yarda.
Tsaki yasmeen tayi tana faďin matsalarkace dai.
Yahau mashin ďin yana faďin kokuma takiba, kina ba'kinciki nasamu amarya, aiko saidai ki fashe nanda wata shekarar za'a sha biki.
Banza tayi masa ta haye mashinďin tana hawaye.
Yanajin shashshekar kukanta, yayi murmushi kawai, azuciyarsa ya ce, "yarinya ta kamu.
Haka sukaita zagaya dangi har yamma, sanan suka koma gida, aďakain hajiya iya suka yada zango, ta ce, "sannunku, kishiya kinsha yawo ko?, yasmeen tayi dariya tana faďin ai daďi, naga gari.
Hajiya iya ta ce, "yayi 'kyau.
Bayan magriba ta tafi 6angaren su kuluwa matar basiru, dayake duk sa annintane, saidai kowaccensu tanada yara uku zuwa huďu, idan ka gansu saika ďauka sun haifeta, yasmeen ta ce, "azuciyarta dayanzu nima haka nakoma a kwangwalan, kai ALLAH na gode maka.
Hira tazauna sunayi, suna labarin bikinta da 'kauyancin dasukayi awajen anata tuntsura dariya, firera matar salmanu ta ce, "aini da akaje wajen dakuka saka waďan nan rigunan kamar aljanu, da hasken wajen ya haskani saina ruďe nashiga ďimuwa, saida basira ta taimaka mini.
Gaba ďaya suka kwashe da riya, hira sukeyi sosai har wajen 'karfe tara, mazajensu suka fara shigowa gida, yasmeen tami'ke tana faďin bari naje na kwanta nima, wlhy duk nagaji.
Tana tashi ta kwalla 'kara, ta zube awajen, cikin tashin hankali suka shiga tambayarta lafiya??.
Ta ce, "wani abu ya cijeni a'kafa, wayyo ALLAHna, da sauri sha'aibu mijin barira ya haska, zuwa sanan Nawaf ya 'karaso waje danjin 'karar yasmeen.
'Katuwar kunama suka gani ba'ki'k'kirin, ta tada bindi sama🦂, sha'aibu ya ďauketa da hannunsa, ya kashe, Nawaf ya'karaso wajen yasmeen daketa zabga zufa.
Ya ďagota zuwa jikinsa, ta ce, "modebbo ka taimakeni tafiya takemin, sai asanan kuluwa tai saurin cire ďankwalinta ta ďaura mata a'kafar.
Nawaf ya rungumota zuwa jikinsa yana share mata zufar, yana faďin sannu kinji yi ha'kuri, salmanu yazo yasaka mata magani, sai sannu suke mata, aka zuba wani aruwa aka bata tasha, dandanan zufar ta 'karu, salmanu ya ce, "yaya ka ďauketa kujecan zata faďi insha ALLAHUi.
Nawaf ya ce, "to, cak ya ďauki yasmeen zuwa 6angarensu, suka rakasu da ALLAH ya kiyaye gaba.
Saman katifa ya direta tanata zufa, ya ce, "sannu".
Ta kaďa kai tana hawaye.
Ya ce, "haryanzu tana miki yawon??, tace ba sosaiba amma.
insha ALLAHU zata daina gaba ďaya, bari acire miki waďanan kayan kinga kinata zufa, batareda yajira amsartaba, yakama zip ďin ya sauke zuwa 'kasa, yasmeen ta rintse ido tana huci, yakama bra ďinta xai cire, da sauri tajuyo tana kallonsa, shima kallonta yakeyi, amma yaďan ďaure fuske, ya ce, "kafiya??".
Cikin rawar murya ta ce, "plz kabarsa kawai, ya ta6e baki yana faďin keni bana son iyayi, bakida lafiyarma saikin jawo munyi, ko ba'kya ganin zufar dakikeyine??,.
Ta ce, "to kafita zan cire da kaina nidai.
Tsaki yayi saidai idan bazaki cireba kuwa, dan wlhy babu inda zanje.
Ta ce, "to maidamini zip ďin rigata, tunda ni yaronkine ba, yafaďa yana kwanciya.
Hijjabi ta jawo tasaka, sanan ta cire rigar, taja zaninta zuwa sama, yana kallonta tana ta zufa, ya ta6e baki, daga nan ya ďauki wayarsa yana danne2nsa, sai wajen karfe goma kunamar ta faďi, yasmeen ta mi'ke waizata tayi wanka.
Nawaf yashiga tuntsura mata dariyar mugunta, cikin jin haushi ta ce, "malam lafiyarka kuwa??, Nawaf yacigaba da dariyarsa batareda ya kulataba, harta kai 'kofa zata fita, ya ce, "wlhy kije kiji'ka tadawo sabuwa, kezakai sha wahalarki ke kaďai, danni ficewata zanyi nabar miki ďakin wlhy.
Ita sai yanzuma tatuna idan kunama ta harbeka ba'a saka ruwa, tadawo bakin katifar ta zauna ta rabga tagumi.
Nawaf yacigaba da dariyarsa ta rainin hankali, itadai banza taimasa ta'ki kulasa.
Yafara faďin modebbo ka taimakeni tafiya takemin.
Tagane kwaykwayon muryarta yakeyi, dan haka ta harareshi tana murguďa baki, ya ce, "yarinya ashe zaki sake shan wata wahalar wlhy.
Ta ce, "wlhy saidai musha, dan ba 'kyaleka zanyiba, yatashi daga kwanciyar dayayi, ya ce, "sake murguďa wannan bakin maikama da na tsintsaye kigani.
Saida tazamo daga katifar sanan ta murguďa😏.
Tami'ke da sauri, zata gudu, taku ďaya yayi ya dam'kota, yamaidata saman katifar, saman cikinta yahaye, yakama fuskarta da hannu biyu, ya haďe bakinsa da nata yashiga kissing ďinta.
Itako sai mutsu2 take nason ta kwace amma takasa, gashi ya danne mata ciki, saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana maida numfashi, tabirkice zuwa rubda ciki tana kuka, tana tofar da yawu, 'kazami kawai, zakawani ta bani yawunka inasha, sai ALLAH yasaka mini wlhy.
Kusada ita yakwanta, yadafa bayanta, 'yammata gobema ki 'kara yimini murguďa baki ki gani, saina miki abinda yafi haka, ya 'kare maganar yana dukan bayanta.
Ta mirgina 'kasa tana cigaba da goge baki da hijjab, Nawaf kuma yana mata sassanyar dariya, yajuya ya kwanta yana murmushi wanda shi kansa baisan na miyeba, a hankali yafurta 'yar rigima.
Saida taga yayi barci sanan tadawo saman katifar, takwanta agefe nesa dashi kamar yanda tayi jiya.
Washe gari tunda safe saddiqu ya wankema Nawaf motarsa, zuwa 'karfe goma suka baro 'kauyen cike da kewar muta nan garin, masu kirki da karrama ba'ko, yasmeen harda hawaye.
Suma 'kyauyen sun tafi sun barsu da kewarsu.
A safana suka yada zango, gidan wani abokin papa, nanma sun zaga dangi, ananma yasmeen taga 'yammatan dasukaje bikinta dayawa, sunyi farincikin ganinta itama haka.
Anan batare suka kwana da Nawaf ba, aďakin matar abokin papa ta kwana, shikuma ďakin ba'ki.
Washe gari suka haďa inasu2 suka garzayo kano, cikeda uwar tsaraba, yasmeen takali Nawaf daketa wani ďaure fuska, ta ta6e baki tana faďin mutum tamkar mai aljanu, yanzu zaka gansa yana dariya, yanzu zai ďaure fuska kamar rundunar sojoji, har suka iso kano basa wata hirar arzi'ki, saidai ita dake tambayarsa sunayen garin dasuke wucewa, ada'kile yake bata amasa, itama daga baya saita kulle bakinta gam.
Dahaka suka iso kano, cikin farinciki su momcy suka taresu, momcy ta ce, "ďiyata kinyi ba'ki wlhy, yasmeen tai murmushi tana sissine kai, hajja ta ce, "Nakuwa haďa muku abinci mai daďi na tarba, dan haka saiku shirya ci.
Nawaf ya ce, "kai hajja da kanki, amma kinyi 'kokari.
Ta ce, "nayi kewarkune shiyyasa.
Nawaf ya ce, "to mungode miki hajjarmu abin alfaharinmu.
Yasmeen ta ce, "momy wai ina su Anwar???, suna islamiyya fateema, amma nasan suna hanyar dawowa, dan tun safe ake shirye2 dawowarku.
Yasmeen tayi murmushi tana faďin ALLAH yadawo dasu lafiya...................✍🏻

Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Whatsapp Number 08138873799
Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents


Assalamu alaikum
Nagode da sakwanin gaisuwarku gareni, harma waďanda basu sami damaba,,,,, happy juma'at khareeeeem! !!!
Luv u oll😘😘😘😘❤❤



©2016



💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞



Page👉🏻35 & 36

......Tunda suka dawo basa shiga harkar juna, sun koma zaman doya da manja, gaisuwa ce kawai ke shiga tsakaninsu, saikuwa girki da yasmeen zatayi, yazo shikuma babu kunya yaci.
Abin yana bama yasmeen mamaki, idan ta tuna abinda Nawaf yarin'ka yimata a safana, takai dubanta ga 'katon hoton Nawaf dake falon, yana sanye cikin jan jc yayi 'kyau sosai, afili ta ce, "mutun 'kya'ky'kyawa a waje, amma azuciyarsa yafi maciji mugunta, ta gallama hoton harara.
Nikam danake gefe na tuntsure da dariya, dan tabani dariye, kome hoto yay mata??.
☆ ☆ ☆ ☆
Ayaune kuma hajja zata lula saudia, fuskar kowa ka kalla a gidan babu walwala, amma babu yanda zasuyi, haka sukai gayya suka rakata airport Anwar sai kuka yake wai saiya bita, papa ya ce, "yabari ayi hutu saiya tafi, hakadai suka dawo gida kowa yana zum6ura baki.
Yasmeen ma dabata daďe da sanintaba saida taji babu daďi, dan hajja tsohuwace mai shiga rai, ga kirki da son mutane, lallai anan momcy ta kwaso 'kyawawan halaye, to saimuce hajja ALLAH ya kiyaye hanya.
Tunda suka dawo daga 'kauye yasmeen batada cikakkiyar lafiya tana 6oyewane kawai, amma yau dole ta kwanta, shi oga Nawaf ma bai saniba, dan yanata hidimar komawarsa Spain.
Saida momcy taga har la'asar yasmeen bata shigo wajensu ba sannan, tafara tunanin ko lafiya, ta mi'ke ta nufi 6angarensu, babu kowa a falon saidai an gyarashi tsaf yanata 'kamshi, kai tsaye bedroom tawuce, da sauri ta 'karasa bakin gadon domin ganin yasmeen a 'kudundune cikin bargo.
Momcy ta zauna agefen gadon taďan ďaga bargon tana faďin ďiyata kina lafiya kuwa?....ta 'karashe maganar a ahankali, danjin zafin zazza6i a jikin yasmeen.
Dan danan momcy ta ruďe tashiga tambayar yasmeen tun yaushene batada lafiya?, yasmeen ta buďe ido da 'kyar, ta ce, "momy tunda daddarene.
Cikin damuwa momy ta ce, "amma shine baki faďaba?, ina modebbo??.
Yasmeen ta ce, "yafita tunda safe.
A'a, baisan bakida lafiyaba ne??, yasmeen ta daga kai alamar eh.
Waya momcy ta ďauka takira Nawaf, modebbo kana inane??, Nawaf ya ce, "ganinan zuwa gida ma.
To saika iso momcy tafaďa.
Abinci mai sau'ki momcy tasaka su talatu su dafoma yasmeen, ta taimaka mata tayi brosh da wanka dantaji daďin jikinta, tana fitowa Nawaf yana shigowa, tayi tsaye kamar gunki shima tsayen yake yana 'kare mata kallo, dan sukaďaine a ďakin, momcy tana falo.
Da sauri yasmeen taja hijjabin sallarta ta kudundune aciki, baki Nawaf ya ta6e yana wani yatsine fuska.
Itakuma tawuce ta zauna bakin gado, momcy tashigo da sallam tareda talatu.
Sai asannan Nawaf yazauna akan kujera, momcy ma ta zauna talatu kuma ta ajiye abinda takawo ta fice, momcy ta ce, "ďiyata saboda mi baki gayama mijinki bakida lafiyaba?, dan ya ce, "mini shima bai saniba.
Saida yasmeen ta kalli Nawaf sannan ta ce, "banaso hankalinsa ya tashine.
A'a wanan ba hujja bace, yaza ayi ki zauna da ciwo saboda kar hankalin mijinki yatashi, daga yau karki sake kinji ko?, yasmeen ta ce, "to momy insha ALLAHU baza'a sakeba.
Nawaf ya ce, "momcy bari na kira mas'ud yadubata, dan naga bai fitaba.
To, yakamata kuwa.
Momcy dakanta ta bata abincin taci, sai yatsine fuska takeyi, ahaka su Nawaf suka shigo suka isketa, mas'ud yay mata sannu, tana gama cin abinci ta tashi da gudu ta nufi bayi, amai ta ringa zazzagawa kamar hanjin cikinta zasu fita, momcy tabiyo bayanta dasauri, ta taimaka mata hartagama tagyaramata jikinta, sanan suka dawo ďaki.
Su Nawaf suka shiga yimata sannu, ahankali take amsawa, tahau gadon ta kwanta, momcy ta ce, "mas'ud ai inagama wanan ciwon na yasmeen baya bu'katar gwaji.
Mas'ud ya ce, "momcy saboda mi??, momcy tayi murmushi tana shafa kan yasmeen ahankali, ta ce, "mas'ud inaga lokaci yayi dazamuga yara suna tsalle2 agidan nan.
Nawaf da mas'ud suka kalli juna cikin zaro idanu.
Mas'ud yadaure ya ce, "dukda haka dai momcy barina dubata, saimuga maganin daya dace abata.
Momcy ta ce, "to zoka dubata, ta tashi takoma kusada Nawaf daya shiga cikin waswasi da faďuwar gaba, momcy tadafa shi ya ďago da sauri yana kallonta, saikuma yamaida da kai 'kasa da sauri, momcy tayi dariya tana faďin modebbo yaukuma kunyata akeji??, ai wanan abin farincikine.
Nawaf ya daure ya ce, "momcy bafa ciki garetaba, ciwone kaiwai nake gani.
Mas'ud ya katse musu hanzari da faďin bari naje nayi text daga nan asamo mata maganin daya dace.
Nawaf ya mi'ke yana faďin muje tare, momcy tabisu da kallo tana murmushi.
Suna fita mas'ud ya tuntsure da dariyar mugunta, Nawaf yabishi da kallon mamaki, kai wai lafiya?, ko ciwon haukane yasameka yanzunnan?.
Cikin dariya mas'ud ya ce, "mutumina aikaine lamarin naka yay kama da abin dariya, wai yaushe akaje wajenne??, har saka mako yafito?.
Nawaf ya yatsine fuska yana faďin ban ganeba?.
Mas'ud ya haďiye dariyarsa, ya dafa kafaďar Nawaf yana faďin abinda nake nufi ai afili yake malam.
Nawaf ya ta6e baki, kai nifa abinda kuke zargi daga kai har mom ba haka bane, babu wani ciki da yarinyarnan take dashi.
Mas'ud ya ce, "ban ganeba kai kana nufin yasmeen batada ciki, harara Nawaf ya sakarma mas'ud, to ana shan cikin aruwane dazakace wani baka ganeba, kainifa wlhy babu abinda yashiga tsakanina da yarinyarnan.
Taf ďijan inji mata, mas'ud yafaďa, to malam momcyfa jika suke so, dan nakula tana cikin farin ciki, amma gsky wannan ba dabara bace, idan kai zaka iya jurewa ai ita kana shiga ha'k'kinta ko??.
Tsaki Nawaf yayi, yana faďin matsalarta ce, nibabu wani ha'k'kinta dake kaina malam kaji.
Dariya mas'ud yayi, humm Nawaf kenan, akwai lokacin dazai zo, kazo neman shawarar hakan agurina, kuma wlhy tanada ha'k'ki a wajenka, kaima kasani sairai, saidai katake sanin,.
Hhhhhh ashe shekarun dayawa kuwa, Nawaf yafaďa.
Dahakadai suka 'karasa asibitin, bayan sunyi duk abinda yadace suka dawo gida da magunguna, amma dai text yanuna ba ciki bane.
Koda suka gayama momcy saitace, babu komai shima cikin yana zuwa insha ALLAHU.
tunda yasmeen tasha magani take barci,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login