Showing 66001 words to 69000 words out of 74786 words

Chapter 23 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

365

mas'ud.
Duk suna falo zaune ameena tana 'kasa ta baje 'kafafu dan cikinta yayi girma ankusa juyo mana baby, mas'ud kuma yana zaune kusada ita yana matsa mata 'kafafunta dasukaďanyi fushi,, cikin tsokana yasmeen tashigo tana faďin mai ciki uhum ganinan tafe, Nawaf da mas'ud suka tuntutsure da dariya yayinda ameena take hararar yasmeen,, habawa yarinya kema aigashinan ajikinki kwana nawane maye yaci amarya.
Yasmeen tazauna tana faďin sannu mayya, inba mayyaba wazai hango kanada ciki??, Ameena ta ce, "ai alamomi sun fallasaki, yasmeen tabi jikinta da kallo tana ta6e baki ke 'yar fata 'kyayi ki barni, mudai kiyi maza ki juyo mana babynmu ko ya ya habibina?, Nawaf ya ce, "gsky ki fancy face.
Mas'ud da Ameena suka kalli juna suna murmushi, harsuna haďa baki wajen faďin tofa haka akayi??, Nawaf ya ce, "haka akayi mi??, A'a basai mun faďaba Alhaji abar kaza cikin gashinta.
Nawaf yay dariya kajidashi dai magulmaci, A'a bro's aikaine babban magulmacin kaida kace..........koda yakedai bari nayi shiru kawai,, A'a kafaďa karta kasheka mana,, A'a arufe rufau kawai.
Sukai dariya gaba ďaya sannan suka gaisa da tambayar Ameena ya jiki??, ta ce, "Alhmdllh, ai nakusa barwa matarka, Nawaf yakalli yasmeen to ALLAH yakaimu lokacin, sukace ameen.
Ameena ta ce, "dan ALLAH yasmeen ki ďakko muku abinsha mana,, yasmeen ta ce, "oni kazo ba'kunta asaka aiki, mas'ud ya ce, "ba babyn ku bane yaja mana, duk yabi yahanamu mu shana ko my honey??, Ameena ta ce, "wlhy kuwa gsky ka.
Nawaf yay dariya toku juyo mana abinmu mana, basaikuje kuyita shanawarkuba, aii muna gab kuwa mas'ud yafaďa yana kunna tv.
Yasmeen tadawo da abinsha, nan suka zauna sunata hira da tsokanar juna, daga baya ameena taja yasmeen ďaki, Nawaf ya ce, "o, mata kun iya gulma, kudai baza'a ta6a zama daku waje ďayaba.
Yasmeen tajuyo tayi masa gwalo, ya ce, "niko?, tashige tana faďin eh,, okey zan kamaki aii yarinya, zaki banbantamin.
Mas'ud yay dariya wai mutumina yaushe aka koma haka?, Nawaf ya ce, "kamar yaya??, harararsa mas'ud yayi kaifa ka iya waskewa wlhy, Nawaf yay dariya yana shafa kai, yashiga bama mas'ud labari, sunayi suna dariya da tafawa.
Aďakima aminai biyu sun 'kulle sunata hira akan abinda yashafesu, yasmeen ta ce, "yauwa ameena yamaganar kayan dakikai min kwanaki??.
Ameena ta tuntsure da dariya 'yammata keda kikace bazaki nemaba??, yasmeen ta ce, "hum kibari kawai fitinar Nawaf dole saina shirya mata, plz kidaina mini dariya mana, ameena ta tsagaita da dariya, to nabari sistona yanzu abinda za'ayi littafin zan baki kawai kiringa haďawa da kanki, danni nafi gane nahaďa abu dakaina, bawai da ankawo nahau shaba alhalin bansan daga inda yakeba.
Hakane amma suna cutarwane??, kai, eh mana, akwai masu cutarwa, wasufa bakasan inda aka haďasuba, kinga kuwa ai za'a iya samun matsala.
Gskyar ki, to amma aina zan samu kayan haďin idan kin bani littafin?, babu damuwa yawanci kayan itatuwane, barema ALLAH yabaki miji mayen kayan marmari, zakiringa samu koda yaushe, sukansu kayan marmarin idan kinasha komai zai zama dai2 kuma zam2, okey to shikenan kibama hanan takawomin littafin dan yanzu babu damar nace zan tafi dashi.
Ameena tayi dariya kina tsoron boss yagani kenan???, hhhh babu wani tsoro ina kare martabatane kawai, suka tafa suna dariya.
Sai bayan isha'i suka koma gidansu, a 6angarensu momcy suka yada zango, saida akasha hira sannan suka wuce 6angarensu, Nawaf yafaďa saman gado yana faďin wash ALLAH na nagaji my xarah.
Yasmeen ta ce, "to yakakeso ayine??, ya ce, "amin wanka dan ALLAH yafaďa cikin shagwa6a, yasmeen ta zauna kusadashi tajawo kansa taďora saman cinyarta, ta ce, "kafa girma habibina amma kake shagwa6a,, ya kamo hannunta yasumbata yana murmushi, fancy face gara nayi kafin yara su zo su kwace mini fadata.
Yasmeen ta du'ko ta sumbaci goshinsa, suka tsurama juna idanu cikin murya mai cikeda so da 'kauna ta ce, "bazasu kwace maka fadaba, dan kaina fara sani kafinsu,, yarungumeta kansa yacusa jikin cikinta, to shikenan fancy face ALLAH yakawo masu albarka, ina addu'ar kafin mu tafi Spain kin kamu.
Yasmeen ta zaro ido waje, kai habibina nifa bazan bikaba ina nan tareda su momcy.
da sauri yatashi zaune yana kallonta, yakamo hannunta, kina nufin zaki barni natafi ni kaďai, xarah??, danayi ha'kurin rashinki akusa dani amma fa yanzu bazan iyaba wlhy, ina kikeson naringa kai matsalolina, ko kinaso mijinki yafara aikata abinda baiyiba yana saurayi??, plz & plz karki bari su momcy suji wannan maganar, wlhy zasu goya miki bayane.
Ya jawota jikinsa cikin taushin murya yafirta ina sonki dayawa fateema, amma ke naga kamar har yanzu baki amintaba, kokuwa ba'kya sona.............da sauri yasmeen ta rufe masa baki, plzzzzz karka faďa wlhy nima inasonka fiyema da yanda kake sona, nima bazan iya rayuwa babu kaiba kaji na rantse maka, da sauri ya rungumeta tsam suna fidda numfashi ahankali, saida zuciyoyinsu sukai sanyi sannan suka ďago suna kallon juna suna murmushi, tafara cire masa ma6allin rigarsa tana faďin tashi muje muyi wankan nafara jin barci.
Tare sukayi wankan sukai shirin barci sai gado, nima na tattaro inawa2 nayo gida.

Haka rayuwa taci gaba da gudu da sauri, komai yana tafiya yanda akeso, su Nawaf suna shan soyayya, koda yaushe suna manne da juna idonsu yarufe gaban kowa soyewa sukeyi, suna 'kyautatawa juna, kowa burinsa yafarantawa ďan uwansa rai.
Yasmeen takan shirya musu girki mai daďi da gamsarwa, suci susha abinsu, tana ma mijinta biyayya duk abinda ya bu'kata tana masa cikin hanzari babu nuna fushi bare ta ce, "tagaji,, aduk lokacin dayazo mata da bu'katarsa takanyi 'ko'karin taimaka masa dan yasamu nutsuwa, kullum sukan kasance cikin farinciki da 'kaunar juna.
Shima Nawaf baya ba'kin cikin 'kyautata mata da 'karfinsa da lokacinsa aljihunsa dakuma farincikinsa,, nakula aurene mai cike da farinciki da 'kaunar juna.
A yaune kuma Ameena ta haihu ďiyarta mace, su yasmeen ana cikin farinciki, kamar su suka haihu, kullum tana gidan suna kar6ar barka sune amarori 'kirjin biki😜.
Kullum a can take wuni, sai dare take dawowa gida, yau kam agajiye tadawo gida Nawaf yana kichin yana haďa shayi, tashigo da sallama ta faďa saman kujera tana kiran wash ALLAH na, Nawaf yafito daga kichin hannunsa ďauke da kofin shayi ya ce, oyoyo my xarah kin dawo??, taďago ido agajiye tana kallonsa ta ce, "eh ammafa yau nagaji dayawa, ya'karaso ya zauna kusada ita, kofin shayin ya ajiye saman tabir ďin gabansu, ya rungumota zuwa jikinsa ayya sorry my dear karki damu ai hidimar babyn muce, ta shafa kirjinsa tana murmushi hakane my handsome.
Shima yay murmushi, nima kwana biyunnan duk an barni cikin kaďaici, ga bu'katun sunyi mini yawa, kullum aka dawo sai ace angaji, yasmeen tayi dariya haba habibi yanzufa kagama faďar cewa hidimar babyn muce.
Ya marairaice murya hakane fancy face, amma itama babynmu tana bu'katar sabon 'kani, atausaya mini plzzzzzz, yasmeen ta murmusa tana masa gwalo, ya ce, "niko??.
Ta ce, "eh tareda 'kokarin tashi, yay saurin matseta ajikinsa yana bata 'kayatattun sumba ako ina na sassan jikinta...................✍🏻




Kuyi hakuri yanzu ina typing kaďan, inada uzurine.
;luv u oll😘❤ kuna 'karamin karfin guywa ngd sosai.



.



©2017


💓bilyn Abdul💓
💓Mrs Abdus'salam💓
💓luv u oll my fan's😘💓
[1/12, 9:10 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💓




Page👉🏻55 & 56

.......A kwana atashi babu wuya gurin ubangiji, yaune sunan baby kuma taci sunan nana khadija, ubangiji ALLAH yaraya mana dukkan 'ya'yan da aka haifa ya albarkacesu.
Su yasmeen ansha shagali, kuma tanun bajinta itada habibinta, sunyima baby alkairi maiyawa harda iyeyen baby, mas'ud har yarasa bakin magana, yasan shida Nawaf sunruga sunzama 'yan uwa na jini, tamkar yanda mahaifansu suke tare, babu abinda suke iya 6oyema juna, ALLAH kuma ya dubesu ya azurtasu da mata 'kawen juna, masu kula dasu dason farincikinsu.
Nawaf yayi hidimar da ko mas'ud bayi rabintaba awajen shagalin sunan,, duk da yasan Nawaf yafishi samun kuďi, dan gsky 'yan kwallo suna samun kuďi sosai, to amma ba kowa bane zai bigi jiki yayi maka hidimar kuďi a irin wannan lokaci da kowa yaďauki rayuwa dagashi sai 'ya'yansa.
To mudai saimuce ALLAH ya sassaka da alkairi, yakuma maida kowa gida lafiya.
Bayan kwana biyu da gama suna suka shirya tafiya saudia, amma harda su momcy da kowa da kowa,, papa ne kawai sai sun kusa dawo zaije su dawo tare.
Nawaf dake kwance yana kallon yasmeen tana haďa musu kaya, ta ďakko manyan kaya wajen kala shidda zata zuba masa a akwatinsa,, ya ce, "fancy face waďan nan kayanfa, waye zai sakasu??, ta ce, "kai mana!!.
Yatashi zaune yana faďin tab fancy face kina gani anan ma basakawa nakeba sai papa yayi magana bare acan,, tacigaba da zuba kayan tana faďin nikam ina son naga kasaka manyan kaya ba 'karamin 'kyau suke makaba, abinda manyan kayan nakama marabarsu da 'kananun kaďan ne, tunda ďinkunan sun cika fitat kamar wani mace.
Ya koma ya kwanta yana dariya, toni ahakamma ina sakawane kawai dan suna takurani wlhy,, hummm zamani yazo damuka ďauki Al'adar wasu muka yafama kammu, bayan kowa yasan kayan yarensa sunfiyimasa 'kyau.
to nidai yanzu ni akema faďa kenan?, tokiyi ha'kuri kwananna zan koma saka manyan kaya sosai tunda kina so kinji.
Yasmeen tayi murmushi aiko danafi kowa jin daďi, dan wlhy manyan kaya suna maka bala'in 'kyau, saidaifa kaine kake haskasu, ta'kare maganar da ďaga gira.
Ya saki wani lallausan murmushi kina cikin aikina fancy face,, kinrigada kin gama mallakeni, nakula kofa aure na 'kara amarya baxata samu farincikina sosaiba.
Dan danan yasmeen ta canja fuska, tamkar zata fasa ihu,, tabama Nawaf dariya amma saiya daure ya gimtse, ya ce, "yayadai naga kin 6ata rai, shiru tayi masa tana rufe akwatinsa dan tagama haďa kayan, ta saukeshi 'kasa tana hawaye,, Nawaf ya mi'ke ya sakko dan yasan shirun datayi ta sha'kane.
Rungumota yayi tabaya dan ta juya masa baya, ya le'ko fuskarta saiyaga hawaye share2, cak ya ďauketa zuwa gado, ya kwantar da ita, shima yana gefenta,, yasa hannu yana share mata hawayen cikin kunnenta ya ce, "kinga nifa da wasa nake miki, plz kidaina bari hawaye suna 6ata mini 'kya'ky'kyawar fuskarnan tawa ni kaďai,, ta harareshi tana faďin maza ai dama kun iya daďin baki.
Ya ce, "woow!! Ni na isa nayima fancy face ďina daďin baki, wlhy iya gsky ta nake gaya miki, kina kula dani, duk sanda nazo da bu'katata kina 'ko'karin biya mini, kina sakani farinciki, ba'kya barina da yunwa,, to idan na 'karo aure ita kuma mixata min??, bayan my xarah tana yimini komai,, ya sumbaci bakinta sorry dear kimin murmushi mana kozanji daďi.
Yasmeen ta sake hararar sa, saiya rungumeta yana dariya, kinga bari na canja hanyar lallashin tunda sunada yawa, da sauri ta ce, "nikam naha'kura habibina,, yaďago fuskarta suna kallon juna ya ce, "ban yardaba,, ta ce, "to mizan maka ka yarda na ha'kura,, ya lashe la66ansa, tayi murmushi dan tasan abinda yake nufi, ta ce, "to rufe idonka, yarufe yana faďin sarkin kunya.
Saida ta 'karema 'kya'ky'kyawar fuskarsa kallo, sannan takai bakinta kan nasa, wasu zafafan kissis take bashi, wanda shi kansa baisan zata iyaba, dan tamaso tafishi shi dayake malamin nata, da'kyar ta janye bakinta ta tashi tana dariya 'kasa2, dan ganin yanda jikinsa yay lakwas.
Shikuma sai binta yake da idanunsa dasukayi jaa, gaba ďaya jikinsa yayi laushi, cikin dariya ta ce, "yakamata mutafi fa tunda kace bazaka barni na wuni acanba,, ALLAH inata zumuďin son ganin umma da abba da yaseer.
Nawaf ya lumshe idanu tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ahankali ya furta to zokiji wani abu mana,, ta ce, "tab aina gane wayonka Alhaji, katashi kawai kayi wanka mu wuce kaga ni tunďazu nayi nawa,, yaďan cije le6e yana murmushin mugunta, ya ce, "to zomiyi wata shawara,, yanda yaďan haďe rai saita ďauka shawarar gsky ce, tanufi bakin gado ta zauna, ya ce, "karaso mana, A'a daga nanma ya isa..... kafin ta rufe baki yayi ciki da ita, na ce, "sai anjimanku,, dan naga soyayya za'a sha..

Ina zaune a waje suka fito Nawaf cikin manyan kaya hardasu hula, yasmeen kuma ta saka atamfa zani da riga ta ďora farin gyale, sunyi 'kyau sunata zabga 'kamshi abinsu, bayan sunyima su momcy sallama suka fito hardasu Abdallah za'aje, itada shi suna gaba su Abdallah suna baya.
Yana cikin tu'ki saiya kamo hannunta, da sauri ta janye, yaďan kalleta, da ido ta nuna masa su Anwar,, ya ďan murmusa yana maida kansa saman titi, babu daďewa suka isa gidan.
Da gudu yasmeen ta shige, da umma ta fara karo, tako rungumeta tana tsallen murna, umma ta ce, "ohni yasmeen wai sai yaushe hankali zai zomikine??, ta saketa tana turo baki gaba kai umma murnar ganinkufa nakeyi!!, to sannu da zuwa, yana ganki ke kaďai bayan kince tare kuke da mijin naki, lah umma suna 'kofar gida hardasu Anwar ma.
Oh ni ALLAH ya shiryaki mamana shine kika barosu awaje, yaseer!!! umma ta kwala masa kira,, yafito da sauri yana amsawa, ganin yasmeen zaune saiya rungumeta suna murna,, umma ta ce, "kaje kashigo dasu Abdullahi........
Bai bari umma ta 'karasaba yayi waje da gudu, acanma rungume juna sukayi da Anwar dan sunzama abokai tuni, ya gaida Abdallah da Nawaf, Nawaf ya ce, "o, yaseer kaima kayi girma wannan tsawo haka, yanzu wanda bai saniba saiyace ka girmi fancy face ďina.
Dariya sukayi sosai yayinda yaseer yay musu jagora zuwa falon abba, yaja hannun Anwar suka fice,, dayake ansan da zuwansu an shirya musu abubuwan ciye2 afalon,, Abdallah ya hau cin abinsa dan dama abinci zaici Nawaf ya azalzalesa yafito.
Nawaf ya ce, "ALLAH ya shiryaka Abdallah kaidai acicine ko??, Abdallah yay murmushi abii wlhy yunwa nakeji, kumafa ni gidannan kamar gidanmu nake ďaukarsa, duk abindazan iya yi aginamu zan iyayi anan, munzama ďaya da ablah aii..
Nawaf yay murmushi danjin daďin maganar ďan 'kaninsa, ya ce, "hakane my dear bro's.
Babu daďewa abba yadawo yazauna sukasha hirarsu dayake mutumne mai sau'kin kai, ga son jama'a.
Umma maidai ta daure yau ta ajiye kunya ansha hira da ita,, yasmeen sai shagwa6a take zubama abba,, ya ce, "mamana har yanzu ba asan an girmaba ko??, ta shgwa6e fuska abba nafa daďe ban gankuba, kuma nasan yaseer yana nan yana ta6ara.
Yaseer ya ce, "oh kina kishi danine aunty??, to aii yanzu lokacinane, ninake shanawa.
Su Nawaf suka saka dariya, Anwar ya ce, "yaseer aii nima addu'a nake abii shima yayi aure abarni ni kaďai nasha shagwa6ata,, Abdallah ya hararesa ďan ba'kin ciki aiba yanzuba saina 'kara hutawa,, gaba ďaya suka saka dariya, duk sanda Nawaf da yasmeen suka haďa ido saiya ďaga mata gira, ita kuma tayi murmushi, hakadai sukasha hirarsu,, Nawaf ya ce, "yaseer yay 'ko'karin kar6o takardunsa zai nema musu makaranta shida Anwar a kasar Rasha, yaseer akaita murna da godiya, suma su umma sun masa godiya, suka ajiye musu alkairi maiyawa suka taho, yasmeen harda ďan kwallanta, tabama Nawaf tausayi,, amma sai ha'kuri duk macen duniya haka ta gada, bishiya agidanku, inuwa a gidan wasu.

Bayan sundawo gida sun gama duk abinda yake al'adar rayuwarsu suka kwanta dan dare mahuta bawa,, yasmeen tana kwance agefen hannun Nawaf ta ce, "shine zaka nemawa su yaseer makaranta amma ni ka lalata mini tawa ko??.
Yashafa kanta yana murmushi to kina kishi da yaseer kenan dgsk??, babu wani kishi, to miye inba kishiba??, ke aii kingama karatunki,, keda kike cikin babbar makaranta mai cike da aikin lada.
Ta 'kara gyara kwanciyar ta tareda rungumeshi, hakane habibina amma wlhy inason karatu sosai,, yajuyo ya rungumeta sosai karki damu my xarah zakicigaba da karatunki, harma saikince kin haji dan kanki, aikine kawai banyarda dashiba,, damun koma Spain zan nema miki makaranta.
Ta 'kan'kameshi sosai tana murna, ta ce, "wlhy ni dama bana karatu dan na samu aiki, inasondai kawai nazama mai ilimi,, saura karatun islamiyya, kai yaka mata kazama malamina mijina.
Yay murmushi waya gayamiki inada kwarewa anan?,, tab ai momcy tabani labainka tun kana yaro, da 'kiriniyar dakayi, ta ce, "min kai Anwar yagado shiyyasa ga yaronnan akwai ilimin addini, kumama kafishi,, dan haka kawai kabada kai..
Ya ce, "shikenan tunda momcy ta fallasa ni insha ALLAHU zamu fara karki damu.
Sunata 'yar hirarsu 'kasa2 har suka fara jin barci, sukayi addu'a suka lula duniyar barci.

Washe gari jirginsu ya ďaga zuwa 'kasa mai tsarki,, tarba akai musu ta mutunci, 'yan uwa cike da gida sunzo tararsu, aginda hajja tsohuwa mai ran 'karfe suka sauka, yasmeen sai ware ido take yau gata a saudia, kasar da aka haifi (mafificin halitta ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) (TSIRA DA AMINCI SU 'KARA TABBATA GA SHUGABAN TALIKAI, MAI CETONMU AWATA RANA MAI CIKE DA HARGITSI DA RUĎANI,, ALLAH yasa muna cikin waďanda zai ceta, ameeeeen.)
Lallai yasmeen ta yarda su momcy 'yan gatane, dan family nasu sunada kuďi da ala'ka mai 'karfi tsakaninsu da masarautar saudia,, abinci har rasa wanda zataci tayi, Nawaf sai dariya yake mata wai kartayi 'kauyanci,, itadai shiru tayi masa dan momcy da hajja suna kare mata,, bayan sunci sun 'koshi an gaggaisa da dangi, suka tafi dansu barsu su huta.
Abin yabama yasmeen mamaki dataga an haďasu ďaki ďaya da Nawaf, itakam gsky tanajin kunya,, takira Abdallah ta ce, "yaje yasanar da momcy dan ALLAH araba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login