Showing 12001 words to 15000 words out of 74786 words

Chapter 5 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

350

ta kwace takardar tafara karan tawa kowa yanaji.

Assalamu alaika babban yaro!!
lallai kacika dak'ik'i mara tunani, kodayake ALLAH ne ya kwaci yarinyar kirki daga hannun fasik'i, wanda bai d'auki sab'on ALLAH komaiba.
Na taya yasmeen murnar barin hannunka.
Faisal ban rama kashi goma daga cikin abinda ka aikata minba, 😭kaine kayi sanadin lalacewar 'yar uwata, ka lalata mata rayuwa ka koya mata fasik'anci, ALLAH ya isa tsakanina dakai faisal.
Kuma yasmeen ba karuwa bace, ita tsarkakrkiyace, kamilar mace, dama kun tursasatane itada mahaifanta akan ta aureka.
To yanzu ALLAH ya bata miji nagari, mai k'yawawan halaye, d'an babban gida.
Amma naso ace nine na auri yasmeen, kodan zuciyarka tabuga, sakari shasha.
Sako daga abokinka mai sonka da k'aunarka
HISHAM AHMAD KT! !!!!!!!!!!!.
Talek'o ta koma😆😆😜😜.

Gaba d'aya dangi suka d'auki sallalami, tareda ALLAH wadai da halin faisal.
Wasuma ALLAH yakara suke cewa.
Faisal kam sulalewa yayi a k'asa saboda bak'in ciki, dahanzari suka yayeshi zuwa asibiti.................✍🏻

Lallaikam yau anayin rikita2 a Najeria😜





💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞

©2016
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻15

....A asibiti kam al'amura sun dai2ta a b'angaren yasmeen, ansaka mata k'arin ruwa tanata barcinta.
Sai yamma lik'is ta farka, dak'ar tasha tee aka bata magunguna, takai dubanta ga Abba dake tsaye jingine da bango, saitaga har yad'an rame, ya ce, "mamana sannu kinji!.
Kai ta d'aga tana hawaye, umma tashiga sharemata hawayen tana rarrashi, yaseer yazo yazauna kusada ita, shikanshi duk yayi wani iri, cikin sanyin murya ya ce, "kiyi hak'uri aunty kibar kuka, na tabbata hakan alkairine agaremu, tunda ALLAH ya ku'btar dake daga hannun wannan d'an iskan!.
Yasmeen ta share hawaye, ta ce, "yaseer gskyarka, na! kub'ta daga hannun faisal, saidai bansan hannun wa? kuma na fad'aba, ta'kare maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.
Abba yakaraso ya zauna d'ayan gefenta, hannunta yakamo yarik'e, yay d'an murmushin dauriya, karki damu mamana insha ALLAHU mijinki na yanzu mutumin kirkine, kuma nasan zakiyi alfahari dashi watarana.
Duk da nima banganshiba, amma yanayin mahaifinsa da kamalarsa yanuna d'an nasama mutumin kirkine, kiyiwa mijinki 'kya'ky'kyawan zato kinji!!.
Yasmeen tad'aga kai tana share hawaye, ahaka likita yashigo ya samesu, ya k'ara duba jikinta, yaga komai normal, babu 'bata lokaci ya sallameta, suka tattara suka nufi guda.
Wannan kenan.

A'bangaren Nawaf kuwa yana cikin damuwa shima, shikam dayasan abinda zai tarar kenan a Najeria dabazaiyi fatan zuwaba, yafitar da huci mai zafin gaske daga bakinsa tareda cije le'bensa na kasa.
Talatu taiyi sallam a 'kofar d'aki, banza yay mata bai amsaba bare yabata ixinin shigowa, takai minti biyar atsaye, jin ba'a amsataba yasa tadannakai cikin d'akin atunaninta baya nan.
Saida gabanta yafad'i yayin datayi tozali dashi azaune, jikinta yana 'bari ta ajiye abinda takawo masa, ta rissina tana gaisheshi!.
Maimakon ya amsa mata saiyaja tsaki tareda watsa mata harara, dasauri tatashi tafito tana rawar jiki.
Kafa yasa ya ture kular, ALLAH yasama abincin bai zubeba, wayarsa tafara neman agaji, kallo d'aya yaymata ya d'auke kai, takatse aka sake kira, nanma yay burus, shikuwa maikiran sarkin naci saiya cigaba da kira.
A'kufule Nawaf yad'auki wayar , amma yayi shiru ya'kiyin magana.
Daga can akace modeebbo wai sai yaushe zaka shigo?, karka manta munyi dakai! zakataho yau da 'karfe 4, amma gashi har 5 tayi.
Nawaf yaja siririn tsaki, ya ce, "saika bari kaga gari ya waye banzoba sannan kayimin 'korafi.
Daga can akace to shikenan, amma yakamata kayi 'ko'kari kasandai kanada matu'kar muhimmanci a wasannan!!.
Banza Nawaf yay masa, saima ya kashe wayar gabad'aya, yana bala'i, kabi ka isheni da surutun tsiya, bakusan abinda yadamu mutumba zaka wani dameni da kira, ku damuwarku kawai kuka sani, yaja tsaki tareda kwanciya ya lumshe idanu.
Ahaka mas'ud yashigo ya sameshi, yad'an girgiza kai ta reda ta'ba Nawaf.
Ahankali ya bud'e idanu yana kallon mas'ud.
Mas'ud ya ce, "haba bro's yanaga baka shiryaba ne, kasanfa ka makara ma.
Nawaf ya yatsine fuska yana yima mas'ud kallon gefe, har ya bud'e baki zaiyi magana saikuma yayi shiru.
Azuciyar mas'ud ya ce, "yau kuma miskilancin ya motsa kenan?, ganin Nawaf ba amsa zai bashiba yasa yanufi bedroom d'insa, kaya ya had'àma Nawaf tsaf sannan ya fito.
Kan hannun kujerar da Nawaf yake kwance yazauna, cikin sigar lallashi ya ce, "kayi ha'kuri my bro's, ka d'auki hakan amtsayi 'kaddararka, kasan kanada matu'kar muhimmanci a wajen wasannan.
Inaso kacire duk wata damuwa ka ajiyeta gefe, ka kar'bi 'kautar da ALLAH yabaka, aure alkairine, kuma nasan wataran zakayi alfahari dashi, idan papa yaga kana cikin damuwa zai d'auka bakabi umarninsaba, ka daure ka kauda komai kaji!!.
Nawaf ya d'ago manyan idanunsa dasukayi jajir ya ce, "mas'ud ina cikin damuwa wlhy, karka manta aurefa papa ya d'auramini batareda nasan yarinyarba, bansan halintaba batasan nawaba, bata sanniba.
yo wai tayayama zamu kasance amatsayin ma aurata?, kokad'an banida niyyar yin aure yanzu kaima kasani, amma papa ya kama 'ka'kaba mini, wlhy idan zaka kasheni bansan yanda zan zauna da macebama ni!!.
Murmushi mas'ud yayi, kaga d'an uwa kwantar da hankalinka, indai yanda zaka zauna da itane damuwarka to zan koya maka, yafad'a cikin tsokana.
Harara Nawaf yasakar masa, aii kaga matsalarka kai bakomai kake d'uka serious ba.
Mas'ud yay dariya kaiwai batareda ya ce, "komaiba.
Nawaf ya mi'ke yanufi bedroom d'insa, bayi ya shiga yasakarma kansa tsawa🚿, (nakula indai yana cikin damuwa yanaso yasakarma kansa ruwa🚿, komiye sirrin hakan??. ) yakai tsawon minti goma ahaka, daga baya yay wankan sosai yafito.
Yaudai ba'ayi wani gayuba sosai, danko sumarsa mai gyaraba yafito, amma yayi 'kyau ba laifi.
Mas'ud dake zaune yana cin abinci ya ce, "yauwa kokaifa, yanzu sauranka abinci, kaci saimu wuce.
Yatsine fuska yayi tamkar wata mace, ya ce, "babu wani abinci dazanci malam, dan konaci bazaiyi amfani ajikina ba.
Mas'ud ya ce, dadai kadaure kaci.
Hanyar waje yanufa yana fad'in kasameni a wajensu momcy.
Mas'ud yay murmushi, wataran yakan rasa Nawaf wane irin mutumne?, yasan duk duniya babu wanda yakaisa sanin halin Nawaf bayan iya yensa, amma shi kansa wata sa'in lamarinsa yana d'aure masa kai, mutimne miskili, masifaffe, saidai bayason yawan hayaniya, ba kowa yake ganin dariyarsaba, bakuma harkar kowa yake shigaba, wannan yasa wasu suke masa kallon mutum mai wula'kanci kuma ba haka bane.
Saika zauna dashi zakaga yanada su'kin kai da son mutane.

Nawaf yana zaune gaban papa sunata yimasa nasiha shida momcy.
Papa ya ce, "yau dadaddare zamuje nida Alhaji khasim gidansu matar taka, abinda shawara tabayar zakaji a waya, saimuji lokacin daya dace ayi biki, kaima yakamata ace kaje kafin kawuce.
Nawaf yad'ago da sauri, ya ce, "papa ayimin afuwa saina dawo, wlhy na makara sosai saikirana koc d'in yakeyi tun d'azu, amma nayi al'kawari idan nadawo zanje.
To shikenan papa yafad'a, ALLAH yabaku nasara, amma zan kar'bi number ta na turo maka, dan kakirata ku gaisa.
To kawai Nawaf yafad'a.
Sun masa nasiha sosai, sannan suka tafi shida Mas'ud da Abdallah da Anwar, dan suma zasuje su kalli wasa.
Tunda suka tafi Nawaf ya jingina da kujera ya lumshe idanu, shi kad'ai yasan damuwar dayake ciki.
Mas'ud dasu Anwar ne kawai suketa hirarsu.
A kaduna suka tsaya sukayi sallar magriba da isha'i, dan gudu sosai mas'ud yakeyi ahanya.
Karfe 8:30pm suka isa cikin birnin abuja, mas'ud ya ce, "bari mufara kaika sanna mu nemi masauki ko??.
Nawaf ya ce, "A'a kumuje ku fara neman masukin sannan.
Hotel suka nufa, suka kama d'aki biyu, Abdallah da Anwar d'aya, mas'ud d'aya, bayan sun kammala komai suka d'auki Nawaf zuwa (trening cam)masukin 'yan wasa.
Tunda suka shigo get d'in ake d'aga musu hannu, sauran 'yan wasa sukazo suka tarbesa sunamai farincikin ganinsa, shima dai dole ya daure ya kauda damuwarsa zuwa gefe yana amsa musu gaisuwarsu.
Bayan komai yalafa su mas'ud suka nufi masaukinsu, sukabar Nawaf cikin takwarorinsa 'yan wasa.


FAISAL
faisal kam yanacan likitoci sun rufu akansa, hajiya jummai sai kuka takeyi, bata son tilon d'anta ya ku'bce mata, shikad'ai ta mallaka a duniya batada kamarsa.
Alhaji buba kuwa sai safa da marwa yakeyi, yakasa zune yakasa tsaye.
Haka dangi sunyi jugum jugum, taron biki yazama taron jimami, dayanzu anacan ana cashewa, amma ango yaja musu zaman tagumi a asibiti.
To shimadai likitoci sunyi nasarar farfad'o dashi, amma anhana kowa shiga wajensa, dan ba'aso ayi masa hayaniya..................✍🏻






💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞

©2016
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻16

.....da daddare su papa suka isa gidansu yasmeen, tarba akayimusu ta mutinci, har cikin falon abba aka kaisu, aka kawo musu ruwa da abinda ya sauwa'ka, bayan an gama gaishe2 suka shiga tattauna abinda ya kawosu.
Alhaji khasim ya ce, "munzone muyi muku godiya da 'kyautar dakuka bamu batarda kunsan ko su waye muba, ALLAH ya d'orar da wannan zuminci yakuma basu zaman lafiya.
Abba ya ce, "ai mune da gidiya, domin kun kauda mana wata damuwa dataso ruguzamu alokaci d"aya, mungode ALLAH ya'kara dan'kon zumunci.
Gaba d'aya aka amsa da amin.
Anan abba yabadua cikakken tarinsa, bai 'boye musu komaiba, har baro garin kwangwalan dasukayi.
Suma sun bashi nasu tarihin batareda sun 'boye komaiba.
Daganan suka tattauna akan biki sainan da 'karshen shekara zuwa sannan yasmeen takammala NCE d'inta.
Abba yaje yakira yasmeen da yaseer sukazo suka gaisheda su, abba ya ce, "ga d'iyar takunan, papa ya ce, "d'iyata zonan kusadani!, akunyace yasmeen taje kusada 'kafafunsa ta tsugunna.
Papa ya ce, "masha ALLAHU, ALLAH yaymuku albarka kinji, yasaukar da alkairi akan wannan had'in namu.
Suka ce, "amin.
Nanadai akayi mata nasihohi, akan takula dakanta, tasan yanzu ita matar aurece akwai banbaci tsakanin da, da yanzu.
Papa ya kar'bi number d'inta, yabata ta Nawaf da tashi da momcy da mas'ud da Abdallah da Anwar, yay mata bayani akan matsayinsu, ya ce, "kuma ta saurari kiran kowannanensu.
Sukai mata alkairi sannan suka tafi, suna mai yabon zuri'ar yasmeen.
Lallai sun yaba da tarbiyyar muta nen gidan.

Tunda suka tafi yasmeen tayi shiru tana tunani, indai yanda iyayen mijin nata suke haka mijin yake lalai ta more, dan taga dattako da kamala a tattare da iyayensa.
To hakama abba da umma sunyi farinciki da samun suriki nagari.
Yaseer ya ce, "gsky aunty kin more, ALLAH yasa haka mijinki yake 'kya'ky'kawa kamar abbansa.
Yasmeen ta harareshi, kaifa nakula bakada kai wlhy, ni tashi kabani guri kazo ka cikani da surutu.
Yaseer yay dariya, sisto plz ki kirashi mana tunda naga an baki number d'insa.
Caja d'in wayarta ta d'akko tana fad'in kasan ALLAH idan baka tashiba zan zula maka ajiki.
Yaseer yatashi yana fad'in A'a wlhy bara natashi, idan kika zulamin wanga caja ai sainayi jinya.

FAISAL
Alhmdllh jikin faisal yana sau'ki, saidai uban sambatu dayake zubama mutane, babu abinda yake kira sai sunan yasmeen, shi sai yanzuma yasan yana sonta, yawan surutun dayakeyine yasa ake masa allurar barci.
Da mutum yazo dubashi zaifara ro'konsa ya kawo masa yasmeen, dan ALLAH karsu bari ya rasata, wlhy yana sonta, dan ALLAH aje asaka wanda ya auri yasmeen ya sakar masa ita, shikad'aine ya dace ya zauna daita.
Hajiya jummai ta matse hawaye tana fad'in Faisal ina saura, kayima kanka aii, nasan babu wani namiji dazai auri yarinya kamar yasmeen ya saketa, duk abinda namiji yake bu'kata awajen mace yasmeen ta had'asu, Tarbiya, ilimi, addini, nasaba, 'kyau.
Duk ta had'a.
Danhaka ka d'auki 'kaddara kawai Faisal.
Faisal ya 'kan'kame Hajiya jummai yana kuka, da sakin sambatun daya saba.
Dole likita yazo yay masa allurar barci, sanna.
Azuciyata na ce, "aii dama duk wanda ya taka rawar💃wani, yarasa filin taka tasa.


ABUJA. 6/7/2012
8:30PM
Abuja international stadium cike take da'kam da matasa maza da mata, kai harda yara da dattijai na 'kasashe daban2, dake Nahiyar Africa, harma da 'kasashen turai, domin kallon (Netion cup ).
Yau Najeria da ghana zasu buga, babu abinda kakeji sai hayaniya irinta al'adar kwallo.
Su Nawaf suka shigo cikin fili suna d'agama jama'a hannu, yayinda suma jama'ar suke d'agamusu hannu saboda 'kauna ko birgesu da 'yan wasan sukeyi.
Bayan addu'a da taken Najeria da 'yan wasa suka gabatar, suma 'yan wasan ghan sunyi nasu.
Sai aka fara 'ko'karin fara wasa, wasa kowannen su yakeyi cikin 'kwarewa.
Can na hango Nawaf sanye da JC mai ruwan tutar Najeria, sunyimasa 'kyau matu'ka, saidai fuskarsa babu walwala, dan buga kwallon yake kamar bayaso⚽🚶🏼.
Gab daza'a tafi hutun rabin lokaci ghana tasmu nasarar zira kwallo 1, nanfa mutanen ghana suka hau ihu da sowa.
And'an fara wasa aka hura, domin tafiya hutun rabin lokaci, saidai 'yan Najeria sun d'an fara shiga damuwa.
Dan haka koc d'in Najeria yaja Nawaf gefe, yana tambayarsa ko bashida lfy ne??.
Nawaf ya ce, "lfyr sa 'kalao.
Nan dai koc yashiga ro'konsu akan su dage, karyazama tun a kolfayin(colfine) su nuna gazawarsu.
Bayan andawo hutun rabin lokaci, aka d'ora wasa, nanma dai ghana sunfi nuna 'kwazo akan Najeria.
Kad'an ya hana Ghana cin kwallo ta biyu.
To daga nanne fa Nawaf ya dage, minti 15 da dawowarsu ya zira kwallo a raga, karkaso kaga murna wajen 'yan Najeria.

Zan iya cemuku harda Yaseer da yasmeen amasu murna, dukda basosai yasmeen take kallon wasanba, amma dayake suna tare afalo itada yaseer sai take d'an kallo.
Ammafa har yanzu batasan Nawaf shine mijin nataba.
Abba yafito yana fad'an ihun da yaseer ya kwala musu.
Yaseer ya ce, "abba kayi ha'kuri wlhy modeebbo ne yaci mana kwallo.
Abba ya ce, "to basai ayi murnar ahankaliba, amma irin wannan ihu haka.
⚽kwallo taci gaba da tafiya yanda ya kamata, dan yanzu Najeria sun dage, suma ghana sun dage, dan haka wasan ya d'auki zafi kowa yana so yazira kwallo tabiyu.
Saura minti 4 atashi Najeria takuma zura kwallo da taimakon Nawaf wani d'an kwallon Najeria ya zura, woyyo ALLAH karkuso kuga murna, koda yake kuma masu karatu na hangoku kuna murna.
Daganan najeria tafara jan 'kafa domin acinye lokacin abanza, aka 'kara minti7, shima dai ashiririta aka cinyeshi, Najeria sai fitar da kwallo suke, suna langyare, harda tsayawa akayi canjin 'yan wasa.
Ahaka dai aka tashi 2-1
Najeria-2 & ghana-1

Wasa yayi 'kyau Najeria sai murna sukeyi.
Yaseer ya ce, "sisto dan ALLAH yakiga gay d'innan, jiba kiga yanda yake gara kwallo cikin kwarewa.
Yasmeen tad'an ta'be baki, kaini wannan mugun baya wani birgeni, kai yake burgewa.
Yaseer ya ce, "sisto muguntar mi yay miki??.
Sai asannan ta tuna yaseer bai san komai daya faru tsaka ninta da Nawaf bafa.
Ta ce, "sai yayimin wani abu zan kirashi mugu, kaga saida safe ni nagaji.
Yaseer ya murgud'a mata baki ya mi'ke shima ya shige d'akinsa.................✍🏻







©2016


💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞



Page👉🏻17

......Yasmeen zaune ta rabga uban tagumi, gaba d'aya tayi kewar school, tanaso takoma makaranta amma batasan yanda zata fiskanci abba da zancrnba, ta fesar da huci mai zafi tareda dafe kanta datakeji yana sara mata.
Waya tajawo ta kira yaseer, kana ina?, naji tafad'a, bansan miya cemataba daga can nagadai ta ajiye wayar kawai.
Babu dad'ewa yaseer yashigo da sallama, ta amsa batareda ta tashi daga kwanciyar datayiba, ya zauna abakin gadon yana fad'in gani auntyna!.
Yasmeen ta ce, "yaseer shawara nakeso miyi.
To wace irin shwara kenan?, yaseer sonake na koma makaranta amma ina tsoron tambayar abba!, ya kake gani za'a ayine??.
Shiru yaseer yayi yana 🤔nazarin mafita, zuwa can ya ce, "ai inaga kibari kawai nafara yimasa magana saimuji amsar dazai bayar koya kika gani?.
Eh yayi kakawo shawara mai 'kyau d'an uwa, yasmeen ta juya tana kallon wayarta datake wringing saidai batasan number d'in ba.
Jiki a sanyaye ta d'auka saidai tayi shiru.
Daga can akace salamu aliki!.
Wa'alaikassalam yasmeen ta amasa.
Amaryarmu ykk??, ta ce, "lfy lao, ta d'ora da fad'in dan ALLAH wanene??.
Mas'ud yay sasanyar dariya, ya ce, "sunana mas'ud khasim, d'an uwan mijinki kuma abokinsa.
ta ce, "ALLAH sarki, sannu!.
Ya ce, "yauwa kema sannunki amarya, dama zan fad'a mikine ki saurari zuwanmu yau da yamma.
Muryar yasmeen na rawa ta ce, "saina ganku.
Ya ce, "to nagode, sai anjima.
Yaseer daya tsura mata idanu tun d'azu ya ce, "sisto keda wa??, ta had'iye wani yawu sannan ta ce, "wanine wai mas'ud!.
Mas'ud kuma?, yaseer ya maimaita sunan, ya ce, "sisto kodai abokin mijinki da aka baki number shi jiya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login